Showing 282001 words to 285000 words out of 332834 words

Chapter 95 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65636

ne ya saka shi maida kudin aljihunsa yai masa addu'a ya fice. Kofar ya rufewa Talba ya kalli Aminatu sai ta sakar masa murmushi ta matsa kusa da shi ta kai hannunta tana taba jikinsa.
 
“Ya jikin?”
 
Ya hade fuska in a cool way.
 
“Ban sani, fushi nake kin ce baki yi mafarkina ba”
 
Sai tai murmushi ta kai hannayenta ta rika fuskarsa ta matse masa kumatun kamar zata kwance shi.
 
“To ban yi ba sai na yi karya”
 
“Da kin kwanta da tunani ai dole ne ki yi mafarki”
 
Ta yi murmushin daya kara ma fuskarta kyau.
 
“To zan yi gobe”
 
Ya mika hannunsa ya shafa hannayenta ya matso da fuskarta a kusa yana kissing din goshinta before ya hancinta sannan ya dire a bakinta, a hankali yana tsotsa soft lips dinta wanda hakan ya saka ta rufe tana shakar numfashinsa, rumgumota yai ya dawo da ita saman jikinsa yana kallon kwayar idonta dake rufe, wani irin zaki yake ji a lips dinta kamar an saka mata honey ga wani taushi da suke masa kamar mada, a hankali ya cire bakinsa sai ya goga mata lips dinsa saman nata ya rike hannunta yana murza yatsunta a hankali.  
 
“Sweet lips”
 
Ya furta da muryar da ita kadai zata iya jinsa, yana kallon lips din nata looking for more. Bude idon tai ta sauka daga saman jikinta.
 
“Ga breakfast dinka nan”
 
Wani irin kallonta yake kamar yau ya fara ganinta, har na Allah ba san adadin kaunar da yake yi ma Aminatu ba, idan tana kusa da shi yana jin kamar ya hadeyeta ta zauna a cikinsa, for him everything about her is perfect.
 
“Ke kin karya ne?”
 
Ya fada looking at her pretty face.
 
“Eh mun karya a can, wannan naka ne”
 
“Hada min”
 
Ya shiga zuba masa abincin kamar yadda ya bukata.
 
“Ka ce yau zaka hada ni da Ya Bashir ko?”
 
“Eh, amman sai anjima za a zo da shi”
 
“Toh”
 
Ta amsa tana murmushin jindadi cike da zakuwa.
 
 
 
 
LEILA POV.
 
Sai da ta ja kofar dakin, sai kuma ta dawo ta tsaya jikin kofar ta kara kunenta tana sauraren abun da Momy take fada ita da Mama Saratu. Sai da ta ji alamar Momy zata fito sannan ta daga jikin kofar ta sauko kasa da sauri ta nufi kitchen din dak falon. Mairo ta samu a tsaye tana wanke kayan da suka bata tana ganinta ta gaishe ta da sauri, sai ta daga mata kai alamar amsawa ba tare da ta amsa da bakin ba. Kofi ta sauka ta tara a tap din ta cika kofin ta shanye tana jin kamar numfashin da take baya wadatar da huhunta.
 
‘Miyasa Momy zata yarda a kashe Madina? Just because of wani ra'ayi na su na dabam? Idan aka kashe ta zai zama musu mafita? Shim asirinta zai rufu har abada? Ko kuma wata matsalar zata kara afkawa? Anya lokaci be yi da ya kamata ta karbi kaddara? Idan wacan kuskure ne yanzu kuma minene? Ganganci right? Ta dade tana mafarkin Baaba da kuma tunanin ita ma da akai akan kuskure kenan? Yanzu kuma idan a tai na ganganci fa? Miye makomarta? ’
 
Kiran da Momy tai mata ne ya katse mata tunanin da take ta juyo a firgice numfashinta har rawa yake.
 
“Na'am...”
 
“Baki tafi ba?”
 
“Ina?”
 
Ta tambaya tana jin kamar kamar wata bakuwa ce a kunnenta. Da mamaki Momy take kallonta.
 
“What are you thinking? Ba cewa na yi ki kaiwa Talba abincin a asibiti ba”
 
“Eh abincin na shigo dauka, Momy dan Allah kar mu sake aikata wani kuskuren”
 
Momy ta kalli Mairo ta kalleta da sauri tana dan zare mata ido alamar bata son su yi maganar a nan. Ita kanta Leila ta manta da Mairo na guri har sai da Momy tai mata ishara da ido.
 
“Je ki kai mishi abinci”
 
“Okay”
 
Ta fada sannan ta juya ta fice daga kitchen din ta nufi dinning, sai da ta dora hannunta kan kulolin sannan ta tuna da key din motarsa, hakan yasa ta dauke hannunta ta juya ta hau sama ta shiga dakinta ta dauko key din da wani karamin mayafi da wayarta ta fito, a hankali take saukowa har ta sauka downstairs ta nufi kulolin wannan karon bata tsaya jiran amsu aiki su kai mata mota ba, sai ta dauka da kanta tare da tray ta nufi kofar fita falon, a nan kam sai da ta aje kayan hannunta ta bude kofar sannan ta dauki abincin ta fice. A front seat ta saka sannan ta zagaya bangaren direba ta zauna tai ma motar key. Cikin mintunan da ba su fi ashirin ba ta isa asibitin, a gurin da aka tanada domin faka motoci ta faka motarta sannan ta bude ta fito ta dauki abinci ta shiga da shi ciki. Tana isa kofar dakin ta tura kofar ta shiga ba tare da tunanin komai ba, and she saw what she didn't expect, Aminatu na zauna kusa da shi yatsun hannunta na tsoke cikin na Talba, she lay down her head on his shoulder tana kallo da wayar da ke rike a dayan hannunsa.
She feel the pain so badly, ba zata iya zaya irin bakinciki da kishin da ta ji a lokacin, wani dauke kai tai ta aje numfashi a hankali, hakan kuma be hanata karasawa cikin dakin ba, jikinta rawa yake sosai kamar tray da ke hannunta zai subuce ya fadi, cikin sakewar zuciya ta duka ta aje tray sannan ta Talba da yai saurin zare hannunsa daga Aminatu, not because of yana tsoronta but because of baya son ya batawa dayansu rai, domin ya san zata ji zafi, Aminatu ta daga kanta daga jikinsa ba tare da ta kalleta ba.
 
“How are you feeling now?”
 
Ta fada idonta na makkale da hawaye, sai ya ji tausayinta ya kama shi, domin Leila bata taba gwada kishi da wata ba ko wani akan komai ba balle akan Talba, and wanda be saba fuskanta zafin da bakincikin kishi ba, zai ji kamar ya haukace idan ya kasance shi.
 
“Feeling much better, abinci kika kawo?”
 
“Yeah, amman na ga ki karya ma already”
 
Ta fada tana kallon kololin da Aminatu ta kawo. Sannan ta mike tsaye.
 
“Ina son mu yi magana da kai”
 
Aminatu na jin haka sai ta tashi rike da wayar ta fice har lokacin bata kalli Leila ba. Sai da ta fice sannan Talba ya kalli Leila ya ce.
 
“Akwai matsala ne?”
 
Ta lumshe ido hawaye ya sauko mata.
 
“Ni kadai nake da matsala ta, na kai wani stage sa babu mai fahimtar yarena a yanzu, ni kadai na san yadda nake ji”
 
Ta yi saurin rufe bakinsa saboda kuka dake son yaci karfinta. Talba ya nuna mata guri kusa da shi.
 
“Zauna a nan”
 
Ta zauna still hawaye an sauko mata kamar ba gobe.
 
“Me ke damunki?”
 
“Abubuwa da yawa, amman a yanzu abun da na fi bukata shi ne ka kasance a tare da ni, saboda na san Daddy ba zai fahimce ni ba”
 
Talba thought Leila tana magana da shi ne saboda Aminatu that's why he say.
 
“Leila, na san kina jin kishi ne kina jin Danuwa, i just want you to know that, ba kaunarki ne bana yi ba, akwai wadansu dabi'u da halayya da bana so na ki, kuma saboda na auri Aminatu ba shi yake nufin bana son ki ba, ina son ki ina sonta kowa da matsayinsa,and i want you to know that I love you no matter what happen”
 
Ta share hawayenta tana dan murmushi.
 
“Zan tafi gida Allah ya sauwake”
 
“Amin”
 
Ya amsa yana karantar yanayinta dake nuna akwai damuwa sosai a tare da ita. Da kallo ya bita har ta fice sannan ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinsa.
 Tana fitowa dakin ta samu Aminatu a tsaye bakin kofar rike da wayar Talba, wani irin abu ta ji ya soki zuciyarta, no matter how she try to control herself ta kawar da komai a ranta sai ta kasa, ji tai kamar ace akwai wuka a kusa da ita ta dabawa Aminatu gurin, sai dai bata iya ce nata komai ba ta nufi hanyar fita ward din tana haki kamar wanda tai gudu. Komawa tai cikin motarta ta dauki wayarta ta kira Ali, sai da wayar tai daf da katsewa sannan ya amsa kiran.
 
“Yau kuma an tuna da ni?”
 
Runtse ido tai wani sabon kuka na zo kwankwaso mata kofa.
 
“Ali... Ali... Ina son magana da kai”
 
Yanayin yadda ta ji muryarta ya san ba lafiya ba.
 
“Okay....kina ina yanzu...”
 
“Ina Asibiti”
 
“Zaki iya zuwa coffee center mu hadu ko kuma na same ki asbitin?”
 
“Zan same ka a can yanzun nan”
 
“Okay”
 
Ta katse kiran sannan ta jingina kanta da sitiyarin motar ta fashe da kuka sosai. Ta bata minti ashirin a haka kamin tai ma motar key ta fice daga asibitin, kai tsaye a inda suka yi za su hadu ta isa, ko da ta fito motarta tana tsaye jikin tasa motar yana jiranta, ganin yanayinta yasa ta karaso kusa da ita.
 
“Leila are you okay?”
 
“I just need someone to talk to, Ba ni da kowa yanzu, my best friend betrayed me, and my mom won't understand, Daddy da Talba na san za za su tsane ne... ”
 
Tana magana hawaye na wanke mata fuska.
 
“Koma cikin motarki zamu yi magana a ciki”
 
Ya fada yana zagaya dayan side din.
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Sai da ta bude motar ta shiga sannan ta fara tunani, anya ya kamata ta fada masa? Idan ma ta fada masa zai sama mata mafita ne ko kuma zata kara tura kanta a hadari ne?
 
“Miya faru Leila”
 
Ya fada yana kallonta cikr da damuwa, sai ta kara sharw hawayenta ta ja mayafinta ta na kara gyara fuskarta, tissue dake gaban motar nata ya mika mata, sai ta karba ta gyara hancinta.
 
“Ba komai daman i need someone to talk to”
 
“Yes I'm here you can talk me”
 
Ta kirkiron murmushin da bata san ta ina ta samo shi ba.
 
“Maganar bata da wani muhimmanci, domin yin ta ba zai canja komai ba”
 
“Wata kila kuma zai canja fiye da yadda kike zato”
 
“Ba zai canja komai ba, ya riga ya aureta kuma ba sakinta zai yi ba, babu abun da zai canja”
 
Ta juyarda maganar zuwa da Aminatu a kokarinta na kwatar kanta daga wacan maganar ta farko da tai. Kallonta yai ba dan ya gamsu da abun da take fada ba, domin matsalar Aminatu ba sabuwar matsala bace da zata saka Leila a cikin halin da take a yanzu, kuma idan har matsalar Aminatu ce miya kawo Madina a ciki har take fadar Daddy zai yi fushi da ita? Talba zai tsane ta? A take zuciyarsa ta raya masa akwai abun da take boyewa, sai dai be nuna mata ba.
 
“Ki yi hakuri Leila, lokuta da dama abubuwan da muke tsarawa ba su suke faruwa ba, karki dubi auren dake tsakanin Talba da Aminatu ki dubi soyayyar dake tsakaninku, zaki zauna a matsayinki na matarsa ita ma haka kowa da muhallinsa, Leila ki cire damuwa a ranki just pray bana son kina saka kanki cikin damuwa”
 
Ta yi murmusa a karo na biyu tana kallonsa da idanuwanta da sukai ja.
 
“Ka fi Talba zuciya mai kyau Ali, a duk lokacin dana shiga cikin damuwa kana kokarin ganin ka cire ni a ciki ka kwantar min da hankali, but Talba...”
 
Sai kuma tai shiru.
 
“Na aje soyayya a gurin da ba muhallinta ba, and yanzu ina tausayin kaina”
 
“No you shouldn't, ba ko wace mace mai sa'a samun saurayi kamar Talba ba, I'm his friend Talba yana da hali mai kyau Leila, kuma nasan zaki fahimci haka idan zaman aure ya hada ku, a krakashin inuwa daya”
 
Ta daga masa kai.
 
“Zan tafi gida kar Momy ta nemi ne”
 
“Okay”
 
Ya bude motar ya fita, sai da ya isa gurin motarsa sannan tai reverse, ta hau titi. Hannu ya saka aljihunsa ya ciro wayarsa da zimmar kiran Talba, sai kuma wani tunanin ya zo masa, a take ya maida wayar aljihu ya nufi motarsa ya bude ya shiga yai mata key, reverse yai ya fita daga harabar sannan ya hau babban titi, yana driving tunani har ya isa gaban gate din gidansu Madina zuciyarsa bata natsu da canja manufar labarin da Leila tai ba. Wayarsa da ya saka aljihu dazun ya sake cirowa ya shiga ma'adanar numbobinsa ya nemo number Madina, shi kansa ya manta when last yai waya da ita. Da sim 2 ya kirata line da be saba kiran mutane da shi ba. Wayar bata wani dade tana ringing ba ta dauka, sai dai jin muryar Ali ya saka ta dan yi jimm kamar ba zata amsa ba.
 
“Na'am Ali ya gida”
 
Ta fada bayan ta dauke wayar daga kunnenta ta duba number da babu ita a wayarta.
 
“Lafiya Kalau ya kike?”
 
“Lafiya Kalau”
 
Ta amsa gabanta na faduwa tsoro ya gama cika mata zuciya.
 
“Kina gida?”
 
“Lafiya?”
 
“Ina son na yi magana da ke”
 
“Da ni kuma akan me?”
 
“Magana ce mai muhimmanci, idan kuma baki da time yanzu zaki iya saka min lokaci sai na same ki same ni”
 
Shiru tai kamar bata tare da wayar, tsoro take ji wata zuciyar na raya mata yana tare da wasu ne, sai dai kuma su waye? Idan har police ne kai tsaye za su shigo cikin gidan ba tare da an kirata a waya ba. Amman kuma me zai saka Ali ya nemi magana da ita?
 
“Zan iya sanin akan me kake nemana?”
 
“Zai fi kyau idan kika fito sai ki ji”
 
“Ka yi horn a bude maka, sai ka shigo harabar gidan mu”
 
“Okay”
 
Ya sauke wayar ya danna horn din kamar yadda ta bukata, he know akwai wani abu a kasa domin yanayin yadda take magana da shi ya nuna haka, domin akwai rashin natsuwa da yarda a tare da ita. Ana bude masa gate din ya kunno kai harabar gidan ya faka a inda ya hango wasu motoci biyu fake, sannan ya bude motar ya fito ya jingina yana kallon harabar gidan. Ta windows ta hango shigowarsa har zuwa fakin din da yai, daker ta iya tattara yawun bakinta ya hade sannan ta mike tsaye ta dauki hijab ta saka, wani irin zallo zuciyarta take na tsoro da fargaba, me Ali ya zo mata da shi? Ya ji wani abu ne? Ko kuma Leila ta fada masa wani abun ne? Ta kasa raba dayan biyu har ta fito dakin not just her heart even jikinta shaking yake. Fitowa tai falon ba tare da ta shiga dakin Hajiya ta sanar da ita komai ba ta nufi kofar fita falon, sai kuma tai tsaye ta jin wani sabon tashin hankali na kusantota.
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
 
Ta furta a hankali, sannan ta kai hannu ta bude kofar ta fita cikin rashin kuzari da natsuwa, ga fuskarta dake kara nuna tashin hankalinta domin ta rame sosai kana kallonta kasan ta rasa natsuwa da kwanciyar hankali. Tafiya take kamar mai koyon tatata har ta isa gurin motarsa suna hada ido gabanta yai mugun faduwa domin ta lura da fuskarsa ba kamar yadda ta saba ganinta ba, dauke kai tai ta kalli wani gurin.
 
“Gani”
 
“Zamu shiga cikin mota ne mu yi magana ko akwai gurin saukar baki a gidanku?”
 
Ya fada yana kara karantar yanayinta, sai da tai fasahar aje numfashi a hankali sannan ta kalli garden din gidansu.
 
“Akwai kujerun zama a can”
 
“Bismillah”
 
Yai mata alama da ta fara wuce da hannu sannan ya bi bayanta, ta riga shi zama domin ta riga shi isa gurin da aka wadata da kujerun roba na zamani masu kyaun da dadin zama. Kallonta yai bayan ya zauna ita kuma ta ki yarda su hada ido sai yawo take da idon nata a kasa.
 
“Abun da na ji ban yi tsammanin jinsa ba Madina?”
 
Ta dauke kai da sauri tana fisgar numfashin dake son dauke mata.
 
“A yadda kuka da Leila be kamata ace an samu haka a tsakaninku ba”
 
He just decided yai mata magana ta wannan sigar, saboda ya samu abun da yake so.
 
“Sam ban yi tsammanin haka daga gareki ba Madina, a tunanina ke mai sharewa Leila hawaye ce, ina tunanin idan Leila tai wani aika aika zata gudu ta zo gareki kuma ki boye ta ki goya mata baya ko da bata da gaskiya, kun tashi tare kun girma tare sai da kuka kai matsayin da ya kamata ku dora yarankun akan tafarkin zumunci sai kuma ku bari sheidan ya shiga tsakaninku? Why?”
 
Hawaye ya fara mata zuba, hakan ya bawa Ali gwarin guiwar dorawa daga inda ya tsaya.
 
“So i just come here to talk to you, maybe zamu iya samun mafita, but i won't force you, domin babu wanda ya san na zo nan daga Talba har Leila?”
 
Ta kalleshi da sauri.
 
“Talba ya san abun da ya faru ne?”
 
“Be sani ba, a yanayin da yake yanzu baya bukatar wani tashin hankali ko bacin rai, ban fada masa komai ba kin san Leila kuma ba zata fuskance shi ta fada masa irin wannan abun da babu dadin ji ba”
 
Ta sauke idon da hawaye ya ki tsaya mata.
 
“Na yi nadamar abun da na aikata Ali, na san na jefa rayuwa a hatsari, duk abun da na yi na yi saboda Talba zuciyata tana matukar kaunarsa Talba Ali ina cikin damuwa, lokacin da zan aikata idona ya rufe bana iya ganin komai, i thought dauke Aminatu zai sama min mafita saboda na kusan haukace a dare dana gansu tare but....”
 
Sai kuka ya ci karfinta. Suma ne kawai Ali be yi a gurin ba, tsakanin furta tana matukar kaunar Talba da kuma dauke Aminatu sai ya rasa wanda ya fi bashi mamaki, be san lokacin da yawun bakinsa suka tsarke shi ba ya fara tari tana kallon wani gurin daban.
 
‘Kenan ita ce ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login