Showing 303001 words to 306000 words out of 332834 words
kokarin canjawa topic din ganin kamar be dace yayi masa wannan magana a yanzu ba.
“Takardar sallamarka ce”
“Maganar da zamu yi ta shafi Aminatu ne?”
Talba ya tambaya, sai Ali yai murmushi.
“Ita kadai ce damuwarka? Aminatu ce kawai take da matsala?”
Talba ya masa wani kallo.
“Kafi kowa sanin abun da yake faruwa da ita, so ina fargabar wani abu ne”
“Maybe idan mun je gida zamu yi magana, kamin lokacin ta huta”
Ali na fadar hakan ya nufi kofar fita, sai Talba ya bishi da ido ganin yanayinsa ya canja. Aminatu na ganin fitowarsa ta juya ta koma cikin dakin idonta ya sauka akan takardar dake hannun Talba.
“Takardar me ce?”
“Sallama”
“Da gaske?”
Ya mika hannunsa ya rikonta, yana kallon wayar idonta.
“Na taba miki karya?”
Sai ra girgiza kai tana murmushi.
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Momy na shigowa Aminatu ta sha jinin jikinta, ta koma kusa da Talba ta tsaya kanta a kasa. Kallonta Talba yai ya kalli Momy be ce komai ba sai dai ko kadan hakan be masa dadi ba, duk wani abun da zai saka Aminatu ta kasa sakewa bana sonshi.
“Ali yace an baka takardar sallama”
Momy ta fada, kamin ya amsa mata Amal ta shigo sanye da uniform dinta Mairo na bayanta.
“Eh, daman na fada masa ko be sallame ni ba zan tafi yau”
Momy ta yi murmushin karfin hali, domin ko kadan bata son bude hakoranta a gaban Aminatu.
“Daman kai ai ba son asibiti kake ba sai ta kama dole, Mairo zata kwashe kayan da suke da muhimmanci a nan, sauran da bama bukata sai a barwa Aminatu ta tafi da su gida”
Talba ya kalleta
“Momy ai tare zamu je...”
Kamin Momy tace komai, Aminatu ta tari numfashin Talba.
“Aa ina son na zauna gurin Yaya, ban taba kwana can ba”
Momy ta yi murmushin gefen fuska.
“Daman idan ba Hajiya Laraba ba ai sai dai idan a asibitin nan zaki kwana, domin kin nuna kiyayyarki ta kwana a gidanmu tun farko yanzu kuwa saboda rashin kunya ba zaki dauki kafa ki ce zaki bi mu ba”
Aminatu bata ce komai ba, ta nufi kofa sai Talba ya kira ta.
“Ina zaki?”
“Gida”
Ta fada ba tare da ta juyo ba, sai yai hanzarin dakatar da ita.
“Dawo, zamu je gida tare sai ta akai ki can, ko kuma na sauke ta yanzu”
Momy ta masa wani kallon mamaki.
“A baka key ka tuka mota ka kaita gida? Daga tasowarka daga aaibiti? Bayan kuma saboda yarinyar komai ya same ka? Ba zata bi mu ba, kuma ba zamu fara zuwa a sauke ta ba, sai dai ta hau abun hawa tafi a kafa ko kuma ta jira har sai matar ta zo”
Talba ta runtse ido ya bude alamar maganar Momy ba ta yi masa dadi ba.
“Momy, yarinyar nan fa Matata ce idan kika wulakantata kamar ni kika wulakanta, idan kika ci mutuncinta ba zan jidadi ba, rashin sakewar da kika mata ya saka bata son zuwa gidan nan, kuma kin san yadda basa jituwa da Leila, yanzu kuma taya kika ganin ni zan tafi na bar ta nan ko kuma na turata ta hau napep bana da tabbacin ta san gidan ma”
Momy ta nuna Aminatu.
“Wai jaririya kake daukar yarinyar nan ne? Okay sai ka haw Napep din kai da ita ka kaita gida idan ka sauketa sai mai Napep din ya wuce da kai gidan”
Ta fada a fusace sannan ta kalli Amal.
“Muje Amal, Mairo kwaso kaya ki saka min a booth”
Talba be ce uffan ba har ta fice, Mairo kuma ta shiga hada abubuwan da Momy ta fada mata, kuloli da jug kawai ta kwashe, ta bar bed sheet da pillow da wasu abubuwan da ta san Momy zata yi kyamar tabawa ko amfani da su. Tana ficewa Aminatu ta kalli Talba da sauri.
“Zan iya gane hanya fa, ko kuma na jirata ta zo, dan Allah ka tafi”
Mikewa yai tsaye ya karasa inda take tsaye ya riko hannunta yana duba yatsunta kamar mai son tantance abu.
“Indai Momy ba zata iya yi min lamanin na sauke ki gida ko ta sauke ki ba, ko kuma mu tafi gidan tare be kamata na tafi na barki ba”
Ya mika dayan hannunsa ya dago kanta daga kallon yatsun nata da yake murzawa ta kalleshi.
“Shalelena ina jinki a zuciya kamar sabon kwai, wanda idan ya fadi zai fashe, idan kuma kai masa rikon ganganci zai samu matsala, bana son ki sake facing wata damuwa ko bakinciki a rayuwarki”
Hawaye ya cika idonta, ba hawayen na bakinciki ko fadan da sukai da Momy ba, hawayen farinciki da sauraren kalamansa. Hannunsa ya saka ya share mata hawayen sannan yai amfani da babban yatsansa yana shafa laulasar fatar kumatunta.
“Zan iya daukar komai a rayuwar nan, ban da hawayenki bana iya jure bacin ranki, kin rasa abubuwa da yawa, baki cancanci komai ba sai farinciki da kulawa, ina sonki irin son da kalmomi sukai kadan su zayyana”
Ya rumgume ta a kirjinsa.
“Idan nace zan kyale Momy ta cigaba da musguna miki, kamar na bata goyon baya ne, nuna mata bana son abun da take yi zai sama miki salama a gurinta, saboda na san Momy tana son yayanta fiye da tunaninki ciki har da ni, to me zai saka ke ta tsane ki?”
Ka ji muryarsa kasan kalaman da Momy tai ma Aminatu dazun ba su masa dadi ba, ciki har da cewar da tai abun da basa so a bawa Aminatu, ya san Momy da kyamar abubuwa sai dai ba kasafai take alheri ba, yawancin duk abun da zaka ji tace a kyautar musamman idan an yi amfani da shi ko kuma tsohon yayi ne to bata son sa ne. Momy na daga cikin irin matan nan wadanda ko ba san son abu sun fi son su bar shi ya lalace.
Hawaye take a hankali kamin ta dago hannunta ta rumgume shi, har cikin ranta take jin kaunar mijinta, ta sani indai Talba yana raye a duniyar nan babu abun da zata nema ta rasa.
Unexpected Ali ya turo kofar dakin ya shigo, Talba ya juyo ya kalleshi sai dai be ce masa komai ba, kasancewar ya bashi baya ne baya iya ganin Aminatu sai dai hannunta data zagaye Talba da shi.
“Ranka ya dade idan ka shirya sai ka fito na sauke ka gida, Momy ta tafi”
Aminatun na jin muryar Ali tai hanzarin dauke hannayenta saboda kunya, kar ya ga ta rumgume Talba.
“Zamu fara kai Shalele gida”
Talba ya fada, ba tare da ya sake juyowa ba, Ali be ce komai ba ya juya ya fice daga dakin. Dagowa tai daga jikinta ta daga kai ta kalli fuskarsa.
“Zai yarda”
Ta fada da rada, sai ya kai bakinsa saitin kunnenta.
“Aa ba zai bari ba”
Ta yi murmushi ta boye fuskarta a kirjinsa, shi ma murmushin yai ya shafa bayanta. Sun dade haka sannan ya dago ta jikinsa.ya rika hannunta
“Zo mu je”
Cire hannunta tai daga nasa, be ce mata komai ba suka nufi kofar fita, da kansa ya fara bude mata ta fita sannan ya fito yaja kofar. A tare suka jera suna tafiya, gwanin sha'awa tana sanye da brown din Hijab dago har kasa, shi kuma yana sanye da kananan kaya komai black har shoe dinsa. Ko da suka isa parking lot din Ali har ya fito da motar harabar, Talba ya kai hannunsa ya bude mata back seat ta shiga ya rufe sannan ya bude front seat ya shiga. Ali ya ja motar suka fita daga asibitin ba tare da yace masa komai ba, Talba ma yayi kamar be san da shi a gefen ba, sai nunawa Aminatu gurare yake kamar wadanda suka fito yawon shakatawa, sam ba zaka ganshi kace shi ne marar lafiyar ba.
“Faka a nan zan siya mata wani abu”
Ali ba dan ransa ya so ba, ya faka gefen titi har lokacin be ce komai ba, and yana ta kokarin ganin be kalli Aminatu ba ko da a madubin dake gaban motar ne.
“Kina da kudi”
Talba ya tambaya yana kallon katuwar restaurant din dake gefensu.
“Aa”
Aminatu ta amsa daga back seat din da take zaune murya kasa kasa. Juyowa yai ya kalleta.
“Amman kina jin lokacin da na ce a tsaya kuma kika kyale”
Aminatu ta zaro ido.
“Ni ban ce a tsayar da shi ba, amman ai”
Ya kashe mata ido daya sannan ya sakar mata murmushi, ya juya ya kalli Ali.
“Bani cash ko Atm”
Sai a lokacin Ali ya kalleshi, ya dauke kai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wallen dinsa ya cire atm din ya mikawa Talba. Bude motar Talba yai ya fita bayan ya karba, ya budewa Aminatu, domin be yarda ya barta daga ita sai Ali ba a motar, haka nan kawai yake jin kamar wani abu Ali zai mata ko kuma ya saka ta gaba yai ta kallon. Fitowa tai sai ya rika hannunta, kallon mutane tai tana mai tsanannin jin kunya ta fara kokarin janye hannunta, a space din yatsunta ya saka nasa yatsun wanda hakan ya bashi damar rike ta da kyau.
“Baki son ina rika ki ne?”
Ya fada yana kallonta kamar wani maye.
“Akwai mutane fa”
Ya fada a shagwabe, sai yai murmushi ya dauke kansa suna kara dosar restaurant din.
“Ba haramun mu kai ba, wasu ba su ma aure ba suke haka, balle mu da muke da lasisi, kuma babu mutanen da ya kamata kiji ma kunya a nan ai, ba Momy Daddy ko Mama babu kowa even Yaya”
Ta yi dariya da yar siririyar muryarta.
“Kai ma Yayanka ne?”
“Yes, saboda ke”
Ya fada yana dayan hannunsa ya ja zirin hancinta, sannan suka shiga ciki, har ya gama zaba mata abubuwan da yake kyautata zaton zata iya ci be saki hannunta, ganin za su fito be siye mata kilishi ba ya saka ta nuna masa shi, sai ya kai bakinsa saitin kunnenta kamar zai shige cikin bakin.
“Me kike so?”
“Kilishi...”
Ta fada a shagwabe lips dinta na taba fatar kunnensa, sai a lokacin ya sake ta ya karasa gurin kilishin ya dauko mata leda 5 ya dawo ya zuba a inda ake lissafin. Bayan sun gama ya mika musu atm din suka cire kudinsu suka mayar masa da abunsa, sannan suka saka masa kayan cikin leda, hannunsa biyu ya saka ya dauko ledadin be yarda ta dauki ko daya ba, suka fito suna tafiya tare har suka iso gurin motar, Ali ya bude musu booth din zuciyarsa nata raya masa rashin adalci da Talba yake yi, because ya san idan Leila ce ba zai mata haka ba, Talba ya saka ledodin a booth sannan ya rufe ya zagayo, ya sake bude mata back seat ta shiga ta, ya rufe sannan ya bude front seat ya shiga, a kusa da sitiyarin motar ya dora ma Ali atm dinsa ba tare da yace masa komai a ba.
“Ban fa san inda zamu je ba”
“Zamu fara sauke Shalele gida”
Talba ya amsa masa, can kuma ya fada masa unguwar, daga haka be sake ce masa komai ba sai da suka isa liyin su Hajiya Labara sannan ya ce.
“Dama... Hagu... Ya isa”
Haka yai ta yi har suka isa bakin gate din gidan. Kusan a tare ita da shi suka bude motar suka fito, Ali ya sake bude musu booth din sai Talba ya isa gurin ya fiddo ledodin suka nufi gate, sai da ta kwankwasa mai gadin ya leko ya ga ita ce sannan ya bude ta shiga ciki, da sauri ya mika hannunsa ya karbi ledar dake sai Talba ya sakar masa, yai gaba ita da shi suna baya. Ko da suka isa kofar falon tuni mai gadin ya shiga cikin falon ya aje kayan a saman kujera sannan ya juyo ya fito. Aminatu ta nufi kitchen inda take jin kamshin soye soye, bata dade ba ta fito tare da Hajiya Laraba da fuskarta ke kumshe da murmushi.
“Maraba da mai Talba, kai da kanka?”
Talba yayi murmushi.
“Eh daman an sallame ni ne, sai tace ita a nan zata zauna shiyasa na kawo ta”
“Okay, To ya jikin naka?”
“Na warke Mama”
“Maa Shaa Allah, haka ake so Allah ya tsare gaba”
“Amin Amin, zan koma daman dai nace bari na fara sauketa sannan na wuce gida”
“Okay Allah ya kara lafiya, an gode sosai”
Be ce komai ba, sai ma kunya da ta rufeshi domin be riko mata komai ba, sai matarsa yai ma siyayya. Yana fita Hajiya Laraba tai mata alama data bishi da baki, sai Aminatu ta nufi kofar, ashe kuwa ta yi sara akan gaba, tana fita sai ta ganshi tsaye gefen kofar yana jiran fitowarsa, kallon harabar gidan yai ya ga babu mai ganinsu, mai gadin kuma hankalinsa yana ta wani gurin sai yai saurin kai bakinsa ya sumbance.
“Sai mun yi waya, i love you”
“Toh”
Ya sakar mata murmushi sannan ya nufi gate, ta bishi da kallo tana jin wata kalar kaunarsa na fisgarta. Sai da ya fice sannan ta juya ta koma ciki. Sai a lokacin ya rufe bayan motar sannan ya bude gidan gaba ya shiga ya zauna.
“Idan kana wani abun sai na rika ganinka kamar ba kai ba”
Ali ya fada sannan ya juya motar suka koma ta inda suka biyo.
“Ka san ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare”
Talba ya fada yana kallonsa da murmushi a fuskarsa.
“Yeah sometimes, amman mafi akasari mutane irinka suna nuna soyayya ne a muhallinta, abun da kake is too much, Momy ta fada min abun da kai mata dazun saboda tace ba zata je da Aminatu ba, bayan kuma. Yarinyar nan ta nuna bata son zama a can, ka ga...”
“Karka nuna min abun da zan yi da wanda ba zan yi ba, akan Shalele na, you're my friend bana fatar jin wata kalma da zata sosa raina akan Mamata daga bakinka”
“Leila was right...”
“Leila is always right a gurinka ai, kana da wani abu mai muhimmanci sa zamu tattauna akai ba, ko kuma waka zaka kunna mana a motar mu saurara?”
Ali yayi murmushi ba tare da ya kalli Talba, sannan ya faka motar gefen titi karkashin wani itacen dogon yaro, ya busar da iskar bakinsa ba tare daya kalli Talba ya ce.
“Talba ina son na tambaye ka wani abu”
Talba ya kalleshi ba tare da yace uffan ba, Ali be damu ba ya aika masa tambayar domin ya san be zama lalle idan ya
“I want you to be honest, idan Leila ta samu kanta a wani hali, zaka iya zama da ita? Staying by her side ka kwantar mata da hankali kuma ka jata a jiki ka bata kariya?”
“Me zai haka? As long as tana da gaskiya”
Ali ya sauke ajiyar zuciya secretly.
“After Daddy da Momy i don't Leila tana da gata daya wuce ka, ko da ace gida daya kuka taso ta cancanci kariyarka da soyayya, balle kuma har ta hada jini da kai karewa da karau ma kai ne mijin da zata aura, idan kowa zai guje a duniyar nan ina tunanin kai ba zaka gujeta ba, ina tunanin you're the first person daya kamata ace ka kasance a tare da ita, a yanayin bakinciki ko farinciki”
“Wait...miya saka tsara wannan zancen?”
Talba ya tambaya with confused.
“Just to remind you how important you're to her, Leila tana son ka sosai Talba, wani irin so da take tsoron rasaka in every minute every second, and ina da yakinin da wani abu zai same ka a yanzu Leila zata zauna da kai no matter what, so a yau ina son ka kasance a tare da ita ka kwantar mata da hankali”
Jimmm Talba yai yana nazari, at first ya dauka ko Ali zai yi magana ne akan Aminatu, domin ko daina zuwa asibitin da tai dubashi ya san saboda Aminatu ne, sai da yadda ya zayyago masa wasu kalaman ya saka shi mamakin dalilinsa na yi masa wannan maganar.
“Leila ta aikata wani abu ne?”
Ya tambaya tana juyowa ya kalleshi. Ali yaja dogon numfashi ya sauke a hankali.
“Yes, amman akan kuskure ne wanda be wuce kowa ba, ko kuma na kira shi da kaddara”
“Please go straight to the point”
Talba ya fada cike da kaguwa.
“Abun da ka dade kana zargin Leila.da shi na kisan Baaba, ta aikata amman ba da gangan ta aikata ba, kuskure ne!”
Baki sake Talba ke kallon abokinsa.
“How do you know?”
Ali ya gyara zamansa, sannan ya kwashe labarin yadda komai ya faru ta fadawa Talba.
“I knew it”
Talba ya fada yana buga gaban motar.
“You shouldn't be angry”
“Why?”
Talba ya tambaya da karfi, sannan ya ware hannayensa.
“Ta san da wannan amman ta kyale iyalan matar nan suna da wahala? And before that Leila har marin tsohuwar nan ta taba yi, that's means tana da intention na aikata komai, saboda bata iya controlling kanta, ji yadda suka mai da komai ba komai ba suna rayuwa kamar babu abun da ya faru?”
“Wata kila tana jin tsoro ne!”
“Tsoron me? Ta kashe rai kuma ta boye, ta karyata kuma ka kira haka da tsoro”
“Amman a yanzu ta yi nadama, kuskure ne babu wanda ya wuce kuskure Talba, kai kanka ka auri Aminatu akan kuskure, duk kuwa da kasan da cewa a lokacin Daddy ya hanaka, kuma idan yaji ransa zai bace, haka Momy da Leila amman a haka ka aureta, so Leila ta aikata kwatankwacin abun da ka aikata, ya kamata kai mata uzuri, ta yi nadama sosai Talba”
Talba ya girgiza masa kai.
“I marry Aminatu because we're mean for each other. Kuma ta yi nadama ne ba dan Allah ba, there must be a reason wanda hakan ya saka kai ma kanka ka sani”
“Yeah saboda Madina ta fara yi mata barazana a rayuwarta tana kokarin ganin ta hana ta aurenka, saboda tana sonka and Madina