Showing 162001 words to 165000 words out of 332834 words

Chapter 55 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65607

isa gidansu Madina ta cikawa bakinta da iska tana furxarwa ya kai sau goma.
 Sau hudu tana danna horn sannan aka bude mata gate din, wani banzan kallon ta watsawa direban cox he got lucky ba a gidansu yake aiki ba da yau sai ta wulakanta shi. A inda ta saba aje motarta ta aje sannan ta dauki wayarta ta kira kawarta Madina, domin sai a lokacin tana doubting tana gida ko tana gurin aikinta.
 
“Ki shigo cikin gida mana na ga fakin dinki”
 
Shine abun da Madina ta fada bayan ta amsa kiran, dai Leila ta kashe wayar ta bude motar ta fita ta rufe ta nufi kofar falonsu, tun kamin ta karasa aka bude mata kofar falon, da wata yarinyar kirkice ko a fuska zata yi ma wacce ta bude mata kofar godiya, amman bata kula ta ba sai ta nufi dakin da Madina take, daman idan ta shigo cikin gidan Hajiya kawai take iya gaisarwa, su kansu kannen Madina har sun saba da yanayinta, ko ba su ba abu ne mai wahala Leila ta ganka a wani gurin tai maka gaisuwa, matukar ba abokin Daddy ko Momy ba ne, su ma kuma ba kowa ba.
Tura kofar dakin tai ta shiga, sai ta samu Madina zaune tsakiyar gado tana duba wasu manyan yan kunne masu matukar kyau.
 
“Miye haka?”
 
“Ina zabar wadanda zan siya ne before birthday na”
 
Ta tabe baki sannan ta zauna gefen gadon.
 
“Madina yau Momy ta yi min abun da zan dade ina bakinciki”
 
“Me kuma ya faru?”
 
“Wai ta fadawa Daddy na ce ina son ayi fixing date din aurenmu da sarkin jin kan nan...”
 
Wani irin bugawa zuciyar Madina tai, har sai da shiga da fitar numfashinta suka samu tangarda na dan dakiku.
 
“What...aurenku?”
 
Ta tambaya tana tuna mafarkin da tai, ashe ba Aminatu tai ma ba Leila tai ma.
 
“To miye matsalar haka?”
 
Ta tambaya tana hade yawu da karfi, gaba daya sai jikinta yai weak.
 
“Haba dai, yanzu zai fara min kallon ni na fara magana fa”
 
Madina ta kama hannunta hawaye na cika idonta.
 
“Leila karki ce aa, kawai kin karba ki barwa Allah komai, you got lucky kina da mai son kuma kike so kamar Talba, ji da kai na me Leila? I'm always telling you this kina da dama a yanzu karki yarda ki rasa ta”
 
Ta karasa na sauko mata, sai ta goge tana murmushi.
 
“Ji yadda nake farinciki daga jin wannan labarin kawai, ina ga kuma na ga lokacin”
 
Ta karasa tana fashewa da kuka sai tai saurin rumgume Leila, ta karawa kukanta kuzari da muryar da Leila ba zata iya ji ba.
 
“Haba dai, Madina kin san fa waye Talba, babu irin zubar da kaina da ban yi ba akan shi, babu kalar Soyayyar da ban nunawa ba bawon Allah ba amman yana min jin kai, ni kuma a yanzu na fishi jin kaina, at least ya kamata ya san na banbanta da sauran mata, amman haka da Momy tai min zai saka ya raina ni kuma yai tunanin na mutu ne akansa”
 
Madina ta dago daga jikinta sai dai hawayen dake zuba a idonta ba su daina bin fuskarta ba.
 
“Ki manta da komai, ki kaddara a yanzu wata sabuwar rayuwa za ku fara, Talba zai daina duk abun da yake idan kuka yi aure, kuma duk wani ji da kai zai aje shi gefe, irin wadannan mazanje, suna kula da matansu fiye da tunanunki, kuma basa bawa matan waje fuska, karki watsawa Momy kasa a ido, kin isa aure Leila ba zan boye miki ba kuma kina da wanda kuka dace da juna”
 
“Miyasa kike kuka?”
 
Leila ta tambaya ganin hawayen dake zuba a idon Madina yaki tsaya mata. Sai Madina tai saurin share hawayen tana dariya.
 
“Look at you my girl, kawata zata yi aure ta bar ni, ofourse abun farinciki ne, amman kina tunanin zan jidadi ne?”
 
“Ke ma dai kamar ba ki san ni ba, idan fa na kafe akan abu daya na dafe kenan, zan tsaya na ga gudun ruwansa, amman ba zan yarda ajina ya zube ba, ke da Momy kun kasa fahimtata”
 
“Na fahimce ki Leila, kawai bana son na doraki akan turbar da zan zo ina nadama ne ni da ke, but i promise myself zan yi fighting ma abun da nake so har sai na samu cikar burina, ke kawata ce for more than 26 years ba zan iya cutar da ke ba”
 
Leila ta yi mata kallon rashin fahimta, gaba daya a bayanin da take mata a baibaiye yake babu abun da ta fahimta, gashi sai hawaye take.
 
“Fight for what?”
 
Madina ta yi saurin share hawayenta ta hade yawu tana kokarin kawarda maganar.
 
“For Alakarku da Talba! Mutumen nan yana son ki, ana da kokarin hadaku sai wani botsewa kike, so. Dole sai na yaki wannan zuciyar taki kamin na samu kanki ki amince”
 
Ta karasa tana kai hannu ta taba kan Leila tana dariyar yake. Leila ta wara ido tana daga hannu sama.
 
“Wayyo Allah, da na san ke ma goyon bayan Momy zaki yi da ban zo nan ba, i need to go somewhere inda za a fahimce ni ace yes Leila abun da kike shi ya dace”
 
Tana fadar hakan ta mike tsaye.
 
“By the way, na yi ma Momy maganar aikinki, ita kuma ta yi ma Daddy ki saurare labari mai dadi soon”
 
“Awwww Thank you”
 
Madina ta yi saurin mikewa tsaye ta rumgume tana murmushi, a yayinda fuskarta ta sauka a kafadar Leila sai wasu hawayen suka zubo mata masu kama da na bakinciki kuma ba bakinciki ba, sai tai saurin saka hannunta ta share hawayen sannan ta dago sai ta kasa hada ido da Leila.
Leila ta mata kallon rashin fahimta, domin bata taba ganin kawarta a irin wannan ba.
 
“Kamar dai akwai abun da yake damunki kamin na shigo? Can we talk”
 
“No babu abun da yake damuna, ai kin san bama boyewa juna komai, kawai dai ina jin kamar karki tafi ki bar ni ne”
 
“Waya ce tafiya zan yi na barki? Mtschee”
 
Ta dauki jakarta tana kara jan tsaki Madina ta bita da dariya, Leila na ficewa Madina ta fadi zaune saman gadonta not knowing what to do, sai kawai ta fara kuka, if har Leila ta auri Talba ta san ita kuma ta rasa shi, amman miyasa ta fada kaunarsa tun farko bayan tasan haka zai iya kawancenwa?
 
“Miyasa? Why from first place?”
 
Ta tambaya da karfi tana fashewa da kuka tare da saukowa saman gadon ta zuba kasa tana jin zuciyarta na mata wani mugun zafi marar misaltuwa. Ta saka duka hannayenta ta dafe fuskarta, tana ta kokarin gano dalili, even if ba Talba ba be kamata ta kamu da son saurayin kawarta ba right? Amiyarta wanda ta bata dukan amanarta!
 
“Ban yi laifi ba, duk macen da tai arba da Talba dole zata so shi, ba laifina ba ne laifin zuciyata ne”
 
Ta bawa kanta amsa tana girgiza kai, sai kuma ta tashi ta shiga bandaki sai amai, duk abincin da ta ci a ranar sai da ta amaye shi tana jin kamar har da zuciyarta zata amayar, bayan ta gama ta daura alwala ta fito ta shimfida carpet ta fara sallah nafila, tana kuka idan tai raka biyu sai ta sallame ta sake dorawa ta sallame ta sake yi haka ta jera nafila har aka kira La'asar, zuciyarta na mata zafi tana jin kamar ba zata kai anjima ba.
 
 
LEILA POV.
 
Yadda ta shigo gidan cikin natsuwa ba zaka ce ita ce ta fita a dazun cikin bacin rai ba. Kusa da kofar falo ta faka motarta ta bude ta fito tana kallon Kabir dake zaune kan kujerun dake kusa da kofar falon yana danna wayarsa. Ta ji faduwar gaba da kunya musamman ma da ta lura da ya zuba mata ido yana kallonta kamar wata bakuwar gidan. Har ta kai hannu ta danna door bell din kofar falon sai kuma ta juyo ta dawo ta zauna kusa da shi amman a dayan kujerar without looking at him.
 
“Na san haushi na kake ji, amman abun da na aikata ba wai na yi da niya ba ne”
 
“Me hakan zai canja? Kin san abun da ya fi bata min rai? Yadda kuka bar iyalin matar nan a cikin zullumi da tunani a Kullum, and look at you kina rayuwarki normal babu damuwa, and now god has blessed you with good friend Madina mace mai kirki not like you, and still Allah zai baki Talba a matsayin miji, kamilin mutun mai kirki”
 
Tun da ya fara maganar har ya gama be kalleta ba, harabar gidan kawai yake kallo.
 
‘Shi ma ai ba wani kyau hali ne da shi ba, sai ji da kai da nunawa mutane isa’
 
Ta fada a ranta tana hararsa, azahiri kuma sai ta mike tsaye ba tare da tace masa komai ba ta nufi door bell din ta danna aka bude mata ta shiga ciki..
 
 
BATURIYA POV.
 
Tun da akai mata aikin cirar cikin bata sake lafiya ba, yau kusan kwana hudu kenan, jiki ba karfi yawun baki sai tsinke mata suke kamar mai cikin. Sai dai duk da haka ba ta fadawa Umma komai ba, kawai ta fake da ciwon mara ne kawai idan aka ce ta tafi asibiti bata yarda wani ya raka ta sai dai ta fita ita kadai da sunan zuwan asibiti, sai ta zagaya ta tafi gidansu Ramlee, idan ta dawo sai tace likita yace ba wata matsala. Sai duk abun da take Umma na lura da ita da kuma yanayinta, hakan yasa ta titseta kai tsaye da abun da take zargi.
 
‘Okay Dear Allah ya kaimu ya tsare hanya i will miss you’
 
Tana ba shi amsa Umma ta jefa mata wata tambayar.
 
“Wai Rafi'a ko dai zubar da cikin nan kika yi?”
 
Baturiya ta dago da sauri daga chat din da take da Fahat ta kalli Umma.
 
“Zubar da ciki kuma? Haba Umma sai kace wanda tai cikin shege?”
 
Umma ta duba da irin duban nan na uwa da ya wanda babu wasa a cikinsa
 
“Karki maida ni karamar yarinya mana, ina lura da yanayinki”
 
Ta yi Shiru kamar mai saka abun da zata ce, can kuma ta dago ta kalleta a raunane kamar zata fasa kuka.
 
“Ba zubarwa na yi ba Umma, zubewa yai”
 
“Watan shi nawa?”
 
“Biyu da kwana shirin da uku”
 
Umma ta sauke ajiyar zuciya.
 
“Da sauki tun da ba a busa masa rai ba, amman karki sake, tun da ba cikin shege ba ne”
 
“Umma gani na yi idan ma na bar cikin wahala kawai zan yi, tun da ba kula zai yi da ni ba, kuma zan yi ta fama da dawainiya da abun da na haifa har sai na yaye sannan na yi wani auren, wani ma idan ya ji cewar kana da yaya biyu ai ba zai aureka ba, amman yanzu kin ga har na cika iddata”
 
“Ni ma na yi miki wannan tunanin, sai dai tsoron shiga hakki yasa ban miki maganar ba, kin tabbatar dai ba a isa busa masa rai ba ko?”
 
“Wallahi Umma ba a busa masa ba, ai da an busa ni ma ba zan aikata ba”
 
“Waya kaiki inda ake zubar da cikin?”
 
“Wata makociyar mu ce, dake can Maman Noor mijinta na yi shi ne na yi mata magana sai ya bani wasu kwayoyi kuma yayi min allura”
 
“Kin tabbatar cikin ya zube kuma ba wata matsala?”
 
“Ba matsalar komai, karfin jiki ne dai har yanzu bana ji, shi ma kuma da na fada masa yace soon zai daina”
 
Ta fada tana mikewa tsaye saboda kiran Alhaji na shigowa wayarta dake silent domin bata yarda ta amsa kiran wani namijin a gaban Umma, saboda ta san zata mata magana ganin tana cikin idda ne, duk wayar da take sai ta boye kanta a daki ko bandaki take iya amsawa, chat ne kawai take yi a gabanta shi ma dan tana da tabbacin ba zata leka wayarta ba.
Sai da ta maida kofar dakin ta rufe, sannan ta nufi bandakin ta shiga ta rufe kanta kana ta amsa kiran tana murmushi kamar tana ganinsa a fili.
 
“Haba Sahiba ta, da tsufana da komai ina ta kira ana min yanga?”
 
“Ba dole ayi maka yanga ba, tun da kai kake nema”
 
Dariya yai irin ta manyan maza sugar daddy sannan ya amsa mata.
 
“To na ji, yanzu yaushe zamu hadu, na zaku mu hadu da juna na yi marmarinki Wallahi, har tafiya nake da ita amman na fasa na tura na dana, kuma maganar zuwa na chine yana nan fa sai da ke zan je”
 
“Karka damu, zan kiraka gobe ina period ne shiyasa nake maka wala wala”
 
“Ohhhh amman ban jidadi ba, ba akwai dan abun da kuke sha ta dauke ba? Tsakani da Allah ina bukatar Baturiyar mata”
 
Ta yi dariyar jindadi.
 
“Zan sha ai, tun da ka matsa, idan ya tsaya min sai na kiraka”
 
“Yauwa haka nake so, zan aiko da na siyen maganin yanzu nan i love you”
 
Ya fada daga karshe yana kashe muryar.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
Ya tabe baki yana kwance saman gadonsa wayarsa makkale a kunnensa yana sauraren dariyar da zolayar da Ali yake masa.
 
“Wato daman ance mai hakuri mawadaci,kai da kai hakuri sai Allah ya hada maka biyu lokaci daya, ka more abun ka”
 
Talba yaja tsaki domin shi be ga abun dariya a ciki ba.
 
“Kana da matsala Ali, kai baka duban irin matsalar da zan shiga? Ina da aure karkashin kasa, kuma yanzu za a kara min da wani a bayyane kuma matar nan fitinanniya”
 
“Sauki ne a gareka Talba, idan ka auri Leila zaka huta wani abun, kuma ita ma Aminatu zata samu zama a gidan cikin kwanciyar hankali, ka ga Leila tana gidanka kana controlling dinta Aminatu kuma tana gidan iyayenka, kuma bana jin zata samu matsala a gidan idan Leila bata nan”
 
“Leila tana da fitina ko bata gidan zata iya hana yarinyar zama lafiya”
 
“To yanzu ya zaka yi?”
 
“Ya zan yi kuwa, gani dai ga Allah”
 
Ali yayi dariya.
 
“An hada maka mata masu kyau da fara da baka, kuma lokaci daya”
 
Talba ya yanke wayar domin ya san Ali zai yi ta damunsa da zolaya ne kawai, kuma he not in the mood. Dan tsaki yaja ya shiga neman number Kaka, sai da ta kusa yankewa sannan Kaka ta daga.
 
“Salamu Alaikum”
 
“Kaka ina Matata?”
 
“Matarka gata nan tana cin abinci, ita kadai ka sani ban da ni”
 
“Eh mana, zan zo gobe na dauke ta”
 
“Ban gane ka dauke ta ba, haka nan kawai ake daukar amarya, ai sai ka fada mana muma mun shirya tukuna, kuma ai ba ita kadai zata je ba dole sai da yan rakiya, sai mun ga gurin zamanta”
 
Tashi yai tsaye yana kallon dakin nasa.
 
“Ban gane ba? Sai an rakota kamar ya? Sai kace dai ba ki san waye ta aura ba?”
 
“Idan na sanka sai na kyaleka ka zo ka dauki amarya ka tafi? Aa dole ne sai na ga inda za a aje ta kuma sai na rakata har dakinta ni da mutane na”
 
Talba ya daga kansa sama ya sauke yana shafa ya tare da cikawa bakinsa iska ya furzar.
 
“Na ji, amman kin san auren nan na yi shi saboda ke, ya kamata ki yarda da ni mana Kaka”
 
“Idan ban yarda da kai ba zan baka auren yarinyar ne? Na yarda da kai amman dai amarya ba zata tare a yanzu ba sai nan da wata uku”
 
Ya zare ido kamar tana gabansa.
 
“Wata uku kuma?”
 
“Eh haka muka yi da Hajiya Laraba”
 
“Kaka miya kawo Hajiya Hanne Laraba kuma a wannan maganar?”
 
“Wannan kuma tsakaninmu ne babu ruwanka, idan mun saka ranar da za a dauki amaryar zan fada maka”
 
“Tana kusa?”
 
“Ita wa?”
 
“Shalele”
 
“Eh amman ba zaka yi magana da ita ba yanzu!”
 
“Saboda me?”
 
“Idan an tare sai ka juyata yadda kake so”
 
“Gaisawa fa kawai zamu yi”
 
“Ai ko muryarta ba zaka sake ji ba, sai an tare”
 
“Kaka an daina fa wannan yayin, lafiyarta kawai zan tambaya ba wani abun ba”
 
“Lafiyarta kalau”
 
Duk yadda ya so yai magana da Aminatu Kaka bata yarda ta bata wayar ba, a haka sukai sallama be gaisa da Aminatu ba. Kansa ya dafe yana mamakin yadda Kaka take kokarin banbanro masa wani babban aiki.
 
“Tsohuwar nan ta cika rigima Wallahi, wani irun tarewa Fisabilillahi? Ni da nake zaton daukar mata kawai zan yi, amman yanzu ai tonon asiri ne”
 
Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya nufi kofar fita yana lalabar keys din motarsa dake aljihunsa. Sai da ya fara bude gate din sannan ya shiga motarsa ya fita da ita ya sake fitowa ya rufe gate din. Slowly yake driving har ya isa gida, haka nan kawai ya ji yana bukatar bata lokacinsa a cikin motar ba tare da aikin komai ba. After like 30 minutes ya bude motar ya fito yana kokarin rufe kofar Leila ta fito ta kofar Kitchen cikin shigar atamfa wanda dikin ya daye jikinta sosai ko'ina na surar jikinta a bayyane yake, hannunta rike da jaka da key da alama dai fita zata yi. Zagoyowa tai ta iso kofar falon tana jiran isowarsa. Tun da ya kalleta sau daya ya dauke kai be sake kallon inda take ba har ya isa gurin kofar sai dai yana ganin irin tsayuwar da tai ya san da magana a bakinta.
 
“Maganar auren da Daddy yai maka, Momy ta yi magana ne ba tare da sanina ba”
 
Kallonta yai.
 
“Really? Bayan kin furta cewar aure kike so yanzu kuma zaki tare ni a nan da wannan maganar? Why don't you talk to daddy about it? Wai kokarin nuna min isa kike a nan ko me?”
 
Wani banzan kallo ta watsa masa zuciyarta na mugun tafasa.
 
“Me kake daukar kanka?”
 
Ya matsa kusa da ita sosai har tana iya juyo saukar numfashinsa, yana kallon cikin idonta, kamar yadda ita ma take kallon nasa.
 
“Wani mutum wanda idan kika rasa shi zaki haukace ki shiga damuwa, wani namiji da ba zaki iya rayuwa babu shi ba”
 
Ta yi murmushi zuciyarta na mugun bugawa da karfi, kowanensu yana shakar kamshin turaren dan'uwansa.
 
“Ka yi kuskure, babu wannan namiji a duniya, wanda Leila zata ce ba zata iya rayuwa babu shi ba, amman akwai mazan da basa iya rayuwa sai da Leila, girman kanka na banza ne tun da har ka amsa cewar kana so na, ji da kanka na banza ne tun da har ka karbi tayin auren da Daddy yai maka da wuri haka, ko da yake samun mace kamar Leila a gurin aure wani abu ne mai matukar wahala”
 
Ya dan matsa baya.
 
“Mai matukar arha dai, musamman a gurin namiji

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login