Showing 300001 words to 303000 words out of 332834 words

Chapter 101 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65638

shi har ina shirin bude masa sabon file a familynmu, na saka a gyara masa daki a kusa da nawa”
 
“Ki ce gata kika shirya yi masa kenan”
 
“Sosai ma, yanzu dai bari na kawo maka ruwa ka sha sai na kawo maka Sultan din”
 
Ta mike tsaye sai yai hanzarin dakatarta ita.
 
“No ni dai ban ce ina jin kishin ruwa ba, dazun ma da kika ga muna tafiya a rana ai danki kawai kika dauke kika bar ni tsaye a rana”
 
“Kai din ne rigimame ba lallai idan na ce maka ka shiga motar na taimaka maka ba ka shiga”
 
Ta fada tana murmushi.
 
“Ko kuma ni na taimaka miki na shiga motar ki samu albarka ba”
 
“A yanzu an fada maka ban samu ba, Sultan fa ya shiga”
 
“Shi ai ba lada ba la'ada, amman da ni kika dauka da lada zaki samu ninki ninki”
 
Ta kara fadada murmushinta tana mamakin yadda Faruk ya sake yana jera mata kalamai kamar ba shi ba.
 
“Ga wannan ban san ra'ayinki ba, sai na zabo miki ra'ayina, zan yi farinciki idan baki raina ba”
 
Ya mika mata ledar sai da tai kamar kar ta karba sai kuma ta saka hannu biyu ta karba.
 
“Na gode sosai, Allah ya saka da alheri”
 
“Ameen, za'a min izinin tafiya da danki?”
 
“Eh amman na kwana biyu kawai”
 
Tana fadar hakan ta juya ta fice daga falon.
 


Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Washe garin ranar da Hajiya Saratu taje gurin bokan ta dawo tana bawa Momy bayanin yadda sukai da shi. A lokacin Leila na zaune dakin tana cin yayan itatuwa, sai dai hankalinta gaba daya yana gurin maganar da Momy take da Hajiya Saratu.
 
“Ya ce komai a daidai yai shi, kuma sunan Aminatun ya saka, na tsakanin Talba da Leila kuma ya bada wani amman yace duk da haka sai ta zo”
 
Ta bude jakarta ta dauko kulli magani a cikin wani kyale ta mikawa Momy, kana ya dauko wani rubutu a gora.
 
“Ya ce ranar da zata ci shi kar ta ci gishiri, wunin ranar, wannan kuma sha zata yi, kuma ta tambaya wai layar da aka bada an saka a karkashin gadon na ce masa an saka”
 
“Allah yasa kin tambaye sa dalilin daya saka Leila take jin warin jaba”
 
Momy ta fada.
 
“Tabbas kuwa na fada masa, sai yace wai zata daina, shi ma be san abun da ya saka hakan yake faruwa ba, amman dai yace zata daina jin komai, kuma na Aminatu ya ce zai canja wani kalar wanda ba sai ta ci ba”
 
“Yauwa haka nake so, b aki masa maganar Madina ba?”
 
Leila ta dago ta kalli Momy, wacce tai tambayar.
 
“Haba dai ke ma dai ai kin san ba zan mata ba, na masa magana na fada masa sai yace zai yi aikin a samu sabon zane a kai masa, zai yi aiki a kai sai a bata zanen ta daura, na ki kuma ya ce na dawo rana wata yau na karba miki na ki”
 
Momy ta yi murmushi.
 
“Nawa yace zai yi aiki?”
 
“Na Madina 30k yace a bashi, na ki kuma 15k sai na Leila ne be fada ba, ina jin nata sai idan ta je din kamar yadda ya bukata”
 
Da mamaki Momy take kallon Hajiya Saratu.
 
“Da arha haka? Allah yasa dai aikin zai yi”
 
“Ai da ace be iya aiki ba da ba zan batawa kaina lokaci ba, kin san mutanen kauye ba su san darajar naira ba da dan birni ne da kudi zai zurara miki da yawa, shiyasa ai ban taso ba sai da na bashi kudi”
 
“Duk da haka dai zan bada 100k ki kai masa, wata kila zai fi maida hankali yai aikin”
 
“Momy har na Madina za'ayi?”
 
Leila ta tambaya, sai Momy ta kalleta da duba irin wanda yafi kama da harara.
 
“To ko a fasa ne? Sai a kai ki gidan yari kin ga rayuwarki zata kare a can”
 
Shiru Leila rai kamar bata gurin, bata sake cewa komai ba har Momy da Hajiya Saratu suka gama maganar da za su yi. Mikewa tai tsaye ta dauki wayarta dake aje ta fice daga dakin, shiga tai dakinta ta karasa gurin kofar dake sadata da backyard ta bude ta taka a hankali tana kallon harabar, wani iska mai dadi na bugunta. Rumgume hannayenta tai ta kara matsawa zuciyarta cike da tunani kala kala, ta sani abun da Momy ke kokarin aikatawa ba abu ne mai kyau ba, amman babu yadda zata yi ta hana hakan faruwa domin ba zata tonawa kanta asiri ba. Hannayenta dale rungume ta saki ta duba wayarta dake ringing. Ganin Number Ali ya saka ta saurin picking.
 
“Hello”
 
Ta fada da muryar dake nuna akwai damuwa ko akasin haka a tare da ita.
 
“Leila kina gida?”
 
“Eh ina gida”
 
“Na shigo, ina compound ina son magana dake”
 
Haka nan kawai sai ta ji gabanta ya fadi for no reason.
 
“Okay”
 
Ta sauke wayar, sannan ta dawo cikin dakinta ta nufi gurin windows dinta ta daga curtains dinta sai ta hango shi tsaye jikin motarsa yana kallon kofar falon. Ba al'adarta bace saka mayafi idan zata fita, hakan ya saka bata saka komai ba ta fito dakin holding her phone kanta ko dankwali babu, sai dai tana sanye da gown doguwa har kasa, tana saukowa downstairs din karaurawar gida tai ta kara alamar akwai bako a bakin kofar, karasawa tai ta nufi bakin kofar ba tare da tunanin komai ba ta kai hannu ta bude. Sai tai arba da jikan Baaba tsaye sanye yana kallon kofar kamar yana jiran shigowarta.
 
“Hajiya..”
 
Ta amsa a tsorace gabanta na tsananta faduwa.
 
“Na'am”
 
“Ya gida ya kowa?”
 
“Lfy Kalau”
 
“Ko Hajiya tana ciki?”
 
“Eh”
 
Ta amsa tana hade yawu, sannan ta saki kofar wanda hakan ya bashi damar shigowa, sai ta juya da sauri ta haye sama, cikin tashin hankali ta tura kofar dakin Momy ta shiga.
 
“Momy ga jikan Baaba nan ya zo?”
 
Kusan a tare Hajiya Saratu da Momy suka kalleta.
 
“Miya zo yi to?”
 
“Ban sani ba”
 
Ta amsawa Hajiya Saratu jikinta sai rawa yake. Momy ta tashi tsaye
 
“Ki kwantar da hankali, abun da nake fada miki kenan, iyalanta kawai idan suka zo gidan nan damuwa suke kina shiga tashin hankali balle kuma a ce an kaiki kotu ya kike tsamanin komai zai kare kenan?”
 
Leila ta kasa cewa komai, Momy ta ratsa gefenta ta fito daga dakin ta sauko kasa fuska a hade tana kallonsa kamar wanda tai arba da bakin maciji. Shi kam yana ganinta abun ka da mutumen kauye dake da girmama mutanen da sanin darajarsu sai ya mika mata gaisuwa daga inda yake duke bakin kofar.
 
“Lafiya Kalau, ya mutanen can?”
 
“Kowa Lafiya Kalau yake Hajiya, ya hidima da jama'a?”
 
“Lfy kalau”
 
Amsa masa take kamar an mata dole.
 
“Daman na ce bari na zo na ji ko an samu wani labari akan Baaba ne?”
 
“Ba a samu komai ba, ina ganin maganar ai tana gurin police ko? Can ya kamata ka rika zuwa kana bincikawa, ba nan ba”
 
“Ai ina zuwa can kusan duk bayan kwana biyu idan na shigo garin nan sai na je na bincika ko an samu wani abu amman ba wani labari”
 
“Muma muma bincikawa kuma abun da suke fada muku shi ake fada mana, na san idan an ganta za su kiraka, ba sai ka wahalar da kanka kana zuwa nan ba”
 
Ya kalleta sai kuma yai saurin sauke ido kasa saboda matsayinsa da nata ba daya ba.
 
“Toh Hajiya Allah yasa mu ji alheri”
 
“Ameen, a gaishe da mutanen gida”
 
Bata jira abun da zai ce, ta tura kofar ta rife falon, sannan ta nufi upstairs, tana shiga dakinta ta haw Leila da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba.
 
“Idan kin ga iyalan matarki sai ki rika wani dari dari, ke da kanki ma baki isa ki yi magana da shi ya wuce ba, sai ki wani dawo kamar mai jin tsoro ki kira ni”
 
Daga nan Hajiya Saratu ta dora da nata, sai dai hakan be saka Leila ta tanka ba, sai kawai ta juya ta fice daga dakin. Da fargaba da ita gurin kofar ta bude ta fita zuwa gurin motar Ali dake fake a kusa da ta Momy. Karasawa tai sai ta zame shi zaune cikin motar domin ya ya soma gajiya da jiranta ya shiga motar ya zauna. Front seat ta bude ta shiga ta zauna sannan ta rufe kofar ta kalleshi.
 
“Sorry na barka kana jira”
 
“Karki damu, you can take your time, idan akwai abun da kike yi zan iyar jiranki ki gama sai mu yi maganar”
 
Ta masa kallo mai cike da alamar tambayoyi.
 
“Magana zamu yi?”
 
“Yes, shiyawa ai na kira ki jiya na tambayaki zaki shigo kika ce min eh, amman ba ki shigo ba”
 
“Bana son zuwa ne sai dole, domin bana son ganin abun da zai bata min rai a yanzu”
 
Ya dan yi jimm sannan ya sake kallonta ya ce.
 
“Yeah na sani, amman duk da haka be kamata ace kin wuni kin kwana baki je kin duba shi ba”
 
“Zan je anjima”
 
Ta fada atakaice. Numfashi yaja ya aje sannan ya soma magana ba tare da ya kalleta ba.
 
“Na yi magana da Madina, kuma ta fada min komai”
 
Ta kalleshi a dazane kamar wanda tai arba da wani mugun abun cutarwa.
 
“Me ta fada maka?”
 
“Komai da komai Leila”
 
Ta fito mata free, wannan karon yana kallonta with serious face.
 
“Cikin har da kidnapping din data aikata, and now i understand why kika zo gurina kina kuka da fadar wasu kalamai”
 
Ta yi saurin kai hannu ta bude motar ta fita sai ya dakatarsa ita ta hanyar fada mata cewar.
 
“Guduwa, da boye boye ba mafita ba ne a gareki Leila”
 
A take ta fashe da kuka da bata san ta inda ya zo mata ba, sai tausayinta ya kara kama Ali.
 
“Ban aikata da niya ba”
 
“Shiyasa nake son mu yi ma tukar hanci tun yanzu, ina son na fuskanci Talba da maganar, amman hakan ba zai samu ba sai da hadin kanki”
 
“Idan maganar nan ta fita Ali rufe ni za'ayi, kashe ni za'ayi, ka taimaka min dan Allah ka rufa min asiri”
 
“No ba mafita ba ne, domin komai daren dadewa dole wannan maganar zata fita, kuma ina ji miki tsoron abun da zai biyo baya”
 
Ta dafe kanta da take jin kamar zai rabe mata biyu saboda tashin hankali.
 
“Madina ta same ka ta fada maka ne?”
 
“Aa ni na same ta na tambaye ta abun da ya shiga tsakaninku”
 
“Ali ka taimaka min dan Allah, kar Talba da Daddy su ji maganar nan, Talba zai tsane ni, Daddy ma ba zai saurara min ba...”
 
Kuka ya ci karfinta.
 
“Look Leila idan har kina son na taimaka miki to ki fara taimakonki, abun da duk mutum be aikata shi da ganganci ba, ba a yanke masa hukunci kwatankwatan wanda ya aikata hakan da gangan, idan har an yi bincike an tabbatar akan kuskure kika hukuncin da za'ayi miki diya ce kawai”
 
“Ali ba zaka gane halin da na jeda kaina ba, i regret everything wayyo Allah...na... ”
 
Ta kara fashewa da kuka.
 
“Miyasa Madina zata min haka? Miyasa mutanen dana yarda da su suke nisantata ne? Ali zan iya mutuwa i will lose everything...”
 
“No idan zaki kwantar da hankalinki ki yi tunanin abun da na fada miki, Madina ta tsorata da sakon da Momy ta aika mata, which means Momy zata ita aikata wani kuskuren a kokarinta na faranta miki, duk wata illa dake tattare da hakan ba zata gani ba, so da yawa abubuwan da kake ganinnsu a wahala masu sauki ne, I'm here to help, tsakani da Allah na damu sosai a lokacin da Madina ta fada min”
 
“Ba da gangan na aikata ba”
 
“Shiyasa zaki samu mafita ai”
 
Ta share hawayenta da sauri ta girgiza masa kai.
 
“No, ba zan bar duniya ta san da wannan ba, mutumcin gidamu da na mahaifina zai zuba, rayuwar da nake mafarki ba zan taba samunta ba”
 
“Miyasa zuciyarki ke raya miki zaki iya boyewa Allah? Baki yi tunanin zai iya jefaki a wani tashin hankali ba saboda wannan abun da kika aikata kuma, Leila ki daina tunanin irin wadannan abubuwan domin idan ba a yi hukunci a nan ba, za'ayi a gaban Allah”
 
Ta kalleshi hawaye na mata zuba kamar ba gobe tana girgiza masa kai.
 
“No i don't want to lose everything, tsoro nake ji, Talba ba zai aure ni ba, wata kila Daddy ba zai sake saurarena ba, shikena rayuwata zata juye, ban aikata da ganganci ba, ban yi da niyar kashe ta ba, kuskure ne Ali.. Kuskure...”
 
Ta bude motar da sauri ta fita tana kuka, ta gilashin motar yake kallon yadda ta nufi kofar falon. Har cikin kahon zuciyarsa yake jin tausayinta, ya san yadda ake ji idan ka aikata wani abu akan kuskure balle kuma kisa. Ya san duk yadda zai yi kokarin fahimtar da ita a yanzu ba fahimta zata yi ba. Bakinsa ya cikawa iska ya busar sannan yai baya ya juya motar ya fice daga gidan.
After ya koma gida yai ta kiranta taki dagawa, daga karshe ma sai ta kashe wayar gaba daya, washe gari ma haka yai ta kiranta bata dagawa.
 
 
 
***   ***    **
Leila na kwance dakinta after sallah la'asar Momy ta turo kofar dakin ta shigo, sai ta tsaya daga bakin kofar tana kallonta.
 
“Zan koma asbitin ni, ko zaki je?”
 
“Aa”
 
Ta amsa daga kwance da take, sai Momy ta tura kofar dakin ta rufe sannan ta karasa kusa da ita saman gadon ta zauna tana kallonta.
 
“Leila me ke damunki? Na ga yanayinki kamar akwai damuwa! And yaushe rabonki da ki je duba Talba?”
 
Ta dago da idanuwanta da su kai yi zurfi ta kalli Momy, bata son ta fada Momy maganar Ali, kar shi ma tace za ayi masa wani abun.
 
“Bana son ganin yarinyar nan ne”
 
“Leila wani lokacin kina ba ni mamaki, kamar ba yar boko ba, yanzu Fisabilillahi Aminatun ce  abar zaki yi ma zuciya da Talba har ki bar mata shi? Taya ke da kike birni yar kauye zata baki tsoro?”
 
“Ba wai na bar mata ba ne, Momy kin san yadda nake son Talba, bana son ganinsa da kowa, sai dai kuma ina jin kamar... ”
 
“Kamar me? Kar ma ki fara ke kadai kike da Talba, ki saka wannan a ranki, na san idan mahaifinki ya ji ba zai jidadi ba, shi kansa Talba ba zai jidadi”
 
“Zan je anjima”
 
“Good, sai kuma abu, za'ayi Madina ta saura zanen nan? Idan an kawo?”
 
“Ni ma ban sani ba Momy, amman da zaki yarda Momy da an canja a yi mata wanda ba zata iya fadar komai ba”
 
“Mun riga mun gama wannan maganar, zuwanki ne kawai zai zama aiki domin ina jin tsoron hanyoyin yanzu, gashi Saratu ta fada min daji ne gurin sosai”
 
Leila bata ce Uffan ba sai tunani take ta yi. Momy ta mata kallon rashin yarda.
 
“Akwai dai abun da yake damunki Leila, ki fada min idan akwai wata matsalar”
 
“Babu komai Momy”
 
“Okay, ina fatar hakan”
 
Ta mike tsaye ta fara tafiya.
 
“Mun yi magana da Hajiya Tsahara, next week zaki tafi Abuja a can za ayi mikin gyara jiki, ba son nake a canja time ba”
 
“Okay”
 
Ta amsa, sannan ta bi Momy da kallo har ta fice. Bata son zuwa asibitin ne saboda maganar da sukai da Ali, ta san yadda Ali da Talba suke basa boyewa juna abu, gani take idan ta je Talba zai mata maganar ne. Ta dayan bangaren kuma tana ganin kamar ya daga mata kafa ne saboda yana asibiti wata kila yana dawowa zai fadawa Daddy. Zabura tai saboda yadda Amal ta turo kofar ta shigo da saurinta, domin Momy na kasa tana jiran saukowarta su koma asbitin tare.
 
“Gashi wani yace a baki sako”
 
Leila ta gyara zamanta tana kallon Envelop din dake hannun Amal.
 
“Waye waya baki?”
 
Ta tambaya a tsoratace tana kallon Envelop din.
 
“Wani ne dazun da muka taso daga makaranta, sai ya tsayar da driver na yana cikin mota ya ba bashi yace ya bani wai na baki”
 
Cike da karfin hali ta mika hannu ta karba, sai Amal ta kalleta kamar ta tambaye ta miye a ciki, sai kuma ta juya ta fice ba tare da tace mata komai ba.
Amal na fita, Leila ta tashi ta rufe dakin ta dawo ta dauki envelop din ta bude, a tunaninta wani abu ne a ciki sai ta yar kasa kadan a ciki da kananan duwatsu. Cige baki tai
 
“Wato Madina ba zaki daina ba ko?”
 
Ta furta sannan ta nufi bandakunta ta juye kasar ya dawo dakin ta kwanta.
 
 
 
AMINATU POV.
 
“Wani zai iya shigowa”
 
Ta fada tana kallon kofar cike da tsoro, sai yai murmushi ya cire hannunsa daga jikinta ya koma ya zauna yana kallonta.
 
“Idan likita ya sallame ni, tare zamu koma gida gurin Momy ko?”
 
Ta kanne kafada.
 
“Aa ni gurin Mama zan zauna”
 
Hannunsa ya mika mata, alamar ta zo, sai ga Ali ya turo kofar dakin ya shigo hannunsa rike da takardu. Aminatu ta sauke kanta kasa, dan murmushi yai yana kallon Talba.
 
“Jiki yayi kyau”
 
“Idan ina fada maka na ji sauki kai da Daddy sai ku ki yarda”
 
“Ba yarda ne bana mu yi ba, gata ne ake nuna maka da kulawa”
 
Yayi murmushi.
 
“I see”
 
Ali ya kalli Aminatu sannan ya sake kallon Talba.
 
“Ina son mu yi magana da kai”
 
Talba yai masa alama dake nuna yana saurarensa ba tare data furta ba. Sai ya sake juyawa ya kalli Aminatu.
 
“Or Maybe zai fi idan ka koma gida, but magana ce mai matukar muhimmanci”
 
Aminatu na jin haka sai ta matsa kusa da inda Talba yake zaune ta dauki dankalinta ta fice. Ali ya sauke ajiyar zuciya ya cika bakinsa da iska ya busar.
 
“Ban san yadda zaka dauki abun ba”
 
Talba ya kalleshi with confused.
 
“Miya faru?”
 
Sai kuma yai dan murmushi kadan ya ciro takardar ya mikawa Talba, yana

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login