Showing 240001 words to 243000 words out of 332834 words

Chapter 81 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65671

yai tari da karfi sai jini ya cika Oxygen din dake bakinsa, da saudi suka cire suka zubar da jinin.
 
“Alhamdulillah”
 
Daya daga cikin likitocin ya fada da karfi, da sauri Ali ya juya ya koma ciki, ya karasa gurin Talba cikin farin ciki. Sun kusa awa daya a dakin sannan suka samu komai ya daidaita, likitoci biyu suka fito daga dakin tare da Ali. Sai da suka fito sannan Kabir ya kira Momy ya fada mata a kokarinsa na kwantar mara da hankali yake fada mata cewar komai ya zo da sauki. Sai dai hakan be saka ta iya rike kanta ba saboda tashin hankali sai ta fara kuka. Kabir na jin haka ya kashe wayar ya Kalli Ali dake tsaye yana kallonsa with shock.
 
“Ka kira kawai ka tada musu hankali?”
 
“Dole ne ai za su sani, kuma tun da har hana raye, komai mai sauki ne”
 
Ali ya dauke kai cike da jin haushin abun da Kabir yai ya fice daga gurin, tura kofar Kabir yai ya shiga ya zauna gurin dan'uwansa.
Ali ya nufo Office dinsa, yana shigowa sai ya samu Aminatu tare da matarsa Haulat tana bawa Aminatu  hakuri akan kukan da ita.
 
“Doc ban san abun da ya faru ba, sai kuka take, kuma na yi na yi da ita ta taso mu tafi ta ki saurarata ma”
 
Ali ya kalli Aminatu.
 
“Ki kwantar da hankali yana can kwance ya samu farfadowa daga suman da yai yanzu haka bachi yake ma”
 
Bata ji ce komai ba kuma bata fasa kukan da take ba, jikinta da muryarta sai rawa suke sosai.
 
“Miya samu Talba?”
 
“Accident yai amman dai da sauki sosai gaskiya, domin ya farfado”
 
“Subhanallahi Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un garin ya?”
 
Ali ya labarta mata a abun da ya faru sannan ya kara da nasa labarin saboda ya kwantar da hankalin Amina.
 
“An yi arziki sosai, kuma yana farkowa sunan Aminatu kawai yake kira sai da muka, masa allurar bachi sannan muka samu salama”
 
Fadar hakan be saka Aminatu ta daina kuka ba, a tunaninta yana fada ne kawai saboda ya kwantar mata da hankali ba wai dan haka din ta faru ba. Tissue ya dauka ya mikawa matarsa ta zara ta mikawa Aminatu.
 
“Share idonki sai ku tafi gida, Maybe anjima da dare ya farka sai a dawo dake ki ganshi, Haulat ki ja ku tafi Momy tana nan Zuwa saboda Kabir ya fada mata, kuma idan ta zo zata iya blaming din Aminatu, Talba kuma ba zai ji dadi ba idan wani abu ya faru”
 
“Haka ne gaskiya, tashi mu je Aminatu”
 
Ta mike tsaye rike da tissue ta kasa share hawayenta sai dai ta rage sautin kukan da take, har yanzu tsoro take ji ji take kamar Ali yana boye mata ne kawai, waya sani ma ko harbeshi akai saboda ya bi bayan wacan mutumen. Haulat ce ta zari wani tissue ta goge mata fuskarta sannan ta rika hannunta suka fice daga dakin zuwa inda ta faka motarta, suna tafe tana yi ma Aminatu kalaman da za su kwantar mata da hankali har suka isa gurin motar ta bude mata ta shiga sannan ita ma ta shiga mazaunin direba tai ma motar key.
 
Sai da Ali ya tabbatar sun yi nisa sosai sannan ya dauki wayarsa dake kan tebur ya kira Leila, haka wayar tai ringing har ta tsinke ba ayi piciking ba, daman kuma he expect that indai har Momy ta fada mata abun da ya faru, ita kanta Momy ya san tana bukatar kalaman da za su kwantar mata da hankali a yanzu balle kuma Leila. Mikewa yai tsaye yana sake kiran number nan ma ba a daga, sai yai deciding ya kira Madina.
He got lucky ringing biyu Madina tai picking ta amsa sallamar da yai mata murya kasa kasa.
 
“Wa'alaikassalam, Doc Ali”
 
“Na'am ya gida”
 
“Alhamdulillah”
 
“Madina wata alfarma nake son ki min please, na san ke da Leila kun samu misunderstanding, ko kuma na ce ke da Momy, but Leila need you the most tana bukatar wanda zai kasance tare da ita a yanzu ya kwantar mata da hankali”
 
Madina ta aje kofin ruwan dake hannunta da sauri tana tambayar Ali.
 
“Miya faru?”
 
In brief ya labarta mata abun da ya faru, sai ta dafe zuciyarta ta fashe da kuka mai tsanani.
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Dan Allah yana raye?”
 
“Yana da rai, amman yana cikin mummunan yanayi gaskiya, but Alhamdulillah tun da yana da rayuwa”
 
Ta rumtse ido ta kai hannu ta rufe bakinta sannan ta yanke kiran ta mike tsaye ta fara kai da kawo a kitchen din idonta tap da hawaye.
 
“Duk ni na ja komai”
 
Ta sadda kai kasa hawayen suka sauko mata.
 
“Na jefa rayuwar mutane cikin hadari, kuma na jefa rayuwata”
 
Ta durkushe kasa ta fashe da kuka marar sauti.
 
“Dubi abun da ya same shi, all because of me”
 
Ta zauna a gurin tana wani irin kuka mai taba zuciya. Sai kuma tai saurin mikewa tsaye ta share hawayenta ta fito daga kitchen din da sauri ta nufi dakinta, mayafinta kawai ta dauko sai key motar ta fito rike da wayarta ta fice daga falon ba tare data sanar da kowa ba. Motarta ta shiga ta tai mata key tai reverse ta fice daga gidan tana driving tana kuka har ta isa asibitin. Tsakanin asibitin da gidansu tafiya ce da ba zata wuce minti biyar ba, tsakanin unguwar su Momy da asibitin tafiyar 40 minutes hakan ya saka ta riga su kawowa. Number Ali ta kira yana picking ta ce
 
“Talba yana ina?”
 
“ICU kin shigo ne”
 
Bata bashi amsa ba, ta kashe wayar ta nufi gurin daya fada mata, sai da ta isa bakin kofar sannan ta fara tafiya a hankali kamar mai jin tsoro gabanta sai faduwa yake hawaye na sauko mata, hannu ta kai a hankali ta tura kofar dakin tana hade yawu sannan ta juyo ta kalli bayanta ko zata ga wani. Juyawa tai ta shiga cikin dakin dankwalinta na sauko daga saman kanta zuwa kafadarta. Da farko ta yi zaton zata samu Leila a dakin, sai tai arba da Kabir zaune kusa da Talba, wani irin tausayinsa ne ya kara kama kamata, domin kana ganinsa kasan yana cikin mawuyacin hali. Hawaye da suke sauko mata ne suka cigaba da aikinsu, sai ta juya a hankali zata fice without making any sound.
 
“Madina...”
 
Kabir ya kirata sai ta tsaya cak, ta kai hannu ta share hawayenta sannan ta juyo tana kokarin hana wasu hawayen saukowa amman bata samu wannan hadin kan ba. Kallonta yake cike da mamakin dalilin kuka da hawayen da take at first ma ya dauka ko tare take da Leila. Har ta bude baki tai magana sai ta kasa saboda kukan daya ci karfinta, kalma daya idan ta fito bakinta kuka ne zai maye gurbinta. Juyawa tai tana kallon kofar da Momy ta shigo tare da Leila da Amal kowanensu fuska kaca kaca da hawaye, Leila ta nufi gurin Talba da sauri ba tare da ta kula da Madina ba, Momy ce ta tsaya kallon Madina da mamaki.
 
“You? Again ban gargade ki akan shiga lamarin Leila ba? Ban miki iyaka da ita ba?”
 
“Shiiiiiiiii Momy asibiti kike fa, kuma a gaban marar lafiya and you see his condition”
 
Kabir ya fada yana mikewa tsaye. Momy ta riko Madina da karfi kamar wanda ya kama barawo ta fito da ita daga cikin ta jefar da ita waje.
 
“Na gargade ki sau daya, wannan ya zama na biyu karki kuskura yin na uku, makira munafuka”
 
Kabir yayi saurin tare Momy daga marin Madina da take son yi.
 
“Get out of here”
 
“Momy Madina ce fa”
 
Kabir ya fada da mamaki.
 
“Na san ita ce ai”
 
Madina da kuka ya ci karfinta ta juya ta nufi kofar fita tana kuka kamar ranta zai bar jikinta, tana tafe tana hawayen mutane sai kallonta suke, wani bangare na asibitin ta nufa, inda daidaikun mutane suke zama, ta samu wani dakali ta zauna tana ta kuka marar sauti, dan tsagaita kukan tai jin motsin tsayuwar mutum a gefenta dankalin da take zaune.
 
 
 
 
AMINATU POV.
 
Tana shiga motar Haulat sai kuka ya yanke mata, sai dai bata ce komai ba har suka isa gidan, duk kuwa da irin kalaman da Haulat take mata na kwantar da hankali.
Da kanta ta bude motar ta fita ta tsaya jiran Haulat ta zagayo ta bude kofar falon. Kana kallonta ka san tana cikin damuwa, domin fuskarta ta fada ga idonta ya kumbura, yanayin yadda take kalle kalle ma kadai ya isa ya sanar maka akwai tunani a cikin kanta kala kala, har lokacin bata iya gani da kyau ga wani uban ciwon kai da take ji da nauyin jiki. Haulat ta isa bakin kofar ta saka key ta bude sannan ta juyo ta kalli Aminatu.
 
“Shigo ciki Aminatu”
 
Aminatu ta kalli kofar dakin a azahiri, sai dai a badini tunani take idan Talba ya tafi ya barta ya zata yi? Tana da mai mata gata a yanzu sama da shi? Haka zata yi ta rasa mutane masu muhimmanci a rayuwarta, bayan Inna da Baba da yan'uwanta yanzu kuma Talba?
 
“Aminatu?”
 
Haulat ta taba ta ganin kamar hankalinta yana wani gurin dabam, sai ta zabura ta kalleta.
 
“Na'am”
 
“Muje ciki mana”
 
“Amman Talba zai ji sauki dan Allah?”
 
“Inshallah, zai samu lafiya sosai ma, kawai abun da yake bukata addu'a”
 
Tafiyar ta fara sai ta ji ina ma bata fada masa mutumen ba! Da yanzu be fita da gudun nan ba, da duk hatsarin nan be afku ba, da yanzu ya kaita gidan Hajiya Laraba ko kuma gidansa. Sai da ta shiga cikin falon sannan wani sanyi da lullubeta sakamakon zazzabin da take ji da ya hadu da sanyin ac dake falon. A maimakon ta zauna saman kujera sai ta zauna masa ta rakube ta rungume hannayenta.
 
“Haba dan Allah ya zaki zauna kasa kamar wata marar gata? Tashi ki zauna akan kujera mana”
 
“Nan ma ya isa”
 
Ta fada tana yin kasa da kanta. Haulat bata sake ce mata komai ba gudun kar ta takura mata. Sai kawai ta nufi hanyar bedroom dinta, sai da tai kusan minti talatin da shiga sannan Aminatu ta tashi ta nufi kofar falon ta bude a hankali ta fito harabar gidan tana kalle kalle sai dai ba kallo irin na duba tsari da kyau gida ba, kallo na tunanin makomarta da rayuwarta ta baya. A dare daya rayuwa ta canja mata, a wacan daren komai na rayuwarta ya zama tahiri, a wacan dare ta rasa kowa da kowa nata. Kamar a yanzu komai yake faruwa haka take ji a cikin kanta abubuwan da suka faru a baya suka dawo mata sabbi suka tsaya mata a rai. Kuka kuma yai mata nisa, tana ta nemansa ya ki ziyartar idanuwanta, a maimakon kukan sai ta samu kanta da murmushin bakinciki.
 
Wai shakikanta a yanzu duk sun tafi sun barta, mutumen dake neman farincikinta kuma a yanzu ba shi cikin hankalinsa, zai dawo gareta ko kuma shi ma rasa shi zata yi? Bakincikin rashin uwa da uba dabam yake, wani kalar babi ne da ke budewa kansa sashe a zuciyar baya, karyar duk wani mai jini da jijiya ne ya fassara maka yadda ake ji matukar be tana rasawa ba. Wanda ya rasa uwa ya rasa abokiyar shawara, ya rasa mai tarbarsa da hannu biyu a ko wane irin hali, ya rasa wanda bata kyamarsa kuma bata yarda wani abun ya same shi. Wanda kuma ya rasa uba ya rasa babban jigo, bango majingina, gata mai share hawayen yayansa. Wanda kuma ya rasa duka biyun fa? Anya alkalami da takardu za su isa a bayyana irin bakinciki da damuwa dake tattaren da wannan rashin? Aminatu ta rasa duka kuma ta rasa majinginar da zata raba a tsakanin yan'uwanta maza ta ji sanyin rashin da tai, domin a jarabawar da aka hada mata har rasa su a ciki...
 
Ta sake yin murmushin bakinciki a karo na biyu tana ganin rayuwarta ta baya kamar a video, yan'uwanta da suke tsokanarta da mahaifiyarta da Mahaifinta da yake raye. Sautin muryarsu da hoton fuskokinsu sai suka dawo mata tana komai a zahiri, wannan karon murmushin da take ba na bakin ciki ba ne, domin wacan lokacin take gani a wacan rayuwar a cikin wacan kauyen da Yaya Sanusi ke tsokanarta shi da Yaya Rilwanu. Till Haulat touch her.
 
“Ke Lafiyarki?”
 
Sai ta yi firgigit ta juyo da sauri ta kalli Haulat kamar wanda ta farko daga dogon bachi, har hadiyar yawu take tana maida numfashi da karfi.
 
 
 
*Done with my test, In Shaa Allah, zamu cigaba kamar yadda muka saba. Fatar za a min afuwa🙏 Na san dai Masoyana basa fushi da ni 🥰*
 
 

Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Madina ta mike tsaye da sauri ta juya tana kallon Leila. Sai Leila tai murmushi.
 
“Da gaske? Kukan akan me?”
 
Madina ta dauke kai tana kara goge fuskarta. Leila ta rumgume hannayenta tana kallonta.
 
“Kin san me? Lokacin da Momy tace min kina son Talba ban yarda ba, karyatata na yi, ashe gaskiya take ta fada min amman hauka da kuma yardar da na yi da ke ta hana ni ganin haka, it's very unfortunate a yadda muka ta so tare da kuma irin yardar da na yi miki ace kin butulce min”
 
Madina ta yi murmushi idonta na sake cika da hawaye.
 
“Ke kanki idan aka tambaye ki ya akai kika kamu da son Talba yaushe kika fara sonsa, ba zaki iya fada ba, saboda kamuwa da so abu ne mai sauki kuma mai saurin shiga a rayuwa, Leila Talba yana da kyau da siffar da kowace mace zata so shi, yana kyau, yana da ilmin, yana da kudi, yana da tarbiya da family ma su asali, kuma ya iya kwalliya, so kamuwa da son Talba abu ne mai matukar sauki, kin san mai wahalar?”
 
Leila ta ki ta amsa tana mata ma Madina wani shegen kallo na tsana, Madina da hawaye suka gama wanke mata fuska ta cigaba.
 
“Fitar da so a zuciya, musamman ace ya zauna a inda ba muhallinsa ba, Leila na yi ta jihadin yakar Soyayyar Talba a zuciyata amman na kasa, a duk lokacin da na yi unkurin haka maimakon na samu nasara da kwarin guiwa, sai sonsa ya kara a zuciyata, ina yawan fadawa kaina cewar be kamata ba, amman zuciyata sai ta nuna min ita abun da take so kenan”
 
Ta karasa tana kai hannu ta taba zuciyarta, sai kuma tai kasa da kanta hawaye na sauko mata.
 
“Shi ne kawai hujjarki? Na raina wayonki Madina, taya zaki tsaya a gaban idona kina fada min yadda kike son mijin da kika san an saka min ranar aure da shi? Ashe ki ji kunya ba? Miya kawo ki nan? Waya fada miki Talba ya samu hatsari?”
 
Leila na maganar tana kai hannu tana tura Madina. Madina ta kalleta.
 
“Ali ne ya fada min, saboda yana tunanin kina bukatar wanda zai kwantar miki da hankali a halin yanzu”
 
“Amman a maimakon ni, sai kika nufo Talba saboda shi ne a ranki. Let me warning you today Madina... Karki sake shiga rayuwata, bana son ma zuciyarki ta ayyana miki a rayuwarki, ki manta da wata alaka da ta taba shiga tsakaninmu ta abota, kuma aikin a kamfaninmu daga yau babu shi, daman ai Momy tace saboda ki samu kusanci da Talba ne kika aikata yanzu kuma na yarda”
 
Madina ta yi saurin rikota.
 
“Kar idonki ya rufe Leila, karki zuciyarki ta raya miki abun da ba shikenan ba, kar daga karshe ni da ke mu sauka a jirgin nadama”
 
Leila ta fisge hannunta.
 
“Nadama kam yanzu haka ina kan yi ta, na yarda da na yi da ke 100% na dauki sirrina na fada miki, har ya baki damar amfani da wannan abun da na yi kika kokarin tsorata ni, a yanzu na gano manufarki ta aikata wannan abun saboda ki lalata aurena da Talba, kuma haka ba zai taba faruwa, kuma ina gargadinki tun a yanzu Madina, ki daina abun da kike yi domin kina wasa da halshen wuta ne kawai”
 
“Kar dai ke ma kin yarda da zancen Momy? Kina jin zan iya aikata abun da Momy take zargina da shi?”
 
“Kwarai kuwa, ai ke ce mai wannan wasan boyan, kuma sake gargadinki ki daina domin akuya bata gasa da kura, Talba ya miki nisa kamar yadda kasa tai ma sama nisa. Babu wanda ya san wannan sirrin nawa sai ke Madina, dan haka karki kuskura ki ce zaki maida ni karamar yarinya”
 
“Amman idan lokacin da kuka aikata abun wani ya ganku fa? Idan akwai wani wanda ya samu labarin fa? Leila taya idonki zai rufe a dare daya ki rika min kallon makiyiyarki?”
 
“Saboda ke din makiyiyata ce, ba wannan kawai ba, har sace Aminatu da akai ke kika aikata Madina, kuma kika shirya komai ta yadda ba za a gane ba?”
 
“Me Aminatu tai min da zai saka na yi mata haka?”
 
“Saboda Talba ya aureta...! And if you're thinking the same akaina, kin yi kuskure karki kuskura ki jefa kanki a matsala, domin zan rusa rayuwarki na saka ki yi nadamar haihuwarki da uwarki ta yi, na shafe tarihinki a duniyar nan, Madina kina wasa da halshen wuta ba tare da kin sani ba”
 
Madina ta share hawayenta tana yi ma Leila kallon takaici.
 
“Ke ce kike wasa da wuta Leila, macen da kika san ta san sirrinki in and out ita kike tsaya a gabanta kina fada mata magana son ranki har kina zagin iyayenta?”
 
“To me zaki yi? Fadawa duniya abun da na yi? Won't change anything, kin san dai iyayena ba zasu taba yarda suna raye ba na tafi gidan yari, dan haka ki daina wannan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login