Showing 186001 words to 189000 words out of 332834 words
kwanta gashi nan ma kai sai yanzu ka shigo”
Daddy ya zauna yana kallonsa da fuskar zolaya.
“Kai yaro ne mana, har gobe kamar jariri nake ganinka, kuma ka san ba ka aje yara ba balle ka ce ka girma a wannan sai yaya”
“Ai dai na kusa Daddy a daina min gori”
Daddy yayi murmushi mai sauti yana kallon Talba cike da kauna, kana ganin fuskarsa ka san ba karamin farinciki yake ji ba idan yai arba da dansa Talba.
“To ya aikin? Ango”.
Talba yayi dariya.
“Alhamdulillah, Daddy ka san maganar yarinyar da na taba maka? ata dawo gidan nan da zama?”
“Yes yes miya faru?”
“Zata dawo din ne yanzu, ina son na sakata a makaranta, domin a can ba karatu take ba”
Daddy yayi murmushi da shi kadai ya san ma'anarsa zuciyarsa na raya masa wani abun.
“Mu'az, ba matsala kana da ikon kai duk abun da kake so a gidan nan”
“Na gode Daddy, bari na barka ka huta, sai da safe”
“Allah tashe mu lafiya”
“Aamee”
Ya amsa sannan ya fice, tafiya yake kamar wanda baya son taka kasa har ya isa bangarensa, yana shiga ya cire dogwar rigar jikinsa, ya kashe wutar dakin sannan ya gabatar da azkar din kwanciya bachi ya kwanta. Bachi yai mai kyau kuma mai dadi kusan rabin mafarkina na Aminatu ne, abun da be taba ba, domin ko a lokacin da take asibiti be taba mafarkinta ba. Amman a yau yayi mafarki event though ba zai iya fadar yadda mafarkin ya zo masa ba, he saw her kuma ya ganta cikin farinciki kusan abun da yake mata fata kenan.
Washe gari da wuri ya shirya saboda yana da meeting, hakan yasa be tsaya gida ya karya ba, sai dai saurin da yake ba hana shi ya gaisa da Momy dake aikin hadawa Daddy breakfast sannan ya fito ya shiga bangaren Daddy ya gaisa da shi. Daman komai saurin da yake baya fita sai ya gaisa da Momy, Daddy ne wani lokacin baya tsayawa gaisawa da shi saboda baya son shiga bangaren idan ba tashi ba.
Misali takwas da rabi shigo kamafanin suka shiga meeting da tara da goma saura suka fito. sai sha biyu ya hada ma kansa abun karyawa daman can ba mutum ne mai cin abincin tun da safe ba, kuma ba lallai ne idan ya tashi ci ya ci mai nauyi ba, and each and every morning sai an kawo sabon bread. Misalin karfe biyu da sun fito daga sallah Azahar yana zaune office dinsa yana wani aikin wayarsa tai ringing. Yana kallon sunan da yai appearing a screen din wayarsa na Hajiya Laraba yai murmushi daman he wanted to call ya ji muryar Aminatu amman yana jin nauyi da ma ace kakace ita baya kunyarta zai iya kira kai tsaye yace ta bawa Aminatu.
“Salamu alaikum”
“Wa'alaikumussalam Talba ya gida?”
“Lafiya Kalau Alhamdulillah”
“Na ce, baka kawo Aminatu ba har yanzu”
Ya dan yi shiru for few seconds, yana tunanin abun da take fada.
“Na'am?”
“Aminatu nace har yanzu ba ta dawo ba?”
“Fita tai?”
Ya bukata yana aje biron hannunsa.
“Ban gane ba, ba jiya ka aiko ka ce ta zo ta karbi sako ba?”
“Ni...!”
Ya nuna kansa kamar tana gabansa.
“E....”
Ta fada masa yadda akai da kuma hanata da mai gidanta yai ta kira shi. Talba ya mike tsaye da sauri.
“No wait wait.... Har cikin gidan aka shigo ko kuma waje?”
“Aa waje ka tsaya”
“I'm not the one Hajiya, ba ni ne na zo ba, rabona da gidanku tun shekaran jiya da na zo muka gaisa da ita, idan ni ne ai dole zan shigo na gaisa da ke, ya zako bari ta fita ta gana da wani da baki da tabbacin ni din ne ko aa kuma har akai yanzu baki kira ni ba? Why?”
Ta tambaya a mugun fusace da wata kalar murya da be taba sanin yana da ita ba, gaba daya ma ya manta da ita din yayar mahaifiyarsa ce.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Wallahi na yi tunanin kai ne sabo... ”
Bata karasa ba yai wurgi da wayar da mugun karfi.
“Damn it....! Why would someone do such things to innocent girl? Why?”
Ya dafa kansa ya shafa fuskarsa da mugun karfi, wani abu be taba faruwa da shi ya ji ransa yayi mugun bachi kamar haka ba. Watsi yai da tarkadun da suke saman teburin, ya daga kafarsa sama ya buga kasa da mugun karfi, da saurin dauki makullin motarsa ya fice daga office da gudunsa, abun da be taba yi ba a tahirin kafuwar kamfanin, duk inda ya bi kauce masa ake wasu kuma suka tsaya kallon ikon Allah, wanda ke shigowa office tana tafiyar kasaita kamar mai tausayin kasa yau shi ne ke fita daga kamfanin da gudunsa. Yana shiga motarsa yai reverse a hanzarce, ya fisgeta da mugun karfi kamar an biyo shi.
________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kamar wani aljani haka ya isa gidan Hajiya Laraba, shi kansa ba zai iya fadar yadda akai har ya kawo kansa gidan ba, ya san dai ya shiga mota ya fisgeta da karfi, adadin gudun da yai kam be sani ba, kawai ya samu kansa a kofar gidan ne and he can't wait har a bude masa gate ya shiga da motarsa a waje ya faka ya fito da sauri ya shiga cikin gidan, key din ma a jikin motar ya barsa all what he know is ya rufe motar. A kofar shiga falon ma be tsaya an masa izini ba ya tura ya shiga ko sallama babu. A tsaye ya samu Hajiya Laraba waya makalle a kunnenta tana kuka.
“Da wa kike waya?”
“Abban su Baby ne”
Ta fada bayan ta sauke wayar, sannan ta zauna.
“Allah yasa yarinyar nan tana cikin koshin lafiya, Wallahi duk daukata tana gurinka ashe ba kai ba ne, ban san waye ba, Allah yasa ba kidnapping dinta za a yi ba”
“Tun farko Hajiya ya kamata ki bincika, ko da nine ya kamata ki tabbatar kamin ki barta ta fita, kuma da kika ga ta dade bata dawo ba sai ki kira waya ki tambaya, tsakani da Allah idan yarki ce zaki mata haka? Waya san su waye? Me suke bukata? Meye manufarsu? Wane hali take ciki? Gashi har an kwana an wuni”
Ya fada cikin wani irin bacin rai har kalar idanuwansa na canjawa, farin ciki ya rine zuwa ja, da karfi ya yarfar da hannunsa ya cige bakinsa. Can kuma ya juya ya fice daga dakin ya bar Hajiya Laraba tana kuka hankalinta a tashe. Gurin mai gadin ya nufa fuska babu annuri.
“Kai malam kasan wanda ya dauke ta?”
“Wallahi Wallahi ba zan iya gane shi ba, saboda ya saka facing cap kuma da mask a fuskarsa, amman fari ne sosai kamar kai”
Ya fada yana karawa da rantsuwa, a take Talba ya dauke shi da mari.
“Wane irin mai gadi ne kai? Baka san ka yi bincike kamin ka kirata ba? And na taba zuwa na ce ka kira min ita ba tare da na shigo ba? Miyasa ba kai tunanin haka ba?”
“Dare ne ranka ya dade ba zan iya gane cewar kai ne ba ko ba kai ba, dab Allah a gafarce ni, ya kwankwasa kofar kawai yace na kira masa Aminatu na ce mata in ji Talba tai sauri zai bata sako, ni kuma ban yi tunanin wani mugu ba ne, sai na shiga na kirata”
“Okay yayi kyau, idan wani abu ya samu yarinyar nan na rantse maka sai ka yabawa aya zakinta, waya sani ko da kai aka hada baki...”
Yana fadar hakan ya juya ya koma cikin gidan Mai Gadin ya bishi yana kuka yana bashi hakuri amman ko saurarensa be yi ba, falon ya sake shiga sai ya same Hajiya a inda ya barta.
“Akwai hotonta?”
Ta mike tsaye da sauri tana gyada kai ta shiga gallery wayarta ta kamo hoton.
“Amman a waya ne sai dai na tura maka”
“Na fasa wayata just give me your phone”
Be jira ta mika masa ba ya kai hannu ya karba.
“Abban Baby ne Password din”
Be ce mata komai ba, ya juya ya fice da sauri, yana fita mai gadin ya shigo yana kuka yana fadawa Hajiya abun da Talba yai masa. Cikin motar Talba ya koma yana kokarin yi ma ma motar key ya kai idonsa kam wayar, sanye take da atamfa sai farin mayafi ta dan sunkuyar da kai tana murmushi, wani kuma ta dago kan with the same atamfa, wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannunsa ya shafa hoton.
“Oh God, Allah ka kare yarinyar a duk inda take, Allah ka kare min ita”
Ya jinkina da motar ya lumshe ido yana jin kamar ba shi da kuzari a jikinsa. Can kuma ya bude idon yai ma motar key yai reverse ya hau titi, police station din dake yankin ya nufa, yana shiga ya gabatar masa da abun da ya kawo shi sannan ya tura musu hoton, a take suka dauki case din suka mikawa masu kula da bangaren bincike na musamman akan satar mutane da kisa. Juyowa yai ya fito bayan yai musu duk bayanin da suke bukata, zaune yai a motar yana jin kansa na mugun sarawa.
“Aminatu where are you? Why would someone do this to me?”
Ya tambayi kansa tambayar da be san amsar ta ba, sai kuma ya kai hannunsa ya shafa kansa, thinking of that night da yake tare da ita, abun d ya fara fado masa a rai is waye ne wannan mutumen da ya haske su? Kuma yai baya baya daga karshe ya gudu? Miyasa ya haske su? Key yai ma motarsa ya fice daga harabar zuwa asibiti. Ko farkin din kirki be yi ba ya kashe motar ya fito ya nufi hanyar da zata sada shi da office din Ali. And he got lucky fitowar Ali daga theater kenan yana shirin zama Talba ya shigo. Ali na kallonsa ya san ba lafiya ba, domin kana ganinsa ka san ya fita daga hayyacinsa, kallonsa Ali yake har ya karaso ya zauna.
“Tell a bad news...”
“Someone kidnapped Aminatu...”
At first dariya Ali yai with shock. Sai Talba yai masa wani mugun kallo.
“What is funny? Labarin ban dariya na baka? Ko kuma you're happy da hakan ya faru da ita?”
Ali yayi saurin girgiza kai.
“No No No.... Haba dai i was shock kamar ya an yi kidnapping dinta? Why would someone do this to her?”
“Not to her, but to me duk wanda yai haka yayi ne saboda ni... Because Aminatu is innocent, bata da matsala da kowa....”
Ya fada yana saka hannayensa duka biyu ya dafa kansa. Ali ya nufi fridge dinsa ya bude ya dauko ruwa a gora ya mikawa Talba.
“Bana iya cin komai Ali, bana da kwanciyar hankali har sai na san halin da yarinyar take ciki”
“Amman ka kai report din ga police?”
“Daga can nake, ba ni wayarka zan kira PA na”
Ali ya mika hannunsa ya dauko wayarsa ya miko masa.
“Amman kamar ka yi gaggawa? Idan wadanda suka saceta kudi suke so fa? Kasan kuma basa son ana kai case din nan gurin police”
“What if ba kudi suke so ba? What if someone plan all this? Shekaranjiya muna tare da ita, akwai motar data haska mu, idan na taka zan tafi gurin motar sai motar tai baya, idan an tsaya ta tsaya, na kira wayarka amman ba mu samu magana ba, na so nace ka zo ka same ni a gurin so that ko waye mu ritseshi, sai kawai suka ja motar suka bar gurin da gudu”
Ya karasa maganar yana tuna yadda ta rirrike shi tana fadin tsoro take ji. Ali yayi shiru yana nazari.
“Baka ga kalar motar ba? Kuma lokacin da zaka je baka ka wani na bibiyarka ba?”
“Ban ga komai ba, no har na faka motar waje na shiga cikin gidan ban ga alamar ana bibiyata ba, sai a lokacin da muka fito na rika hannunta sannan aka kunna fitilar motar aka haska mu, sai a lokacin ma na lura da motar a gurin”
Ya shiga contact din Ali ya nemo number PA dinsa, daman Ali yana da number PA din da wasu family members na Talba. Talba ya kira line PA nasa, bugu biyu ya dauka cikin ladabi.
“Jamal ka duba office dina zaka ga wayata somewhere in the office a kasa, ka cire sim din ka siyo min sabuwar waya ka kawo min gida yanzu nan”
“To Ranka ya dade”
Talba ya kashe wayar sannan ya dorata saman tebur din.
“Ka fasa wayarka ne?”
“Yeah”
Ya amsa yana hade yawu tare da aje numfashi da karfi. Ali kallonsa yake yana mamakin yadda ya shiga damuwa haka, sam be taba ganin abokinsa a cikin irin wannan fushin ba sai yau, ya san Talba na da saurin fusata amman ba kamar wannan karon ba.
“Ka fadawa Leila inda Aminatu take?”
Ali ya daga hannayensa.
“That's it, kullum Leila ce first wanda kake fara zargi akan komai”
“No she's my second suspect, Kabir is the first one”
Sai a lokacin Ali ya zauna da mamaki yake kallon Talba.
“Kabir fa kace?”
“Yes ya dawo gida before na dawo, and Amal tooo ta fita a wannan daren, leila ma zata iya fita kuma ta hana mai hadi ya fada min komai, and Kabir was the first person da ya fara kirana da ango a daren nan”
“No look karka zama mahaukaci mana Talba? Me zai saka Kabir yai maka haka? Think about it mana”
“I don't know kamar yadda ban san manufar wanda ya dauke ta ba, and you too because you're the only one dana fadawa inda Aminatu take, maybe cikin labari ka fadawa Leila ba tare da tunanin zata yi wani abun ba”
“Nooo har abada, ba zan taba sirri da kai na kwashe na fadawa Leila ba, god forbid, I'm always on Leila side amman ba zan fada mata wannan ba”
Talba ya kai hannu yana taba hancinsa tare da lumshe ido.
“Leila can do this, maybe Kabir ya fada mata”
“Please Talba, wacan karon ma ka zargi Leila, karka ce zaka zarge ta ma a wannan karon wannan rashin adalci ne...”
Talba ya mike tsaye cike da fusata.
“Don't tell me what to think, kai zan zarga? Ina da bashin gaba da wani ne da zai sace Aminatu? Duk wanda ya aikata wannan abun nan yana kusa da ni ne, kuma ba zan kyale ko waye ba”
Yana kaiwa nan ya mari kujerar daya tashi a kai sannan ya fice fuuu kamar walkiya. Ali na kiransa ko saurarensa be yi ba, Ali yayi saurin daukar wayarsa ya shiga neman number Kabir, bata wani dade tana ringing ba Kabir ya dauka.
“Hello”
“Kabir kana ina?”
Kabir dake zaune yana duba laptop dinsa ya dan yi fuskar mamaki.
“Gida...ya akai?”
“Dan Allah ka bar gidan for now”
“Saboda me?”
“Kawai ka fita dai”
“Okay”
Ya amsa sannan ya sauke wayar, ya tashi da sauri ya dauki keys dinsa ya fice. After Ali ya kira Kabir ya kira Leila sai dai har wayar ta gama ringing Leila bata daga ba, da sauri shi ma ya nufi inda keys dinsa suke ya dauka ya fice.
MADINA POV.
Bata san da fitar Talba daga kamfanin ba har sai da ta kammala aikinta ta doshi gurin sai ta same shi a kulli, tsaye tai tana mamakin yadda akai ya tashi daga aiki da wuri haka kuma ace har sekatarinsa ya rufe office din. Wani irin faduwar gaba ta ji sai ta juyo ta dawo offices dinsu kasancewar ba ita kadai ba ce a office din kusan su bakwai ne sai dai kowa da bangarensa kuma an sakawa kowa shamaki.
Nata teburin ta nufa ta dauki jakarta da sauran takardun tai musu sallama sannan ta fito, tana tafe tana sake sake a ranta, har ta shiga mota tunani take yi. Tafiya tai mai nisa har sai da ta kusa isa gida sai kuma ta juya motarta ta dauki hanyar gidansu Leila, daman tana son magana da ita tun a jiya saboda tace akwai abun da take son ta fada mata. Horn biyu tai aka bude mata kofar ta shiga tai farkin a harabar sannan ta kashe motar ta bude ta fito ba tare da jakar ba. Tana gyara mayafinta ta nufi entrance din hannu ta kai ta knocking a yayin da ta isa bakin kofar daki. Mairo ce ta bude mata sai Madina ta sakar mata murmushi ita ta mayar mata da murmushin tana mika mata gaisuwa, daman suna yabawa da halinta domin bata da jin da kai kamar Leila, gashi tana sakar musu fuska, Leila kam ko gaisuwa suka mata ba zata amsa ba balle har su ga murmushinta.
“Leila na ciki?”
“Eh tana ciki sannu da zuwa”
“Yauwa sannu da aiki”
A inda aka tanada domin aje talkami ta aje takalmin data shigo da su, sannan ta shigo cikin falon tare da daga kanta sama tana kallon Amal dake saukowa sanye da uniform din makaranta, da alama bata dade da dawowa daga makarantar ba.
“Ya Madina”
“Na'am Amal ya kike?”
“Lafiya kalau, bari na kira miki Leila”
Cewar da Amal tai zata kira mata Leila yasa ta fasa zuwa dakin Leila kai tsaye, sai ta zauna a falon tana jiran fitowarta, Amal kuma ta juya da ta koma sama, sai da ta sanarwa Leila sannan ta sake fitowa kamin ta karasa saukowa ta ji ana danna door bell din da karfi abu ba a taba ba, domin Momy bata son karar door bell yai yawa, da sauri ta nufi kofar kamin ta karasa hawa har da dukan kofar ake.
TALBA POV.
Yana isa cikin gidan yai fakin kusa da entrance