Showing 228001 words to 231000 words out of 332834 words

Chapter 77 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65566

iso kofar gidan, sai ya danna horn aka bude masa,  ya shiga har gaban entrance din ya faka motar ya bude da sauri ya fita ya shiga knocking din kofar da karfinsa. Babban dan Ali ne ya bude kofar mai shekara bakwai, yana ganin Talba yai saurin gaishe shi.
 
“Daddy ina kwana”
 
“Lafiya Kalau Sadiq, shiga ka ce ma babanka yana da bako”
 
“Toh”
 
Ya juya da sauri ya koma ciki, Talba ya dawo cikin motar ya kashe ac, ya juyo yana kallon Aminatu dake ta faman sauke ajiyar zuciyar kamar zata tashi sama saboda kukan data sha. Hannunsa ya kai ya kama hannunta ya rike yana kallonta kamar zai cinye ta.
 
“Karki sake yarda ki kebe daga ke sai Leila, bana son wani abu yana faruwa”
 
“Bana son wannan matar bana kaunarta”
 
“Shiiiiii”
 
Ya fada yana kai hannunsa ya bakinta.
 
“Ki daina fadar haka, ki da ita dole me ku ko yi zama da juna, domin a karkashina zaku zauna, dole ne ku hada kai ku kaunaci junanku, bakinki ya daina furta irin wannan irin wannan maganar, ita ma zan yi magana da ita”
 
“Gori fa ta min tace min, wai ya na ji lokacin da aka min fyade... ”
 
Ta kara fashewa da sabon kuka. Gana daya sai Talba ya ji jikinsa ga mutu, he never thought Leila zata iya yi mata irin wannan maganar.
 
‘Why Leila miyasa baki jin magana ne?’
 
Ya fada a ransa yana jin haushin abun da tai, kamin ya fita daga motar ya ganin Ali daya fito da sauri ya daso inda ya aje motar.
 
“Allah yasa dai lafiya”
 
“Ina lafiya Leila ta taba min Shalele, N san ba kowa ne likita ya fito ba a yanzu 7 ba bata yi ba, dan Allah ka duba min ita”
 
Ali ya karasa gefen da Aminatu take ya bude motar, sai Aminatu ta dago ta kalleshi tana hawaye.
 
“Subhanallahi miya faru?”
 
“Zamu yi magana daga baya, yanzu dai so nake a dubata, ayi mata hoto a duba kanta idan bata samu matsala ba”
 
Har Ali yayi kamar zai yi magana, sai kuma na hadewa, tunawa da yadda Talba yake daukar zafi akan Aminatu.
 
“Okay, but yanzu zan rubuta mata magani, hoton anjima idan masu yi sun fito sai a kaita sh dauki hoton”
 
“Rubuta min”
 
“To ka shigo da ita ciki mana”
 
Talba ya leka fuskar Aminatu.
 
“Zaki fito?”
 
Ta lake kafada, alamar aa.
 
“Bana son ko'ina ni ka kai ni gurin Mama”
 
“Bata so, Rubuta min maganin kawai, kai yi hanzari please ”
 
“Amman Talba...”
 
Sai kuma ya fasa ta hanyar yanke maganar ya nufi cikin gidansa. Ba jimawa ya fito rike da takarda ya mikawa Talba.
 
“Gashi Allah ya sauwake”
 
Talba ya karbi takardar da sauri ya shiga motar, tun kamin ya gama juya motar mai gadin gidan ya bude masa gate ya fice da gudu kamar an koroshi. Ali ya bishi da kallo kamin ya girgiza kai.
 
“Talba zai haukace akan yarinyar nan”
 
Juyawa yai ya koma ciki yana mamakin abun da ya hada su da har Leila ta ji mata wannan ciwon.
 
A gaban wata katuwar Pharmacy Talba ya faka, ya fita rike ta takardar ya shiga, be dade ba ya fito ya dawo cikin motar dauke da ledar maganin. Bude maganin yai ya balla kowanen, ruwan dake motar ya bude ya mika ya kai mata a baki.
 
“Bude bakin”
 
Ta bude ladan sai ya zuba mata ruwan sannan ya saka mata maganin, daker ta hade maganin saboda bata kaunar magani balle kuma allura.
 
“Yi hakuri Shalele daure ki hade”
 
Ya kara kai mata wani maganin, ta bude baki tana ya mutsa fuska.
 
“Ba zan iya shanyewa duka ba”
 
Ta fada ganin maganin yana da yawa.
 
“Idan kin shaye zan kai ki gidana ki huta tukuna sai na kaiki gidan Mama”
 
“Aa ka kai ni gidan Mama yanzu”
 
“fo shanye maganin duka”
 
Ta bude baki ya zuba mata ruwa sannan ya saka mata maganin kana ya kora mata da ruwa. Sannan ya rufe gorar ya mika hannunsa gurin sitiyarin motar yaja motarsa ya dauki hanyar da zata sada shi da gidansa.
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Tana ganin yayi parking a bakin gate din gidan ta gane inda suka zo, juyawa tai ta kalleshi tana son fashewa da sabon kuka.
 
“Ba nan nace ba, gidan Mama”
 
“Okay zaki huta anan kamin mu je can gidan Mama din, kin san idan ta ga idonki haka hankalinta zai tashi”
 
Ya fada sannan ya bude motar ya fita, ya saka key ya bude gate din ya dawo ya shiga da motar ciki, sake fita yai yaje ya rufe gate din ya dawo bangaren da Aminatu take ya bude side dinta.
 
“Fito muje ciki ki kwanta ki huta”
 
“Gidan Mama zaka kai ni”
 
Ya fada hawaye na sauko mata, sai ya resina gabanta ya mika mata hannunsa.
 
“Bani hannunki”
 
Ta mika masa hannunta, sai ya rike ya sakar mata murmushi.
 
“Kin yarda da ni?”
 
Ta daga masa kai.
 
“Good ai ba zan kaiki inda zaki cutu ba, ba nace zan aje ki a nan ba har na tsawon lokaci, no zan ki zauna ki huta idan kin farka zan kaiki gidan Mama ki zauna a can har na gama gyara inda zamu zauna”
 
Ta sauko da kafarta sai ya mike tsaye yana rike da hannunta ta fito motar ya rufe. Rumgumota yai ya kwanto sa ita kirjinsa yana tafiya a hankali har suka isa bakin kofar ya saka keys din hannunsa ya bude kofar falon suka shiga. Dukawa yai ya dauke ta cak ya nufi upstairs, be sauketa ko'ina ba sai akan gadon dake dakin, ya saka hannunsa ya cire mata hijab ya kwantar da ita.
 
“Kwanta ki huta bari na nemo miki abun da zaki ci”
 
“Amai nake ji”
 
Ta fada tana jin zuciyarta na tashi.
 
“Eh saboda kin sha magani ne baki ci abincin ba”
 
Ta sauke ajiyar zuciya da karfi, sai ya gyara mata kwanciyarta ya sumbaci kumatunta sannan ya sauka daga kan gadon. Sai da ya sake bude gate din ya fita da motar sannan ya rufeta ta ciki ya dawo ya cikin motar. Be yi wata tafiya mai nisa ba ya faka gaban wata  restaurent ya shiga ciki waina ya siyo mata da miya da nama, sannan ya dawo cikin gidan. Ko da ya shigo ya samu ta yi bachi sai ya shiga kitchen ya dauki cooler ya saka wainar ya rufe ya dawo cikin dakin. Inda ya saba aje tawul dinsa ya nufa ya dauki daya, sai da ya juyo ya kalleta ya ga idonta a rufe sai ya juya ya cire tufafinsa ya daura tawul din, ya nufi bathroom, shower ya kunna yai jika jikinsa sannan ya dauki sabulun Showel gel a murza a jikinsa. Bayan ya gama wanka ya fito ya daure da tawul dayan hannunsa kuma rike da karamin tawul yana goge jikinsa. Turare ya dauka ya shafa a jikinsa sannan ya fesa body spray, sannan ya juyo ya hau saman gadon, zuwa yai bayanta ya kwanta a hankali ta kai hannunta ya rumgume ta sannan ya sumbancin bayan kanta. Ya saka hancinsa cikin gashin kanta yana shinshina har shi ma bachin ya dauke shi.
 
Bata farka ba sai kusan goma na safe tana bude ido sai ta jita a jikinsa, idanuwanta suka sauka kan kirjinsa da sauri ta tashi zaune ta matsa baya, sai ya bude idon ya kalleta.
 
“Ya akai?”
 
Ta juya baya da sauri ta sauke kafafuwanta daga kan gadon, sai ya kalli jikinsa da idon bachi yai murmushi ya mika hannu ya riko hannunta.
 
“Ni bana bachi da riga a jikina, kuma ai ba wani abu ba ne, ni mijinki ne muharraminki”
 
Ya tashi zaune ya matsa kusa da ita ya rumgumeta ta baya.
 
“Za...za...za..za...”
 
Ta kasa fadi maganar sai rabe mata take ta kasa hada kalmomin ta fada. Sai yai murmushi ya sake ta ya sauko saman gadon, wani dan karamin daki ya nufa ya saka tufafi sannan ya fito yana kallonta.
 
“Yanzu fa?”
 
Ta ki ta yi magana, kuma ta ki ta kalleshi gaba daya kwarjininsa ya kamata, ta kasa daina ganin kirjinsa da idanuwanta sukai arba da su a dazun. Ya rika hannunta yana murmushi.
 
“Ta so muje ki wanke baki, sai ki ci abinci na siyo miki waina kina sonta?”
 
Ta mike tsaye a zatonta hannunta zai ja su shiga ciki, sai ta ji  ya dawo bayanta ya rumgumeta tana turata gaba kadan kadan suna tafiya, har suka shiga cikin bathroom din, har gaban madubin ya tsaya da ita ya ware hannayensa ya matsa toothpaste  a brush daya ya kai mata a baki.
 
“Bude”
 
Ta bude bakin kamar yadda ya umarceta, sai ya saka brush din yan soma murza mata a hakora, sai ya wanke mata bakin tas sannan ya tara hannunsa yana zuba mata ruwa tana kurkurewa ya zubar ya wanke mata fuskarta. Kana ya sake  zuba toothpaste din a jikin brush din ya wanke bakinsa sannan suka fito tare. Saman gadon ya zaunar da ita ya fita ya dauko wainar da plate da ruwa ya kawo dakin ya aje. Yana saka mata biyu ta ce.
 
“Ya isa”
 
Ya kalleta.
 
“Waina biyu? Fushi kike da abincin ne?”
 
Ta yi shiru can kuma ta ce.
 
“Ya ishe ni ne ai”
 
“Waina biyu ba ta da yawa, ki dauri ki ci ko uku”
 
Ya fada yana saka wainar guda biyar a plate.
 
“Sun min yawa”
 
“Tare zamu ci”
 
Ya zuba miya, sannan ya sauko da ita kasa kamar wata yarinya ya saka hannunsa yana deban wainar yana kai mata a baki, kadan kadan take taunawa tana hadewa, idan ta hade sai ya kai mata wata, haka haka dai har ta cinye biyu ganin shi be ci yasa ta kalleshi.
 
“Baka ci ba”
 
“Zan ci amman sai kin koshi”
 
Ta bude baki ya saka mata wainar, sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya cire hannunsa, yana kokarin mikewa tsaye ta ce.
 
“Baka ci ba”
 
“Ni bana son waina daman, bana son cin abu mai nauyi da safe, zan soya kwai na ci”
 
Sai da ya kwashe komai sannan ya dawo ya rika hannunta.
 
“Ta so muje ki soya min kwai kin iya ai ko?”
 
Ta gyada masa kai, ta mike tsaye suka fice daga dakin. Kitchen suka nufa yana rike da hannunta, babu wasu kayan aiki sosai saboda shi kadai yake zaune a gidan kuma ba yawan zuwa yake ba sai idan ta kama. Gas ya fara kunnawa sannan ya kalleta.
 
“Sai ayi me ma?”
 
“Sai an fara fasa kwai an kada an saka magi da komai sannan ake hura wuta fa, sai a soya mai a saka albasa idan ta yi sai a zuba kwan”
 
Ya wara ido yana kallonta.
 
“She kin iya, okay kin ga inda kwai yake can bari na dauko miki magi da sauran kayan sai ki soya min”
 
Ya fada yana nuna mata, sannan ya dauko, mata komai ya aje ya fice daga kitchen din. Bedroom dinsa ya koma ko da ya shiga wayarsa na vibration karasa yai ya dauki wayar, yana dubawa kamin ya kaita a kunnesa.
 
“Hello Momy”
 
“Na'am Talba kana ina? Baka karya ba ka fita ita ma kuma bata karya ba”
 
Ya dan yi shiru kamar mai nazarin abun da zai ce. Sai ta sake aiko masa wata tambayar.
 
“Na yi zaton a gida zaka barta Kabir ya dubata, ka kaita asibiti ne?”
 
“Eh”
 
“Yaushe zaku dawo?”
 
“Ta ce tana son na kaita gidansu Hajiya Laraba ta kwana biyu”
 
“Aa aa dan Allah karka kaita, kasan tana gani ranta zai bace ka dawo da ita gida, na maka alkawari babu abun da zai sake faruwa”
 
“I will talk to her idan ta aminta tana so zan dawo da ita, idan kuma tace sai can zan bar a can ta kwana biyu kamin na gama gyara inda zamu zauna”
 
“Ka biye mahaifinka kenan, haba dai saboda wannan abun daya faru har ya kai ace zaka yi fushi ka dauki mata ku tare a can? Ina da plan din abubuwan da na yi maka, ko na ce na yi musu, ina son idan Leila zata je gyara jikin sai a tafi Aminatun ayi musu komai tare, tarewar ma sai a saka lokaci daya ayi musu walima da komai a tare”
 
“Aa Momy, bana son Leila ta sake kebewa da yarinyar nan, saboda idan Leila ta sake kai hannunta a jikin Matata ni kaina ban san iya abun da zan mata ba, yanzu ma na kyale ta ne saboda Daddy ya gama magana kuma yayi abun da ya kamata, ban yi zaton saboda a wulakanta ta kika bukaci na kawo ta gidan ba, kuma ni ma ban kawo ta saboda a wulakantata ba”
 
Momy ta yi murmushi.
 
“Talba kenan, yau ni kake fadawa haka? Saboda soyayyar yarinyar nan? Allah ya kyauta”
 
Ta kashe wayar yana saukewa kiran Hajiya Laraba na shigowa. Sai ya sake picking.
 
“Hajiya ina kwana?”
 
“Lafiya Kalau Talba ya Auta da jiki?”
 
“Alhamdulillah”
 
“Tana kusa?”
 
“Aa ina wani guri yanzu, ita kuma ta fita tare da Momy”
 
“Da Momy kuma?”
 
“Eh”
 
Hajiya Laraba ta yi jimmm kamin ta tabe baki ta ce.
 
“Idan ta dawo ina son magana da ita, kuma yaran nan suna son zuwa gurinta”
 
“Eh idan ta dawo zan fada miki sai su zo”
 
“To, a dai ji tsoron Allah a rike amana”
 
Yayi murmushi.
 
“Inshaallah”
 
Ya sauke wayar sannan ya aje ya fito daga dakin zuwa kitchen, ko da ya shiga ya same ta tsaye a gurin gas din ta soya kwan na farko ta sauke zubi na biyu kuma yana kan wuta, tana ganinsa tai saurin tare wanda ta soya saboda ya dan kone.
 
“Ga wani nan ina soyawa”
 
“Wanda kika soyan fa?”
 
Ya fada yana leken bayanta, sai ta kara karewa.
 
“Ya dan yi kauri shi ne nake soya ragowar”
 
“To ni ba a min barna a gida”
 
Ya karasa kusa da ita ya janyeta ya duba kwan, sai ya saka hannunsa ya dakon.
 
“Zaki ci wannan ni zan ci na kan wuta, saboda ke kika kona shi”
 
“To ai kai ka cika wutar har ya kone, yanzu ne na rage shiyasa zai so yu da kyau”
 
Ya saka dayan hannunsa ya rikota with serious face.
 
“Ni ba ruwana, ke zaki cinye shi”
 
Ya ware zaro ido.
 
“Mai kauri?”
 
“Eh waya saka yayi kaurin?”
 
“To waya ce ka tafi ta bar ni a kitchen din?”
 
“Waya na amsa, kuma ke kika ce kin iya”
 
Ya fara kokarin saka mata kwan da karfi, ita kuma tana ta son kwatar kanta amman ta kasa, tun tana yi da gaske tana son masa kuka ganin da gaske kwan yake son saka mata a baki har ta gaji ta fashe da dariya, sakamakon cizon data gantsara masa yayi ihu.
 
“Wayyo ta cije ni”
 
Dariya take sosai tana kallonsa kamar ba ita ba. Shi ma dariyar yai yana kallon yadda nata dariyar ya kara mata kyau. Ya rikota ya kai hancinsa a a nata yana goga mata a hankali yai kasa da bakinsa ya kama lips dinta yana sotsawa a hankali, sai ta lumshe ido yana sauraren yadda halshensa yana yawo a bakinta yana sotsar soft lips dinta kamar ya samu sweet. Sai da ta soma jin kauri sannan ta bude idon, ta dago hannunta tai masa magana sai ya saka hannunsa na hagu ya rike mata hannu. Ya cire bakinsa daga bakinta zuwa gurin wuyanta yana lasa yana mata tafiyar tsutsa.
 
“Kwan ya kone”
 
Ta fada tana jin jikinta na wani irin tsammm sigar jikinta na tashi, ganin ba shi da niyar daina abun da yake yi yasa ta matsa baya, hakan ya bashi damar manna jikinta da ginin gurin ya kai bakinsa ya kama kunnenta yana kissing.
 
“Wayyo Yallabai dan Allah ka daina”
 
Ta fada da muryar dake nuna tana daf da fashewa da kuka. Sai ya dago ya kalli kwayar idonta ya sake kai hannunsa ya rika kunkurunta.
 
“Shalele ki daina jin tsoro kinji? Ni mijinki ne”
 
Ya fada murya kasa kasa idonsa kamar ba nasa ba. Sannan ya sake ta, sai kuma ya juyo da sauri ya rike ta ganin tana kokarin barin kitchen din, ya janyota ya motsa da ita kusa da gas din ya kashe wutar ya sauke kwan sannan ya zube na hannunsa ciki ya ya matsa jikin tap ya sakata tsakiyarsa ya raba hannayensa ya wanke hannunsa jikin tap diin sannan ya kashe tap din ya juyo da ita ya dagata sama da dora a gurin ya matsa daf da ita yana kallon fuskarta.
 
“Ba zaka ci kwan ba?”
 
Ta tambaya jikinta na dan rawa tana jin tsoron irin kallon da yake mata, domin ta hangi tashin hankali da fitina a idonsa.
 
“Ya kone”
 
“Bari na soya maka wani”
 
“No”
 
Ya amsa yana kai hannunsa ya dage doguwar rigar jikinta ta fara shafa cinyarta still yana kallon cikin idonta.
 
“Zan yi fitsari”
 
Ta fara kokarin tureshi. Sai ya dauketa ya lakar da ita jikinsa ya sumbancin kirjinta, kokarin saukowa take ya hanata, ta fara tafiya da ita a haka ya suka shiga bedroom din ya sauke ta saman bed shi ma ya hauro saman gadon yana kokarin kwantar da ita.
 
“Ka ce zaka kai ni amin hoto anjima asibiti”
 
“Eh zan kai ki”
 
Ya sake ta ya sauka saman gadon ya rike kansa ya rumtse ido sosai.
 
“Ta so muje ki yi wanka”
 
Ya fada sannan ya bude idon ya miko mata hannunsa.
 
“Na iya wanka ai”
 
“Muje ki yi na gani idan kin iya din”
 
Ta girgiza masa kai.
 
“Ni dai na iya”
 
Be sake ce mata komai ba ya hauro saman gadon ya fara kokarin cire mata rigar jikinta.
 
“To tsaya tsaya zan cire a bandaki”
 
“To muje”
 
Ta rigashi sauka saman gadon ta nufi bandakin, tana shigewa ta maida kofar ta rufe ta saka key. Dariya yai ya kwanta saman gadon yai ruf da ciki ya rumtse ido yana kije baki.
 
 
 
FAHAT POV.
 
Baturiya ta kalleshi ganin tun da ta shigo motar yayi shiru be ce mata komai ba, tana kallon fuskarsa ta san akwai damuwa a tare da shi.
 
“Kamar akwai abun da yake damunka”
 
“Yes”
 
“Miya faru dear”
 
Ya sauke ajiyar zuciya.
 
“Mommy na ce, ta ki amincewa dake”
 
Ta kalleshi da sauri.
 
“Kamar ya?”
 
Ya sake sauke ajiyar zuciya.
 
“Cewa take ba ki dace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login