Showing 288001 words to 291000 words out of 332834 words

Chapter 97 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65597

moving up da rayuwarka.
 
“Sun kashe Baba, da Inna kisa na wulakanci da kaskanci, sun tarwatsa rayuwarmu, ko kadan wadannan mutanen basa da tausayi, su rasa wani abu mai girma da ake kira da imani, sai su kashe mutane ta tashi gari su kwace mata, ban san abun da suke so ba, ban san abun da muka yi musu ba, basa tsoron hakki”
 
Aminatu ta fada cikin kuka, sai Ali ya busar da iska bakinsa a hankali ya saka hannayensa aljihu. Hajiya Laraba ta ce.
 
“Ni abun da nake ganin, mun riga mun riski wani zamani da Annabi ya fada cewar kisa zai yawaita har wanda za a kashe be san dalilin da ya saka aka kashe shi ba, wanda yai kisan kuma be san dalilin daya saka ya aikata kisan ba, mu shigo wani zamani da ake fito na fito da Allah, kuma ba a jin tsoronta ba a fargabar azabarsa, mun riski wani zamani da ake kaunar haram ana ganin kamar ba komai bace, so idan Allah ya maka imani baka daga cikin mutanen dake aikata abubuwan da Annabi ya fada sai ka godewa Allah, domin hakan yana nuna zuciyarka mai kyau ce, domin dole ne wadannan abubuwan za su yi ta faruwa tun Annabi ya fada, sai dai ga wa za su faru Allah masani, kuma alkawarin Allah ba zai taba tashi ba, cewar Allah yayi alkawarin sai ya cika wuta, kuma a wata fadar Allah yace ki kare rayuwarku da iyalanku daga wuta, domin makamashinta shi ne mutane da duwatsu Allah ya tsare mu”
 
Sai duk suka amsa da Ameen.
 
“Ameen”
 
Sun dan dade suna tattaunawa da shi da Talba, da Hajiya Laraba kamin Ali ya katse su.
 
“Ya kamata ka huta nan, ina jin yau mutane da yawa sun ziyarce ka, kuma you talk alot marar lafiya kuma hutu ake so a gurinsa”
 
“Ai bari mu tashi, ka samu ka huta zan tafi da Aminatu domin ba zan barta nan tana ta kura ba, na lura da yadda take kin sakewa idan Momy ta shigo ba son haka nake ba”
 
Talba yayi murmushi yana kallon Hajiya Laraba da tai maganar.
 
“Idan kika ce zaki m rika dauke ta, ya azayi su saba? Momy dole na ta karbi Aminatu kamar yadda ya zama dole Aminatu ta karbi Momy a haka har su saba”
 
“Humm. Idan dai Allah ya baka lafiya, Aminatu zata tare a gidanta Inshallah”
 
“Daddy ma ya bani sati daya, ba dan ciwon nan ba da yanzu muna nan muna shirye shirye tarewar, ni kaina kuma na yi wannan tunanin”
 
“Ya dai kamata, Allah ya baka lafiya”
 
“Ameen”
 
Hajiya Laraba na mikewa tsaye, Aminatu ta mike tsaye Bashir ma haka, sai da ya mikawa Talba da Ali hannu sukai sallama yana yi ma Talba fatar samun sauki.
 
“Sai na samu lafiya zan zo har gidanka mu san juna da yardar Allah, amman kamin nan ka saka min number ka a wayar nan”
 
Talba ya fada yana mika masa wayar, sai ya karba ya saka masa number.
 
“Amman dai zai fi kyau Aminatu ta kwana a gidana ita kanta zata fi sakewa”
 
Talba ya karbi wayar yana jin kamar ya musanta hakan kuma baya son musantawa domin hakan na nuna be aminta da shi bane, ya san idan ya hana Aminatu ba zata jidadi ba, shi ma kuma ba zai ji ba. Sai dai halin da suka fito baya son wani abu ya sake faruwa da Aminatu.
 
“Ba a dade da sace yarinyar nan ba, idan kun zauna zata fada maka abubuwan da sukai ta faruwa, even Mama bana iya ce mata aa ne kawai Wallahi, domin har yanzu ba mu san wanda ya aikata hakan ba, kuma ba mu san dalilinsa na aikatawa ba, domin ba su yi requesting na kudi ba, that's mean akwai manufa a kasa”
 
Hajiya Laraba ta wara ido tana kallon Talba da mamaki. Can kuma ta girgiza kai ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba, shi kuma yaki yarsa ya dago kai su kalli juna ita da shi.
 
“Amman dai yanzu za su iya tafiya ku gaisa da a gidanka tare da matarka”
 
“Inshallahu babu abun da zai same ta”
 
Talba dai be sake cewa komai ba, har Hajiya Laraba ta fice Bashir ya fita sai ya rage daga shi sai Aminatu da Ali.
 
“Ranka ya dade zaka ba ni dama na yi sallama da matata ko kuma ya?”
 
Talba ya fada yana kallon Ali ya kalli Aminatu sannan ya nufi kofa ya fice daga dakin. Talba ya mike tsay still yana jin ciwo a kirjinsa sai dai ba kamar jiya da dazun ba.
 
“Come here”
 
Ya ware mata hannayensa sai ta matsa kusa da shi ta rumgume shi sosai.
 
“Na gode”
 
Ya saka hannunsa ya dago fuskarta yana kallon kwayar idonta dake yawo cikin nasa kwayar idon.
 
“I love you so much yarinyar nan”
 
Ya sauko da fuskarsa saman nata ta dora bakinsa saitin nata ya fara aikin nasa daya saba, sannan ya cire ya tsotsa tsirin hancinta yana shafa bayanta a hankali.
 
“Pray for me, in two days time na samu lafiya mu koma gidanmu”
 
“Allah ya baka lafiya”
 
Ta fada da yar siririyar muryarta.
 
“Ameen”
 
Ya sake maida bakin nasa cikin nata, wannan karon yawo yake da hannunsa a jikinta har zuwa gurin cikinta, sai ya dan rika mararta kadan ya matsa.
 
“Please ki kula da kanki, ban da wani ya zo yace ana sallama dake ki fita, ban da zuwa bakin gate ma ko da da yan gida ne, yanzu sai mun gano ko waye ya aikata wannan abun sannan hankali zai kwanta mu samu natsuwa”
 
“Tau”
 
“Tafi kar mu bata musu lokaci”
 
Ta sake shi ta nufi kofa, sai kuma ta juyo ta dawo ta rumgume shi. Murmushi yai ya shafa kanta dake cikin hijab yana jin kaunarta na kara shiga ransa. Sakinsa tai ta nufi kofar tana jin kunyar rumgumarsa da tai ta bude ta fice ba tare da juyo ba. Zaunawa yai saman gadonsa yana kallon kofar kamar ya san Ali zai shigo, yana kallon yanayinsa har ya iso kusa da shi, daya daga cikin alluran da suke gurin ya dauka ya fara hadawa.
 
“Kamar akwai abun da yake damunka”
 
“No gajiya ce kawai”
 
“A tunanina bama boyewa juna matsala ko damuwa”
 
“Wannan tana da banbanci, be zama lallai ka fahimta ba, kuma be dace ma fada maka a yanzu ba, maybe idan ka ji sauki”
 
“Na samu sauki sosai Ali, you know ina samun kulawar daya dace, kuma Alhamdulillah ina jin sauki sosai a jikin nawa fiye da jiya ko shekaranjiya, ni da nake fatar jibi na koma gida ma kasan bana son zaman asibiti ba”
 
Ali yayi murmushi, because he's friend was right ko kadan Talba baya son zaman asibiti sai idan ta kama dolen dole.
 
“Ba ni hannunka”
 
“Bana son allurar bachi ba”
 
“Bachi kake bukata yanzu, kai da kake son ka yi saurin warkewa kuma kake musu da likita”
 
Talba yayi dariya, ya mika masa hannun.
 
 
***   ***   ***
Sai da suka fito sannan Hajiya Laraba take maganar Momy da Aminatu domin tun a dazun da ta marairaice a gabanta saboda shigowar Momy dakin ya tsaya mata a rai.
 
“Wannan tsoro tsoro da kike da Momy wahala zaki sha, wannan matar da kika gani bata da tausayi bata da imani ko kadan ga son kai, da ganin ta fi kowa saboda tana da dukiya, jira take har sai ni na fara mata magana saboda ba baiwa ta aje, bata san ko jin kai na fita ba, ayi mutum ace babu tunani babu Allah a ransa, wannan matar sai na ke ganin har wani abu zata iya yi ta raba tsakaninku da Talba, saboda yarta kuma kina ganinta kin san bata kaunarki”
 
Bashir ya girgiza kai duk da kasancewar ba san wanda ake magana akai ya ce.
 
“Wallahi bata iya komai da Aminatu, Auta.....tab muma da muke maza Baba ya tsaya mana da maganin kariya balle auta da yake ji da ita ba, ai ka'ida ce indai zuri'ar gidan mu ne, basa yi ba a musu”
 
Hajiya Laraba ta kalleshi da mamaki.
 
“Toh ashe ba banza kuka ba”
 
Yayi dariya yana shiga Napep dinsa, su kuma suka shiga baya yai ma Napep din key ya fara tukawa yana fadin.
 
“Indai asiri ne, ba dai ya kama mu ba, sai abun da Allah ya riga ya rubuta zai same ka iri wanda ba zaka iya tsallakewa ba din nan, amman ko iska bana jin zai iya zama a jikin Aminatu balle asiri, kuma duk wanda yai zai koma masa kai ma idan kai ma wani zai dawo maka”
 
Hajiya Laraba ta kalli Aminatu da mamaki ta ce.
 
“Toh mutanen kauye fa basa wasa, ka ce nan da nake gani an girka Aminatu”
 
Aminatu ta yi murmushi. Shi ma Bashir din murmushi yai ya ce.
 
“Babu wani girka, ai yan bori suke wannan, wannan ayoyin kur'ane da kuma abubuwan tsari irinsu kainuwa da kaikayi da su tunfafiya da ake hadawa ana sha, sai kuma addu'o'i ina dai ba a nan ba, kin ga ko wannan na tunfafiya idan mutum ya sha shi je kai bachinka, to sai idan boka zai iya zuwa saman ruwa ya shimfida Buzunsa (Windi) ya hau ya zauna a kai ruwa be natse da shi ba sannan zai maka aiki ya kamaka kin ga kuma abu ne mai wahala ko ma na ce ba zai taba faruwa ba, kin ga Bismillah dubu idan kika sha ta koma kawai ki kwanta, musamman kika hada da kai ka yi koma kan mashekiya da kula'uzai hmmm ba dai mutum sai dai Allah, ga kuma addu'a Aminatu ai ba ta wasa da addu'a domin tun muna kanana Baba yake koya maka ita kuma ya nuna maka muhimmancinta sai dai idan ka watsar dan kanka”
 
“Toh ai kin ji, haka ake so to ki kara rike addu'o'in nan da kyau ban da wasa, domin na tsorata sosai da matar nan wannan kiyayya ina dalili, ni ma fa saboda ke ne nake jin yau ta kara dauke min kai, domin can da ai ta kan dan gaisa da ni sama sama, yanzu kuma gani take mun aura miki Talba mun zama mikiyanta”
 
“Wacece wannan matar?”
 
Hajiya Laraba ta fara bashi labarin Momy da yadda akai ta rika shi har zuwa auren da akai da Aminatu, yadda komai ya wakana sai da Hajiya Laraba ta fada masa. A gidansa kofar gidansa ya faka Napep dinsa sannan ya fito tare da su Hajiya suka shiga cikin gidan, Maman Walida kamar ta hade Aminatu dan murna har da hawayenta, a gidan Aminatu ta wuni, Bashir ya tafi kai Hajiya Laraba na nata gidan domin a lokacin mijinta na gurin aiki balle ya zo ya dauke ta, tafiya kuma sai ta zama ta dole sannan yake  aiko mata da direban gurin aikinsu ko kuma kannensa yace ya kaita inda zata je.
Aminatu kam sai kusan Isha'i sannan ya kaita gidan Hajiya Laraba, bayan sun sha hira da matarsa da kuma shi kansa har yana kiran wasu yan'uwa da yake da numbers dinsu ya fada musu Aminatu tana raye gashi ma tare da ita, duk wanda ya kira aai ya bata wayar ta gaisa da su, a gidan ma Aminatu ta sha kuka sosai saboda zancen mutanen da aka kashe da suke, da kuma labarin da take ba shi na yadda akai ta fito daga dajin. Be sha wahalar gabe gidan ba, domin ya ga gurin dazun da ya kai Hajiya, a hanya ya kashe mata kudin da ya kai 5k duk abun da ya gani sai ya tsaya ya siya mata, ban da kayan dadin da yai ta kwaso mata dazun da rana.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
FARUK POV.
 
Bayan ya gama wayar da yake da Shamsu ya saka wayar aljihu ba tare da ya duba sakon daya shigo masa ba.
 
“Ya ce yayi magana da mutumen, akwai wasu a kasa kuma zai saka cijiya, zai nema min”
 
“To Allah ya taimaka, yanzu zaka je ka duba wadanda suke nan kenan”
 
“Eh haka ya ce”
 
“Allah ya tsare ya saka alheri”
 
“Amin”
 
Ya matsa kusa da cooler abinci ya bude ya dauki guri ya zuba, ya zauna saman kujera da zimmar ci amman ya saka cin saboda farinciki kuma ba dan baya jin yunwa ba. Two spoon yai ya aje ya dauki ruwa ya sha, Mama dai sai kallonsa take cike da kauna da kuma farinciki a lokaci daya.
 
“Ba zaka iya cin abincin ba?”
 
Yayi murmushi mai sauti
 
“Da ka daure ka fita ka siyo ko lemu ka sha, na san farinciki ba zai barka ka ci abincin ba”
 
“Wallahi ga kuma yunwa ina ji amman bana jiya cin komai”
 
Ya fada yana ciro wayarsa daga aljihunsa da zimmar tabawa, sai idanuwansa sukai arba da mail din dake saman screen din, hannu na rawa ya bude mail din, karantawa yake amman ya gagara kai wa karshe dai ya tsallake ya duba wanda ya turo masa sakon.
 
“What... ”
 
Ya furta kamin ya sake komawa farkon sakon yana karantawa, haka yai ta maimaita sakon tun yana karantawa a hargitse har ya natsu yana karantawa wai ya tabbatar ko ba gaske ba. A take ya aje wayar ya dubi inda yake kyautata zaton nan ne gabas a asibitin yai sujadar godiya ga Allah, Mama sai kallonsa take da mamaki sai dai tunaninta be bata cewar wani abun bane sabo, a zatonta duk murnar kudin daya samu ne. Dagowa yai daga sujadar hawaye na bin fuskarsa.
 
“Mama aiki na samu?”
 
“Da gaske? Aiki dai? Baban yarinyar ne ya baka?”
 
Ya kasa amsa mata tambaya ko daya, zuciyarsa sai bugawa take da mugun karfi yana jin wani irin farinciki marar misaltuwa, farincikin da be taba jin irinsa ba, hannu ya saka ya dage kansa yana hawaye.
 
“Alhamdulillah Allah, Faruk baka amsa min ba? Baban yarinya ne ya baka aiki?”
 
“Aa aiyukan da nake ta applying ne wani ya fito, Mama daga Xullers Company, wani babban kamfani kasar China ne dake hako ma'adanai a Nigeria, Wallahi na kasa yarda”
 
Mama ta rufe baki da mugun mamaki tana zaro ido.
 
“Kai da kanka Faruk? ”
 
“Mama gashi”
 
Ya mika mata wayar duk kuwa da kasancewar ya san ba zata iya karantawa ba.
 
“Kuma ba yan dafara ba ne? Na ji ana fadar mutane suna damfara ba, balle kai da aka ji ka samu kudin nan”
 
“Yau kwana uku da turo sakon Mama, ba damfara ba ce”
 
“Allahu akbar Allah mai kyauta da kari, Allah mai yadda ya so a lokacin da ya so ga wanda ya so, Allahu Akbar”
 
Mama da fada ita kanta tana hawayen farinciki. Komai ya zo musu kamar mafarki, tsakamin shi da Mama sai ka rasa waya fi wani farinciki.
A daren ranar Faruk kwana yai yana godiya ga Allah ya raya dare da sallah nafila. Washe gari ya tura musu duk wani abu da suka bukata ta mail din. Within a week rayuwar Faruk ya canja ya koma wani mutum na dabam da be taba mafarkin zama ba, balle tunaninsa ya bashi wata rana haka zai faru da shi. Gida suka kamfanin ya bashi a Lagos inda babban branch dinsu yake, da kudi mai yawa da zai wadatace shi ya kimtsa rayuwarsa na wani lokaci. Kwansa biyu a Lagos ya suka masa booking din jirki ya sauka sokoto, daga can ya hau mota zuwa Gusau, yana isowa wanka kawai yai ya shirya cikin wasu tufafin masu tsada da yai kuzurinsu tun daga can ya nufi asbitin gurin Mama, domin har lokacin tana asibitin suna bata kulawa da ya kamata. Tun kamin ya tura kofar dakin ya shiga ya ji dariyar Rukaiya, na fada musu yau zai dawo sai dai be fada musu lokacin da zai sauka ba sai ganinsa kawai sukai kamar daga sama.
 
“Yan Tafiya har an sauka”
 
Mama ta fada, sai Ramla tai murmushi ta dauki kular da ta kawo ma Mama farfesu kamar yadda ta saba kullum sai ta shigo mata da wani abun idan zata zo.
 
“Sannu da zuwa”
 
Ta fada tana kallonsa, sai ya amsa mata da murmushi a fuskarsa.
 
“Sannu Ramla ya aiki”
 
“Alhamdulillah”
 
Ta amsa tana murmushi sannan ta nufi kofa ta bude ta fice, for no reason ya juya yana kallonta har ta fice, sannan ya juyo ya kalli Rukaiyah dake kallonsa tana murmushi, dan hade rai yai gudun kar ta samu wata dama ta yin masa zargi ko wani tunanin.
 
“Sannu da zuwa”
 
“Yauwa”
 
Ya amsa sannan ya zauna kusa da mahaifiyarsa da ita ma kanta ta canja kala. Balle kuma shi da har wani kamshin tsadadden turare yake.
 
“Mama ya jikin?”
 
“Alhamdulillah Wallahi na samu sauki sosai, na ji ma suna maganar sallama ta gobe”
 
“Maa Shaa Allah, haka Rukaiyah ta fada min jiya a waya ai”
 
“Ya hanya? Ina ta tunani da zullumin ashe har ka dawo”
 
“Na dawo, shiyasa ai ban fada miki lokacin da zamu ta so ba na san zaki yi ta jin tsoro, duk da jirgi muka hau da zamu tafi a dawowa ma jirgin muka hawa”
 
“Laaa Yaya jirgi ka shiga?”
 
“Ni kaina na ji dabam, i never thought wata rana zan shiga jirgi zuwa wani gari da sunan aiki, ko gidan da suka ba ni abun kallo ne Mama ga motar kamfani idan ina bukata, amman na fada musu zan siye tawa motar”
 
“Gaskiya kam, kara dai ka siye taka to wai yanzu a can zaka zauna kenan?”
 
“Eh a can zan zauna, amman aikin ana canja zai iyu yuyuwa a canja ni zuwa wani gari nan gaba ko ma zuwa wata kasar, amman for now dai a Lagos zan zauna”
 
Mama ta yi murmushin jindadi.
 
“Shamsu yana ta hidima yaron nan yana da kirki, duk abun da ya saka a sabon gidan nan sai ya zo ya fada min, wani lokacin har a wayarsa yake nuna min hotuna

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login