Showing 183001 words to 186000 words out of 332834 words
daga dakin kamin ta karasa saukowa ta ji motsin Amal a bayanta ita ma tana saukowa.
“Momy na ina sallah na ji Leila ta yi ihu ta kiraki kuma ta daki kofar dakinki da karfi miya faru?”
Momy ta tsaya cak sannan ta juyo ta kalli Amal tana kokarin boye tashin hankalinta.
“Shiga dakinki ki kulle”
“Yan fashi ne suka zo”
Ta tambaya tana zaro ido, sai Momy ta daka mata tsawa.
“Yan ubanki ne suka zo, go back to your room i said”
A yadda Momy tai mata maganar ta san she's serious domin babu alamar far'a a tare da ita, and bata ji ma Momy ta taba zaginta sai a yau. Juyawa tai ta haye saman tana yi tana waigen Momy har ta isa bakin kofar dakinta, sannan ta tura ta shiga. Sai da Momy ta tabbatar ta shiga sannan ta juya ta karasa sauko tana rabon ido a falo. Can ta hango Envelop din a tsakiyar falon da kuma dankwalin, da tsoro Momy ta fara takawa zuwa inda dankwalin yake tana kallonsa, kaminnta duka cikin karfin hali ta dauki dankwalin, daddabe yake da kasa ta kana gani kasan kasar ta dade a jikinsa. Sai kuma ya juya ta dauki envelop din ta bude ciki ko zata samu wani abu, har kasa ta zazzage bata ga komai ba. Kofar kitchen ta kalla duk ta tasan masu aikinta basa a nan irin wannan lokaci domin da zarar sun gama jera mata abincin dare suke ficewa zuwa BQ, bata basu damar tsayawa a falon ma balle kuma zama.
Mamaki take waya aikata haka? Miye manufarsa na aikata hakan? Dankwalin Baaba da gaske ko kuma wani ne yake son yi musu wasa da hankalinsu, idonta ta kai kan dankwalin tana kara tantancewa, and yes dankwalin Baaba ne. Da sauri ta saka dankwalin a cikin envelop din ta nufi kofar fita daga falon, bata ko tsaya saka talkami ba haka ta fita ta bar kofar a bude, BQ ta nufa, tun kam ta karasa ta kwalawa Mairo da Zulai kira, sai ga su sun fito da sauri cikin tsoro a tunaninsu ma wani laifin suka yi.
“Waya karbi sakon dazun?”
“Ni ce Hajiya”
Zulai ta amsa Mairo kuma ta nuna ta.
“Waya bada sakon?”
“Mai gadi ne”
“Yusufa”
“Be ce miki komai ba da ya mika miki sakon”
“Cewa kawai yai gashi a bawa Hajiya Leila”
Momy ta daga musu kai sannan ta juya ta nufi gate din, gurin da masu gadin gidan suke zama ta nufa suna ganinta sai duke suka mike tsaye wadanda suke cikin daki ma suka fito waje, domin police uku da masu gadi biyu ke kula da gidan.
“Wa aka bawa sakon nan?”
“Ni ne ranki ya dade”
Yusufa ya amsa.
“Waya baka sakon nan?”
“Wallahi ban san shi ba, ya dai kwankwasa gate na leka na ga mutun a tsaye ya faka motarsa gefe, sai ya miko min yace gashi dan Allah na bawa Leila, ba zai samu shigowa ba sauri yake!”
“Zaka iya gane fuskarsa?”
“Aa Wallahi Hajiya, saboda yana sanye da da abun nan da ake yayi na rufe fuska, Mask kuma ya saka facing cap da bakin gilashi, amman ya da dan jiki haka kuma dogo ne sosai motarsa kuma ja ce 406”
“Amman kai wani irin wawa ne Wallahi jahili, ko da yake ba kai kadai ba har da sauran ma, taya wani zai kawo sako ba ku tsaya kun bincike shi ba? Idan kuma Bomb ya kawo fa? Ko kuma yana dauke da bindiga fa? Wani irin tsaro kuke ba mu ne? Miye amfaninku?”
Cikin daga murya sosai Momy take musu fada, suka hau bata hakuri da fadin za su gyara a gaba.
“Hajiya akwai abun da be dace ba ne a cikin envelop din? So that's mu dauki mataki tun yanzu”
Daya daga cikin police din ya tambaya. Sai ta amsa masa da karfi.
“No stay out of this babu komai, ku kula da aikinku kawai”
Tana kaiwa nan ta juya ta nufo kofar falon da tunanin wanda ya aiko da sakon da kuma nufarsa ta yin haka, tana shiga cikin falon ta maida kofar ta rufe sannan ta kalli Leila dake tsaye ta rumgume hannayenta tana kuka.
“Momy kashe ni za ayi”
Momy ta girgiza mata kai da sauri ta karasa kusa da ita tare da aje envelop din kan kujera.
“Ki daina fadar haka, wannan wace irin magana ce? Ba zan iya bari a kashe ki ba, ba zan haka ta faru ba, ko da kuwa komai dana tara zai kare”
Ta karasa tare da rumgume ta tana hawaye.
“Put this in your mind ba da gangan kika aikata ba, ba kina nufin ki kashe ta ba”
“Momy tsoro nake ji, idan Daddy ya sani ko Talba...”
Ta fada cikin kuka tana kankame Momy, bata karasa ba Momy ta dakatar da ita.
“No one is gonna know, no one...”
Sannan ta saketa ta dauki envelop din ta rika hannunta suka hau sama. Momy na shigewa Amal dake labe jikin kofar dakinta ta bude a hankali ta fito taje jikin kofar Momy ta kara kunnenta. Momy har ta zauna sai kuma ta tashi ta isa gurin kofar ta bude a hankali sai kuwa tai arba da Amal a tsaye tsamo tsamo tana kallon Momy.
“Momy daman cewa na yi yanzu zaki ci abinci ko sai zuwa anjima...?”
Momy ta watsa mata wata uwar harara wanda ta saka ta juyawa da sauri ta koma dakinta. Bin bayanta Momy tai har cikin dakin ta cire key din dakin sannan ta fito ta rufe ta daga waje ta cire key din ta nufo dakinta. Shigowar da Momy tai a dakin ma sai da Leila ta zabura saboda tsoro domin a firgice take gaba daya. Momy ta rufe kofar sannan ta karasa kusa da ita ta zauna.
“Waya san da maganar Baaba bayan ni da ke da Kabir da Amal?”
Ta girgiza kai da sauri.
“Babu”
“Think... Dole akwai wanda ya san da maganar nan!”
Har ta fara girgiza kai sai kuma ta ce.
“Ma.. Madina....”
Momy ta daga hannayenta.
“Leila ke wace irin yarinya ce? Ban gargade akan kar kowa ya ji maganar nan ba? Ke baki da sirrin kanki dole sai kin bude cikinki a gurin kawa”
“Momy Wallahi Madina ba zata iya yi min haka ba, i trust her kuma Madina mace ce ba zata yarda tai risking rayuwarta ba for this? Mi zata samu idan ta yi?”
“Okay Kabir ne zai yi ko Amal? Ko kuma ni kaina?”
“Aa amman me Madina zata samu idan tai min haka?”
“Waya sani, amman duk wanda ya fara shirya wannan abun yanada manufa ta yin haka”
“What if lokacin da muke rufe gawar wani ya gam mu? Ko kuma mai gadin gurin ne?”
Momy ta yi shiru tana nazari if could be possible wani ya gansu ko kuma mai gadin gurin yai haka saboda ya samu kudi. Da sauri ta tashi ta nufi inda wayarta take ta dauka ta shiga contact dinta, thinking of da wane suna tai saving din number mai gadin gurin, haka tai ta yawo a muhallin bata samu sunan ba.
“Zan je yanzu na duba shi ki zauna a nan”
Leila ta yi saurin dakatarta da ita.
“Momy karki je cikin daren nan, baki san abun da suka taka ba, kar su kara yin wani abun”
Momy ta koma ta zauna jiki a sanyeye, can kuma ta kalli Leila dake hawaye sosai ta ce.
“Ki tashi ki wanke fuskarki ki kwanta, karki bari kowa ya gane kina cikin damuwa, kuma ki kwantar da hankalinki, indai ina raye babu abun da abun da zai faru”
Ta gyada kai a hankali sannan ta yunkura ta tashi har lokacin jikinta rawa yake kuma tsoron be bar jikinta ba. Bathroom din Momy ta shiga ta kunna fanfo da niyar wanke fuskarta sai kawai ta fashe da kuka tana nadamar abun da ta aikata, event though ba da niya tai ba. Kawai dai ta ture Baaba ne saboda ta fusata, a jikin madubin ta rika kallon kanta idanuwanta har sun kumbura, ga hawayen sun ki su tsaya mata, kallon tap din tai kamin ta kai hannunta ta debi ruwan ta watsa a fuskarka, sai kuma ta sake fashewa da kuka, ta duke a gurin tana rike da tap din.
“Leila wannan abun da kike kina tonawa kanki asiri ne kawai, ki wanke fuskarki ki fito kamin na bude Amal”
Momy ta fada daga can cikin dakin, sannan ta fice. Cikin karfin hali Leila ta mike tsaye ta wanke fuskarta sannan ta fito ta nufo gadon Momy ta zauna tana ta jin tsoro, sai kallon kofar dakin take. After like 20 min Momy ta shigo rike da tray dake dauke da fruit da madara sai kuma ruwan mai sanyi.
“Ki ci sai ki sha magani ki kwanta”
“Bana iya cin komai Momy”
“Sha madarar ko kadan ne”
Ta dauki cup din madarar ta kai baki ta kurba kadan, sai ta ji ta kamar babu komai a ciki, kamar ba madara ba. Da sauri ta aje ta dauki ruwa ta sha da yawa, Momy ta miko mata maganin ciwon kai.
“Sha”
Ta karba ta sha, sannan ta haye gadon gaba daya ta kwanta jikinta da zafi wani zazzabi ya taso mata ga sanyi da take ji. Momy da kanta ta janyo blanket ta lullubeta.
HAJIYA LARABA POV.
Har ta gama cin nata abincin Aminatu bata dawo ba, sai dai bata ce komai ba saboda tana tunanin ko ya tsayar da ita ne, kamar yadda yai jiya da ya zo, daman ta san za a rina tun da ya ga an gyara masa mata.
Misalin tara ta tashi ta shirya gurin kwanciyar yaranta da suke kanana daman ta saba musu idan zaku kwanta sai ta musu wanka ko kuma ta saka yayarsu tai musu. Bayan sun kwanta ta fito falon tana hamma.
“Rilwan je waje ka ce Aminatu ta shigo gida haka nan”
Rilwan din ya amsa tare da aje remote din hannunsa ya tashi ya fita, tafiya yake a hankali har ya isa gate din ya bude ya leka. Wayam babu kowa babu mota balle kuma Aminatu. Juyowa yai ya dawo cikin gidan.
“Mama ban ganta ba, kuma ban ga ma mota a gurin ba”
Tun daga bakin kofar falon ya fada mata sannan ya karaso ya zauna.
“Kila daukarta yai suka fita, shiyasa ya ki shigowa cikin gidan, ko kunya baya ji, ita kuma wata salula sai ta bishi su tafi”
Ta karasa tana dan jan tsaki, sannan ta dauki dankwalinta dake kan kujera ta daura, ta cigaba da kintsa falon. Wasa wasa har goma ta wuce sha daya saura Aminatu bata dawo ba, a nan ta fara damuwa tana tunanin wata kila wani abu yake mata shiyasa be dawo da ita ba. Misalin Sha daya daidai Mai gadin ya kwankwaso kofar falon, a lokacin tana zaune tare da mijinta ta saka shi a gaba yana cin abinci tana masa hira. Yunkurawa tai ta tashi ta bude kofar falon.
“Garba”
“Na'am Hajiya, na ce a rufe gidan ko kuma mu tsaya jiran bakuwar ta dawo?”
“Aa dan jira bari na kira shi, sai mu san idan can zata kwana”
“To”
Ya amsa sannan ta saki kofar ta dawo tana fadin.
“Mazan yanzu dai kam ba su da kunya Wallahi, tun fa da isha i ya fita da yarinyar har da wani cewa ta zo ta karbi sako ashe so yake.ya dauketa su bar gidan gaba daya”
“Tsakani da Allah ma yama yi hakuri fa, idan ba shi ba yaushe za a aura maka mata a hana ka tarewa da ita har na tsawon wata uku ko hudu ma ko? Ai yayi kokari ki barshi ya huta sa amaryarsa”
Mijinta ya fada yana dariya.
“Ai kiransa kawai zan yi na ji idan can za su kwana kar sai mun rufe gate din kuma ya dawo”
“Tun da ya kai yanxu kam ai kin san ba zai kawo ta yau ba, musamman idan ya san yayi aika aika, ki kyale shi kawai sai da safe”
“Shi ma ai rashin hakuri ne, tun da an kusa kai masa matar ba sai ya jira ba”
Ta fada tana jin haushin abun da yai, sannan ta kira Garba a waya tace ya rufe gate din.
Washe gari ta yi tunanin ko zai dawo da ita da safe amman be dawo da ita ba har kusan azahar hakan yasa ta yanke shwarar kiransa.
TALBA POV.
Sai a waje ya tsaya yai sallah Isha'i sannan ya shigo gidan. A inda ya saba fakin yai farkin sannan ya bude motar ya fito. Bangarensa ya nufa sai da ya fara yin wanka ya saka boxer ya dora jallabiya sama sannan ya fito yana ta kamshin turare ya nufo bangaren Momy. Sau daya ya danna door bell din ya jaya ya tsaya sai Momy ta bude masa.
“Barka da dare”
“Barka dai”
Ta amsa masa cikin yanayin damuwa, kallonta kawai yai ya dauke kai ya nufi sofa ya zauna. Da farko ta yi niyar zama a falon sai dai sanin Talba zai iya damunta da kallon tuhuma ko tambayar abun da yake damunta yasa ta nufi upstairs. Da ido ya bita har ta haye sannan ya mike tsaye ya nufi dinning yana tunanin yanayinta a yau, ganin Momy cikin damuwa abu ne dake daga masa hankali domin ya san halin Momy ba komai take bari ya zama mata damuwa ba, tana son rayuwarta da jikinta hakan yasa take ba su kulawa na musamman, idan har damuwa ta bayyana a fuskarsa to ya san ba karamin abu ba ne. Kujera ya ja ya zauna ya dauki karamin tea cup ya soma hadawa kansa tea. Cube din sugar daya ya saka ya dauki tea spoon ya motsa sannan ya kai tea bakinsa, cup din na taba lips dinsa ya tuna da Aminatu daman wunin yau a cikin zuciyarsa ta wuni, abu daya da biyu sai ya tuna abun da yai mata da reaction dinta.
“Ya Talba”
Ya juyo cikin izzar da be san yana da ita ba ya kalli mai Amal dake saukewa upstairs sanye da riga da wando na material.
“Little Sis”
Ya sakar mata murmushi, ita ma murmushin ta mayar masa, ta karasa taja kujera ta zauna.
“Wai sai yanzu zan ci abincin dare yunwa nake ji, tun dazun Momy ta rufe ni daki”
Ta fada ne kawai saboda tana son ta yi masa gulmar, domin ko kadan abincin dare be dame ta ba wani lokacin sai dai ta sha ruwa kawai ta kwanta ko tea, amman yau ita ce da fadin bata ci abincin dare sai kace wanda ta kai karfe daya kulle a daki. Ta yi hakan ne kawai domin ta ji idan Talba da Leila sun yi fada ne ko kuma Momy da Talba ko Daddy, bata san dalilin Momy na rufeta ba, gashi kuma ta ji Leila nata kuka kamin Momy ta rufeta a dakin.
Jin Talba be ce mata komai ba yasa ta kalleshi ta ce
“Ya ko dai kun yi fada ne? Na ga ran Momy ya bace sosai har tana zagi kuma ka san Momy bata zagi”
Talba yayi shiru yana nazari abun da Amal take fada masa, compare to yanayin da ya ga Momy a yau.
“Aa ba mu yi fada ba”
Ya fada yana tunanin motar data haske su jiya.
“Little Sis jiya ina kika je?”
“Shopping direba ya kai ni?”
“Kun biya wani gurin?”
“Aa”
Ta kai lomar tuwon a bakinta. A iya saninsa Direba ba zai fara masa haka ba ko da kuwa Amal ta bashi umarni, idan ma Amal ce ta ganshi ba zata gudu ba, zata fito tai magana da shi ne saboda gulma, and he don't think Momy zata iya rike maganar bata ce masa komai ba har yanzu, amman idan ba haka ba miya saka Leila kuka? Aje cup din yai ya mike tsaye ya nufi upstairs Amal ta bishi da kallo tana ji kamar ta tashi ta bi bayansa, sai dai gudun kar Momy tace ita tai masa gulmar yasa ta zauna ta cigaba da cin abincinta. Sai da ya fara kwankwasa kofar dakin sannan ya tura ya shiga, a mugun firgice Leila ta tashi zaune tana kallonsa, Momy ma dake zaune kan carpet tana waya kallonsa tai. Karasawa yai kusa da Momy ya zauna sai ta yanke wayar da take tana kallonsa da dan faduwar gaba, ba mamaki Amal ta fesa masa.
“Momy akwai wata matsala ne?”
“Kamar ta me?”
Ya kalli Leila wacce ta koma ta kwanta sannan ya sake kallon Momy.
“Na ga kamar kina cikin bacin rai”
“Na komai, Leila ce bata jindadi”
Sai a yanzu ya daina mamakin ganinta a kan gadon Momy a kwance, Amal ce ta mai mai wannan dabi'ar ba ita ba.
“Allah ya sauwake, kin sha magani?”
Ya tambaya yana kallonta, he did what he did saboda a gaban Momy ne kar tace be nuna mata kulawa ba, because ya san ba amsa masa Leila zata yi ba, and he's right bata amsa masa din ba sai ma juya baya da tai. Mikewa yai tsaye ya fice daga dakin tare da ja musu kofar dakin. Downstairs ya nufo kamin ya karasa saukowa wayarsa tai ringing, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayar ya amsa kiran da Ali yake masa.
“Talba na yi magana da wani yace zai zama mana gida mai kyau, amman za a bashi 200 per two days kuma wai duk abun da ya bata ko ya fashe za a biya”
“Okay akwai komai a ciki?”
“Komai akwai, na ma bashi kudin kuma na fada masa on Saturday zamu kawo Amarya a gidan yace kamin lokacin zai hannata mana keys din gidan, akwai ma mai gadi a gidan”
“Okay Allah ya kai mu”
“Aamin”
Har Talba yayi kamar ya fada masa abun da ya faru jiya akan motar nan sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai kawai ya katse kiran ya saka wayar aljihu.
“Little Sis zan je na kwanta, it past 10, ke ma ki kwanta da wuri saboda gobe a akwai school”
Ya fada yana kallon katon agogon dake falon makkale kamar zai yi magana.
“To ai mun kusa gamawa mu huta, Ya me take yi ma kuka?”
Ya dan daga fadunsa.
“Wai bata da lafiya, tana dakin Momy ki shiga ki mata sannu”
“Toh”
Ya daga mata hannu sannan ya nufi kofar falon. Bangaren Daddy ya nufa tana taba kofar ya ji ta a bude sai ya tura ya shiga, ya nutsa kai har karamin falon Daddy inda ya same shi tsaye yana kokarin cire babbar rigarsa.
“Daddy yanzu ma ka shigo kenan?”
“Yes Momynka ma bata san na shigo ba, ba kai bachi ba”
Talba ya saka dariya daman ya san sai Daddy ya zolayeshi, abu ne mai wahala a wuni Daddy be zolayeshi ba sai idan basa tare.
“Haba Daddy sai kace yaro karami, karfe goma zan