Showing 270001 words to 273000 words out of 332834 words
tunanin barazanarki zata haifar miki da da mai ido? Kina ganin a kanki zan bar Leila ta fasa auren Talba? Kina kara jefa kanki ne a cikin matsala, kuma kina kara nuna mana cewar baki da imani, tun da har zaki iya fasa kabari ki ciro hakoran gawa ki aiko mana, to ki saurare sakamakonki_
Madina na gama karanta sakon, ta yi saurin tashi daga kwancen da take ta zauna tana kara duba number Momy, domin tana da number a wayarta kamar yadda Momy ma take da number ta.
“Kenan Leila bata ji maganar da na yi mata ba? Sai da ta fada Momy? Ko kuma dai ta yi haka ne saboda na dauka Momy ce? Ko kuma Momynce da gaske?”
Magana take da kanta tana kara duba sakon.
“Wane irin hakora kuma? Yaushe na aika da wani sako?”
A nan ma bata samu amsar tambayarta ba, sai ta fita daga message din ta shiga contact list dinta ta nemi number Alfa ta kira shi. Kamin yai picking zuciyarta har bugawa take.
“Alfa...”
“Ranki ya dade...”
“Ka sake aika sakon gidansu Leila ne?”
“Eh, na aika mata da sako”
“Saboda ne? I thought mun yi magana da kai cewar ka dakatar da aika mata komai”
“Ke dakata, ba a min tsawa, yanzu ni nake da iko da ke ba ke kika da iko da ni ba. Kina yin wasa zaki jefa kanki a matsala, kin san case biyu ke kanki ko? Bayan na Leila akwai na yarinyar da kika saka muka dauke, and Ina ta tabbacin cewar kin ji cewar yarinyar nan ta gan ni”
Baki sake Madina take saurarensa.
“Amman na cika maka kudin aikinka a kan yarinyar nan? Miyasa zaka bari yarinyar ta ganka? Wannan ba matsalata ba ce i think na yi nawa yanzu kuma sai ka samawa kanka mafita”
Yayi dariya.
“Sai dai ki sama min mafita, gidan kina son yarinyar nan ta daina ganina dole ne sai ki siye ni, idan ba haka ba duk inda yarinyar nan ta gan ni zata shaida ni kuma asirinki ne zai tonu, shi ne amfanin barin fuska bude da muke ai, saboda irin wannan kasuwancin”
“Ya kake magana kamar ba kasan da wanda kake magana ba”
“Na sani mana, ni zan miki wannan barazanar kuma na kara tunatarda ke cewar kina kara jefa rayuwarki a hatsari ne kawai”
“Ina ka samu hakoran da ka aikawa, Leila, at first na dauka kana amfani da wata atamfar ne saboda ka tsoratata, sai dan yanzu mahaifiyarta ta aiki min sako cewar ka aika musu da hakora da hoto a ina ka samu”
“Ba a tambayar irinmu ina muka samu abu, sai dai ana tambayarmu miyasa muka aikata, ke dai muradin ki a tsoratata ko? Kuma na yi aikina ya rage na ki si siyeni ko kuma ki bar ni na cigaba da abun da zai amfane ni”
“Idan Leila da mahaifiyarta suka mika lamarin a hannun hukuma, ni da kai duk rayuwarmu tana cikin hatsari, domin haka nake shawararta da ka daina abun da keke tun yanzu, kuma ka daina takurawa gawar matar nan”
“Gawar da aka aje a zaune? Aka rufe da kasa kuma aka dorawa dankin ruwa? Wahalar ta nawa kuma? Masu son su wahalar da ita ai sun yi, yanzu kuma kina son ki yi amfani da ita ki samu biyan bukatarki”
Ta lumshe ido ta bude tare da mikewa tsaye ta sauka saman gadon ta nufi windows din dakinta ta tsaya.
“Alfa me kake so?”
“Kudi...”
“Bayan kudin da na baka na aikinka”
“Wacan na abun da za a gabatar miki ne, na yanzu kuma wanda yake tsakanin ni da ke ne”
“Nawa kake bukata?”
“Zaki biya ne gaba daya ko kuma na raba miki”
“Ka fadi ko nawa kake so, zan baka amman zaka min alkawarin cewar ko ganina kai ba zaka tana nuna ka san ni ba, saboda a yanzu kana neman jefa rayuwata ne a cikin matsala”
“Haka nake so, da zarar kin ba ni wannan kudin ba zan sake waiwayarki ba, kuma ba zan sake shaidar fuskarki ba”
“Nawa kake so?”
“Miliyan talatin, idan ya miki nauyi zaki iya ba ni goma yanzu, sai idan na waiwayeki sai ki sake bani goma ko ashiri, ni bana ma matsawa mutane ko biyar kika da hali zan karba na yi sha'anina”
“Are you fucking kidding me? Miliyan talatin? Ina zan samu miliyan talatin? Ai ko rai na kashe diyar bata kai haka ba”
“Ai wannan abun da kika aikata kusan hukuncinsa daya da kisan kai, da zaki kashe rai ki biya diya da zai fi miki abun da kika aikata a yanzu, saboda wannan kina neman rufin asirinki, tsabanin biyan diya da kowa ya san abun da kika aikata”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, daman haka kake? Daman can kai baka a mana da kai? Miyasa zaka juyar da wannan abun a kaina?”
“Baki san iya yadda na yi na kawar da komai ba kamin na samu biyan bukatarki, even mai gadin gidan da aka aje gawar nan kin san yadda na yi da shi? Kin san yadda na yi na gano inda gawar take? No...! Abun da kawai kike so a tsorata Leila kuma an yi”
Ba kai aya ba ta tari numfashinsa cikin kuka.
“Amman ai ba mu samu biyan bukata ba, ban samu abun da nake so ba, Alfa karka jefa rayuwata a hatsari, zaka saka Momy ta fara bibiyar rayuwata, zaka raba min hankali gida biyu”
“Daman can baki shirya ba kika fara, mu haka muke na mu kasuwancin indai har kina son zaman lafiya, dole ne ki bani wannan kudin da zarar kin biya babu ni babu ke”
Ta sauke wayar ta katse kiran tana lumshe ido, bata taba jin tashin hankali ba irin wannan. Baya baya tai har ta isa jikin gadonta ta zauna ta dafe kanta.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, na jefa kaina a cikin hatsari, Momy zata iya kashe ni saboda Leila, kuma wannan mutumen ya sako ni gaba why?”
Ta fashe da kuka mai karfi, kamin tai saurin rufe bakinta, ta mike tsaye ta nufi kofar fita, da sauri ta fito dakinta da zimmar shiga dakin mahaifiyarta sai dai jin motsinta a kitchen yasa ta nufi kitchen din da saurinta tana hawaye. Hajiya dake aikin wanke hannu a tab ta kalleta.
“Madina lafiya”
Madina ta share hawayenta shiga message ta bude sakon da Momy ta turo mata ta mika mata wayar hannunta. Hajiya ta yarfar da hannunta dake da sanyin ruwa sannan ta karbi wayar ta shiga duba sakon.
“Miyasa kika sake aika musu da sakon?”
Ta girgiza kai tana kuka.
“Ban aika komai ba Hajiya, shi ne ya tura mata sakon da sunan ni na aika, kuma na kira shi na yi magana da shi ya ce min sai na bashi miliyan talatin, idan ba haka ba zai tona min asiri har dauke Aminatu da na yi zai tona”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, kin ga ni ko? Kin jefa kanki a matsala saboda son zuciya, kin biyewa zuciya gashi nan ta kai ki ta baro, kin saka kanki a matsala, kuma Momy zata yi komai ta cire yarta daga masifa kuma ta wankenta, ke fa? Kim dorawa kanki dutsen da ba zaki iya dagawa ba balle ki tashi”
“Hajiya ki taimaka min dan Allah, mu bashi kudi, zan yi magana da Leila”
Ta fada tana kama hannayen Hajiya ta rike duka biyun tana kuka domin hankalinta yayi matukar tashi.
“Ba bada kudin ne matsala ba, irin wadannan mutanen da kike gani dama suke nema, ko an bashi wannan kudin zai sake dawowa ya nemi wasu, idan ma mun ji da na shi na Momy ki yi yaya da shi?”
Madina ta mike tsaye hawaye na sauko mata kamar ba gobe.
“To ya zan yi? Talba zan fadawa gaskiya ko kuma yaya?”
“Idan kika fada masa gaskiya kuma, daureki zai yi, a gidan yari zaki kare rayuwarki, babu ke babu auren wani ma dabam balle Talba, kuma duniya zata kalleki a matsayin macuciya, ko wace jarida zata yi ado da ke ace kin ace matar wanda kika kauna saboda son zuciya, kin lalata rayuwarki tun da kurciyarki, ba Talba ba ko wani dabam ba zai aureki ba Madina”
Hajiya ta karasa tana fashewa da kuka mai taba zuciya.
“Kullum ana nuna muku hanya, ba ku gani, kullum kun fi son ku aikata abun da ranku yake so, a kullum ba ku kallon abun da zai biyo baya, burinku kawai, wannan abun da kika aikata zai zubar da kimar gidan nan, kuma ba kedai zai shafa ba har yan'uwanki sai ya shafa”
Hajiya ta dafe kirjin tana jin wani zafi da zuciyarta take.
“Tun ba yau ba, Madina ina ta nuna miki illar abun da zuciyarki take raya miki amman kin kasa ganewa, kin kasa ganin komai, taya zaki ce Talba ya aureki bayan kin san Momy tana raye, kin fi kowa sanin Momy ba kowa take son yana kusantar familynta ba, balle kuma kin san cewa Talba Leila zai aura, yanzu ina fa'idar abun da kika yi? Ina amfaninsa? Da kika aikata hakan ya saka Talba ya so ne? Sai dai ya kara tsanarka, bama Leila kadai ba kin saka wata wanda babu ruwanta a cikin lamarin nan, shine babban abun da zai haifar miki da matsala, da ace Leila ce kawai kika yi ma haka da mafitarki mai sauki ce”
Madina ta kalli Mahaifiyarta.
“Hajiya, da kin san abun da nake ji a zuciyata, da baki lisaffa min duk wannan abun ba, na san na jefa kaina a matsala, amman ban gane hakan ba sai yanzu, yanzu kuma mafita nake nema”
Hajiya ta yi kokarin tsagaita kukan da take ta aje wayar Madina dake hannunta.
“Taya zamu yarda cewar idan aka ba shi wannan kudin zai rabu dake? Zan iya yin magana da Momy zan iya fahimtar da ita, wata kila ta fahimta kuma tai miki uzuri, amman shi wannan fa, taya zai kyale ki?”
“Ba ni da miliyan talatin yanzu Hajiya”
“Ni zan yi mafitar miliyan talatin, kin sani ba zai gagara ba, matsalar kar ya sake waiwarmu ne yace sai mun ba shi wani kudin, kuma na san zai iya”
“Momy ma zata iya kashe ni, zata iya yi min wani abun saboda biyan bukatarta ina jin tsoron Momy fiye da wannan mutumen, domin shi da ni asirinmu daya ne, idan nawa ya tonu nasa zai tonu, amman Hajiya ba zata taba yarda asirin Leila ya tonu ba, kuma ba zata kyale ni ba, tun da har ta san da cewar na san sirrinta”
Hajiya ta kalli yarta cike da tausayin rayuwar data jefa kanta.
“Yaran zamani kenan, ana baku tarbiya kuna daukar taku dabam, ban miki irin wannan tarbiyar ba Madina, kuma ban nuna miki wannan hanyar ba”
Ta karasa tana share hawayenta, sannan ta fice daga kitchen din ta bar Madina a tsaye tana kallon kitchen kamar bakonta.
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
AMINATU POV.
Kwantar da kanta tai jikin Hajiya Laraba tana jin kamar mahaifiyarta.
“Mama ko zamu je gidansu mutumen, ya nuna mana gidan Yaya Bashir ki ganshi, ni ma ina son na sake ganinsa”
“Wace unguwa yake?”
Ta dan yi shiru tana nazari kamin ta amsa.
“Ban san sunan unguwar ba, amman dai gidansu abokin Yaya Talba ne, wannan likitan ki kira shi ki tambaye shi kin ji?”
Hajiya Laraba ta yi murmushi.
“Ba zaki hakura har Talba ya gama nasa binciken ba?”
“Mama na kagu na ganshi, ba ki san yadda nake ji ba a zuciyata, ji nake kamar na runtse ido na je gurinsa”
“To bari na kira Talba ba tambaya, amman ai yanzu dare yayi ba zasu ce mun zo musu a dare ba”
“Ba zasu ce ba Mama dan Allah”
“Toh”
Mama ta kai hannunta cikin jakarta ta dauko karamar wayarta ta kira Talba ta kara a waya.
“Amman karki fada masa cewar tare za mu je, zai iya hanawa”
“Na san yadda zan masa ai”
Hajiya ta fada sannan ta maida hankalinta gurin wayar.
“Hello”
“Salamu Alaikum”
“Wa'alaikissalam Mama har kun isa?”
“Eh, magana ma nake yi da Abban su yake tambayar inda inda abokin naka yake domin su bincika”
Talba yayi murmushi kamar ya san manufar Hajiya Laraba.
“Mama mikawa Aminatu wayar”
“Toh”
Sai Mama ta cire wayar daga kunennta ta mikawa Aminatu, da sauri Aminatu ta daga daga jikinta tana girgiza mata kai.
“Aa Mama ki ce masa bana nan mana”
Sai a lokacin Hajiya Laraba ta fahimcin katobarar da tai, sai tai saurin rufe baki. Talba ya fadada murmushinsa daman yayi hakan ne saboda ya gane idan tana tare da Aminatu, domin ya san ba su isa kaiwa gida ba. Aminatu ta karbi wayar ta kai kunnenta kamar zata yi kuka.
“Hey Baby ban fada miki zan yi bincike akai ba? Why zaki takurawa Mama zai ta kai ki gurinsa?”
“Ya akai ka gane?”
“Ai na san Matata, na san zaki iya haka, ki daina damun kanki gobe zan saka a zo da shi ku yi magana, na san kin kagu ki ganshi ko?”
“Eh sosai”
“Toh zaku yi magana gobe, shikenan?”
“Eh”
“Okay i love you, ki yi addu'a kamin ki kwanta”
“Toh sai da safe”
Ya katse wayar, ta mikawa Hajiya Laraba wayar tana fada mata yadda su kai da shi.
“To kin ga haka ma yafi, gobe idan Allah ya kai mu sai ki taho da wuri”
“Toh Mama”
Ta sake kwantar da kanta jikin Hajiya Laraba. Bata daga ba sai da suka isa gidan, kanen mijinta ne dake tukin motar ya fara budewa ya fita sannan suma suka bude suka fita.
“To ka je ka kai mishi motar na san yana can yana jiranka”
“Toh”
Ya amsa sannan ya koma cikin motar. A dakin da suka saba kwana lokacin da suna gidan ta kwana tare da yayan Hajiya Laraba, sai dai Aminatu ba ta yi wani bachin kirki ba saboda tunanin haduwa da zata yi da Bashir gobe, duk kuwa da kasancewar bata kwanta da wuri ba saboda ta dade suna hira ita da Hajiya Laraba tana fada mata abubuwan da suka faru a gidan Momy lokacin da Talba ta tafi da ita har zuwa ganin da tai ma wanda ya sace ta. Washe gari ana sallah azuba Hajiya ta shigo ta tashe su sukai alwala sukai sallah, sauran suka koma bachi ita kuma ta fito falo ta zauna tana tasbihi da hannunta, daman ta saba zamanta a gidan Hajiya Laraba ta saba mata idan tai sallah azuba bata komawa bachi, tun a wacan lokacin tare da ita suke shirya abun karyawa kamin ta iya ta fara shiryawa da kanta. Tana zaune saman kujerar Hajiya Laraba ta fiton dakin mijinta dake kusa da nata dakin tana sanye da karamin Hijab. Da sauri Aminatu ta duka ta gaisheta.
“Mama ina kwana”
“Lafiya Kalau an tashi lafiya”
“Lafiya kalau”
“Baki koma bachin ba? Ai da kin koma kin kwanta zan shirya muku abun karyawa sai na diba miki wanda zaki kai masa asibiti”
“Aa Mama zan taya ki”
“To, amman kamin nan shiga dakina ki duba kan madubi zaki ga wayoyi ki dauko karamar ita ke da kati sai na kira miki mijinki ki gaishe shi”
Hajiya Laraba ta fada tana murmushi, sai Aminatu ta amsa da to, ta tashi ta nufi dakin Hajiya Laraba kuma ta nufi kitchen dinta. Gas ta fara kunnawa ta tana kokarin dora ruwan zafi Aminatu ta shigo rikr da wayar.
“Mama gashi”
Ta aje pot din ta mika hannu ta karba, ta kira shi sai da wayar ta fara ringing sannan ta mikawa Aminatu tana fadin.
“Wata kila ma be tashi daga bachin ba, tun da baya jindadi”
“Sallamu Alaikum”
Aminatu ta yi masa sallama murya kasa kasa tana jin kunyar Hajiya Laraba data cigaba da aikin da take.
“Daman na ce yau tun asuba zaki kira ni, saboda kin kwana kina tunanina, kuma kin yi ta mafarkina”
Ta dan saci kallon Hajiya Laraba sannan ta girgiza kai.
“Aa Mama ce tace na kira na gaishe ka”
Ya dan tabe baki.
“Kenan dai albarkacin Mama na ci, ba dan kin kwana kina tunani na ba, shikenan na gode”
“Ya jikinka”
“Ban ji sauki ”
“Saboda me? Da gaske?”
“Saboda baki kusa da ni”
“Sai anjima”
Ta fada tana dan murmushi sannan ta sauke wayar tana danna inda ya nuna mata ana kashewa idan ta kira ko an kirata, ma'ana gurin jan maballi.
“Miya ce miki?”
“Wai na yi mafarkinsa shiyasa na kira shi, shi ne na ce masa ke kika saka na kira shi”
Hajiya Laraba ta yi murmushi tana kallon Aminatu.
“Toh ai dan kin ce masa mafarkinsa kika yi kika kira shi ba laifi kika yi ba, ba saki san Namiji yana son ana nuna masa kulawa ba? Namiji yana son a nuna masa an damu da shi, ko da tunawa kika da wani abu da mijinki yake miki na jindadi just picked up your phone ki fada masa na tuna da abu kaza da abu kaza da kake min, zai jidadi kuma zai yi da son yai miki idan na kyautata wa ne zai so ya cigab da kyautata miki, ba laifi ba ne dan kin nunawa mijinki kulawa da jindadin wani abu, Allah yasa dai karatun da muka miki ba ki zubar da shi ba a banza”
Aminatu ta rufe fuskarta da sauri tana murmushi. Hajiya Laraba ta yi dariya.
“Ato, kin ga dai mijinki yana son ki, kika yi sake sai Leila ta kwace miki shi. Ni jiya ma ta tunanin maganar da muka yi na kwana a raina”
“Wace magana”
“Anya ba Leila ce ta saka a saceki ba? Idan ba ita ba waye zai yi haka? Ko ita ko mahaifiyarta kuma Allah kadai ya san abun da suka so su yi miki dan dai kawai Allah be ba su sa'a ba ne”
“Ni ma ina wannan tunanin, saboda tana da zuciya sosai kuma kin ga tana jin haushin na auri mijinta”
“Mijinki dai, ki daina cewa mijinki mijin wata, ko da ta riga ki shiga gidansa balle kin