Showing 279001 words to 282000 words out of 332834 words
ba”
“Amal a gaban idonta komai ya faru, amman ban fada mata yadda na yi da gawar ba, sai dai na gargade na ce ko da wasa ta fadawa wani a cikin gidan nan abun da ya faru sai na kasheta, Kabir kuma nace idan ya fadawa wani zan tsine masa”
“Ba dan haka ba kam, da Amal ta tona miki asiri. Allah ya tsare gaba kuma sai yi taka tsantsan domin za a iya bincikar gidan nan naki fa, a yanzu din ma baki san miye a ciki ba tun da mai gadin ya gudu kuma an rufe gidan”
“Shi me tsorona Wallahi, ni da ina tunanin ko na samu wasu na sa a bincika min gidan?”
“No ai karin tonon asiri ne, abun da ya kamata ki yi kawai ki saka a bankawa gidan wuta a kone ko'ina da komai da komai dake cikin gidan, kin ga ko akwai gawa ba zata shafe ki ba, domin kamin ki bude gidan masu kawo agaji sun rigaki kuma komai ya kone”
Momy ta dan yi shiru tana nazari.
“To idan mun yi haka ita kuma Madina fa?”
“Madina na fada miki binne ta za'ayi”
“Ni fa ban gane binnewar nan ba”
“Gurin wannan bokan zan je yayi mana aiki, ko dai a halbeta ta mutu ko kuma a canja mata gari taje can tai ta hauka”
Leila ta girgiza kai.
“Haba dai mu da muka neman mafita sai kuma mu sake aikata wani laifi? Haba dai mu ji da hakkin dai mana, kar a sake aikata wani abun da zai zame mana fitina, ni abun bokanyen nan ma ba wani yarda na yi da shi ba, gashi nan wannnan da akai ma Aminatu har yanzu shiru kamar ba ayi komai ba”
“Karki damu, komai sai kama ki bar gaggawa”
Leila ta juya ta kalli Momy tana girgiza mata kai.
“Momy aa dan Allah, kar a sake kashe wani rai, wacan kan kuskure ne, gashin alhakin yana ta bibiyata balle kuma idan muka kashe da ganganci”
Momy ta daga mata kai.
“Shikenan, ni ma hakan be min ba, zamu canja wata shawarar dabam, yanzu tashi ki tafi ki kaiwa Talba abun karyawarsa”
“Toh, amman Momy dan Allah dan Annabi Karku kashe Madina dan Allah, idan ma ya zama dole ayi to a nisantata da garin nan amman kar mu kasheta, ita ma zuwa zata rika min a mafarki tana fargita ni kamar Baaba, kuma kin riga kin tira mata wannan sakon dole za a zarge mu”
“Ba zamu yi hakan ba, ki kwantar da hankalinki, ke ma kin san ai ba zan yarda na kara wani kuskurenba”
Ta gyada kai ta share hasayenta ta tashi tsaye ta fice daga dakin daga Hajiya Saratu har Momy binta sukai da kallo sai da ta fice sannan Hajiya Saratu ta kalli Momy ta ce.
“Yarinyar nan bata da wayo sam”
“Ina fa, kin ga garin wannan sakarcin nata ne har kawarta ta ji komai, ai ba zan biye nata ba ta kai ni ta baro, yaushe zaki je gurinsa?”
“Aa ni yanzu da na shirya ai ba zan dira ko'ina ba sai gidansa, irin wannan babban lamari har sai an kwana kansa? Daman kuma ina je saboda na Aminatun nan yanzu kuma sawun giwa ya take na rakumi”
“To, gama karyawa ki shirya ki tafi, daga nan ki fada masa har yanzu ba mu samu ta ci na miyar ba, idan akwai yadda zayi a canja mana da wani sai ya fada, kudi ba matsala ba ne ke kin sani. Ni ma bari na shirya na tafi asbitin”
Momy ta karasa tana mikewa tsaye.
“Zan fada masa komai, har na warin da Leila ta ji zan fada masa”
“Toh, idan zaki tafi ki min magana na baki ATM dina, idan kuma transfer za a miki ya ma fi sauki”
“Wannan kuma ki bar har sai ya fadi abun da za a bashi”
“To ba matsala, Allah yasa mu ji alheri”
“Ameen”
Momy ta fice dakin ta bar Hajiya Saratu da mamakin da ya ki fita cikin kanta.
FARUK POV.
Ya kusan minti talatin zaune a falon, sannan Ramla ta fito a kofar data shiga tare da mahaifinta suna tafe suna hira yana dariya, kana ganin su kasan akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu. Sai da mahaifinta ta fara zaunawa saman kujera sannan ta zauna kusa da shi tana murmushi, Faruk kuma ya mike tsaye ya karasa inda yake mika masa hannu suka gaisa. A lokacin ne mahaifinta ya kalleta.
“To Madam a bani guri business zamu yi”
Ta yi dariya mai sauti.
“Dady korata ma kake yi?”
“Eh mana, kin ga ai ni har yanzu ban san nawa kika dauka albashinki ba, dan haka ba zan bari ki san sana'ata ba, kudi be fi kudi ba”
Ta mike tsaye tana dariya.
“Na ji amman idan an gama a bani la'ada ta”
“Na ji”
Mahaifin ya fada sannan ta kalli Faruk ta dauke kai ta fice daga falon, ko kadan bata nunawa mahaifinta ta san Faruk ba, a cikin dakinsa m da ta matsa masa ya fito cewa tai wani ne a falo yake nemansa kuma ya dade a zaune. Bayan ta fice mahaifinta ya karbi Zinarin dake ciki wata karamar doba, yana dubawa, sannan ya ciro wayarsa ya kira wani yaronsa.
“Ka zo nan falo da kayan awo ka auna mana mana nauyi da ingancin zinari nan”
“To ranka ya dade”
Mutumen ya fada sannan ya katse wayar, babu bata lokaci mutumen ya iso da kayan awonsa ya auna ya fada wa Alhajin ingancinsa da komai sannan Alhajin ya fada masa ko nawa suke sayen kila, da kuma wanda ba kilo ba. Ba karamin mamaki ne ya kama Faruk ba ganin Alhaji Isma'el Zabarma ya siye zinari da be wuce wani karamin dutse ba, har mikiyan bakwai da dubu dari biyu.
“A account za a saka maka kudin ko kuma kasa za a baka?”
“Ranka ya dade a account dai, riko kidi a hannu yanzu ai sai manya”
Alhaji Isma'el yayi murmushi ya kalli mutume dake zaune kasa kusa da shi ya ce.
“Ka karbi account dinsa ka fadawa Ibrahim a saka masa kudinsa yanzu nan”
“Toh ranka ya dade”
Mutumen ya karbi account number din Faruk ya turawa wanda aka umarta, sannan ya dauko littafi ya shiga yi musu takardar shaidar ta mai siye da mai siyarwa kamar yadda al'adar cinikayya da Alhajin take. Kamin ya gama rubuta har kudin sun shiga account dinsa. Da mugun mamaki da farinciki Faruk ya rike wayar yana duba yadda aka jera zerukan dake son rikita shi.
“Ko sun shigo ne”
“Sun shigo Alhaji na gode sosai Allah ya saka da alheri”
Alhaji ya daga masa kai yana murmushi, sannan aka mika masa takardar suka rike daya, kamar zai yi tuntube ya fadi haka ya fito falon cikin wani irin farinciki da zumudi marar misaltuwa. Daga gidan Alhajin asibitin ya nufo gurin mahaifiyarsa, tana ganin yadda fuskarsa take kyalli ga bakinsa daya kasa ruwa ta san danta ya samu biyan bukata. Kusa da ita ya zauna yana murmushin farincikin daya manta when yayi irinsa.
“Mama ya siye, kuma ya saka min kudin a account kin gan su nan”
“Alhamdulillah, Allah ya sa albarka Faruku, Allah yasa silar arzikin ka ne”
“Amin Mama. Amin..”
Ya amsa yana jin kamar ya hade kansa saboda tsabar farinciki.
“Mama wai kin san me?”
“Aa sai ka fada”
“Alhaji nan da na kawai zinarin nan ya siye mahafin nurse din nan ne data kawo miki snacks”
Mama ta kalleshi cike da mamaki.
“Da gaske?”
A nanya kwashe labarin komai ya fadawa Mama, sai tai murmshi.
“Ai kana ganinta ka san yar babban gida ce, yarinyar ta burge ni, ko kadan bata da daukar kai, ko bayan fitarka sai da ta shigo nan tana tambayar inda zaka je wai ta ga ka fita da gaggawa”
Faruk ya dan yi murmushi yana kokarin siyen data ta line sa na Mtn. Rabonsa da chat ma har ya manta.
“Ta cika rawar kai ne, ba zaka ganta ka ce wannan mutumen nan mahaifinta ba ne”
“Kai dai kam kamar baka gama karantar mutane da rayuwa ba Faruk, ai yan adama kamar yatsun hannu suke kowa Allah yayi shi dabam dabam”
“Haka ne, bari na kira Shamsu na tambaya yadda akai maganar gidan”
“Ya kamata kam domin tun da zafi zafi ake duka karfe”
Cewar Mama tana murmushi zuciyarta kal da farincikin daya kasa boyuwa a fuskarta. Yana kokarin kiran Shamsu sako ya shigo email dinsa sakamakon data daya kunna, sai dai be tsaya duba sakon ba ya kara wayar a kunnesa.
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Yana gama waya da Aminatu Ali ya kira wayarsa, sai da ya gyara zamansa sannan yai picking call din ya saka a speaker domin baya jin kai wayar a kunnensa.
“Hello”
“Ranka ya dade ya jikin naka?”
“Alhamdulillah”
“Kana jin wani ciwo yanzu?”
“Yeah kirjin ne kawai sai kuma cikin kaina ina jin yana dan sara min sai dai ba sosai ba”
“Waya kwana da kai Momy ko Aminatu ko Kabir or...”
“Sabuwar dokar asibiti ce dole ku san wanda ya kwana da wani?”
Ali yayi murmushi mai sauti.
“No, akwai abun da nake son tambaya ne”
“Go straight to the point”
“Ba da kai zan yi ba da wanda ya kwana da kai zan yi”
“Kabir”
Ya amsa masa a takaice.
“Okay good zan yi magana da shi, and karka ci abu mai zafi please”
“And you know me bana son abu mai sanyi”
“Yes a yanayin da kake a yanzu ba a son ka ci abu mai zafi ko mai yaji, idan ya zama dole to kar yayi zafin da kake shan tea, jiya ma mantawa na yi ban fada maka ba”
“Na ji, ina neighbor din ku yake?”
“Yana gidansa”
“I need to talk him, Shalele ta damu tai magana da shi”
“You said sai an yi DNA and so on kamin ka barshi ya ganta”
“Yes, just to make sure yayanta ne na gasken, kuma za a je har gurin police tare da Lawyer na, ayi duk abun da ya dace”
“Arrest din shi zaka yi?”
“Why would i?”
“Then why are you taking him to police station with your lawyer?”
“Ba zaka fahimta ba, mutane yanzu ba abun yarda ba ne were not so sure yayanta ne or not, za a iya rabarta a cutar da ita kamar yadda akai a baya, secondly wani zai iya kawo wannan shawarar”
“Amman idan an kawo ita bata san yayanta ba? Haba Talba Aminatu fa ba jaririya ba, ta san idan dai dai ta san akasin haka”
“She's more than that to me, mace bata da wayo ai no matter how old she's balle wannan da yanzu take sanin rayuwa, na bukata ci kamin haka ne saboda ka san halin da nake ciki, da lafiya nake zan iya yin komai da kaina”
“Shikenan, sai kai ma Lawyer naka magana ai”
“Zan tura masa sako yanzu, and the DNA test...”
“I will handle it”
Talba ya katse wayar, sannan ya maida hankalinsa gurin tasbihin da yake da yatsun hannunta. Misalin 7:30am Daddy ya kira shi amsa kiran yayi daidai da shigo Kabir a dakin, kallon kawai Talba yai ya dauke kai yana mikawa Daddy gaisuwa ta wayar.
“Good morning Daddy”
“An tashi lafiya? Ya jikin naka?”
“Alhamdulillah”
“Kana samun sauki?”
“Sosai ma Daddy”
“Ya kirjin naka?”
“Da ji sauki fa Daddy, komai ya daina min ciwo yanzu”
“Alhamdulillah, Allah ya kara tsarewa, kuma sai ka kula da kanka Mu'az, yanzu fa iyali zaka fara, kai da ya kamata ace idan kaga wani yana yi ka hana shi sai kuma ace kai kake yi? Ita rayuwar daya ce, rai daya ne da zarar ka rasa shi ba zaka sake samun wani ba, idan ma kana ganin kamar kai idan ka mutu baka da wata matsala kai tunanin mutanen da suke tare da kai, su ya zasu rayu idan baka raye kuma ya za su ji idan wani abun ya same ka”
“In Shaa Allah zan kiyaye Daddy haka ba zai sake faruwa ba, sai dai abun da Allah ya kawo”
“Haka nake son ji, Allah ya kara tsewa, akan mutumen kuma i talk to CP akwai wadanda za su zo za su dauki Aminatu su tafi da ita gurinsu ta zayyana musu fuskar yadda mutumen take so that a gano waye shi”
“Yanzu?”
“No not now Maybe tomorrow ko anjima, be dai fada min takamaiman lokacin da za a kaita ba”
“Okay, amman da za su bari na ji sauki zai fi Daddy domin ita ma yanzu hankalinta ba kwance yake ba”
“No ba matsala zan yi magana da shi, shi ma kuma na san ba shi da matsala”
“Na gode sosai Daddy”
“Ur welcome”
Kabir ya kalleshi yana dura allura a syringe.
“Daddy's Boy, bani hannunka allura za a maka”
“Bana son ta bachi please”
“Jiya ba ka yi bachi daya kamata ba, ko da aka kira sallah idonka biyu”
“Amman ba ciwo ne ya hana ni bachi ba”
“Miya hana ka bachi?”
“I don't know kawai dai ina ta tunani sai bachi yaki ya dauke ni”
“To mi kake tunani? Kai da kake da komai a kusa da kai, and you got lucky mata biyu ka samu a lokaci daya”
Talba yayi murmushi.
“You know kana tsara rayuwarka, Allah yana tsara maka yadda zata kasance, i never thought zan iya zama da mata biyu, kai ma kuma ai dan baka so ba ne”
“Na kusa ai, ban samu wanda nake so ba ne, kuma ni har yanzu Daddy da Momy ba su maida hankali akaina ba, balle su min maganar aure ko irin dan hadin nan da ake na zumunci ayi min, wai ko bana da farin jini ne”
This time around Talba dariya yake yi sosai.
“Oh Man wane irin farin jini kuma? I swear a whole handsome like me, ace mata basa crushing a akaina, to ko dai aljana ta aure ni ne?”
“joke apart, kai ne dai baka ba su dama, ka cika daure da yawa, and kai ma kanka baka tana ganin wata ka ce kana so ba”
“So nine na cika daurewa? Talba kai har kana da bakin fadawa wani yana daurewa da yawa? Kai ma zuwan yarinyar nan ne ka waye, ta wayar da kai ka shigo gari har kake sakewa da mutane”
Yayi murmushin gefen fuska.
“I love her”
“I know...”
Kabir ya amsa masa, sannan ya zauna kusa da inda yake zaune, ma'ana saman gadon.
“When you meet someone you love, wani abun baka sanin ka yi shi, so babu ruwanshi da matsayi babu ruwansa da kyau ko muni, babu ruwansa da kudi sarauta ko talauci, so na gaskiya babu ruwansa da wannan, yana canja kowa kuma ya caja kowa”
Talba ya kalleshi yana murmushi da kuma tunanin yadda yake magana.
“Ka samu wanda kake so ne?”
“No ban samu ba, zuciyata dai ta fara son wata yarinya”
“A familynmu?”
“No... A cikin asibitin nan, farkon abun da ya fara burge da ita shi ne natsuwarta, natsuwa da kunya yana daga cikin abun da ke karawa mace kyau da kwarjini, ka ga yayan talakawan nan suna da mugun shiga rai, suna da tarbiya sosai ga kunya”
“Ba dukansu ba, ko'ina akwai na kirki a akwai bata gari”
“Na sani, amman mafi yawansu haka suke, suna da natsuwa da tarbiya”
“Finally Kb is in love”
Talba ya fada yana dukan kafadarsa. Sai ya kara fadada murmushinsa.
“Yes, but the most funniest part is i don't even know how to approach her, should I say hey beauty how are you can i get your number or hey I'm Kabir by name what is your name? Or no maybe it will better if i say yan mata zan iya kai ki gida? No...”
Ya dafe hancinsa yana jin kalaman sun masa wani irin, sam a rayuwarsa be taba taron mace ya tsayarda ita da sunan so ba, not even in chat be san ya nunawa mace wani abu soyayya ba. Talba yayi murmushi mai sauti.
“Or Maybe it will be better if you help her idan mai neman taimako ce, kasan wasu matan basa son tambaya kai tsaye, wasu ma zasu ga kamar wulakanci cewa ka rage musu hanya or something like that, kar kuma kaje wa mace kai tsate wai ina kaunarki, ka fara da wani abun da take so ko yake burgeta, is she working here?”
“No i think jinya take yi”
“That's mean you can lose her anytime, you have to make some effort to save your love”
“Duniya juyi juyi yau kake ba ni tips akan love”
Kabir ya fada yana kallon Talba da murmushi a fuskarsa, Talba ma murmushin yayi
“Yes, because now you're in my shoes”
“Fine ba ni hannunka, na bar allurar ta sha iska”
Ya fada yana kokarin canja needle din.
“No please na fada maka ina bana son ta bachin nan, zan yi bachi da kaina anjima”
“Okay, but make sure kana cin abinci ka sha maganinka”
Ya aje allurar.
“Okay Doc”
Kabir yayi dariya tare da juya ya kalli kofar da aka turo aka shigo. Aminatu ce dauke da basket din abincin da Hajiya Laraba ta zuba Talba, Mijin Hajiya Laraba yana bayanta. Kabir da Talba suka hada baki gurin amsa masa, sai ya karasa gurin Talba fuska sake yana masa ya jiki, Talba ya amsa yana tambayarsa ya aiki da yara.
“Komai lafiya, mamanka tace a gaishe ka, zata zo anjima”
“Okay Allah ya kaimu”
Kabir ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya fice daga dakin ya wanda hakan ya bawa mijin Hajiya Laraba zaunawa yana fadin.
“Ai abun ya zo da sauki ma sosai, Allah dai ya kara tsarewa”
“Ameen Ameen”
Sai ya mike tsaye.
“Bari na wuce yara zan sauke school kar su yi lati”
“Okay”
Ya ciro kudi mai dan dama ya mikawa Aminatu.
“Karbi wannan kya rage wani abun”
Sai ta girgiza masa kai da sauri.
“Aa akwai komai a nan babu abun da muke siye”
“To kyauta ake ba ku, in da ke da kurciyarki, karbi mana”
Ya fada, sai Talba ya ce.
“Wallahi babu abun da zamu karba, haba ziyarar ai ita ce mai muhimmanci”
Rantsuwar da Talba yai