Showing 222001 words to 225000 words out of 332834 words
su hadu. Bayan sallah magarin ya dawo falon ya zauna, plasma ma kawai yake kallo Amman hankalinsa yana can gurin Aminatunsa, samun kansa yai da murmushi tunawa da yai da wasu abubuwan da suka wakana a tsakanisna da ita. Yana zaune a falon har Mairo da Zulai suka Gam jera abincin dare sannan suka fice zuwa bangarensu. Sai da akai sallah Isha'i sannan Kabir ya shigo falon, a lokacin Talba na zaune yana taba wayarsa.
“Kai kadai kake zaune? Ina amarya?”
Talba ya dan yi murmushi ba tare daya kalleshi ba.
“Ka karbo wayarka?”
“Yeah, amman ba wani update, wai Mutumen da suka gani a line wani igbo ne”
Ya fada yana kokarin zaunawa. Talba ya dago ya kalleshi.
“An ganoshi ne?”
“No mutumen da tai register line dai”
“Maybe sun siye line ne suka yi amfani da shi”
“Su ma haka suke tunani, amman dai zasu cigaba da bibiyar line ko za su samu wani abu”
Talba yayi shiru be ce komai ba. Kabir ya nufi dinning ya bude warmers din sai kamshi ya fara tashi na tuwon siyo da miyar danyen kubewa data ni ganda da kifi da nama.
“Wow...”
Ya fada sannan yaja kujera ya zauna. ya dauki plate ya zubawa kansa abincin ya fara ainawa cikinsa. Har ya ci ya koshi ya tashi ya bar falon Talba ne motsa daga inda yake ba. Contact dinsa ya shiga ya kira line Amal ringing daya ta dauka.
“Ya Talba?”
“Ba zaki ci abincin dare ba ne?”
“Zan ci”
Tana amsa masa sai ya kashe wayar, sai gata ta sauko sanye da tufafinta na bachi kanta babu dankwali, gabanta sai faduwa yake domin har yanzu ganin take Talba zai iya mata magana akan abun da tai.
“Ya kai ma zaka ci?”
“Me aka dafa”
Ta karasa dinning din ta bude tana dubawa.
“Tuwo ne”
“Na san tuwo ne ai, tuwon me?”
“Semo”
Ya girgiza mata kai alamar aa. Sai taja kujera zata zauna.
“Je ki kira mai sunan Momy ku ci abincin tare”
Fasa zaman tai ta juyo ta nufo dakin da Aminatu take, daga bakin kofa ta tsaya tana mata magana.
“Ya Talba ya ce ki ta so mu ci abinci”
“A nan zan ci”
Amal ta juyo ta kalli Talba.
“Wai a nan zata ci”
Talba ya fyada mata kai, sannan ya mike tsaye ya isa dinning ya zuba mata abincin da kansa ya saka man shanu sannan ya dauka ya nufi dakinta, ba tare da wahala ba ya shige dakin sakamakon barinsa bude da Amal tai a dazun. Amal dai sai kallonsa take gulma na cinta rai kuma bata san da waye zata yi ba. Zaune ya same ta saman dankwalinta tana kallon kofar dakin.
“Ki daina kadaice kanki, idan kina so ki rika fitowa kina zaunawa a falo ko harabar gidan”
Ya fada bayan ya aje mata abincin, ita dai bata ce komai ba, ta sauke ido kasa tana kallon tuwon da yai mata kama da na masara.
“Tuwon masara?”
“Aa na Semo ne, shi ma yana da dadi ki ci ko koshi kin ji?”
Ta daga masa kai, sai ya juya ya fita be dade ba ya dawo dakin da ruwan sanyi na roba da cup ya aje mata a gabanta.
“Karki yi saurin bachi, maybe Daddy zai kai goma na dare kamin ya dawo, ina son ku gaisa da shi”
“Toh”
Ta fada tana auna yadda zata ci tuwon da cibi domin da hannu ta saba cin abinci. Matsawa yai kusa da ita ya sumabanci goshinta ya shafa fuskarta sannan ya fice daga dakin. Tana ganin ya fita ta tashi ta shiga bandakin ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin tuwon.
Sosai ta ci shi saboda yunwar da take ji gashi kuma ta ji shi kamar tuwon masara da suka saba ci a garinsu.
Bayan ta gama ta wanke hannunta ta dauki plates din ta fice da su daga dakin zuwa falo, bata ga kowa a falon ba sai Amal sai ta doshi inda Amal din take tana cin abinci.
“Ina ake aje kwanuka idan an ci abinci?”
Amal ta nuna mata da hannu, Aminatu ta nufi kitchen din farkon shigarta sai ta rasa inda ma zata aje kayan, sai da ta kare kallon yadda tsarin kitchen din yake da yadda aka kawata ko'ina sannan ta matsa kusa da inda ta ga an aje wasu kwanukan ta aje, fito.
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Yana fita daga falon ya koma part dinsa ya dauki key din motarsa ya fito ya shiga motar, yana mata key ya danna horn alamar fita zai yi, da sauri masu gadin suka bude masa gate. Reverse yai ya fice daga gidan, sai da ya isa bakin gate din gidan Ali sannan ya kira shi ya sanar masa yana wajen gidan. Kashe motar yai ya fito ya zagaya bayan motar ya tsaya yana kallon gidajen dake makota da Ali.
“Yau kuma a wajen kake son tsayawa? Ko kuma fushin har yanzu baka gama ba?”
Ali ya fada yana dariya, sai Talba ya juyo ya kalleshi da dan murmushi kadan a fuskarsa.
“Sai ka ce wani karamin yaro dai?”
“To ai naga ka dauka da zafi ne sosai, ka ki ka sauko”
“Wanda ka taba ce mai zafin shiyasa ban saurara maka ba, you know sometimes zaka iya yi ma mutum abu ya share weather ya ji zafin ko akasin haka, amman idan ka taba wanda yake da muhimmanci a rayuwarsa sai ya ji yafi tsanarka fiye da kowa a duniyar nan”
“Yeah”
Ya fada yana tuna yadda yake ji idan ya musgunawa Leila ko ranta ya bace. Shi ma yana jin ba dadi saboda ya damu da ita, ba wai dan yana sonta ba.
“So you have to be very careful next time, idan ma akwai wani da kake ji a zuciyarka game da Aminatu, ka aje shi a cikin ranka, she's my wife and i love her, ko da ace bana sonta ba zan lamunci wani ya ci mutuncin ko fada mata wata magana marar dadi ba saboda tana karkashin ikona kulawarta tana karkashina, balle kuma ina sonta”
Yayi murmushi mai sauti.
“Yanzu ka yarda kana sonta kenan? Da can baya ai baka yarda ba”
Shi ma murmushin yai ya kalli bangarensa na dama.
“Na yarda, domin na ji abun da ban taba ji ba, a lokacin data bata, kamar na yi hauka haka na ji, kuma data dawo sai na gane na fi batanta haukacewa, i believe ba tausayi ne kawai ba har da kauna”
“Tana ina yanzu? Asibiti?”
“No tana gida, Momy ta bukaci na aje ta gidan i have no other choice, sai idan na ga da matsala sannan na canja mata guri, kuma na san zaman da zata yi na dan lokaci ne”
Ali yayi murmushi.
“Leila zata yi kishi wata zata rigata tarewa, Talba baka da kirki”
“Na yi kokari fa Ali, na yi bibiyar yarinyar nan mu yi aure amman taki, kuma ka san at my age ya kamata ace na aje yaya ma, kuma ni kaina ina bukatar auren Ali”
“To ai kai ne baka fiton ta sigar da zata gane ba, kai ka rika yin abu cikin izza da nuna isa”
“Amman duk da haka na nuna, kuma yi magana ai ya kamata ta saurareni ta amince ko?”
“Ai ko yanzu da kai da wanda be yi auren ba duk daya, tun da baka tare da matar ba”
Cewar Ali yana masa dariya.
“Da babu ai gwara ba dadi, kuma idan Momy bata duba ta ji tausayina ta barmu mun tare ba, matsala zata biyo baya, domin ba zan ga samu na ga rashi ba, wai ance ga koshi ga kwanan yunwa”
“Ina mamakin yadda kake sakewa da yarinyar Aminatu, baka yin haka da Leila”
“Nima ina mamakin kaina wani lokacin, sai dai ka san komai shi yake samawa kansa muhalli, Amina bata da girmankai da jin kai kamar Leila, ita dai barta ga shagwabar kuka, idan na ce ta daina abu kaza zata daina, kuma na fahimcin tana da jin magana tun a yanzu, what do you expect idan mun zauna a gida daya a matsayin miji da mata? But look at Leila the way da take dress ta fita bana so, kuma ban isa na yi magana ba, ba canjawa zata yi ba, wani abun kuma Momy zata fara shigar mata tana cewa wayewa ce ko kuma ina takura mata, Ali abun da baka sani ba, Leila tana takama da kudi, tana jin Daddy yana raye, and even between her and Amal Momy ko da yaushe tana side din Leila, so Leila tana jin babu abun da zata rasa, not like Aminatu, data rasa Mamanta Babanta da duka familynta, and now na aureta idan ban tausaya mata ta ji sanyi a gurina ba a ina zata ji shi? Bana ma fatar juya mata baya”
“Haka ne, kana da gaskiya, Allah ya baka ikon rike su duka da amana da kuma adalci”
“Aamin, shi ne fata na gari”
Ali ya jingina jikin motar ya rumgume hannayensa yana kallon Talba.
“Na Kira ne na kara baka hakuri ne akan abun da na yi, na ji ba dadi gaskiya”
Har Talba ya bude baki zai yi masa wata magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi.
“Saboda kana... Ba komai komai ya wuce ai”
“Secondly kuma Madina ta kirani tana kuka wai Momy ta zarge ta da shirya abun da ake yi ma Leila”
“Me ake yi ma Leila?”
“I don't know, na tambaye ta, sai tace min be kamata ma ta yi min maganar ba, saboda sirrinsu ne”
“Wane irin sirrin kuma bayan ta fada maka?”
Ali ya daga kafardarsa.
“Ni ma dai shi na gani, amman kuka take sosai gaskiya”
“Amman ni miya kawo ni cikin maganar ta ne?”
“I don't know ko kai zata fada maka abun da yake faruwa, kuma a yadda suke da Leila be kamata ace Momy ta mata haka ba, ya kamata a shiga lamarin aji me ke faruwa, ko ba komai ta maks hallaci na aje maka Aminatu”
Talba yayi murmushi.
“Abun bashi ne?”
“No amman dai ya kamata ka shiga tsakani gaskiya”
Talba ya kalli agogon, ya sake kallon Ali.
“Zan yi magana da ita, on Monday idan ta shigo office”
“Okay duk yadda kuka yi da ita, please let me know”
Talba ya gyada masa kai.
“Zan tafi kar dare yayi”
“Yayi kyau ango”
Ali ya fada da siffar zolaya yana murmushi. Talba ma murmushin yai ya bude motarsa ya shiga.
“Lokacin da kai naka ai babu wanda ya rikama, ka jira ma wani abun sai na tare”
Ali ya saka dariya sosai, yana kallon Talba cike da mamaki, sai da yai reverse sannan ya fisge motar da karfi. A hanya ya tsaya gurin wani mai gasa kasa ya siya mata daya ya kara gaba ya sai yogurt. Karfe goma da yan mintuna ya faka harabar gidan kusa da motar Daddy. Kashe motar yai ya bude ya fito ya bar kazar a ciki, ya nufo bangaren Momy. Sau daya ya danna door bell din Amal ta bude masa.
“Sannu da zuwa Ya”
“Yauwa, baki kwanta ba?”
“Eh yanzu zan kwanta dai”
“Good je ki kwanta”
“To sai da safe”
Ta nufi upstairs dana yi tana waigensa daman gulma ce ta tsayar da ita har yanzu bata kwanta ba. Tsaye yai dai da ya tabbatar ta haye sama sannan ya juya ya bude kofar ya barta bude ya koma gurin motarsa da sauri ya bude ya dauko ledar kazar da Yogurt ya dawo falon, kamar wanda yai sata haka ya tura kofar dakin Aminatu ya shiga. Kwance ya hangota saman gadon sanye da hijab tana ta sharar bachi. Karasa yai kusa da gadon ya aje mata ledar sannan ya dan risina ya kai hannunsa ya taba ta.
“Shalele”
Ko matsawa ba ta yi ba balle ta amsa, da alama bachin ya mata dadi kuma ya nina. Mikewa yai tsaye gaba daya ya matsa gurin kanta ya cire mata hijab din jikinta ya dauki dayan zanen gadon dake gefen gadon ya lulluba mata, sannan ya zauna kusa da ita yana kallon fuskarta, can kuma ya kai hannu ya shafa fuskar.
“Na ce miki karki yi bachi, saboda ki gaisa da Daddy amman kin yi”
Ya fada yana murmushi still yana shafa fuskarta, yaja hancinta ya kai bakinsa ya hura mata iska a ido.
“Cute girl”
Ya fada sannan ya sumbance ta ya mike tsaye ya fice daga dakin. A hankali yaja kofar dakin ya rufe sannan ya nufi upstairs, tura kofar dakin Momy yai ya shiga da sallama, sai ta amsa masa fuska ba yabo ba fallasa.
“Barka da dare”
Ya fada bayan ya zauna saman kujera, sai ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba.
“Barka dai”
Sai ta cigaba da duba akwatin sarkokin da take, ta yi banza da shi kamar bata san da zamansa dakin ba. A zatonsa zata ce ya kai Aminatu gurin Daddynsa su gaisa amman bata ce masa ba. Yana kokarin tashi wayarsa tai ringing.
Da murmushi yai picking call din Daddy.
“Daddy”
“Ranka ya dade kana ina?”
“Gani dakin Momy”
“Yayi dan gidan Momy, to a sanar da ita na dawo kuma ina son ganinka idan da hali”
“Gani zuwa”
Ya fada yana mikewa tsaye, sai da ya saka wayar aljuhu sannan ya kalli Momy.
“Daddy yace a fada miki ya dawo”
“Toh”
Har yayi kamar yai mata maganar Madina, sai kuma ya fasa ya sa kai ya fice daga dakin, a tunaninsa zai fi kyau ya ji daga bangaren Madina kamin yai magana da Momy, maybe zai san yadda zai bullowa lamarin. Ta cikin falon ya bude kofar da zata sadashi part din Daddy. A falon farko ya samu Daddy zauna yana kallon labarai, sallamar da Talba yai ne yasa ya juyo ya kalleshi with smile.
“Ranka ya dade sai na bukata ake zuwa ganina”
“Daddy da safe baka fita da wuri fa, kuma kasan ka'ida ne idan baka tashi ba, ba zan tayar da kai ba, secondly kuma na yi shiru”
“I know that's why na kiraka ai na bka hakuri, yau na ke da niyar zuwa na dubata sai gashi da dare Momynka na fada min za'a sallame ta yau kuma a nan zata zauna, shiyasa na ce bari na bari sai kun dawo ta gida”
“Amman Daddy...”
Sai kuma yai shiru sakamakon daga masa hannu da Daddy yai yana murmushi.
“Ba sai ka fadi komai ba, na san ina da laifi ai, amman duk da haka ai ya kamata ku zo tare a gabatar min da ita ko? Dan dai kasan gidana na iyalina ne ni kadai, na baku aro ne”
Ba Talba ba har Daddy da yai maganar sai da yai dariya, balle kuma Talba.
“Na ce kar ta yi bachi zata zo ta gaisheka, but kamin na dawo sai na tarar ta yi bachi”
“Ba kai ya kamata ka kawo ta ba ai, Momynka, zan yi magana da ita, je ka kwanta”
“Okay Daddy mu kwana lafiya”
Ya fada yana mikewa tsaye, Daddy ya bishi da murmushi, wannan karon da zai fita ta kofar gaba ya fita ba kamar dazun ba, da ya shigo ta kofar part din Momy.
Aminatu bata farka ba sai asuba, rabon da tai yi bachi mai dadi irin wannan har ta manta, sauka tai saman gadon ta nufi bathroom din dake cikin dakin tana murza ido, alamar bachi be gama fita idonta ba. Fitsari ta fara yi sannan tai alwala ta fito ta nufi inda carpet take shimfide, sai a lokacin ta tuna hijabinta data kwanta da shi.
“Waya cire min Hijab to”
Ta tambayi kanta tana juyowa ta karewa dakin kallo, sai tai arba da zanen gadon daya lulluba mata.
‘Talba ne’
Ta fada a ranta, domin ta san shi kadai zai iya shigowa dakin ya cire nata hijab ya lullube ta, Leila dai ba zata mata haka ba, balle kuma Momy Kabir kuma be isa ya shigo dakin ba har ya lullube ta. Murmushi tai ta nufi inda Hijab din yake ta dauka ta saka sannan ta dawo ta fara sallah.
Raka'a biyu tai ta sallame, a sallamarta ta biyu ne ta lura da bakar ledar dake gafen gadon data kwanta, bata taba ledar ba sai da tai addu'a ta gama, sannan ta kai hannu ta janyo ledar mai cike da maiko. Budewa tai sai tai arba da katuwar kaza, dayar ledar kuma yogurt ce a ciki. Murmushi tai ta shiga bandakin ta wanke bakinta da brush sannan ta dawo ta zauna ta tisa kazar a gaba tana ci. Tun tana ci a hankali har takai bata da gurin numfashi a cikinta, har wani uban nishi take kamar wanda aka ce dole sai ta cinye duka. Ragowar kazar ta hade da kassa ta maida inda ta ganta, yogurt din kam ko taba shi ba tayi ba. Daker ta tashi tana gyatsa ta shiga bandakin ta wanke hannunta ta fito tana ta raunar naman data gagara hadewa. Zaunawa tai bakin gado sai kuma ta haye gaba daya ta kwanta rairai tana kallon fankar dake kashe, ac ne kawai ke aiki. Ba shiri ta zabura ta tashi zaune tana kallon kofar shigowa da ake murdawa, a zatonta Talba ne sai tai arba da Leila dake sanye da tufafin bachi.
“Gimbiya sai ki ta so mu shirya breakfast ko?”
Ta fada tana dan harararta a kaikaice. Uffan Aminatu bata ce ba, duk kuwa da kasancewar ta fahimci abun da take nufi, domin a makarantar da take zuwa talla da kuma mu'amala da dalibai da take tana tsintar wasu kalamai na turanci.
“Ke fa nake jira”
Leila ta maimaita ganin ko motsawa Aminatu ba ta yi ba. Sai a lokacin ta sauko daga kan gadon tana kallon Leila
“Ni ba komai na iya dafawa ba”
“Tare zamu yi ai, ki same ni kitchen”
Leila na fadar haka ta saki kofar dakin ta juya. Aminatu ta turo baki gaba, domin ta san wahalar da ita ne kawai Leila take son yi, tun