Showing 192001 words to 195000 words out of 332834 words
kunna shower ta tara jikinta, sai da ya jike shak sannan ta dauki shower gel ta fara murzawa a jikinta, ta murza ko'ina na jikin da kyau sannan ta daura tawul ta fito rike da wani karamin tawul din tana goge jikinta. A gaggauce ta shirya cikin wata farar abaya ta lullube jikinta da mayafin abaya sannan ta dauki jakarta da key motar da wayarta ta fice daga dakin. Har lokacin mahaifiyarta na zaune a falo inda ta barta kana ganin fuskarta kasan akwai damuwa a tare da ita.
“Ina zaki je?”
“Gidansu Leila?”
“Gidansu Leila”
“Ba yanzu kika fito daga can ba?”
“Suma tai ya kamata naje na dubata”
“Idan har son gaskiya kike wa kawarki ba zaki taba tarayya da abun da kika san rasashi a gareta babbar matsala ba ce”
Madina bata ce komai ba, ta sauke kai kasa ta nufi kofar fita sai kuma ta daga kai ta kalli Tima, sannan ta fice. Tima ta nufo Hajiya rike da serving spoon tana fadin.
“Wallahi Yaya Madina mugun tausayi take ba ni, tana cikin tsaka mai wuya, ki duba halin da take ciki amman duk da haka tana kokarin ganin ta bawa Leila kulawa”
“Nima tana ba ni tausayi, amman idan na ce zan saki zuciyata na nuna mata haka, zata bi son zuciyarta ne wanda zai iya kaita ga halaka mu kuma ya saka mu a dana sani”
“Haka ne”
Ta amsa sannan ta juya ta koma cikin Kitchen din.
Madina na fita daga gidan ta nufi gidansu Leila, sai dai bata tararda kowa a gidan ba, masu gadin suka fada mata an tafi da Leila asibiti. Hakan yasa batai wahalar shiga ba tai reverse tare da daukar wayarta ta kira Ali.
“Hello Ali kana tare da Leila ne?”
“Eh muna asibiti”
“Okay”
Ta katse kiran sannan ta karawa motarta gudu, cikin yan mintuna ta isa asibitin da Ali yake aiki. Ta faka a inda aka tanada dan aje ababen hawa, sannan ta bude motar ta fito ta sake kiran number Ali, sai ya fada mata cewar shi yana office, Momy da Kabir kuma suna ICU room 21. Asibitin ba bakuwarta bace hakan yasa bata tsaya tambayar kowa ba ta doshi ward din tana tafe kalaman Talba na mata yawo a kai har ta isa bakin kofar dakin. A hankali ta tura kofar dakin ta shiga da sallama muryar kasa kasa, Kabir ta samu a jingine ya rumgume hannayensa yana kallon kofar shigowa, Amal kuma na zaune a kujerar dake facing din gadon Leila, Momy na zaune kan gadon kusa da Leila ta zuba mata ido, bata dago ba har sai da Madina ta karasa kusa da gadon.
“Momy ina wuni?”
Momy ta kalleta kamar ba zata amsa mata ba, sai kuma ta amsa mata din ta dauke kai.
“Lafiya Kalau”
“Ya jikin Leila?”
A nan kam Kabir ne ya amsa mata, domin Momy bata sake kallonta ba ma balle ta amsa mata din. Ita kanta sai ta sha jinin jikinta saboda yanayin yadda Momy tai mata, daman can bata saba sake mata ba, sai dai wannan karon tafi daure mata fiye da ko yaushe, wata kila saboda tana cikin damuwa ne, wata kila kuma saboda ta yi kuka ne a dazun ta fita ta bar gidan bata tsaya duba halin da Leila take ciki ba. To ko dai ta yi wani abun da be dace ba ne? Haka dai tai ta yi ma kanta tambayoyin da bata da amsarsu. Kasa zama a dakin sai kawai ta juyo ta fito ba tare da ta yi musu sallama ba. Tafiya take cikin rashin jindadi tana kallon mutane dake kai kawo, amman sam bata lura da Ali ba saboda hankalinta yana wani gurin dabam.
“Madina...”
Ta kalleshi da sauri, sai kuma tai murmushi.
“Ban lura da kai ba”
“Na ga alamar hakan ai, kin dubata”
“Naga alamar hakan ai hankalinki yana wani gurin, kin dubata”
“Eh, tana bachi kuma na ga Momy da Amal suna kanta shiyasa na fito”
“Okay, gida zaki je?”
“Eh.. Talba fa?”
Ta tambaya tana takawa, sai Ali ya bita suka fara takawa tare yana mata rakiya.
“Ban san a inda yake ba a yanzu, na kira shi be daga ba”
“Amman ya kamata ka sance tare da shi saboda yana bukatar abokin magana a yanzu, na san abun da yai be kyauta ba, amman shi ma zai iya shiga damuwa”
“Haka ne, dukanmu ido ya rufe mun aikata kuskure, ko da yake ba laifin mu ba ne duk kidnapping din yarinyar da akai ne ya janyo haka”
Madina ta dauke numfashi a hankali ta sauke a asirce.
“Amman kai wa kake zargi?”
“Na rasa wa zan zarga, wata kila wadanda suka dauke ta sun dauke ta ne saboda neman kudin fansa, wata kila sun ganshi a tare da ita, ko kuma suna bibiyarta ba tare da shi ya sani ba, ko kuma suna bibiyarsa ba tare da ya sani ba, da ba su samu sa'ar sace shi ba sai suka dauke ta, ko kuma suna son sace wani wanda ya fito daga gidan da take ne. Ko kadam bana zargin Kabir bana jin Kabir zai iya yi mata haka, kuma Kabir ma be san inda yarinyar take ba i think, kuma ba zai rika bibiyarsa ba akan abun da ba zai amfane shi ba, Leila ma bana zaginta, saboda tana son Talba, na san tana da zafin kishi amman ba zata aikata irin wannan abun ba, saboda zai ja mata tsana ne kawai da kiyayya a gurin Talba, ba Talba kasai ba ni kaina da duk Familyn gidan nan za su tsaneta saboda abubuwan da suka faru a yau na bacin rai, kuma Daddy zai iya fushi da ita, idan ma har Leila ta ga wani abu makamancin wannan nine mutum na farko da zata fara kawa ma karar Talba, kuma idan ma ta tsara wannan abun ai zaki sani tun da kawarki ce...”
Ya karasa tare da kallonta. Wani irin dauke wuta Madina tai ta hade abu da karfi sannan ta gyada masa kai.
“Ba.. Ba.. Ba Leila ba ce, amman duk wanda yai wannan abun be kyauta ba ko...?”
“Be kyauta ba gaskiya, domin Talba ba zai taba yafe masa ba, na san yadda Talba ya bada cigiyarta In'Shaa Allahu za a ganta, ko ma suwaye za a kama su, kuma dole su fuskanci hukunci”
“Allah ya bayyana ta cikin aminci.”
Madina ta fada, sai Ali ya amsa da amin. Har gurin motarta ya rakata sai da ta shiga sannan ya juyo ya dawo cikin asibitin. Key tai ma motar sai da a bar asibitin sannan ta faka gefen titi ta kai hannu ta dafe zuciyarta ta lumshe ido.
TALBA POV.
daga office din Daddy gidansu Hajiya Laraba ya wuce, ya dade a wajen gate din tsaye yana kallon daidai inda suka tsaya ranar, da irin nishadin da suka yi sannan ya danna horn aka bude masa ya shiga ciki. Ya faka a harabar gidan ya bude ya fito ya doshi kofar falon dake bude ya shiga da sallama ba kamar wacan karon ba daya shiga babu sallama kuma hankali a tashe, a yanzu ma hankalinsa ba a kwance yake ba, sai dai a yanzu yana cikin natsuwarsa.
“Allah yasa an dace”
Kallonta kawai yai ya kawar da ido ya mika mata wayarta daman tun cikin mota ya tura hotunan Aminatu a sabuwar wayarsa.
“Ga wayarki, na saka report ta ko'ina, kuma police dinsun ce idan bukatar bincikenku ya ta so zasu neme ku”
“To Allah yasa a dace, amman dan Allah karka fadawa Kaka saboda hankalinta zai iya tashi kuma ka san tana da hawan jini”
Ta fada cike da damuwa, fatar idonta har ta yi taushi saboda kuka. A gidan yai sallah La'asar gaba daya addu'arsa a sujadar karshe akan Aminatu ne. Bayan ya gama ya fito ya shiga motarsa yai mata key ko kamin ya danna horn an bude masa gate, sai da ya hau titi sannan ya fara tunanin inda zai je, gida? No ba gida ba, office no ba can ba, gaba daya sai ya rasa inda zai je. Fakawa yai gefen titi ya kunna data wayar ya shiga Instagram app ya saka details dinsa yai loging sannan yai rubutun cigiya a page dinsa ya saka hoton Aminatu da goron da zai bawa duk wanda ya gano inda take. Yana posting kiran Daddy na shigowa wayarsa, da sauri ya dauka cike da son jin labari mai dadi.
“Hello Daddy”
“Mu'az ka same ni a office din CP yanzu nan”
“Daddy an ganta ne?”
“Aa yace za a fara wani bincike ne na musamman”
“Okay”
Ya katse kiran ya juya motarsa ya hau titi, cikin kankanen lokaci ya isa gurin, ya kira Daddy ya sanar masa a inda yake Daddy ya aiko da police aka shiga da shi ciki. Few tambayoyin Cp yai masa bayan sun gaisa har yake tambayar ko akwai wanda yake zargi? Talba ya kasa amsawa taya zai ce yana zargin Kabir ko Leila a gaban Daddy anya Daddy zai jidadi ko da be nuna masa ba ya san hakan zai taba shi.
“Ka fada mana, so that mu saka ido akansu”
“Aa babu wanda nake zargi”
“Amman bayan kai waye ya san inda yarinyar take?”
“Ni ne kawai”
Ya fada saboda baya son saka Ali a cikin matsalar kar su fara bibiyarsa shi ma.
“Okay, zan hada ka da sashen bincike na musamman za su yi aikin mai kyau, kuma za su je su kwaso duka mutanen da suke cikin gidan saboda amsa wasu tambayoyin, idan ta kama ma har cikin gidan za su shiga su yi bincike, ina fatar za su samu hadin kai”
“Ba matsala”
Talba ya amsa. Kamar yadda ya fada haka akai ya hada Talba da masu bincike kan kisan kai da kidnapping suka hau yi ma Talba tambayoyi kamar ance musu shi ya sace ta, sannan suka aika da mota aka gayyato Hajiya Laraba da mijimta da duka yaran gidan har da Mai gadi suka hau yi musu tambayoyi jikin mai gadi sai bari yake yana amsa musu a tsorace. Sai kusan magariba Talba ya baro gurin Daddyn ka daman tun da CP ya hada Talba da masu binciken ya bar gurin zuwa asibiti.
A waje yai sallar isha'i sannan ya shigo gidan cike da damuwa, gaba daya sai ya rika jin kamar daman can ya saba da Aminatu kamar a gidan suka rayu yau kuma bata nan, kewarta ta kama shi. Yana shiga dakinsa ya jingina da kofar yana kallon dakin kamar a yau ya fara ganinsa, sai dai gaba daya hankalinsa ba a gurin yake ba. Closet ya nufa ya raba jikinsa da sutura ya sannan ya daura tawul ya nufi bathroom, yana shiga ya cire tawul din ya aje ya kunna shower ya sakarwa kansa ruwa. Da ya gaji da tsayuwar sai ya zauna a cikin bathtub din ya lumshe ido yana ta sauraren yadda ruwan ke sauka a kansa.
AMINATU POV.
Ba zata iya fadar hanyar da aka bi ba domin idanuwanta a rufe suke, iyakar abun da ta sani sun yi tafiya mai nisa da ita kuma sun yi ta karwade karwade kamin su isa inda zasu aje ta. Bayan sun faka suka fito da ita suna haska fitila zuwa cikin katon gidan mai kama da sabon gida, sai dai ota baya iya ganin komai saboda idanuwanta a daure suke, mutumen daya daukota kuma ya sabata ne a kafada, saurare take ta yi har ta suka isa da ita cikin wani daki suka sauke ta, sannan dayan ya kai hannunsa ya bude mata idon, dayan kuma ya haske mata idanuwan da fitila sai ta kara runtse idon daman bata budesu ba.
“Ka tada mana injin mana”
Ta natsu sosai tana sauraren muryarsa, wai ko zata ji muryar wanda ta sani. Bata bude idon ba har sai da aka kunna engine din haske ya maye ko'ina na dakin, sannan ta bude idonta a hankali ya kallesu, zaratan mazaje ne gudu hudu saba uku da ta gani lokacin da suka je dauko, daya bayan daya ta bisu da kallo dukansu fuskarsa a rufe take ban da mutum daya dake tsaye s gabanta, fari ne fes farin har ya so yai masa yawa, gashi faffada da jiki sai dai ba sosai ba, ta fi kura masa ido saboda shi ne fuskarsa take a bude kuma shi ne yai mata yanayi da Talba a lokacin da ya saka face mask, sai dai a yanzu ta gane a farin ne kawai sukai kamanceceniya, a fuska ba su da kama ko kadan.
“Kin san ni ne?”
Ta sauke kai kasa. Sam ba zaka ganta ka ce tana jin tsoro ba, domin bata nuna tashin hankali ba, kuma bata yi wani kwakwaran motsi ba, sai dai behind her face duniyar tsoro ce da zullumi, gaba daya sai wacan abun daya faru a wacan daren ya dawo mata sabo, su ma wadannan fyaden zasu mata? Miyasa suka dauko ta? Tana jin lokacin da suka fita suka rufe kofar dakin da karfi har da saka makulli, sai ta rumgume hannayenta ta kwanta akan tiles din hawaye da suka duniyar idanuwanta suka sauko mata sai har lokacin bata bude idon ba. A gurin suka barta ta kwana har safe sai takwas da wani abu suka bude dakin suka shigo sai suka same ta a zaune tana kallon kofar kamar dama tana jiran shigowarsu, wannan karon ma kowa ya rufe fuskarsa ban da mutum daya din nan na jiya. Abinci suka aje mata tare da ruwa.
“Kina bukatar wani abu?”
Dayan mai sanye da mask ya tambaya, sosai bakinta yai mata nauyi sai dai hakan be hanata yakar nauyin bakin ba har ta samu fitar da kalamanta tana kuka.
“Ba ni da uwa, ba ni da uba, ba ni da kowa, idan ma kun dauke ni ne saboda a ba ku kudi babu wanda zai ba ku, an kashe min kowa, kuma ban yi ma kowa komai ba, dan Allah karku cutar da ni, idan ma wani abun na yi muku ba tare da na sani ba, dan Allah ku yi hakuri”
Ta hade hannayenta tana rokonsu. Juyawa suka yi suna fita daga dakin daya bayan daya.
“Ni musulma ce, ina son zan yi sallah”
Ta fada kamin dayan ya karasa ficewa, sai ya juyo ya nuna mata kofar bathroom.
“Ga bandaki can kusa da ke”
Yana fadar hakan ya fice, sai ta juya a hankali ta kalli bathroom din, sai a lokacin ta lura da shi, kwantawa tai a gurin tana wani irin kuka mai taba zuciya, kalaman Inna suka dawo mata na cewar ta adana hawayenta kuka na gaba, a yanzu ta yarda da wannan.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Ta fara maimaitawa tana bugun tile din gurin kamar zata ballashi.
________________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
BATURIYA POV.
Ji tai kamar kasa ta bude ta shige ciki, duk sanyi ac dakin sai ta ji gumi na kefo mata. Shi ma kansa kunyarta yake ji kuma yana jin kunyar kansa, ya kasa kallon inda take sai girgiza kai yake, be taba tunanin neman matansa zai kawo sa gurin kanwarsa, sam be ma taba tunanin kanwarsa na aikata irin wannan bakar sana'ar ba, kamar marar lafiya haka ya tashi ya nufi gefen gadon can nesa sa ita ya zauna ya dafe kai yana jin kamar yai kuka kuma ba kukan zai yi ba. Tana ganin haka ta sabi jakarta ta sulale ta nufi kofa, garin sauri ta fice daga hotel din ta manta face mask dinta har wani hade kafafuwa take. Tana isa gate din ta fara kalle kalle ko zata ga Napep, tafiya tai mai nisa sannan ta samu isa gurin da Napep din take sai da ta shiga ciki sannan ta fada masa inda zai kaita, nesa da gidan ya ajeta ta fita ta ciro 500 ta mika masa bata ko tsaya karbar canji ba ta fara waige waige ko zata ga wanda ya ganta. Sai da ta ga babu mai binta sannan hankalinta ya kwanta, ta daidaita natsuwarta sannan ta karasa gidan tana ta sake saken abun da zata fadawa Umma. Da sallama ta shiga falon ido wiki wiki kamar an kama barawo.
“Umma ba ki kwanta ba?”
“Karfe nawa yanzu? Yaushe aka gama sallah Isha'i ma”
“Ok ke haka ne”
Ta fada sannan ta zauna tana Allah Allah kar Umma ta tambeye ta inda ta tafi, a zatonta Umma zata yi tunanin ko suna waje ne suna zance.
“Ina kika je?”
Ta hade yawu.
“Wai yayarsa ce da bata da lafiya, shi ne yace na je na dubata, shi ne muka je tare”
“Yayarsa kuma? Yaushe kuka hadu da shi da har zai fara gabatar da ke a gurin danginsa?”
“Gaskiya mun kwana biyu da haduwa, kuma yana zuwa akai akai kawai dai ban bashi dama ba ne”
“To ya kamata ki tsayar da mutum daya, tun da kina da maneman nan, na fara gajiya da yawan fitar nan da kika”
“Ai yanzu kam indai ba wani uzuri ba da wahala na fita”
Umma ta yi shiru bata ce mata komai ba, ganin haka yasa Baturiya ta tashi sususu ta shige dakinsu. Cire hijabinta tai ta zsuna ta rafka tagumi tana tunanin daman duk gani ganin da take yi ma yayanta yana wannan dabi'ar? Tana boyewa gashi yanxu tun ba ta yi nisa ba asirinta ya fara tonuwa duk da ta san ba lallai ne ya fada ba saboda shi ma nasa mutuncin zai zuba a idon mahaifiyarsu. Hannu ta saka a jaka ta dauko wayarta ta kira Ramlee tana dagawa ta fara bata tambayarta inda ta san wannan