Showing 309001 words to 312000 words out of 332834 words
baki fada min takaimaman abun da ya faru tsakaninki da Fahat din da da kuma Faruk din da naji kina ambata”
Rafi'a ta ji gabanta ya fadi, domin An hanata abota da Ramlee saboda rashin tarbiyarta da kuma wasu halaye da ake ganin ta kirkiro ma kanta tun suna secondary school a lokacin Mahaifinta yana da rai, babu irin jan kunne da be yi mata ba, akan kar ya sake jin sunan Ramlee ma a bakinta, kasancewar sun shaku a makaranta sanadiyar kudin da Ramlee take samu a gurin maza tun tana da kurciya, tana kashewa yan makarantar sai dai ta fi kyautata Rafi'a domin jininsu yafi haduwa not because of Baturiya tana yar iska ko wani abun makamancin haka, sai dan jininsu da Allah ya hada, Ramlee tana son Baturiya sosai, ita kuma Baturiya ta tashi da kwadayi abun hannun Ramlee na burge ta hakan ya saka suke shiri sosai, ada can har gidansu Rafi'a Ramlee tana zuwa ta wuni ko ta kwana, sai dai daga lokacin da Mahaifinta Baturiya ya samu labarin abubuwan da Ramlee take sai ya datse abotarsu ya hana ta zuwa gidan kuma ya ja kunnen Baturiya akan Ramlee.
Duk irin tsoron da Baturiya take yi Mahaifinta be saka ta rabu da Ramlee ba, tana abota da ita a boye, har zuwa lokacin da Ramlee ta zama rikakkar yar duniya ta waye ta iya barikin ta gwane, sai dai babu wanda ya taba sanin alakarsu ta cigaba saboda bata nunawa a gidansu. A kokarinta na dauke hankalin Umma daga zancen Ramlee ta dauko mata labarin abun da ya faru a ranar, a lokacin ne wani sabon kuka ya zo mata, Umma kuma ta cika da tsakanin mamakin yadda akai Fahat da Faruk suka san juna, amman bata yarda da zancen da Baturiya ta fada mata cewar Fahat ya ce Faruk ya samu aiki ba, idan ma ya samu bata tunanin wani babban aiki ne, kai koma dai babban aiki ne, tana jin yarta ta fi karfinsa a yanzu, kuma zata iya samun wanda ya fishi ya fi Fahat komai da komai.
“Lallai ma Fahat din nan ya cika tsohon dan iska marar mutunci, bayan yace ya fasa aurenki sai kuma ya biyo ki da wasu kalaman banza har yana dauko Faruk ya kawo miki, ke kika son saka kanki cikin damuwa tun farko, namijin da ba shi da tabbas zaki zauna kina wahalar da kanki akansa? Ba gashi shi har ya manta ba? Har yana neman ci miki fuska, da acw da gaske yake sonki so na tsakani da Allah ai da ba zai biyoki da wata maganar banza ba, sai rarrashin”
Baturiya dai ban da zallar hawaye babu abun da take, ba zata iya fadar cewar ta yi nadamar saka son Fahat a ranta ba for now, kamar yadda ta kasa ayyana bakincikinta na rabuwa da Faruk a yanzu tana ganin wata aikata laifi ba, sai dai ta kasa natsuwa da ko wanne.
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Fasa shiga motar Talba yai sai ya baro jikin motar ya nufo inda Daddy yake faka motarsa. Direba na yin parking Daddy ya bude da kansa ya fito yana kallon Talba.
“Ina zaka je?”
Talba yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada.
“Daddy sannu da zuwa”
“Jikin da sauki sosai? Na fadawa Ali kar ya bari ka dawo sai ka samu sauki sosai”
“Na ji sauki Daddy”
“Haka ake so, amman karka ce min driving me zaka fara yanzu”
Ya dan yi murmushi ba tare da ya ce komai ba, suka jera shi da Daddy zuwa bangaren Momy. Talba ya mika hannu ya danna door bell din kofar yana kallon Daddy dake fadar.
“Kabir ya kira ni yanzu, wai an gano Madina ce ta sace yarinyar nan?”
“No, ba Madina ba ce gaskiya, me zai saka Madina tai haka?”
“Ni ma abun da nake tunani kenan, abun ya daure min kai sosai”
Wannan karon ma Amal ce ta bude kofar falon. Ganin Daddy yasa gabanta faduwa kamar ta san ya ji abun da ke faruwa.
“Daddy sannu da zuwa”
“Yauwa Amal”
Ya amsa sannan ya shigo cikin falon Talba na biye da shi. Kabir na ganin Daddy ya mike tsaye Momy kuma ta dago jajayen idanuwanta ta kalleshi. One seat ya nufa ya zauna yana kallon fuskokinsu musamman na Kabir dake nuna tashin hankali karara, fuskar Momy kuma tana nuna alamar ta yi kuka.
“Ba Madina ba ce Daddy, Kabir kai ka fada masa? Ai ba a tabbatar ba”
Talba ya fada yana yi ma Kabir alama da ido.
“Yeah ba a tabbatar ba Daddy”
Daddy ya kalli Talba ya sake kallon Kabir sannan ya kalli Momy.
“Akwai matsala a cikin gidana, kuma idan har ba Madina ba ce dole wani na gida ne ya aikata wannan abun”
“Wallahi ba cikin gidan nan ba ne Daddy kuma ka ji na rantse maka”
Daddy ya kalli Talba da yai maganar yana murmushi.
“Hakan na nufin kasan wanda ya aikata”
Talba ya sauke kai kasa ya kasa kallon Daddy domin ba al'adarsa ba ce yi ma Daddy karya, even for once be taba ba, ko minene zau fade shi kai tsaye ko da ba zai yi ma kowa dadi ba.
“Akwai abun da kuka boyewa, anyway zan yi magana da CP za a bincike ta, akwai wani evidence?”
“Babu Evidence Engr, ba mu da tabbacin ita ta aikata ko ba ita”
Wannan karon Momy ce tai maganar, gaba daya jikinta ya kara mutuwa tun da lokacin da ta fahimci Kabir ya kira Daddy ya fada masa. Daddy ya mike tsaye
“To bincike zai tabbatar da haka, idan babu rame miya kawo maganar rame? Dole akwai wani abu a kasa”
Har ya fara tafiya, Momy ta mike tsaye tana fadin.
“Alakar Madina da gidan nan, be kamata ace an mata haka ba, ko da ace ita din ce ta aikata ballantana babu tabbacin hakan”
Daddy ya juyo ya kalleta ya fara magana cikin fusata da daga murya data cika duka katon falon.
“Ita bata kalli alakar gidan nan ba ta aikata abun da ta aikata, surukata fa aka dauka matar ďana, kuma kina tsammanin saboda wata alaka ta banza da ba yan'uwanta ba sai ta saka na kyale ta? Wallahi ko da ace Leila ce ko Amal ko Talba kansa ya aikata wannan mummunan abun sai na hukunta shi! Idan ma bata aikata ba bincike sai tabbatar da haka, saboda kidnapping din nan na kusa rasa ďana kwanakin baya, kuma kike ganin zai duba alaka na kyale shi”
Sautin muryarsa ne Leila dake dakinta ta ji, sakamakon barin kofar dakin da tai a bude, sai ta taso da sauri ta fito ta fara saukowa stairs din hawaye na sauko mata. Daddy ya daga kai ya kalleta, sai dai be ce komai ba, ita kuma ta gagara saukowa gaba daya sai ta tsaya rabin stairs din tana kallonsa.
“Ka dubi girman Allah ka bar maganar nan Engr, a yafewa Madina har sai idan ta sake aikatawa dan Allah”
Momy ta fada cikin kuka, tana hada hannayenta alamar rokonsa. Kabir ya matsa kusa da Daddy
“Daddy please”
Daddy ya dauke idonsa daga kallon Momy ya kalli Kabir sai kuma ya kalli Talba da fuskarsa ke cike da rauni, kamin ya kalli Amal da ita ma hawayen take, sai kuma ya sake maida dubansa gurin Momy zuwa ga Leila.
“Da hadin bakinki aka aikata”
Talba ne ya amsawa Daddy amadadin Leila da kanta.
“Bata sani ba Daddy, ba da hadin bakinta akai ba, lokacin da Madina zata aikata bata fada mata ba kuma bata nemi shawararta”
Daddy ya kalli Talba, sai dai be ce komai ba, ya juya ga cigaba da tafiyarsa, sai Leila ta kira shi muryarta na rawa.
“Daddy...”
Ya tsaya sannan ya juyo, Momy ta yi saurin kallon Leila.
“Je ki dakinki ki huta, zan masa magana da kaina”
Ta girgiza kai alamar aa tana takowa a hankali ta sauko. Talba ya nufeta
“Leila yanzu Daddy ya shigo, ki bari idan ya huta sai ki je bangarensa ki riko shi akan maganar Madina”
Leila ta kalli Talba.
“Ba rokonsa zan yi ba”
Ta kauce daga tare ta da Talba yai ta fuskanci Daddy dake tsaye.
“Akwai abun da ya kamata na sani ne?”
Daddy ya tambaya yana kallon fuskokinsu daman zuciyarsa ta raya masa akwai abun da ake boye masa.
“Daddy akwai”
Leila ta fada, sai Momy ta daka mata tsawa da wata irin muryar.
“Leila... Ki wuce dakinki na ce”
Leila ta kalli Momy ta girgiza mata kai.
“Aa Momy, lokaci yayi daya kamata Daddy ya san komai, idan aka cigaba da boyewa ba mu san iya inda abun zai kai mu, wata kila lokacin da gaskiyar zata bayyana zai fi yi mim ciwo da Daddy fiye da yanzu”
A hankali take furta ko wace kalma kamar ba ita ba, idanuwanta har wani lumshewa suke saboda hawayen da dake mata zuba.
“Daddy... Na san kasan da zancen batan Baaba.... Ba bata tai ba Daddy... Ni na zama silar ajalinta, ta hanyar turo ta da na yi daga stairs ta fado kasa, a bisa kuskure ban yi dan ta mutu ba, kuma ban yi dan ta fado kasa ba, kawai dai na fisgota da karfi ne na jefar... ”
Ta yi shiru saboda kukan dake cin makoshinta, Momy sai girgiza mata kai take, alamar kar ta fadi.
“Mun dauke ta mu kai ta asibiti, kamin mu isa ta rasu.. Na binneta a tsohon gidan gonar Momy... Wannan ya saka Madina take min barazana saboda tana son Talba, shiyasa ta sace Aminatu...”
Ba Daddy kadai ba, Har Kabir da ya san da zancen kisan sai a yanzu ya san yadda akai da gawar Baaba da kuma dalilin Momy na hana a kama Madina. Tsaye Daddy yai kamar hoto yana kallon Leila, zuciyarsa na bugawa da karfi sai ya ji kamar an watsa masa ruwan zafi a kirjinsa. Can kuma ya sauke kansa kasa ya runtse ido sai dai ya masa motsawa har lokacin. Amal ta nufo shi da sauri ta taba shi.
“Daddy ka ce wani abu please...”
Shiru be furta komai ba kuma be dago ta sake kallon kowa ba.
“Na san na aikata kuskure, sai kuma na sake yin wani kuskuren na boye abun da na aikata, duka na yi hakan ne saboda ina jin tsoro, kuma ina kallon irin kimarka da abun zai taba, Momy tana tsoron kar a akama Madina ne, saboda zata iya bayyana cewar ga abun da na aikata. Ni kuma na zabi fada maka gaskiya ne saboda na gyara abun da na bata kuma na shirya karbar kaddarata da hannu biyu Daddy Kwatankwacin hukuncin da zai wanke ni a gaban Allah domin ni na san rayuwa a nan ta kare, wannan kaddarata ce Daddy na yarda a hukunta ni...”
Ya kara fakowa ta mikawa Daddy hannyenta alamar ta shirya a saka mata handcuffs, hawaye na sauko mata. Momy ta fashe da kuka ta zube a kasa ta dora hannunta a saman kai. Amal ma kukan take, Kabir ma hawaye yake, ban da Talba da ya kasa yin ko daya sai kallon Leila yake, tun da yake a rayuwarsa be taba jin yana tausayin Leila matuka gaya ba irin na wannan ranar. Tabbas kaddararta ce, wala mai kyau ko akasin haka, ya'alla ta ture Baaba da niyar kasheta ko kuma aa, an rubutu faruwar hakan tun gabanin ta fito duniya, hadisi ne ingantacce daga bakin wanda baya karya, Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wassalam. Daddy ya daga kai ya kalleta a yanzu dai ba zai ce yana tausayinta ba, kuma ba zai ce ya tsani yarsa ba.
“Kin shirya amsa laifinki har gaban alkali?”
Leila ta daga masa kai.
“Na shirya Daddy”
Talba yayi saurin juyowa ya kalli Daddy.
“Aa Daddy dan Allah kar maganar ban ta fita, zata taba kimarka ba kowa zai maka fahimta mai kyau ba, kuma zata shafi dukanmu”
“Ni ma wannan yana daga cikin kaddaratata, ku ma ku dauke shi a haka, ko kake na boye abun da ta aikata saboda wata biyan bukata ta duniya? Na tashi a gaban Allah ka rasa kalmomin da zan kare kaina da su a gabansa? Bayyanawa duniya abun da ya faru, da kuma karbar hukuncin da duk aka yanke shi zai tabbatar da cewar Leila ta yi nadama, kuma shi zai nuna cewar dukanmu mu karbi hakan a matsayin kaddararmu”
Daddy ya karasa muryarsa na rawa, alamar yana daf da fashewa da kuka domin hawaye tuni suka wanke masa fuska. Sannan ya juya ya fice daga dakin zuciyarsa na rawa kamar yadda jikinsa ma yake yi.
Leila kuma ta juya a hankali ta fara tafiya har ta haye sama, Talba ya rasa wa zai rarrsa tsakanin Momy da Amal, Kabir ma zaune akan cushion din ya dafe kansa yana jin wani kalar yanayi mai wuyar fassara. Talba ya nufi kofar fita falon sai ya ji muryar Amal tana fadar.
“Yaya dan Allah ka roki Daddy yayi hakuri, idan aka fita da Leila daga gidan nan za a iya kasheta dan Allah dan Annabi ka roke shi ya canja shawara kar ya kaita gurin police”
Talba ya juyo ya kalleta sai kuma ya juya ya cigaba da tafiyar har ya fice na tare da ya ce mata komai ba. Bangaren Daddy ya nufa yana isa sai ya samu kofar a bude, Daddy na zaune falon farko ya soke kai kasa ya hade hannayensa duka biyu guri daya, kana ganinsa kasan maganar ce take cinsa. Talba ya karasa kusa da shi a hankali ya zauna kasa yana kallon fuskarsa.
“Saboda gudun shiga damuwarka, ya saka na yarda na bar maganar a boye, idan akwai abun da nake gudu nake tsoro yanzu a duniyar nan tashin hankalina ne da na Momy, babu bawan daya isa ya wuce kaddararsa Daddy, idan har wani abu ya samu mutum na alheri ko sheri daman can an rubuta masa hakan zai kasance, kamar yadda idan kaddara ta wuce ka, ko ka tsallake ta daman can an rubuto abun ba zai same ka ba, kowa da inda Allah yake jarrabarsa na yarda wannan jarabawar ta Leila ce da kai da Momy da mu gaba daya, amman Daddy dan Allah kar wannan abun ya saka ka yanke hukuncin cikin bacin rai, kuma kar wannan ya saka kai fushi da ita ko da Momy”
Daddy ya dago kansa ya kalli Talba da idanuwansa da sukai ja sosai, ba kuka yake ba, sai dai bacin rai da bakinciki ya saka fuskarsa yamutsewa haka zalika idanuwansa ma sun canja kala.
“Miyasa ma boye min babban abu mai girma kamar wannan Mu'azz, miyasa?”
“Ni ma ban san da faruwar hakan ba sai dazun dazun nan, kuma Ali ya sanar min, shi ma ya ji ne ta hanyar Madina...”
Talba ya fadawa Daddy kadan daga abun da Ali ya fada masa ta yadda akai ya ji. Kamin Daddy ya ce komai Momy ta shigo dakin ta karaso gurinsa ta zube kasa zaune ta kama kafafuwansa tana wani irin kuka na tashin hankali.
“Ban tana bukatar wani abu mai nauyi a gareka ba Engr, a tsawon shekarun da muka yi tare kullum muna rufawa junanmu asirina, na sani kana da iko da karfin duniyar da zaka iya binne labarin kamar ba ayi ba, ko da kuwa ace duniya ta sani, balle a yanzu da duniya bata san komai ba. A yau ina son na roki wata alfamar a gurinka”
Momy ta hade yawu sannan ta kirashi da asalin sunansa.
“Mu'azu... Ka dubi girman Allah, dubi shekarun da muka ayi a zaman aurenmu, ka dubi mutuncinka da kimarka da mutane suke ganinka da shi, ka duba makomar yata, ka tausaya mata, ka rufa mata asiri ka yardar da cewar kaddara ce ta fada mata, ka bar maganar nan a cikin gidan nan! Leila bata aikata hakan da ganganci ba...”
Daddy ya kalleta yana murmushin da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo.
“Wannan shine yardar da kaddarar, Tabbas ina da iko da karfi da dukiya zan iya magance komai, amman ba zan yi haka ba saboda tsoron Allah, idan na yi haka ban karbi tawa kaddarar ba, kuma ba zan jidadin karbarta ba lokacin da Allah zai yanke min hukuncin a kotunsa. Kin ba ni mamaki Amina, taya zaki boye abu mai girma irin wannan? Har ki bar yarki ta binne gawa saboda gudun a yi mata hukunci? A ace Leila ta san kima da girman Baaba, Wallahi da ko a hanya Baaba zata wuce Wallahi sai Leila ta kauce ta bata hanya ta wuce, amman ace har Leila zata iya saka hannu ta janyo Baaba ta jefar saboda tana jin ita din ta isa, shin idan mahaifiyata ce ko taki mahaifiyar zaki yarda Leila ta yi mata abun da tai ma Baaba? A kullum kokarinki na nuna yayanki ba su da laifi ne, abun da suke so shi kike ba su damar yi ba wanda ni ko ke ko addini ya ce ayi ba? Shin Amina arziki hauka ne? Dukiyar da Allah ya ba ni ba kisan jarawa ba ce? Idan Yayana suka ci mutuncin wani ko suka musguna masa saboda dukiyata ko kuma ni na bi ta wata hanya da bata kamata ba da dukiyar, Wallahi sai Allah ya tambaye ni, matukar ina sane akai komai, naira biyar sai na fadawa Allah yadda na same ta da yadda na kasheta, ashe ko arziki jarabawa ce mai girma wanda ta wuce ta talauci”
Hawaye ya saukowa Daddy.
“Kina raye, kina sanye aka binne gawar matar nan ba tare da an yi mata sallah ba, irin wanda addinin musulunci ya shar'antawa mamaci, ya rasa wannan sallah, ta rasa sutura irin wanda ake yi ma musulmi idan ya mutu, kin hana a kwantar da gawarta cikin