Showing 267001 words to 270000 words out of 332834 words

Chapter 90 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65574

da sunan fada mana wani abu naka ba, alheri ko sheri, bana ma jin tana sa number wani a cikin familynmu, kuma ba laifinta ba ne, laifin mahaifinka ne shi da be nuna mata ba, kai ma ba dan Aminatu ta so a kira ba na san ba zaka kira ba”
 
Yayi murmushi.
 
“Wani lokacin bana son na tashi hankalinku ne, ko yanzu ina rokon alfarmar kar a fadawa Kaka”
 
Hajiya ta tabe baki.
 
“Kai da ka sani, ban taba ganin mai watse da dangin mahaifiyarsa ba irinka, su da kake son ka tashi hankalinsu ai sun sani”
 
Murmushi yai, daman ya san halin Hajiya Laraba indai gurin fada ne ba a barinta baya. Hannu ya saka tana tashin Aminatu sai ta bude ido ta kalleta ganin Hajiya Laraba yasa tai saurin tashi zauna.
 
“Laa Mama”
 
Ta sauko saman gadon ta rumgume ta cike da farinciki. Hajiya Laraba ta yi murmushi.
 
“Auta yar albarka”
 
“Mama na gode kika zo”
 
Ta fada tana kallon sauran yaran Hajiya Laraba tana murmushi su ma murmushin suka mayar mata.
 
“Mama na ga Ya Bashir”
 
“We don't know yayanki ne or not sai mun tabbatar, ki daina saka abun a ranki da yawa saboda kar ayi bincike ya zama ba haka ba ki fara damuwa”
 
Talba ya fada da iyakar gaskiyarsa.
 
“Ba a bincika ba?”
 
“Eh nima na ji labarin ne daga bakinta sai kuma Ali, kuma Hajiya kin san inda muka fito, ba lallai ne na yi saurin aminta da wani ba sai na yi bincike mai tsanani”
 
“Haka ne, kara ayi bincike gaskiya saboda gudun abun da zai je ya dawo”
 
Talba ya kalleta da mamaki.
 
“Hajiya idan har da gaske yayanta ne, ya akai baki san shi ba? Kuma kuna gari daya?”
 
“To ai zumuntar ce ta zama sai a hankali, yan uwan kusa na ba kowa ka sani ba balle na nesa”
 
“Ashe ku muka gado, Hajiya a daina ganin laifina”
 
Ya fada yana murmushi, sai Hajiya ta tabe baki.
 
“Ka ji da shi”
 
Ta mayar masa sannan ta zauna gefen gadon, kallon kofar dakin yai sannan ya kalli Aminatu.
 
“Za ku iya tafiya ai, saboda dare yayi idan Momy ta zo zan fada mata kin bi Hajiya”
 
“Eh Hajiya tashi muje kar ta zo”
 
Aminatu ta fada, har Hajiya ta bude tace wani abu sai kuma ta hade maganar ta mike tsaye.
 
“Ba mu riko maka komai ba, na san ko ma mun riko ba lalle ne uwarka ta bari ka ci ba, idan kuma akwai abun da kake so ka fada gobe idan zamu dawo sai a zo maka da shi”
 
“Aa bana bukatar komai”
 
“To Allah ya sauwake”
 
“Amin”
 
Yaranta suka masa sallama suka fara fita sannan Hajiya Laraba ta bi bayansu.
 
“Sai da safe Allah ya sauwake”
 
Aminatu ta fada zata juya yai saurin riko hannunta, ya sumbanceshi.
 
“Haka nan ake sallama da miji? Kiss me mana”
 
Ta kalli kofa sannan ta matso kusa da shi tai masa kiss din.
 
“Allah ya baka lafiya”
 
“Amin”
 
Ya sake mata hannun, sai ta fice da saurin jikinta har rawa yake kar Momy ta dawo ta ce ba za a je da ita ba. Bata yi minti biyar da fita ba Kabir ya turo kofar dakin ya shigo, sai da ya kalli ko'ina na dakin kamar mai neman wani abu sannan ya kalli Talba.
 
“Ina matarka?”
 
Talba ya masa wani kallo dake nuna he is not ready to say anything.
 
“Momy tace na saka mota tare da Mama Saratu”
 
“Hajiya Laraba ta tafi da ita”
 
Ya amsa a takaice sannan ya tashi nufi gadon ya hau ya kwanta yana kallon ceiling dakin. Kabir ya dan tabe baki kadan ya juya ya fice daga dakin yana ciro wayarsa ya kira Momy ya fada mata, sai ta hau shi da fada kamar shi yace a tafi da ita.
 
“Taya zaka bari su tafi da ita? Ban fada maka ka saka mota tare da direban da zai kawo ka ba ya kawo ta ita da Hajiya Saratu?”
 
“Momy Easy mana nima ko da na shigo na tarar bata nan. Already matar ta zo har ta sun tafi tare”
 
“Mtssss bari na kira shi”
 
Ya sauke wayar ya nufi wani bangaren na asibitin, iskar dake kadawa tana ratsashi, wani sanyi mai dadi na shiga jikinsa. Fitowa yai harabar asibitin ya zauna a inda mutane suke zaman domin amsa waya ko yin hira, guri ne dake da itace kamar garden kuma ba garden ba, an wadata gurin da muhalin zama na irin na sinti. Zaunawa yai ya ciro wayarsa yana latsawa, can kuma ya dago kansa yana kallon Rukaiya dake zaune gefe daya tana kallon wani gurin na dabam, murmushi yai ya kashe data ya saka wayar aljihu ya mike tsaye ya nufi inda take zaune.
 
“Salam...”
 
Ta dago ta kalleshi.
 
“Sannu”
 
“Sallamata ya kamata ki amsa”
 
“Wa'alaikassalam”
 
“Good, me kike yi a nan around this time?”
 
Ya tambaya yana karewa gurin kallon.
 
“Ina jinyar Mama”
 
“I say a nan not in the hospital, duk wanda ka gani asibiti a irin wannan lokacin dole ce ta saka”
 
Ta dan kalleshi ta sauke ido kasa.
 
“Gurin yana da dadin zama ne”
 
“Yeah, that's why na zo na karbi kudin zaman guri ai, dole ne ki biya”
 
Ta yi murmushi mai sauti.
 
“Haba karka zama AA mana”
 
“Waye AA?”
 
Ya tambaya look so confused.
 
“Wani Jarumi ne a cikin wani littafi dana saurara mai suna Fulani, so AA ya fi kowa son kudi a cikin book din, sunansa Sardauna, ya hadu da wata yarinya yar Sarki, tana zuwa Restaurant dinsu ta zauna, to idan ta yi bachi sai yace sai ta biya kudin bachi da ta yi”
 
Kabir yayi dariya.
 
“Aiko yayi daidai ai mata sai da haka, kuna kudi da mu muma ya kamata mu fara tunanin mafita akanku, dan haka ba wani wayo da zaki min sai kin biya”
 
“So yanzu dai ka zama AA kenan?”
 
“Ko ma AC na ji na zama din”
 
Ta yi dariya mai sauti.
 
“Yanzu dai zauna sai na ji nawa zan biya”
 
Ba musu ya zauna, sai tai hanzarin tashi tana fadin
 
“Idan ka tashi biyan naka, ka biya har da nawa, kaga ba ni kadai na zauna ba kenan?”
 
Kyalkyale Kabir yai da dariya, yana kallonta cike da burge.
 
“Ni zaki yi ma wayo ko?”
 
Murmushi tai masa ta juya ta fara tafiya zuwa cikin asibitin, sai ya bita da ido yana kallonta har ta bace masa.
 
“Cute girl”
 
Ya furta sannan ya sake ciro wayarsa ya dora kafa daya saman daya ya jingina da kujerar kunna date sa.
 
 
LEILA POV.
 
Daga asibitin gida ta nufo cikin damuwa, a harabar gidan ta faka motarta ta bude kofar ta saka kafarta daya a waje ta jingina da motar tana jin kamar tai kuka kuma ba kukan take son yi ba. Ta rasa abun da yake mata dadi, miyasa abubuwa za su zo mata a haka, a irin wannan yanayin? The most painful part is yadda Madina ta juya ya zama makiyiyarta, har tana neman ruguza rayuwarta, after auren da Talba yai a bayan idonta? Wata ta rigata shiga gidan aurenta? Kwantar da kujerar tai baya ta lumshe idonta tana sauraren bugun zuciyarta, da yadda kwakwalwarta take kawo mata abubuwa mabanbanta, tunani kala kala ta kulla wannan ta kwance, ta sake kullawa. Bata bude idon ba har sai da ta ji motsin keys din motar da Kabir yake kokarin sakawa a jikin motarsa dake kusa da inda ta faka motarta, ta bude idon ta sauke su kan Kabir. Ta sani da da ne ya ganta a irin wannan yanayin ba zai iya wucewa ba, sai ya nuna mata kulawa, zai fara tambayarta abub da yake da damunta, idan a tsakaninta da Talba ne zai bata shawara ko da ace ba zata mata dadi ba, amman a yanzu komai ya canja.
 
“Kabir...”
 
Ya juyo ya kalleta.
 
“Kai ma na zama makiyiyarka ko?”
 
Ya rufe motar daya bude ya karaso kusa da ita.
 
“Ya akai?”
 
“You change”
 
“You change too”
 
Ta kawardar fuskarta hawaye na cika idonta, sai kuma ta sake kallonsa.
 
“Miya ba zaka dauki abun da ya faru da ni a matsayin kaddara ba? Miyasa sai kaddara mai kyau kawai ake yarda da ita ba a yardar da marar kyau”
 
“Saboda ke kanki da abun ya faru dake baki yardar kin dauki kaddarar ba, taya mu zamu yarda da ita mu dauka?”
 
“Amma ba zan aikata hakan da gangan ba, ba zan taba kashe rayuwar da zata zo tana addabata a bachi ba, ba zan kashe ran da yau kawata zata koma tana blackmailing dina da shi ba, i didn't do it intentionally, Wallahi ban yi dan na kasheta ba”
 
Ta karasa cikin muryar kuka.
 
“Tun ba yau ba, Leila kina da wata rayuwa, hitting people anyhow, idan ranki ya bace sai ki ce komai zaki iya aikatawa. And ba abun da yafi bani mamaki kamar yadda kuka kasa kai matar nan asibiti, babu wanda ya san inda kuka kaita, kuma kuka bar yan'uwanta yayanta jikokinta da tunanin inda take, kuma sun kasa yin komai saboda sun san ba zasu iya da gidan nan ba, har yanzu ba su sake waiwaar gidan nan akanta ba, kin san saboda me? Saboda suna tsoron kar su munana zato ace sun yi sheri za a hukunta su, and do you really think hakkin matar nan da iyalanta zai barki ki zauna lafiya? Hakkin rai? Wallahi karya ne Leila, babu wanda ya zai kashe rai ba a bisa hakki ba kuma Allah ya bar farinciki ya dawwama a zuciyar wannan mutumen, ban san abun da yake damunki ba a yanzu, amman zaki yi ta ganin abubuwa na rashin jindadi da kwanciyar hankali ta bangagori dabam dabam wani abun ma har ta inda ba ki yi tsammani ba”
 
Yana kai aya aka bude katon gate din gidan, direban Momy ya kunno kai ta, bayan motar Leila Momy ta saka direban ya faka motar sannan ta bude ta fito tana kallon Kabir. Karaso tai kusa da su still tana kallonsa.
 
“Lafiya?”
 
“Lafiya kalau”
 
Ya juya ya nufi motarsa.
 
“Ka je asibiti ka kwana da Talba, and Hajiya Saratu tana can, make sure ka saka Aminatu a motar nan sai su taho tare da Hajiya Saratu, direba zai koma yanzu ya dauko su”
 
“Okay”
 
Ya amsa sannan ya bude motar ya shiga, reverse yai Momy ta bishi da ido har ya fice daga gidan. Momy ya karaso saitin inda Leila take zauna ta kalleta.
 
“Ki same ni ciki zamu yi magana yanzu”
 
Tana fadar hakan ta bi gaban motar ta wuce ta hau stairs din da zai sadata da falonta.
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Sai da ta share hawayenta, sannan ta dauki envelop din ta fita motar ya rufe ta fara takawa kamar mai jin nauyin kafafuwanta, kamin ta kara gaban kofar falon ma wani sabon aiki ne. Tana kai hannu ta kwankwasa kofar sai ta ji a bude, turawa tai a hankali ta shiga sai kuma ta samu kanta ta tsayawa tana kallon stairs din kamar mai tunanin hawa. Ta hade yawu yafi a kirga sannan ta cira kafarta ta fara takawa har ta isa gurin stairs din ta hau ta shiga dakin Momy. A tsaye ta samu Momy tana jiran shigowarta, maida kofar dakin tai ta rufe sai ta tsaya jikin kofar tana kallon Momy cike da damuwa.
 
“Zauna”
 
Momy ta fada tana nuna mata gadonta, sai da ta kalli gadon sannan ta karasa ta zauna, Momy ma ta karaso ta zauna kusa da ita.
 
“Miya faru?”
 
Ta Mikawa Momy envelop din, tsayawa tai kallon Envelop din kamin ta mika hannu ta dauka, ta bude cike da tsoro tana duba abun da yake ciki, mikewa tai tsaye ta zazzage abun da ke cikin envelop din a kasa sai ta matsa baya da sauri. Hakora ne da ba zata iya shaidar na Baaba ba ne ko akasin haka, sai kuma hotunan gurin da aka rufeta.
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, me Madina da zama ne? Taya zuciyarta ta bushe haka? Har zata iya ciro hakoran gawa ta turo mana? Bata yarda mun gane ta ba ne?”
 
Momy ta nufi inda wayarta take ta dauka cikin bacin rai. Sai Leila ta kalleta tana hawaye.
 
“Momy that's enough...”
 
Momy ta kalleta.
 
“Dole mu yi wani abu, ba zamu zuba mata ido tana yi mana yadda take so ba?”
 
“Me zamu yi? Mu kasheta? Ko kuma mu fara mata abun da take mana? Momy Madina ta fada min idan har ban fasa auren Talba ba, zata tona min asiri”
 
“Okay shiyasa kika zauna a mota kina kuka? Me kika fadawa Kabir? Ita har ta isa ta baki umarni ki bi? Kuma kika yarda zaki nade hannayenki akan abun da kika kauna saboda wata banza? Laifinki ne tun farko na gargadeki akan karki fada mata amman baki ji ba, yanzu ai gashi nan abun da kika ja mana”
 
“Momy, da ban aikata ba da Madina bata yi min barazana da wannan ba, and we.....”
 
Ta kasa karasawa, sai ta fashe da kuka mai karfin gaske. Wani irin tausayinta ne ya kama Momy, sai ta matsa kusa da ita ta zauna da sauri tana hawaye.
 
“Ya isa Leila, na san yadda kike ji, ga matsalar Aminatu ga ta Madina right”
 
Leila ta daga mata kai tana kuka, sai Momy ta kwantar da kanta jikinta.
 
“Is okay, zan sama miki mafita, ba zan iya barin wasu wawayen mutane su ruguza farincikinki ba, i can't.. Ina kaunarki Leila ina kaunarki fiye da duka yayan da na haifa, zan magance miki komai, komai zai wuce and zan nuna miki kina da uwa a raye kuma jajirtacciya i promise you this”
 
Cikin kuka Momy take maganar cike da tausayin yarta.
 
“Kisan kai ba sabon abu ba ne, balle ke da kika aikata akan kuskure, ba zan wannan sirrin ya bayyana ba, mutuncin mu ba zai zuba be, babu abun da zai canja daga yadda muka tsara shi, zaki auri Talba, and dole ne Madina ta barki ki huta dole... Duk abun da yake na ki will be yours forever”
 
Leila ta kamkame Momy tana kuka.
 
“Idan Daddy ya ji zai tsane ni, kamar yadda Kabir yake min a yanzu, and Talba ba zai aure ni ba, kuma duniya zata san abun da na aikata, Momy ki sama min mafita”
 
“I will i will i promise, komai zai zo karshe soon”
 
Ta fada tana kara rumgume ta tana hawaye. Sannan ta sake ta ta dauki wayarta ta kira Kabir tana tambayar domin ta ji idan ya saka Aminatu a motar, ba karamin bacin ranta yai ba jin cewar ta ji Hajiya Laraba. Katse wayar tai tana tsaki, sannan ta kira wayar Talba, ringing daya ya daga.
 
“Hello”
 
“Ban fada maka yarinyar nan gurina zata kwana ba?”
 
“Eh tana jin bachi ne sosai shi ne Hajiya ta ce.... ”
 
“Hajiya uwarka ce? Hajiya bata san da kai ba sai da na raine ka ka girma yanzu zata nuna min fin karfi akan matarka? Taya zan fada maka yadda nake so na kira waya yanzu ka ce min wata banza ta sauy...”
 
“Nooo Momy karki zurfafa, ita da ke duka daya kuka a gurina, ita ma uwata ce kamar yadda kike uwata, baki koya min yadda zan raina danginki ba, dan haka be kamata ki bar ni na raina dangin mahaifiyata ba balle kuma ke da kanki ki aikata, taya kika ganin zan jidadi ki kira kanwar mahaifiyata da banza a cikin kunnuwa, just because of ta tafi da Matata”
 
“How dare you questioning my orders? How dare you Talba?”
 
Ta fada da kakkausan halshe sannan ta yanke wayar.
 
“Daman ance idan ka yi sake, sai ayi maka Sakkiya, abubuwa da yawa da ya kamata na aikata tun tuni ban yi ba, gashi nan ina ganin yadda komai yake juyawa, gidaje da yawa ina ganin yadda matan gidan suke mulki idan suka fada ba musawa amman ban da gidana, da wata macen ce Wallahi mijinta be isa ya yanke hukunci ba tare da izininta, amman kalle ni Engr har saki na yai saboda na kira dansa da tsintacciyar mage, mayan gidaje da yawa mazan ne suke tsoron matansu amman ni, ni nake tsoron mijina tabbas na yi sake Saratu ta taba fada min haka ban saurareta ba amman yanzu na fahimta, duk wani kuskure da na yi a baya sai na gyara shi, Wallahi da wata mace ce umarni kawai zan bawa Talba na ce ya saki yar kauyen nan kuma dolensa ya saketa, amman dubi yadda yake min magana wai ina kiran kanwar mahaifiyarsa da banza! Hmmm”
 
Ta kalli Leila.
 
“Tashi ki wanke fuskarki ki, ki samu wani abu ki saka a cikinki kamin ki kwanta”
 
Ta share hawayenta sannan ta tashi ta fice daga dakin, Momy ta shiga call list din ta kira line Hajiya Saratu, sai ta Hajiya ta dauka sannan Momy ta kara wayar a kunne.
 
“Saratu, direba ya dawo zai dauko ki ina son ki zo gidan nan ki kwana, akwai abun da nake son mu warware tare da ke”
 
“Toh, Aminatun fa?”
 
“Wai Talba ya bawa kanwar mahaifiyarsa ta tafi da ita”
 
“What? Baki fada masa gurinki zata kwana ba?”
 
“Hmmm ke dai zai kin zo, zan je na shiryawa Engr abinci kamin ya dawo”
 
“Yanzu shi Talba har ya isa ki fadi abu ya tsallake?”
 
“To ya na iya? Ai ba ni da gata a gidan nan Saratu, sai kin iso”
 
Momy ta sauke wayar, tana kallon wardrobe dinta kana ganinta ka san ranta a bace yake domin har wani kashe ido take. Can kuma ya dauki wayarta ta shiga wayarta ta nemi number Madina ta rubuta mata sako ta aika mata sannan ta saka wayar a key ta aje ya mike tsaye ta nufi bandakinta ta dauko safa ta saka sannan ta kwashe hakoran da hotunan ta saka a envelope din ta nufi karkashin gadonta ta saka, kana ta sake komawa bandakin domin tsabtace kanta.
 
 
MADINA POV.
 
_Madina yanzu aka fara wasan, ba kin zabi cigaba da abun da kika yi ba? Kina

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login