Showing 243001 words to 246000 words out of 332834 words
wasan tun yanzu, ki sallame yan wasanki ki watsar da makamin, idan ba haka ba zaki gina ramen binne kanki da kanki”
Madina ta yi murmushi.
“Kina magana kamar kin sha wani abun maye, kisan kai fa kika aikata Leila, kika kashe tsohuwar da zata ji ba, ba ta gani ba, saboda muguwar zuciya irin taki, kuma kin bar yayanta da wahalar nemanta da tunanin dawowarta, me kike zato idan iyalinta suka san abun da kika aikata? A tunaninki Talba zai aureki idan ya san kin kashe Baaba saboda bakar zuciya? Idan ma Momy da Daddy sun goyi bayanki, duniya zata goyi bayanki ne? Kina ji a ranki kina da sukunin da zai barki ki yi yawo a cikin mutane kamar wanda bata aikata komai ba? Sai Human Rights da yan uwan matar su saka miki ido saboda kawai kina da uwa da uba a raye? Ko ba komai kin bata sunan mahaifinku kuma kin lalata rayuwar aurenki! Kin yi kuskure Leila, kuma ina gargadinki karki sake aikata wani kuskuren, domin shi kike kokarin yi a yanzu, gyara barna da barna, bana bukatar dukiyarki ko wani abu na ki, ya kamata ki san wannan, ashe ko idan har son Talba ne kawai abun da yake damuna ashe abu ne mai sauki daya kamata ki bi ta lala saboda samawa kanki mafita, idan ba haka ba sai na ruguza rayuwarki na lalata zancen aurenki”
Leila ta yi dariyar da ta fi kama da ta yake.
“Kuma a tunaninki hakan zai saka Talba ya fasa aurena? Nooooooo”
Madina ta taka daya zuwa biyu ta matso kusa da ita.
“Yes, na san Talba fiye da naki sanin, matukar ya ji wannan ba zai tana aurenki ba, and Yes Momynki da ke kanki kun yi gaskiya, ni na aika sakon da ake kawo miki, ni nake shirya komai, kuma tabbas saboda na tashi hankalinki ne na lalata zancen aurenki da Talba ba”
Wani kalar kallo Leila take yi ma Madina da mugun mamaki. Madina har ta juya sai kuma ta juyo ta nuna Leila da yatsa.
“A yanzu ma, ba fasawa zan yi ba, wasan ne zai sauya salo, domin umarni zan baki wanda ya zame miki dole ki bi, ina son ki fadawa Momy da Daddy cewar kin fasa auren Talba”
At first Leila ta ji abun kamar a mafarki, not just abun da Madina ta fada mata a yanzu even the whole conversation din ta ji kamar a mafarki ne ba gaske ba, taya Madina zata tsaya a gaban idonta tana fada mata irin wannan maganar?
“Madina ni kike fadawa wannan maganar?”
Leila ta tambaya tana nuna kanta with shock.
“An Fada miki, ni ba a yanzu kika gama fada min magana ba? Kenan idan wani ne ya shirya wannan abun ba ni ba yarda za ki yi, why not ki fara karyata kunnuwanki ki kyamaci abun a ranki? Idan har zan gwada yakar zuciyata na hanata son abun da kike so, ya kamata ke ma ki gwada yi min kawaici ko da sau daya ne, amman a maimakon haka sai kika manta da komai, babu amana a kawancen mu Leila. Kuma idan har zan rasa Talba ke kika fi cancanta da ki rasa shi, domin be dace da ke ba”
“How dare you look in to my eyes and tell me Talba be dace da ni ba? Da ke ya dace kenan? A yanzu na gane ke macece mai mugun son kanta Madina, shiyasa kika sace Aminatu, me kike idan Talba ya samu wannan labarin?”
“Ni ban sace Aminatu ba, kuma a lokacin da aka sace ta, daga ni har ke ba mu san cewar Talba ya aureta ba, and even if i did kina da wata ahauda da zata tabbatarwa duniya cewar na aikata? You better watch your mouth Leila? I'm not as nice as I used to be”
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga harabar gurin cikin bacin rai, har hade kafafuwa take kamar zata fadi. Leila ta hade yawu tana binta da kallo.
“A snake in the grass, a hidden enemy, we can not believe every one”
Ta juyo ta fara takowa zuwa cikin asitin har lokacin mamakin abun da ya faru be sake ta ba. Ko da ta dawo ward din ta samu Daddy a tsaye yana kallon Ali ransa a bace, Momy da Kabir na tsaye, Amal ta kwantar da kanta kafadar Leila Kabir har lokacin hawaye take.
Ajiyar zuciya Daddy ya sauke bayan Ali ya gama fada masa yadda komai ya faru.
“Allah ya sauwake, ina ita matar tasa take?”
“Na saka Haulat ta zo ta dauke ta ta tafi da ita gida”
“Saboda me? Ga kowa a nan, can ai hankalinta ba zai kwanta ba”
“Idan ma ta tsaya me zata yi masa ranka ya dade? Ni Wallahi bana kaunar ganin yarinyar nan, kalli halin da yake ciki saboda ita ne fa”
Momy ta fada cikin bacin rai, sai Daddy ya daga mata hannu.
“Aa karki zama marar tauhidi mana, duk wani abu da zai samu bawa an rubuta masa shi tun ba yau ba, ko da ita ko ba da ita ba, daman can an rubuto haka zai faru kuma dole sai ya faru, dan haka ki daina ma dora nata laifi kina kokarin kwace hanya, kuma dole ne a bata hakkinki domin matarsa, ta riga ta zama daya daga cikin iyalan gidan nan a yanzu”
“Shi kansa idan ya farka be ganta ba, ai ba zai jidadi ba, tun da tana nan lokacin da abun ya faru”
Kabir ya kara da na shi.
“Amman dai mu nan ai mun wadatar ba sai mun ta zo ba, tun da ba cire masa ciwon zata yi ba”
Momy ta fada tana jin wani tsanar Aminatu na kara taso mata. Sai Daddy ya kalli Kabir cike da jindadin kalaminsa domin Daddy yana son mutum mai tunani da fadar gaskiya ko aiwatarda ita, yana daya daga cikin dalilin daya saka yake kaunar Talba.
“Yes kuma ya riga ya aureta, ko ganin kika yi zai wulakantata be kamata ki kyale ba, domin a yanzu kamar Amana take a gurinkinsa da kuma mu iyayensa”
Momy ta dauke kai tana tabe baki ba tare da tace komai ba, ta kalli Leila da hankalinta yake wani gurin dabam kana ganinta ka san tunanin wani abun take.
“Ka dawo da ita a nan tare da mutane, zai fi can da zata zauna da tunani”
Daddy ya fada yana kallon Ali, sai Ali ya dan risina alamar girmamawa.
“Okay Daddy”
Ya amsa sannan ya ciro wayarsa ya fice daga gurin. Daddy ya juyo ya kalli Leila.
“Ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru da yardar Allah”
Leila ta sauke kanta kasa, a cikin kalaman da Daddy yai mata last sentence dinsa kawai ta ji, domin har lokacin hankalinta yana can duniyar tunani. Momy ta fara takawa a hankali cike da kasaitar data zame mata jiki, tana tafe fana lasa waya tana fadawa yan'uwanta, sai da Daddy ya kara shiga ya duba Talba sannan ya fice.
AMINATU POV.
Rikota Haulat tai suka shigo falon, saman Cushion din falon ta zaunar da ita, tai mata kalamai masu kwantar da hankali sannan ta shiga kitchen ta dora girkin dare, sama sama take jefowa Aminatu hira saboda ta dauke mata hankali, amman Aminatu bata cewa komai har Haulat ta ci ta shude.
Kiran wayarta da ake ne yasa ta fito kitchen din da saurin ta nufi inda wayar take ta dauka ganin number mijinta yasa rai saurin picking, ta juya ta koma kitchen din tana amsa masa.
“Hello Doc”
“Na'am ya gidan?”
“Lafiya kalau ya mai jiki?”
“Alhamdulillah, Aminatu na tare dake?”
“Eh lafiya?”
“Lafiya Kalau, Daddy ya ce a dawo da ita, wai hankalinta zai fi kwanciya idan tana nan”
“Gaskiya kam, domin hankalinta a tashe yake a nan, bata cewa komai sai tunani take, har bata sani idan an mata magana sai an taba ba, abun ya shiga ranta sosai”
“Ai dole, ki kawo ta yanzu”
“Okay”
Ta fada sannan ta sauke wayar, tana kallon girkinta dake kan gas, sannan ta juyo ta fito kitchen din ta nufo inda Aminatu take zaune, ganinta ya saka Aminatu ta mike tsaye da sauri tana kallonta gabanta na faduwa daman tun da tai picking call din ta ji ta ambaci sunan Doc hankalinta ya tattara ya koma can.
“Kin yi sa'ar siriki Aminatu, Daddy ya ce a dawo dake asibiti wai idan kina ganinsa hankalinki zai fi kwanciya”
Aminatu ta daga kai da sauri daman abun da take nema kenan, sam anan bata jin zata iya samu natsuwa, kara a can tana kusa da shi ko da kuwa ba zata iya hana komai faruwa ba, zata fi samu sukuni ace tana ganinsa kuma ta san halin da yake ciki, tsabanin nan da tana zaune ne kawai amman hankalinta yana can. Haulat ta yi murmushi.
“Ni ma ai na fada masa haka, amman na san da Momy ce ba zata ce a kawo ki ba, kuma dan Allah komai Momy tai miki ko ta ce miki kar ranki ya bace, kar ma ki biye nata ki maida hankali gurin mijinki”
Ta daga kai.
“Wa zai kai ni?”
“Ni yanzu girki nake, kuma yara suna nan dawowa daga islamiya, amman ai zaki gane gurin ko?”
“Eh”
“Okay bari na kira Maman Walida na ji idan mijinta na kusa sai ya kaiki, domin Napep yake ja”
“Toh”
Ta amsa ta koma ta zauna tana jin kamar tai tsuntsuwa ganta a gurin. Haulat ta shiga contact dinta neman number Maman Walida, ta aika mata kira. Wayar bata wani dade tana ringing ba ta dauka da sallama.
“Wa'alaikissalam, Maman Walida ya gida ya su Walida”
“Lafiya Kalau Hajiya ya yau”
“Lafiya Kalau, dan Allah tambaya bake ko Abban su Walida na kusa, wata yarinya zai kai asibitin da Doc yake aiki”
“Eh gashi nan yanzu ma ya gama cin abinci, bari na masa magana”
“Okay”
Ta kalli Aminatu bayan ta sauke wayar.
“An yi sa'a yana gida, daman da maraice yake dawowa cin abinci idan ya tashi shago mun yi sa'a yana gida. Amman idan kin je karki fada cewar ba ni na kawo ki ba, zai iya yin fada ki ce ina kawo ki na aje ki na wuce saboda ina girki kuma yara za su dawo makaranta yanzu”
“Toh”
Aminatu ta amsa da sauri, sannan ta mike tsaye daga zaunen da take. Haulat ta koma Kitchen din ta duba girkinta, sai ga wayarta ta sake ringing.
“Hello Maman Walida”
“Na'am ya ce wai ta fito kofar gida yanzu zai fitar Napep din Titi”
“Okay”
Haulat ta fito kitchen din ta nufi dakinta ta dauko Hijab dinta ta nufi kofar fita daga falon.
“Zo muje”
Aminatu ta bi bayanta da sauri suka fice, har gurin gate din Haulat ta kaita sannan ta tsaya jiransa domin ba su tarar da kowa a gurin ba, after like five minutes ya fito kwararon dake gefen gidansu, domin gidansa yana cikin kwararon ne kasancewarsa mai karamin karfi ba kamar sauran mutanen unguwar ba. Yana daf da kawowa gate din wani tunanin ya zo ma Haulat tunawa da an taba sace Aminatu kar wani abu ya sake samunta a yanzu dalilinta ya san kuma ba saurara mata kowa zai yi ba.
“Ko dai na kashe girkin na kai ki da kaina, kar wani abun ya faru na shiga uku”
Ta bukata tana kallon Aminatu dake kallon napep din data karaso kusa da inda suke tsaye jikin gate din. Da sauri mai Napep din ya fito daga cikin Napep din yana kallon Aminatu irin kallon nan na mamaki. Aminatu ta gwalo ido tana kallonsa tare da kai hannayenta duka biyu ta rufe bakinta sai yawo take da kanta kamar wata tababbiya.
“Ya ya Bashir.... Ya ya....Bashir... Da gaske Yaya Bashir... Da gaske....”
Shi kam ya kasa cewa komai sai kallonta yake baki sake da mugun mamaki. Haulat na ganin haka ya bude gate din ta fisgo Aminatu ta saka ta ciki, sai Aminatu ta fara kokuwar kwace kanta tana kuka.
“Yayana ne....dan....uwa... Na... Na... Ne... Yayana..ne.... Ya Bashir.... ”
Ta kwala masa wani irin kira da mugun karfi tana tsalle.
“Kai rufe gate din nan”
Haulat ta fadawa mai gadinta, sai ya tashi ta sauri zai rufe gate din sai Bashir ya kwankwaso kofar gate din.
“Auta Auta Auta...”
Haka yake ta kiranta sai ta amsa daga can cikin gidan Mai gadin ya rufe gate din da karfi. Har sai da Bashir yaja baya da sauri ya koma cikin Napep din ya juya ya kwayar daya fito jikinsa na rawa.
“Wallahi yayana ne dan'uwana ne shi kadai ya rage min”
Aminatu tana kuka sai kokarin kwatar kanta take daga rikon da Haulat tai mata amman ta kasa.
“Ban yarda da wannan ba, ki bari idan na hannataki da mijinki ko ma minene sai ayi, amman yanzu kam wani abu na zai same ki ba ace Haulat ce”
Haulat ta fada sannan ta saketa ta nufi cikin gidan, kitchen ta shiga ta kashe girkin sannan ta shiga dakinta ta dauko keys din motarta ta fito ta bude motar tai mata key.
“Ki taso ki shiga motar nan na kai ki gurin mijinki idan ya farfado sai ayi wanda za ayi, amman ba a yanzu ba, idan kuma ba zaki je ba na koma na cigaba da girkina amman ba zan yarda ki ga kowa ba yanzu”
Ta fada da iyakar gaskiya, domin tsoro take kar wani abu ya faru, kai tsaye ba zata ce ta gamsu Mijin makociyarta Maman Walida da Aminatu suna da alaka ba, ba kuma zata karyata ba, domin gari da kamani sun nuna haka. Aminatu ta taso tana kuka ta nufo inda Haulat ta kunna motar ta bude front seat ta shiga ta zauna tana kuka.
“Dan Allah ki bari na yi magana da shi, dan Allah Wallahi dan'uwana ne”
“Aa ki bari idan kin tafi can ki fada musu”
Ta fada tana tana reverse din motar, wanda yai daidai da shigowar kira a wayarta da number Maman Walida, sai dai bata yi piciking sai ta aje wayar a gefe ta cigaba da tukinta har ta isa gate. Mai gadi na bude gate din sai ta hango Maman Walida da Mijinta tsaye da sauri ta saka motar lock ta yadda Aminatu ba zata iya budewa ba, sannan ta sauke gilashin motar na gefenta ana kallon Maman Walida.
“Laaa Wallahi Auta ce”
Maman Walida ta fada, sai Aminatu ta leko ta gurin tana kallon Yayanta.
“Yaya Bashir”
Ya karaso gurin motar da sauri yana kallonta idonsa na cika da kwalla.
“Aminatu, Auta Auta... Auta... ”
“Baban Walida dan Allah ku kwantar da hankalinku, yanzu zan kai yarinyar asibiti gurin mijinta, idan hankali ya kwanta a can sai ayi ta nan, babu inda zata je kawai dai yanzu bana son wani abu ya faru tana gurina ne ni kadai ba tare da sanin kowa ba”
“Mijinta kuma? Aminatu bata da aure...”
“Kai ne baka sani ba, yanzu dai hakura har na dawo sannan ayi komai dan Allah”
“Toh”
Ya amsa yana jin kamar ya saka hannu ya fisgota, ba dan ya san Haulat da mijinta farin sani ba, da babu yadda za ayi ya yarda ta tafi da Aminatu dake ta kuka tana son bude kofar motar ta fita faki budewa, zagaya yai gefen ta Aminatu take yana kallonta yana murmushin farinciki tare da yi ma Allah hamdala. Hankali Aminatu be kara tashi ba har sai da Haulat taja motar suka hau titi sai ta hau gaiye tana kallon Ya Bashir tana jin kamar ba zata dawo gareshi ba. Sai da suka yi nisa sannan Haulat ta dan kalleta.
“Da gaske yayanki ne?”
Aminatu ta daga mata kai da sauri tana hawaye sai matsar kukanta take kar ya fasa bakinta ya fito. Sai a lokacin Haulat take tuna cewar dan garin su Aminatu ne, da kuma irin hirar da suka sha ita da Maman Walida lokaci aka kai hari a garin, da yadda ta fada mata cewar yan kashe iyayen mijinta da yan'uwansa, ita kanta wasu iyayen nata an kashe su. Sai da suka shiga cikin asibitin sannan Aminatu ta share hawayenta, Haulat na yin farkin ya kira wayar mijinta ta sanar masa inda take. Be a dauki dogon lokaci ba ya iso gurin sai a lokacin ya cire motar daga lock ta bude ta fita ta bar Aminatu a cikin motar, magana tai da Ali ta fada masa abun da ya faru, sai ya bude bangaren da Aminatu take zaune ya lekota.
“Ya akai kika gane yayanki ne? Ba kin ce an kashe yan uwanki ba?”
“Shi kadai zai iya amsa min, dan'uwana ba zai taba bace min ba”
“Amman kin san a nan yake zaune?”
Ta daga masa kai.
“Amman ban san cewa yana raye ba, kuma ban san inda yake zaune a birnin ba”
Ajiyar zuciya Ali ya sauke, sannan ya kara fadada kofar.
“Fito muje ciki”
Ta fito kamar yadda ya bukata, sai ya rufewa matarsa motar yai mata sallama yai gaba Aminatu ta bi bayansa, tana tafiya kamar mai koyon yadda ake takawa gaba daya ranta a jagule yake, ta rasa abun da zata yi murna ko kuma? Abubuwa biyu mabanbanta sun same ta a lokacin daya. Kanta a kasa har suka isa ward din, sanin ba jituwa za su yi da Momy ba, yasa be kaita a inda suke ba tare da mutanenta da wasu yan'uwan Daddy da suka samu labarin abun da ya faru ta hanyarta suka taho asibiti. Sai ya kaita dakin da Talba yake kwance kai tsaye, duk kuwa da kasancewar ya san Leila tana ciki. Shi ya fara isa bakin kofar ya tura ya shiga sannan Aminatu ta shigo. Leila dake tsaye rumgume da hannayenta ga kalli Aminatu ta kalli Ali da mamaki.
“Kawo ta ka yi?”
“Daddy yayi umarni da haka, kuma a gabanki kin san kuma ban isa na ce aa ba”
“Ai sai ka amsa masa, amman ka share maganar a bayan idonsa, ta zo nan ta yi miye, har wanda be san yayi wannan shegen auren ba yanzu zai sani, abun kunya kalleta da Allah”
Leila ta fada tana nuna Aminatu. Aminatu ta kalleta da idanuwanta da suka yi ja ta ce.
“Ni na fi cancanta zauna kusa da shi sama da ke, domin ni matarsa ce ba budurwarsa ba, ko ba komai saboda ni komai ya faru, ashe kuwa na fi kowa cancantar zama kusa da shi”
Leila ta matso kusa da ita kamar zafa daketa.
“Ke ni kike fadawa magana?”
“Ba magana nake fada miki ba, gaskiya nake nuna miki wanda kika kasa gani, a rayuwata ban taba ganin wani mutum mai son wata mace tsakani da Allah ba kamar yadda Talba yake so na, ya san zai iya mutuwa ko wani abu