Showing 159001 words to 162000 words out of 332834 words
ko na shi ba ba zan yi sharing miji da wata ba”
“Idan ke zaki iya bari yarinyar ta waye ta goge irin gogewar da har zai iya furta cewar yana sonta balle har ta kai shi ga aurenta, ni ba zan yi wannan saken ba, ko kwalliya ba zan bari tai ba, kuma ba zamu dasa mata komai ba sai bakinciki, Leila ke wawuya ce Wallahi da ace ni nake da damar da kike da ita da yanzu komai ya zama labari”
Leila ta yi murmushi tana jin dadin yadda kawarta take daukar komai nata da zafi, musamman ta bangaren Leila.
“Ke ma kin san ai ba zan bari ba, kuma ina da ke hankalina a kwance yake, ban matsawa Momy har sai ya dawo da ita gidan nan In Shaa Allah”
“Haka yayi, kuma karki manta da maganar aikina, ko dai na cire rai wai?”
“Haba kawata, ki kwantar da hankalinki na miki alkawari cikin satin nan za a gama komai”
“Na gode, and lastly ya kamata ki saka ido akan mijinki fa, ki rika dauka kamar kin aure shi ne, ki rika sanin ina yake zuwa me yake zuwa yi”
“Madina kina yin abu kamar ba kisan wacece ni ba, ni ma fa na san kaina, ba rokonsa na yi nace ya aure ni ba, god forbid ba zan ma taba yin haka wa namiji ba, ina ma da ina da aji ba zan yi abun da zai zubar min da kima ba, idan ya fita can zai yi rayuwarsa dabam a cikin gidan nan ma zai yi yadda yake so, abun da kawai ba zan dauka ba shi ne, ya auri wata bayan ni ko kuma kamin ni, dan haka ki daina wannan maganar”
“Leila ke nan, wata rana zan baki mamaki Wallahi, ke wai baki san soyayyah ba ruwanta da wani aji ba? Shi miyasa be duba nasa ajin ba yake ta kula yarinyar nan?”
“Wannan kuma ai dabam, ni dai ba zan iya zubar da kaina a gurin namiji ba, ni fa macece karki manta da wannan”
“Ni kuwa kin ga zan iya komai dan na samu abun da nake so, durkusawa wada ai ba gajiyawa ba ne”
“Ni dai ba zan iya ba”
Ta fada tare da kashe wayarta. Madina ta yi murmushi tana taba idonta daya kumbura saboda kukan da tai.
LEILA POV.
Tana aje wayar ta mike ta nufi gurin kofar dakinta da Amal take ta knocking. A fusace ta bude kofar domin Amal ta dade tana dukan kofar tana kwala mata kira.
“Kamar kina bina bashi zaki zo kina dukan kofar dakin nan mi ya faru?”
“Miye idan zaki yi waya sai kin wani rufe kofa, ki fito Ya Kabir yana kiranki”
Amal ta karasa tana murda mata baki, a take Leila ta kai hannu ta tura Amal baya, abun ka da tiles sai Amal ta zame a gurin ta fadi kasa hannunta ya bugu da tile din. Kamar wata karamar yarinya haka ta bude baki ta fashe da kuka ita ala dole auta ce, ta tashi ta nufi hanyar dakin Momy, sai Leila ta rufa mata baya, Yaa Kb dake kasa yana jin kukan Amal ya taso ya nufo upstairs.
Da kuka Amal ta tura kofar dakin Momy ta shiga.
“Momy kin ga Leila ta ture ni na fadi saboda Ya KB yace na kirata”
Momy ta kalli Leila wanda ta shigo dakin da saurinta.
“Momy zuwa tai ta rika dukar min kofar daki kamar na ci bashinta kuma ta karasa min magana tana murguda min baki”
“Leila mi yake damunki ne? Miyasa idan ranki ya bace ba zaki iya controlling kanki ba? Har da yar'uwarki ba ki bari ba? So kike ki tureta ta fadi ta mutu kamar yadda kikai wa Baaba ko kuma kareta kike son yi? Ki duba halin sa kika jefamu saboda bakar zuciyarki, yanzu kuma yar'uwarki ba zaki shafa mata lafiya ba?”
“Amman Momy ai kin san halin Amal”
“Saboda na san halinta sai na bari ki ji mata ciwo?”
“Ita ma Baaba ba da gangan na aikata ba”
“Da sunan ba da gangan ba, Allah kadai ya san abun da kika aikata a gidan nan da wanda kike shirin aikatawa, ya kamata ace kina iya controlling kanki dai”
Leila bata sake cewa komai ba ta juya ta bude kofar dakin zata fita sai tai arba da Kabir a tsaye, kamar an zuba mata ruwan zafi a jiki haka take fatar jikin ma saukowa kasa saboda tashin hankali arba da tai da Kabir.
“Shiga ciki”
Ya fada yana mata wani shegen kallo, sai tai baya baya wanda hakan ya bashi damar shigowa, sai ya maida kofar dakin ya rufe ya kalli Momy dake rike da hannu Amal.
“Ashe ke nan Baaba ba bata tai ba, Leila ta kashe ta, kuka kaita wani gurin kuka jefar ko kuma kuka binneta”
Momy ta saki hannun Amal ta mike tsaye tana kallonsa.
“Wace irin magana ce wannan kuma?”
“Momy na ji komai, kuma abun da kuka aikata be kamata ba, saboda gudun a hukuntata zaki biye mata ku aikata son zuciya? Kuma ku bar bayin Allah iyalanta da zullumin nemanta da tunanin inda take? Rai fa ta kashe Momy rai”
Ya furta a fusace yana jin kamar ya hade zuciya saboda bacin rai.
“Ni ban kashe ta ba, ban ai...”
Bata karasa ba wanke mata fuska da mari.
“Wawuya, sai yanzu na fahimci dalilin daya saka Talba ya tsane ki, baki da zuciya mai kyau Leila, dan'uwana be cancanci aurenki ba Wallahi”
Momy ta daka masa tsawa.
“Kabir.. Karka manta alakarka sa Leila tafi alakar dake tsakaninka da Talba, wannan jininka ce, uwa daya uba daya, kuma karka kuskura ka bar maganar nan ta fita, idan wani ya ji maganar nan ban yafe maka ba!”
Ta mugun mamaki ya kalli Momy ya nuna Leila kana ya nuna kansa.
“Momy saboda Leila ta aikata kisan kai zaki ce ba ki yafe min ba? Wani irin so kike yi ma Leila ne? Kin goyi bayan abun da ta aikata kenan fa!”
“Irin son da nake maka, shi nake mata, fita ka bar min daki”
Momy ta fada tana nuna masa kofa, juyawa yai da sauri ya fice a fusace, fusata iri ta mamakin da bakinciki yadda Momy ta goyi bayan Leila. Sai da Kabir ya fice sannan Momy ta kalli Leila.
“Ki cigaba da abun da kike, har ta kai Talba ya ji maganar nan yanzu dai kin yi nasara Kabir ya ji, sai ki zuba ruwa kasa ki sha”
Leila ta share hawayenta tana hararar Amal.
“Yanzu ma ai Amal ce taja komai, da babu wanda zai ji”
Amal dai bata ce komai ba ta mike tsaye ta nufi kofar fita ta fice daga dakin. Downstairs ta nufo tana saukowa rike da hannunta domin har lokacin tana jin zafin buguwar da tai, bata karasa saukowar ba door bell din falon tai kara, yanayin yadda aka danna door bell din ta gane cewar Ya Talba ne, sai ta karasa kofar da saurinta ta bude masa.
“Wow Ya ka yi kyau kamar ango”
Ta fada tana kallonsa sama da kasa, bata fadi karya ba domin yayi kyau sosai fuskarsa sai haiba take, yana rike da babbar rigarsa a hannu dayan hannunsa kuma rike da hula.
“Da gaske?”
“Eh Wallahi ka yi kyau, Ya ina kaje?”
Tsayawa yai cak yana kallonta sai kuma ya juya ya fice ba tare da yace mata komai ba, kai tsaye ya nufi bangarensa, yana shiga ya canja tufafin jikinsa sannan ya fito nufi bangaren Momy.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Momy ta tsayar da cin abincin da take ta kalleshi.
“So...?”
“Ina son na dawo da ita nan, saboda ta samu ilmi da kula, kin ga can kauye ne, rayuwarta zata fi kyau a nan”
Wani kalar dadi ne ya lullube Leila jin an tabo mata inda ke mata kaikaiyi, sai dai bata yarda ta nuna ba gudun kar Talba ya zargi wani abun.
“Miyasa kake tunanin zan iya zama da mace da tai sanadin mutuwar aurena? Just because of kana son taimakonta sai ka kawo ta nan? A can kauye babu makaranta?”
“How tai sandiyar mutuwar aurenki?”
Leila ta tambaya da kanka.
“Idan har zaki hukunta wani akan hakan it should be Talba not her, domin bata cikin gidan ma lokacin da abun ya faru”
“Kar so ya rafe miki ido Leila”
“Idan har so zai rufe min ido, ai laifinta zan gani bana Talba ba, kawai ina fadar gaskiya ne, idan baki son ta zauna a gidan nan ba laifi, amman dora mata laifin da be shafeta ba shiga hakkinta ne”
Ba Momy kadai ba har Talba kallon mamaki yake mata, domin bata taba gwada yi ma wani haka ba. Bata taba yabawa wani da yake kasa da ita ba ko da kuwa shi ne da gaskiya. Kabir M kallonta yake yana tunanin kalamanta.
“Shi ke nan, sai ka yi magana da Daddynku idan ya amince ba ni da matsala”
Momy ta fada tana mikewa tsaye taja kujera baya ta sauka ta nufi hanyar upstairs. Leila ma tashi tai ba tare da ta kalli kowa a cikinsu ba ta bi bayan Momy.
“And do you really think Leila da zuciya daya tai maganar nan?”
Kabir ya fada yana kallon Talba, Talba ya dan tabe baki.
“Bana ji, amman mi zai saka ta yi haka?”
“I don't know, amman bana son ka yi abun da zai cutar da kai da kuma ita yarinyar, if possible ka barta a can kauyen ta zauna, besides ta samu iyali a yanzu then miye na takura kanka sai ka kawo ta nan? Ko aurenta kai?”
Talba ya masa wani kallo, na mamaki. Sai yai murmushi.
“Na ga ranar daka dawo ka saka fararen kaya, har da babban riga a hannunka kuma a tarihin rayuwarka baka taba saka babbar riga ba”
Talba yayi murmushi.
“Ka gan ni ko kuma dai Amal ta fada maka”
“Trust me na ganka, domin ina harabar gidan lokacin daka shigo”
“Saboda na saka babbar riga sai ka fara zargin na yi aure? Taya zan yi aure Momy da Daddy ba su sani ba”
“I don't know”
Kabir ya fada yana mikewa tsaye. Talba ya bishi da kallo har ya fice sannan shi ma ya tashi ya nufi sofa din falon ya yana kokarin ciro wayarsa ya kira Daddy.
“Hello Daddy”
“Mu'azz ya kake?”
“Lafiya kalau, Daddy kana office”
“Yeah akwai matsala ne?”
“No gani dai zuwa”
“Okay”
Yana sauke wayar ya mike tsaye ya fice daga falon cikin natsuwa yana wani irin tafiya kamar wanda baya son taka kasa. Ya kusan minti biyar zaune a cikin motarsa sannan ya yi mata key, kamin ya isa gate din har masu gadin sun bude masa. Be faka ko'ina ba sai gaban katon kamfanin ya bude kofar ya fito ya doshi hanyar da zata sada shi da office din Daddy. Sai da akai masa iso sannan ya shiga bayan yayi knocking sau daya.
“Daddy ina da bukata daya a gurinka”
Ya fada tun kamin ya zauna.
Daddy ya mika masa hannu suka gaisa
“Ina ma ina da abubuwa biyu da zan fada maka, the first one is request the second one kuma abun da kake nema ne ya samu”
Fuskar mamaki Talba yayi.
“You go first...”
Daddy yayi murmushi.
“Na farkon Leila ce ta kawo min kararka, wai tana son ka dauki kawarta Madina aiki kaki, ni kuma na ce zan maka magana, a kawancensu da Madina be kamata a kasa sama mata gurbi a gurinka ba”
“Wannan ba matsala ba ce Daddy, zan yi magana da Pa na In Shaa Allah cikin satin ma zata fara aiki, fada min daya”
“Sai ka bani goro, domin ka dade kana jiran zuwan wannan ranar”
Talba yayi murmushi mamaki, ya fara canke canke, har wata zuciyar na raya masa ko dai Kaka ta kira shi ta masa wata maganar ne!
“Momy ka ta yi min magana akan cewar be kamata a zuba muku ido, ita kanta Leila ta fadawa Momy cewar a yanzu ta shirya, and daman nasan abun da kake nema ne, dukanku kun mallaki hankalin kanku kana da aiki zaka iya komai ita ma kuma ta gama karatu ban san zaman jiran me kuke ga a yanxu”
“So...”
Ya tambaya gabansa na dan faduwa.
“Mun yanke shawarar saka muku rana, amman nace sai na fara magana da kai na ji lokacin da kake so”
A take Talba ya nemi annashuwa ya rasa, yana jin kamar be shirya auren Leila a yanxu ba, bayan kuma da can abun da yake ta nema ne.
“Amman Daddy ita Leila da kanta tace ta aminta? Bana son ayi forced dinta ne!”
“Karka damu, idan bata aminta ba Mahaifiyarta ba zata fadi haka ba, kasan yadda take son Leila ai, i don't think tana son ku yadda take son Leila”
Talba ya dauke kansa yana kallon wani gurin daban, not happy and sad, ya samu kansa a cikin wani yanayi mai wuyar fassara.
“Mu'az”
Daddy ya kira sunansa yana kallon yanayinsa. Sai ya juyo ya kalli Daddy yana murmushin yake.
“Allah ya tabbatar mana da alheri Daddy, duk date din da kuka saka yayi daidai”
“Mu saka kusa ko nesa?”
Still Daddy na reading reaction nasa.
“Kusa”
A kokarinsa na kawar da zargi ya amsawa Daddy yana murmushi. Daddy ma yayi.
“Good domin be kamata kai azumi ba mata ba, ga azumi ya kusa”
Ya yi ma Daddy murmushi as respond sannan ya mike tsaye ba tare da ya fada masa abun da ya kawo shi ba, gaba daya maganar da Daddy yai masa ta saka ya manta.
“Baka fada min maganar ba?”
Sai ya dawo ya zauna.
“Daddy Kaka ta kira ka ne?”
“Aa akwai wani abun ne?”
“No daman saboda yarinyar nan ne... ”
Ya gabatarwa Daddy da bukatar, sai dai wani bangare na zuciyarsa na raya masa ko dai Daddy ya san da maganar auren ne shiyasa ya bullo masa ta wannan sigar ya ga iya gudun ruwansa! Be gama bawa kansa amsawa Daddy ya amsa masa.
“Ba matsala, daman can ko ba yar'uwa ba ce ai tana da yancin zama a gidan balle kuma tana jininka, ba wata matsala, zan yi magana da Momynka”
“Sai da na yi magana da ita sannan na zo nan, tace min ba matsala”
“For the first time yau ka fara sirri da ita kamin ni, I'm jealous”
Talba yayi murmushi domin ya san halin Daddy da zolaya. Sannan ya sake mikewa tsaye ya nufi gurin da fridge din Daddy yake ya bude ya dauko gorar ruwa.
“Sai ka shigo Daddy”
Daddy ya daga masa kai yana murmushi, shi kuma ya fice rike da ruwan. Be sha ba sai da ya shiga motarsa sannan ya balle murfin ya daga gorar ya kai bakinsa be sauke ba sai da yai rabin gorar sannan ya sauke gorar yana haki.
“Abubuwa biyu lokaci daya!”
Ya furta yana yi ma motar key, at first gida ya nufa sai kuma ya canja hanya ya dauki hanyar da zata kai shi gidansa. A gaban gidan ya faka motarasa ya fita ya nufi gate din ya bude sannan ya shiga motar ciki ya dawo ya rufe gate din.
LEILA POV.
Tana shiga dakin Momy ta zauna kusa da ita tana fadin.
“Momy i thought mun yi maganar nan da ke, sai kuma gashi ya bukata da kansa miya ba zaki yarda?”
Momy ta kalle.
“Baki da wata magana sai ta Madina, duk abun da Madina ta dora ki akai shi kike, ko da abun nan ba mai kyau ba ne”
“Madina ma ba zata dora ni a wani abu marar kyau ba, kawata ce i trust her, shekara nawa muna tare”
“Fine ranar da zata baki mamaki karki nemi taimakona”
“Haka ma ba zai taba faruwa ba, ya maganar aikinta kin fadawa Daddy?”
“Eh na masa magana, kuma na masa maganar aurenku”
“Aurenmu as how Momy?”
“Nace a saka muku rana, ban san abun da kike jira ba, kina ta bin shawarar zuciyarki, kin gama karatu shi ma kuma yana aiki, to jira na me? Da can ina goyon bayanki amman a yanzu kam bana goyon bayan zaman da saki yi ta yi, domin na lura shawarar Madina kike bi, har yanzu kin kasa fahintar Cewar tana son Talba ne”
Leila ta mike tsaye da sauri tana kallon Momy.
“Momy idan kin tsani Madina ba wani abu ba ne, amman abun da kike jifan Madina da shi yanzu ba zai taba faruwa ba, na san wacece Madina, har abada ba zata taba min abun da kike tunani ba”
Momy kallonta kawai take domin ta lura ba karamin fusata tai ba saboda furucin Momy, ba lallai ne ta fahimta ba balle har ta yarda.
“Ni ban shirya aure yanzu ba?”
“Sai yaushe? Sai ranar da zata yi?”
“Momy please you parents should know your limits, Momy ku ma fa kun yi na ku zamanin haka bata faru, Wallahi a waje ba ayi ma yaya haka, kowa yana da right dinsa”
Momy ta kalleta da kyau.
“Kin manta cewar mu musulmai ne? Kuma idan kin yi karatu a waje that's was before, yanzu kuma kina a nigeria a nigeria ma a zamfara, kuma ke bahaushiya ce karki manta da wannan”
“Na san duk wannan amman ni kuna tauye min hakki, ko da yaushe Talba ne mai gaskiya shi ne mai yanke hukuncin komai, a duk lokacin daya bukaci aure ko wani abu ana bashi kai tsaye, na san shi zan aura, amman ni ma fa ina da right Momy, ku rika min adalci”
“So yanzu dai baki shirya auren ba?”
Momy ta tambaya tana daka mata tsawa, sai ta dauke fuska tana jin bacin ranta yana karuwa.
“I'm not ready gaskiya, or i will think about it”
Tana kawai nan ta juya a fusace ta fice daga dakin kamar walkiya. Dakinta ta shiga ta dauki key din motarta ta yar karamar jaka da wayarta ta fito, daman abu ne mai wahala ka ganta da mayafi idan ma ta saka to ba wai wuce karami ba irin wanda zai tsaya daidai wuya. Yanayin yadda take saukowa daga stairs din ma kadai ya isa ya sanar da bachin ranta, Mairo dake aikin gyara dinning dinbda suka ci abinci sai kallonta take kasa kasa. Da karfi ta bude kofar falon ta fita, kamar an biyota haka ta isa gurin motar ta bude ta shiga, tsakanin hannunta da jikinta ba zaka iya tantance mai fiskar wani ba.
Masu aikin bude gate din gidan sun karanci halinta fiye da kowa a gidan, macece mai matukar wulakanci idan ka shiga konarta, ga ji da kai da daukar kowa ba komai ba, ita dai a idonta kowa kaskastacce ne. Hakan yasa suka bude gate din da sauri tun kamin ta iso, kamar an rubuta cewar Leila kadai akai yi wa wannan titi haka ta rika gudu zuciyarta sai tafasa take. Kamin ta