Showing 237001 words to 240000 words out of 332834 words

Chapter 80 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65629

nisa ya kusa fita gate sannan ta bude motar ta fito da sauri.
 
“Wacan mutumen shi ne wanda ya sace ni”
 
Daga Talba har Ali kallon inda take nunawa sukai da sauri.
 
“What... ”
 
Talba ya amsa da karfi sannan ya zagaya da gudu ya shiga motarsa, sai Aminatu da fita daga cikin motar da sauri sai ya miko hannu ya rufe gambun yai reverse a haukace ya fisgi motar ya yana hawa titin da zai sada shi da gate din motar wacan mutumen na ficewa daga gate din. Ali kuma yai hanzarin koma ciki ya fadawa securities din ciki su fadawa na gate su rufe gate din su tare mutumen, amman ina kamin ya isa gurin ma har mutanen ya fice daga gurin. Aminatu kam komawa tai gafe ta tsaya ta rumgume hannayenta tana jin tsoro sai hawaye suka fara mata zirya, sai da ta soma tsawalla da yadda mutane ke kallonta sannan ta juya ta koma inda Talba ya shiga da ita dazun, da zimmar ta koma office din Ali sai ta kasa gane gurin, ta bace hanya. Hakan yasa ta nufi wani ward din da babu mutane sosai ta tsaya daga jikin kofar farko ta jingina tana hawaye sai tsoro take ji. Bude kofar akai Faruk ya fito rike da hannun Sultan, dan tsayawa yai kallonta.
 
“Lafiya?”
 
Ta ki ce masa komai ta kalli Sultan kawai ta juya ya koma gaban wata kofar ta tsaya.
 
‘Ko wani take nema? Ko kuma mutuwa akai mata’
 
Ya raya a zuciyarsa, be sake ce mata komai ba ya rika ja hannun Sultan zai wuce. Sai jikinta ka fara rawa wani irin tsoro da faduwar gaba suka taso mata sai jiri ya fara dibanta, fashewa tai da kuka ta sulale kasa idanuwanta suna son rufewa. Da sauri Faruk ya saki Sultan ya karasa kusa da ita sauri.
 
“Subhanallahi....”
 
Ta kalleshi da idanuwanta da suke daf da rufewa, sai ga wani duhu ya baibaye idon nata, daga lokacin me ta masa jin komai ganinta ya bace bat.
 
 
 
***     ***      ***
 
Yanayin yadda Talba ya fito da motar saya securities din gate din hanzarin rufe gate din. Talba ya faka motar ya fito da sauri yana fadin.
 
“Bude min gate din nan wanda ya fita yanzu kidnapper ne nemansa muke”
 
Zuwa sukai suka rike Talba, saboda an kira daga ciki an ce su rufe gate din, a zatonsu Talba ne Wanda ake nufi domin shi ya zo a guje. Duk yadda ya so su sake shi sai suka ki har sai da Ali ya iso gurin.
 
“Ku sake shi ba shi ba, wanda ya fita yanzu mai 406 ash color”
 
Talba ya koma motar da sauri cike da fatar ganinsa, sai suka bude masa gate din ya hau baban titi kamar an koroshi sai kalle kalle yake wai ko zai ganshi, ba ankaro ba wata babbar mota ta bugi motarsa domin ya taho a guje babban motar kuma ta fito kan kwana, sai aka hankada motar Talba can gafe ta sake bugun wata motar, shi kuma ya buge wasu masu babur suka fadi sai sitiyarin motarsa ya fito da karfi ya daki kirjinsa.
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
 
Ya furta yana jin wata kalar azaba a kirjinsa, kamar an hura mata wuta a ciki, daga nan be sake sanin inda hankalinsa yake ba.
 
 
LEILA POV.
 
Ta sauke wayar cikin da bakinciki, har ita Talba zai sakawa sharadi saboda ta fadi abun da yake gaskiya akan Aminatu? Amman ba laifinsa ba ne laifin Momy ne da ta saka ta kira shi ta bashi hakuri, bayan kuma Daddy ya gama wulakantata ya saka ta bata hakuri. Ta cika  bakinta  da iska ya busar.
 
“Ko da yake Momy ta min rantsuwa ai, Allah kasa na iya rike kaina, kamin komai ya kallama”
 
Ya fada tana wurga wayarta kan gado.
 
“A yanzu ba ni da burin daya wuce ganin yarinyar nan ta wulakanta Wallahi, ji wai har wani kareta yake yana fada min magana, wai ni Leila”
 
Ta nuna kanta, can kuma ta fara shinshinar jikinta tana jin wani wari da bata san na miye ba.
 
“Me na taba haka”
 
Ta fada tana yamutsa fuka, domin bata san wani abu mai wari haka ba, kuma bata san ta taba wani abu ba balle tace shi ne. Da sauri ta cire tufafin jikinta ta daura tawul ta shiga bathroom tai wanka. Sai da ta gama wanka ta fito sannan ta daina jin warin jaban, sai dai ita bata san warin jaba ne domin bata ma san jaba ba balle ta san warinta. Sai da ta fara zuwa gaban madubi ta gyara jikinta sannan ta nufi wardrobe dinta ta dauko wasu tufafin ta saka, bata damu data daura dankwalin tufafin ba ta dauko wayarta ta fito dakinta zuwa dakin Momy. Wani kalar farinciki ne ya lullube ta ganin Hajiya Sadiya kusa da Momy suna hira.
 
“Mama Sadiya kin zo?”
 
Hajiya Sadiya ta kalli Leila tana murmushi.
 
“Ba dole na zo ba, Mamanki ta kirani tana fada min abu ba dadi? Ai tana gama fada min na shirya na tafi kauyen nan yanzu haka na ba ni wani maganin amman ya ce na tsakanin yarinyar ne da Talba, na tsakanin ke da Talba kuma sai kin zo da kanki”
 
Kamin Momy tace komai, Leila ta ce.
 
“Wallahi zan je, yaushe zaki koma Mama Sadiya? Saboda yarinyar nan ta ishe ni Wallahi, yanzu ma baki ji abun da yake fada min ba saboda ita har da rantsuwarsa”
 
Hajiya ta tabe baki.
 
“Ai ba a banza yake komai ba, shi kansa malamin ya fada min asiri aka masa yake ta faman hauka akanta”
 
Momy ta daga kai.
 
“Abun da nake ta fada mata kenan, amman ta ki ta gane, sai wani wuta wuta take, shi fa yanzu baya hayyacinsa, amman idan kika bi komai a sannu sai ya tafi yadda ake so, ba rantsuwa na miki sai na raba shi da yarinyar nan ba? Ai ki zuba ido ki gani”
 
“Na fada masa haka, yace zai yi farraqu tsakaninsa da ita, zai raba su rabuwa ta har abada, ko dazun da na tafi gurinsa sai da na jaddada masa haka, kuma ya ce min na saka ido kawai na yi kallo”
 
Cewar Hajiya Sadiya. Tsabar jindadi da murya yasa Leila ta rumgume Hajiya Sadiya cike da farinciki.
 
“Na gode Mama na gode”
 
Ta fada cikin farinciki marar misaltuwa.
 
 
 
 
 
TEAM Leila
TEAM Aminatu
TEAM Madina
TEAM Faruk
TEAM Baturiya
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
*Khadeeja Candy*
 
 
Kamar wanda aka jefowa rai haka ta farko da karfi tana haki, but still dishe dishe take gani ga wani uban nauyi da kanta yai. Faruk da ya kusa kawai karshem ward din ya dawo da sauri yana kallonta.
 
“Sannu...”
 
Ta dago a hankali ta kalleshi amman bata iya gane fuskar waye, muryar kawai take ji, wani irin faduwa ta ji gabanta na yi.
 
“Sannu”
 
Ya sake furtawa yana kallonta, sai ta yunkura zata tashi ta kasa.
 
“Bari na dubo likita zauna nan?”
 
“Aa zzza... Zan iya tafiya”
 
Ta fada bakinta na rawa kamar yadda jikinta ma yake rawa, har Faruk ya mika hannu ya rikata sai tai saurin matsawa duk da kasancewar bata iya ganinsa da kyau.
 
“Ina da aure ni matar aure ce”
 
Saurin janye hannunsa yai daga rikon da yake da miyar yi mata.
 
“Zaki iya tafiya?”
 
“Eh zan iya”
 
Ta amsa tana dafa ginin gurin.
 
“Dan Allah kasan inda Office din Doc Ali yake?”
 
“Ban ma san waye Doc Ali a nan ba, amman bari na tambaya miki”
 
Ya juya ya koma dakin da Mama take, Maman Safiyya ta kalleshi.
 
“Faruk har ka dawo?”
 
“Daman ban yi nisa ba, wata yarinya ce ta fadi a nan, dan Allah dan zo ki rikata”
 
Maman Safiyya ta mike tsaye da sauri tana fadin.
 
“Subhanallahi ina take”
 
Mama dake kwance dagowa tai tana kallon kofar. Faruk ya fara fita Maman Safiyya ta bi bayansa da sauri, sai suka samu Aminatu a tsaye tana kallon ward din kamar mai tunanin yadda zata isa gurin. Maman Safiyya ta rikata da hannu biyu tana mata sannu Faruk kuma ya wuce gaba, a nan Aminatu ta samu kuzarin takawa Maman Safiyya na rike da ita, har suka fita daga ward din. Gurin da ta fito Faruk ya nufa ganin ya fi mutane wai ko a can za a samu wanda ya san office din Doc Ali, kusan duk mutanen dake kai da kawo idan ya tambaya cewa suke ba su sani ba, hakan ya saka ya nufi reception din inda nurses suke.
 
“Dan Allah Doc Ali muke nema”
 
Faruk ya tambaya, sai wata nurse ta nuna masa shi daga inda take zaune.
 
“Ga shi can”
 
Faruk ya juya ya yana kallon Doc Ali dake kokarin bude back seat nurse din dake gaban motarsa suka matso da gado da taimakon ma'aikatan jinyar aka fito da Talba suka dorashi saman gadon sannan suka shiga kofar emergency da shi.
 
“Ina ganin yana busy ne, ina ne office dinsa”
 
“Eh abokinsa ya samu hatsari”
 
Wata nurse din dabam da ba wacan ta farkon ba ta amsa masa. Wani irin amsawa gaban Aminatu yai sai ta juya tana kallon gurin duk kuwa da kasancewar bata iya gani sosai.
 
“Ina office din nasa yake da wanda ke nemansa nan sai a kaita ta jira shi?”
 
“Kabi ta can, kwana ta biyu zaka ga wani ward na yan haihuwa kusa da gurin akwai offices ko wane da suna a jiki zaka ga an rubuta sunansa”
 
“Okay mun gode”
 
Faruk ya fada sannan ya nufi gurin, Maman Safiya na rike da Aminatu dake ta kallon wajen Emergency, komai dishe-dishe take ganinsa sai dai jinta sarai yake, kalmar abokinsa ya samu hatsari ya shiga kunnenta kuma ya nemi guri a kwakwalwarta ya tsaya, takawa take amman hankalinta da tunaninta sun tsaya cak akan abun da Nurse din ta fada, zuciyarta sai bugawa take da karfi kirjinta na mata zafi marar misaltuwa. Kwatancen da akai ma Faruk shi ya bi ya isa kofar office din ya kai hannunsa ya bude sai yai arba da wani mutum zaune a office din yana operating system, sai da Faruk ya gaisa da shi sannan ya gabatar masa da Aminatu.
 
“Okay ta zauna a nan, Doc baya nan”
 
“Eh mun ganshi a waje ance abokin ya samu hatsari”
 
“Abokinsa?”
 
Mutumen ya tambaya yana kallon Faruk kamim ya kara da fadin.
 
“Subhanallahi”
 
Maman Safiyya ta mufi kujerar ta zaunar da Aminatu.
 
“Allah ya sauwake”
 
Aminatu tana son ta bude baki tace mata Amin kuma ta mata godiya amman ta kasa yin ko daya, saboda rikewar da zuciyarta sai bakinta ma yai nauyi sosai. Kusan a tare Faruk da Maman Safiyya suka fita, Aminatu ta zauna a gurin kamar hoto, numfashi kawai take fitar amman ko motsi kasa yi tai, mutumen dake zaune ya kalleta bayan ya gama abun da yake ya ce.
 
“Zan rufe office din”
 
Ta mike tsaye cikin rashin kuzari ta nufi inda take kyautata zaton kofa ce, da taimakon hannayenta ta fito daga office din ta dafa kujerar dake gefen kofar ta zauna, sannan mutumen ya fito ya rufe office din. Sai da ya kusa awa daya da tafiya sannan Doc Ali ya shigo ward din kana ganinsa kasan yana cikin damuwa da tashin hankali marar misaltuwa, rage tafiya yai hango Aminatu zaune ya san shi take jira ko Talba, for the first time ya ji ta bashi tausayi. Taya zai fada mata Talba ya samu hatsari? Ta ma zata ji. Sai da ya kawo kusa da ita sannan ya sauke ajiyar daya gagara saukewa tun lokacin da abun ya faru.
 
“Aminatu”
 
Ta kasa amsawa, sai kallonsa take ta kai hannu ta fara murza idon ko zata ganshi daidai. Hannu ya kai ya murda kofar office din sai ya ji a rufe, juyawa yai ya koma inda ya fito be dade ba suka dawo tare da mutumen dazun wanda ya rufe kofar.
 
“Yauwa yarinyar nan tun dazun take jiranka, har na gama abun da zan yi na ce ta fito na rufe office din”
 
“Karka sake yin haka, ka barta a ciki office din Matar Talba”
 
“Ai ban santa ba ne shiyasa ko shi... ”
 
Mutumen be karasa ba, Ali yai saurin dafashi ya girgiza masa kai ta sigar da Aminatu ba zata gani ba. Sai da aka bude office din sannan Ali ya kalli Aminatu.
 
“Ta so ki shiga ciki”
 
Ta mike tsaye ta nufi kofar ta shiga a hankali tana dafawa har ya isa gurin kujerar data zauna dazun ta sake zaunawa, sai ta bishi da kallo, so kawai take ta ji ya mata magana, shi kuma ya gagara hada kalmomin da zai fada mata komai.
 
“Bari na kira Mama ta zo ta tafi dake, amman kina jin wani ciwon ne?”
 
Ta lumshe ido.
 
“Ko baki da kuzari ne?”
 
Nan ma bata ce masa komai ba.
 
“Aminatu”
 
Ta bude idon ta kalleshi.
 
“Kina jin wani abu ne?”
 
“Talba...”
 
Ta furta daker tana jin wani abu na sokar kirjinta.
 
“Ya tafi ya kai report gurin police ne, shi ya ce na kai ki gidana, zai je can ya daukeki”
 
Ta sauke kai kasa ta kasa cewa komai, kuma ta masa yin kuka ta kasa yin wani kwakkwaran motsi, ta rasa wani tunani zata yi. Yana kallonta yana dialing number matarsa har kiran ya shiga, sai ya mike tsaye ya nufi windows hawaye na cika idonsa.
 
“Ki zo yanzu yanzu office dina ki tafi da Aminatu, Talba ya ce akai ta can kamin ya zo”
 
“Lafiya?”
 
“Lafiya Kalau, ta ga wanda yai kidnapping dinta ne kuma ta fada masa to ya bi sawun mutumen ne”
 
“Okay, gani nan, zuwa”
 
Sai da ya share hawayensa sannan ya juyo ya zauna saman kujerar ya fara ya kulle bakinsa gam, can kuma ya mike tsaye yana dialing Number Kabir ya fice daga office din. Sai da yai nisa da office din sannan ya amsawa Kabir.
 
“Kana ina?”
 
“Gida”
 
“Zaka iya zuwa Asibitin nan yanzu?”
 
“Miya faru?”
 
Ali ya kai hannunsa ya shafa kansa hawaye na sauko masa.
 
“Bana son na fada maka abun da zai tada maka hankali, saboda bana son hankalin yan gidanku ya tashi musamman Leila”
 
“You can tell me”
 
“Talba ya sami accident, and mun yi duk iya kokarin da zamu yi mu har yanzu be farka ba?”
 
Kabir dake zaune Garden ya mike tsaye da sauri Laptop din dake jikinsa ta fadi kasa.
 
“How Ali how?”
 
“Aminatu ce ta ga wani mutum tace shi ne wanda yai kidnapped dinta, sai ya shiga motar yabi bayansa bayan mutumen ma yayi nisa, shi kuma ya fita da gudu mutanen da suka san abun da ya faru sun ce babbar mota ce ta buge shi, shi kuma ya bugi wasu masu babur, ni kuma na bi bayansa ko da na isa hatsarin har ya afku daker muka samu ciroshi cikin motar saboda tarin motar ya danne masa kirji, jini sai fito masa yake ta baki da hanci, mun kasa dawo da numfashinsa Kabir yana raye amman ba numfashi”
 
Kabir ya kashe wayar ya fito da gudu ya nufi part dinsa ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa yana mata key ya yai reverse kamar mahaukaci ya har wani hayaki ke fita, horn din saya danna yayi goma lokaci daya, da gudu suka bude masa gate din ya dauki hanyar asibitin.
Ali na jin Kabir ya kashe wayar ya daga kansa sama yana kokarin ganin be yi hawayen da suka cika idonsa ba su zubo ba, sannan ya sauke kan ya juya ya koma office din. A tsaye ya samu Aminatu tana kallon kofar office din kamar tana jiran shigowarsa.
 
“Kin gaji da zaman ne?”
 
Ta kasa cewa komai, sai dai ta koma ta zauna tana murzar idonta.
 
“Ko wani abu ya samu idonki ne?”
 
Ta daga masa kai kawai ta kasa cewa komai, kujerarsa ya nufa ya zauna yana kallonta, sai tausayinta ya kara kama shi. After like five minutes Kabir ya turo kofar office din ya shigo da saurinsa hankalinsa a tashe.
 
“Ina yake”
 
Ali yayi saurin kallon Aminatu sannan ya mike tsaye ya nufe shi.
 
“Could we talk outside?”
 
“No Ali wannan ba magana ce da za a rufe ba, just ka fada min ina dan'uwana yake? Transfer za a masa zuwa wata asibiti”
 
“Muna da dukan nin abun da asibiti, idan har muka kasa yin wani abu wace asibiti kake tunanin zaka kai shi duk fadin garin Gusau?”
 
Kabir ya shafa kansa ya lumshe ido ya bude, zai yi magana sai suka ji Aminatu ta fashe da kuka jikinta ya shiga rawa sosai.
 
“Ka gani ko? Shiyasa nake shakkar fada maka, kai kanka ka kasa rike kanka yanzu ka zo nan ka tashi hankalinta”
 
Kabir ya juya ya fita yana lasa wayarsa sai Ali ya bi bayansa.
 
“Wa zaka kira?”
 
Ali ya tambaya bayan ya rufe kofar office din.
 
“Daddy mana”
 
“No you can't do this Kabir, kasan yadda Daddy yake son Talba zaka tayar masa da hankali ne kawai, miyasa kake abu kamar mace?”
 
Sai da wayar ta fara ringing sannan tunanin yadda Daddy zai ji ya zo masa, a dole ya yanke kiran ya juya da sauri ya nufi hanyar daga ward din, Ali ya bi bayansa. Ali ya rigashi isa ICU din, likitoci biyu dake tsaye kan Talba suka kalli Ali.
 
“Ya motsa?”
 
Ali ya tambaya, sai dayan ya amsa masa da sauri.
 
“No, but he is still alive”
 
Ali ya girgiza kai yana jin kamar ya dora hannu akai yai ihu, daya daga cikin nurses din da suke tare da Docs din ta kalli Ali da ke cikin tashin hankali ta ce.
 
“Doc be kamata ka shigo a cikin wannan yanayin ba”
 
“I know”
 
Ya fada jikinsa na kara mutuwa, juyawa yai ya fice daga ICU din, Kabir dake tsaye bakin kofar ya juya ya fara safa da marwa. Kamin ya juyo ya kalli Ali
 
“Hoto ya kamata masa yanzu, maybe jini ya taba wani guri ne a jikinsa ko zuciyarsa, maybe sai an kwashe jinin zai samu farfadowa, transfer za a masa zuwa asibitina”
 
Kabir na rufe baki Talba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login