Showing 294001 words to 297000 words out of 456519 words
komai matarsa warce ita ce mahaifiyar Abdallan ta dakatar da shi, cike da takaici tace "Kar ka ce mata komai, kar ma ka fara Alhaji, fuskar yarinyar nan kawai zaka kalla and it says it all" Juyawa Dattijon yayi ya sake kallon Mayraah, zuwa sannan ne Aunty Sadiya ta shigo parlon tana kallon Ammi wanting to know their mission a gidan Babban yayansu don sai yanzu ta tuna a inda ta taɓa saninta wato ranan da suka je kai lefen Mayraah da kuma sanda suka je amsowa, Hajiya Ramatu ta fashe da matsanancin kukan takaici a parlon tana girgiza kai, Ceo ta juya tana kallon Abba hawaye cike idonta tana nuna masa Abdallah, Calmly tace "Alhaji wannan mutumi da kake gani shine yayi assaulting Kanwata many years ago, putting her in a family way, a sanadin haka har ta samu 'ya mace out of wedlock...." Sai kuma ta nuna masa Dattijon wanda aka fi sani da Hon Alhaji Kabir Saminu tana murmushin takaici hawaye na sauka idonta tace "Wannan kuma shi ne mahaifinsa wato kakan Mayraah wanda ya sa aka kulleni gidan yari na wata bakwai" Da sauri Abdallah ya karasa gun Aaria da wani expression yana zare ido bakinsa na rawa yace "Did you hide anything from ur sister afterward Maryam??" Wani kallo Ceo ta jefa masa strictly tace "Kar ka kuskura ka firgita min kanwa Malam, stay back" Abdallah ya koma gun mahaifiyarsa cikin kidimewa ya durkusa gabanta yace "Mommy duk fa kun san abinda ya faru 22 years ago, babu abinda baku sani ba don Allah ku ce wani abu" Mahaifiyarsa dai sai goge hawayen dake ta sauko mata take tana girgiza kai ta kasa cewa komai tsabar takaici da zafin da zuciyarta ke mata, Mami kam rike kanta da yayi mata nauyi tayi tana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta, in dai abinda ya faru ne a wancan lokacin ai duk kowa a family ya sani ba boyayyen abu bane, zuwa sannan Aunty Sadiya ƙafafuwanta sun kasa daukarta sai bin kowa na parlon take da ido abu ne wanda ya zo masu dukkansu a ba zata, durkushewa Musharraf yayi a nan kasan parlon zuciyarsa na wani irin bugawa, Tuni Hon Alhaji Kabir ya mike ƙasan tsadadden carpet da yake zaune ya koma kan kujera ya zauna da kyar ya jinginar da kansa jikin kujeran ya dafe gefen kirjinsa, mikewa matarsa tayi da sauri ta nufesa ta zauna kusa da shi cikin rawan murya tace "Baka da lafiya Alhaji, pls let's take everything easy, we should take everything bit by bit, kar kayi stressing kanka, ka kwantar da hankalin ka don Allah" Tana fadin haka ta mike ta kama hannun Mayraah dake kuka ta zaunar da ita saman carpet din gently sannan ita ma ta zauna hawaye na sauka idonta, dafe kanta tayi bayan few seconds ta dago cike da karfin hali take kallon su Abba tace "Alhaji plss ku zauna" Sai a sannan Abba ya sauke wani ajiyar zuciya da kyar ya daga kafa ya karasa cikin parlon ya zauna saman kujera, Ammi dake hawaye ita ma ta tafi ta zauna, Usman da Maheer that were more then shock too duk suka zauna parlon kowa na parlon nan ganin abun yake kamar almara banda Ceo da kanwarta, Ceo na rike da hannun Aaria suka nufi kujera ta zaunar da ita sannan ta zauna tana goge mata hawayen dake sauka idonta da handkerchief. Hajiya Ramatu na kallon dan nata cikin karfin hali tace "Abdallah what happened 22 years back?" Ya juya ya kalli Aunty Sadiya da ita ma hawaye ya cika idonta, sai kuma ya kalli mahaifiyarsa cike da damuwa yace "Amma Mommy ke da Daddy kun san komai fa, even Aunty Halima...." Hajiya Ramatu ta dakatar da shi tace "In mu mun san komai duniya fa??" Ya runtse ido ya mike yana kallon Aaria ya nufeta yana girgiza kai yace "Maryam, why did you chose to hide things from ur sister?" Aaria dake ta kallonsa cikin sanyin murya tace "Like?" Ita dai Ceo da duk sauran occupant din parlon kallonsu suke, banda Mayraah da kanta ke sunkuye tana hawaye, Abdallah ya durkusa gabanta trying all best to compose himself yace "Yes i assault you da farko kamar yanda yayarki tace i can't deny that, amma daga baya fa Maryam? Me yasa na dinga bibiyanki after that? Why did u hide that part from ur sister?" Aaria ta daga kai ta kalli Ceo dake kallonta Keenly don ko da wasa Aaria bata taɓa gaya mata komai ba, Aaria ta sunkuyar da kanta kamar baza tace komai ba, sai kuma a hankali tace "I can't remember anything" Abdallah ya girgiza kai da damuwa yace "You are not saying the truth Maryam.... But why pls?" Ita dai taki ce masa komai, ceo bata fasa kallonta ba tana son jin wani truth ne ta boye mata, Abdallah ya juya yana kallon mutanen parlon bayan few seconds ya dake yace "Bayan encounter dina na farko da Maryam, i was disturbed and regretted all what that happened that day, and that was so unusual of me don kuwa my father was very rich, i was an only child don haka duk wani abu da zan aikata i always have my way babu wanda ya isa ya hukunta ni domin mahaifina zai tsaya min a ko ina kuma bana taɓa regretting, but in Maryam's case it was different don na shiga damuwa sosai hakan yasa na ci gaba da bibiyarta har gidansu, a sannan yayarta na fita kasuwa kullum da safe bata dawowa kuma sai karfe shidda, duk zan je gidansu Maryam tare mu ke zuwa da Aunty Halima warce ita ma ban boye mata abinda ya faru ba, though aunt dita ce ita amma kuma na girmeta sosai don ita ce autansu Babanmu kuma a gidanmu ta tashi bayan kakannimu sun rasu shi sa muka shaku da ita, a ranan ma Dad dina ne yayi niyyar zuwa makaranta ya daukota amma sai tafiya ya kamasa ni naje makarantar, after a while of following Maryam ina mata magiya sai ta dan fara sakin jiki da ni partially har ya kai ta sanar min a little about her self and her sister da irin rayuwar da suke tun bayan rasuwan iyayensu, har cikin raina naji ina son zan auri Maryam duk da karancin shekaru na don komai nayi offering dinta as gift bata amsa kuma bana jin dadin haka" Bude baki Ceo tayi tana kallon Aaria babu ko kiftawa, Abdallah ya rufe idonsa ya bude ya ci gaba "Na samu Dad dina na sanar masa ni na samu matar da nake son zan aura a lokacin, shi da Mom dita sun yi mamaki sosai don tun ma kafin su ji wacece suka yi against din auren wai i am still young, Dad dina ya kara da cewa kasar waje yake son tura ni in yi karatu, daga karshe saboda yanda nayi persisting akan ni fa aure nake so, sai suka ce min wace yarinyar nake son aura kuma a ina suke zaune a Adamawa, being an only son sannan nasan babu wani abu da nake so da iyayena basa min sai ban boye masu wacece Aaria ba, dad dina na jin wacece ita yayi min iyaka da ita nan take, duk da nayi kokarin fahimtar da shi ita tana addinin musulunci amma ya ki saurarata, he was so mad at me ban taba ganin bacin ran Dad dina ba irin na ranan, ya dinga min fada wai shi zan kawo ma arna cikin zuri'a, to kaf zuri'anmu ba a taɓa haka ba kuma baza a fara a kan ɗan cikinsa ba, cikin fushi ya koreni daga parlonsa, ina bedroom dina cikin damuwa Mom dita ta shigo ta dinga consoling dina don My dad's No is always No, still dai ban daina zuwa gun Maryam da ta saki jiki da ni ba a lkcn, babu yanda ban yi da Maryam a kan mu je wani gari mu yi auren mu ba amma taki, always reminding me of how her mother suffered because of her father's relatives, sannan karatu yayarta take son tayi, duk wannan abubuwan sun faru ne within few months da na fara haduwa da ita don i had to wait to be sure she didn't conceive after our first encounter tun da har raina ina son aurenta ne, and i repented from my bad ways because i was deeply in love with Maryam wanda a lokacin ni kaina ban san wani irin so nake mata ba, kawai watarana na zo da wani plan don naga iyayena are not even giving me listening ears anymore, after coming up with my plan sai naje gidansu Maryam don in sanar mata, coincidentally ranan yayarta bata je kasuwa ba wai bata jin dadi sun fito tare za su je Chemist, nan ta turke kanwarta ta tambayeta waye ni jin na kira sunanta, Maryam is somebody that is so naive and meek, sannan matsoraciya ce, sai ta boye ma yayarta wanene ni, nan yayar ta nuna bata son ina zuwa wajen kanwarta duk tunaninta ai zance ke kawo ni unguwan, nan dai ta ja min layi da Maryam tace min karatu take son kanwarta tayi, a haka dai na kama hanya na bar anguwan" Ceo dai ta kasa dauke idonta a kan Aaria don sai bayan da Hajiya Amina ta gano tana dauke da ciki bayan sun turketa tace ai wannan mutumin da suka taɓa haduwa sanda za su je Chemist ne, a sannan ne kuma ta gaya masu wanene mutumin tunda kowa yasan babansa a garin, Aaria dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, A hankali Abdallah yace "Bayan yan kwanaki ban hakura ba na sake komawa gun Maryam hoping yayarta ta tafi kasuwa, luckily muka hadu da Maryam yayarta bata nan, she was so afraid seeing me ta dinga min magiya in tafi kar in sake dawowa bata son yayarta ta kara ganina, it took me almost an hour to persuade Maryam to follow me, na kuma yi assuring dinta ba dadewa za mu yi ba zan dawo da ita immediately, plan din nawa da nayi niyyar gaya mata wancan ranan kawai na fasa don aiwatarwa kawai nake da niyyar yi, after some minutes ride muka je can wani local government a nan Adamawa not too far away, na kai ta har gun wannan limami da ya riga ya san da zuwan mu, i wasn't bothered with how shock Maryam was bayan ta gano what I was up to, a haka aka daura mana aure da Maryam auren da a washegari aka warwaresa amma kafin a warware auren nan I took advantage of Maryam for the second time on that same day, bayan na koma gida ranan nan banyi bacci ba kawai tunanin yanda zan bar Adamawa tare da Maryam ba tare da ta bani ciwon kai ba nake, first na fara tunanin ko in fara kai ta gun Kanin Dad dina wanda sunansa naci, sannan yana mugun ji da ni, Allah ubangiji ya ji kansa da gafara wato Dad din su Musharraf, plan dai iri iri na dinga yi a raina, ashe duk baza ayi haka ba don a ranan cikin wa enda ke zaune masallacin da aka daura mana aure akwai wanda ya gane ni kuma yasan Dad dina, tun yamma yake unguwanmu tunda waya bai yi yawa ba a lkcn, Mai gadinmu ya sanar masa Dad dina yayi tafiya baya gari, washegari haka mutumin nan ya sake dawowa yana unguwan har Dad dina ya dawo sannan ya sanar masa abinda yaga ya faru a masallaci, Dad dina bai taba mari na ba sai a ranan nan bayan yaje har masallacin tare da ni yayi confirming abinda aka gaya masa, i was thinking daga marin nan shikenan zai hakura Maryam ta ci gaba da zama matata, amma i was mitaken, don immediately nan take ya sa na saketa, shi kuma wannan mutumi da ya kawo masa zancen abinda nayi dubu dari ya basa, i was so heartbroken, hatta Aunty Halima sai da ya nuna mata bacin ransa sosai bayan ya gano duk tare muka yi plan din kuma ya rabata da Maryam na har abada, even goodbye bai bari naje nayi ma Maryam ba bayan ya daukeni muka tafi Abuja, after few weeks ya fitar da ni daga Nigeria zuwa makarantar da ya samar min a UK, bayan 3 years na dawo Nigeria don a sannan ne ya yarje min in dawo hutu, i never knew Maryam conceived after our second meeting, Aunty Halima ce ta sanar min duk abinda ya faru bayan bari na Nigeria 3 years ago da kuma prison da Dad dina ya aika Yayar Maryam har na wata 7, a ranan da na dawo naje gidansu Maryam aka ce min ai sun ma bar garin kwata kwata, i was so sad, ban sake haduwa da Maryam ba ban kuma san inda zan nemota ba, 5 years back kawai sai muka hadu da yayarta a Uk, ina ganinta kuma na gane ta, tun daga sannan nake bibiyarta nake mata magiyar ta hada ni da Maryam sai ta kai karata gun yan sanda daga nan ne na hakura amma kullum da Maryam nake kwana nake tashi a raina, a saboda haka har yau ina nan ban yi aure ba, ko na yunkura zan yi auren sai a samu matsala one way or the other, tun iyayena na min magana har sun hakura suna jiran lokacin da Allah zai kaddara inyi auren idan suna da rabon ganin jikokinsu....." Ceo kuka take sosai tana kallon Kanwarta cikin rawan murya tace "Me yasa kika boye min duk wannan abun Aaria? You told me he forced you" Hajiya Ramatu da hawaye ke zuba idonta ta jawo Mayraah dake kuka zuwa jikinta, Aaria dai kanta na kasa hawaye na zuba idonta, Ceo ta kasa daina kallon kanwarta hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, wa ya ga kuka wajen Ammi, nan kuwa kukan farin ciki kawai take with how things later turn out, Abba ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya yana hamdala a zuciyarsa, Maheer couldn't stop looking at Mayraah that is crying profusely a jikin Hajiya Ramatu, Mami da Allah yayi ta mace me dakiya a ko wani hali ta daura kan Musharraf a shoulder dinta seeing how emotional he was, MD dai kansa na kasa haka ma Usman da tun da Abdallah ya fara magana shi ma bai dago kansa ba, Silence din kusan minti uku ne ya ziyarci parlon, everyone was so speechless and never saw this coming, nobody expect things to turn out this way, Abba yayi karfin hali yana kallon Alhaji Kabiru Saminu yace "Watannin baya da suka wuce idan ba mantawa nayi ba har da kai aka zo nema ma dan ka auren yarinyar da duk duniya mutanen da suka san ba mu ne asalin iyayenta ba basu da yawa, don wani sirri ne babba da muka rufe wanda ita kanta yarinyar bata san ba mu ne iyayenta ba, hatta 'Ya yan da muka haifa a cikinmu bamu bude masu wannan sirri me girma ba, ana saura kwanaki daurin aure sirrin nan da muke ta boye wa na shekara da shekaru ya fallasa wanda hakan ya girgiza mu ainun, babu rashin mutunci da tijaran da yan uwanka basu zo sun mana ba ana gobe daurin aure, suka kirani karamin mutum, suka kirani makaryaci a fakaice daga karshe suka amshi kudinsu suka ce sun fasa wannan aure, though ban ga laifinsu ba don a zance na gaskiya ya kamata ace na buda masu wacece yarinyar nan tun farkon zuwansu neman aurenta amma wllhi wani lokacin mu kanmu mantawa muke ba mu muka haifeta ba, we want nothing but the best for the innocent girl da muka tsinta a walakance shekaru 22 da suka wuce bama san duk wani abinda zai tarwatsa mata farin cikinta gashi ta taso tana mana kallon iyayen da suka haifeta, amma na so su yi considering cewar yarinyar nan bata da laifi in laifin ne ma ni da Amminta ne masu laifin da muka rufa wnn sirri, yarinyar nan tana da tarbiyya, tana da ilimin addini da na boko, wanda shi yaron naku ma lecturer dinta ne a jami'a kuma da bai yi na'am da tarbiyarta ba bazai fara nemanta da aure ba, amma yan uwanka suka rufe ido suka mana abinda suka yi, lefen da suka kawo ma haka nan aka zo aka amsa a nan din ma dai babu irin tijaran da matata warce ita ta rike yarinyar nan tun tana jaririya bata gani ba, to wannan yarinyar da ku ka hana dan ku aurenta don bata da asali ba a san ko er wacece ba ita ce can a zaune, We named her MAYRAAH" Abba ya kai karshe yana nuna Mayraah dake rungume jikin Hajiya Ramatu, Ceo na murmushi hawaye na sauka idonta tace "Kuma yarinyar dake zaune can ita ce warce kanwata ta haifa bayan dan ku yayi putting dinta in a Family way, tana haihuwarta kuma saboda takaicin abinda uban dan yayi min na kai ni prison don na nemi kwatar ma kanwata hakkinta na faki idon kanwata na saka jaririyar cikin kwali na kai ta nayi deserting dinta a wani anguwa wanda a can ne wannan bawan Allah da matarsa suka tsince suka riketa har zuwa yau, bayan raba kanwata da er ta ta shiga halin rashin lafiya har zuwa yau da nake wannan maganar, sai ga shi Allah ya hadani da er kanwata a asibitina na garin Abuja, yanzu kawai DNA test za ayi to clear away doubt din kasantuwarta er Abdallah" Hajiya Ramatu na kara jan Mayraah jikinta ta girgiza kai tace "Babu batun DNA test, don wannan yarinya kamanninta sak na surkata warce ni kaina sai a hoto na taba ganinta tun ina amarya kuma hoton" Mami ta sauke ajiyar zuciya a karo na farko tace "Da naje dubata asibiti da tayi rashin lafiya nima na ga kamannin don ban taɓa ganinta ba sai ranan, har nake gaya ma Musharraf da ya