Showing 249001 words to 252000 words out of 456519 words

Chapter 84 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70668

the pain yace "Dysmenorrhea?" Gyada masa kai tayi da sauri, ya mike ya bar wajen, magani ya yafi ya dauko mata da ruwa a glass cup, hannunta na rawa ta amsa ta sha, shi dai yana duke gabanta yana kallonta, don bata daina kukan da take ba, bayan kusan minti goma yace "Tashi ki koma daki..." Ko rufe baki bai yi ba cikin rawan murya tace "Aa wallahi bai daina ba, kilan allura zaka min, dama allura ake min" Daga sama har kasa ya kalleta seeing how confident she still is in between pains, Bai yi niyyar mata alluran ba saboda ta riga da ta sha drugs, but ganin she is still in pain har karfe uku kawai ya hada alluran ya mata, nan parlon ta fara bacci ya tasheta ta wuce daki. Washegari har karfe takwas bata tashi ba, har sai da ceo ta shigo ta tashe ta, bayan ta fito daga wanka ta shirya sannan ta dau wani jacket dinta dake akwati ta sa sannan ta fita parlor, Ceo na kallonta tace "Breakfast yana dinning table" Mayraah ta nufi dinning din ta zauna. Wajen karfe goma na safiyar Mayraah na waje tare da Usman da zuwan sa kenan, yana kallonta yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki" yace "Me yasa baki kirani jiyan ba, though the ceo might not gree to that since...." Shiru Usman yayi bayan ya hango MD da ya fito daga cikin gidan, tunda Mayraah ta kallesa sau daya ta dauke kai gabanta na faduwa yake, kallonsa kawai Usman yake kamar yanda shi ma MD ke masa kallon cikin ido, har ya zo ya wucesu leaving his designer perfume scent behind, Usman ya dinga kallon jacket din da ya daura shoulders dinsa, can ya kalli Mayraah da ta juya kai taki kallonsu, a kan gado fa ta ajiye jacket din nasa ashe ya shiga ya dauka, Usman yace "Mayraah" Da sauri ta juya ta kallesa, yace "Wannan ba Jacket din da kika ce min Ceo ta baki bane?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Yaya shi ne, amma ai kilan shi ma ta basa ne ya sa...." Kana jin yanda take maganar kasan karya take, Calmly yace "Mayraah" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Whose jacket is that?" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Na shi ne, a airport ya bani saboda ni ban ciro nawa a akwati ba don ban san haka sanyin yake ba, shine sai ya bani nasa in saka" Kallonta kawai Usman yake, ta daga kai ta kallesa jin yayi shiru, after some seconds yace "To kin yi kokari" Tana ganin ya juya zai bar wajen ta marairaice tace "Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi ina tsoron kar ka min fada ne shi yasa nayi maka karya" Yace "Infact karya kike still kice min babu komai tsakaninki da wannan mutumin, saurayin ki ne" Mayraah ta buda baki tana kallonsa da mamaki, juyawa yayi ya bar wajen ta bi sa da kallo, tafi minti uku tsaye wajen daga karshe ta juya a hankali ta fara tafiya zuwa cikin gidan.....





[8/12, 3:41 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah ta daga kai a hankali jin an bude kofar dakin, Ceo ta karaso da cup din hot chocolate ta zauna gefenta tace "Here dear" Mikewa zaune tayi ta amshi cup din hade da sauce dinsa tace "Thank you Ma" Murmushi ta mata tana kallonta calmly tace "You are welcome" Mayraah ta fara shan chocolate din a hankali, Ceo ta mike ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo dakin da few pizza slices a plate ta ajiye mata tace "Will you be okay with this?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Thank you Ma" daga haka ta dau slice daya ta fara ci, after some minutes ceo ta mike ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita ta jawo mata kofar ta rufe, Mayraah ta sauke idonta tana ci gaba da cin pizza din, bayan ta gama ta dau handbag dinta ta ciro wayarta dake ciki, cikin minti kadan tayi activating international roaming sannan ta fara dialing number Maheer, yana fara ring ya daga, a hankali tace "Yaya" Yace "Mimi" Tace "Ka fara bacci ne?" Yace "No Mimi, was waiting for ur call, i couldn't reach you... ya hanya?" Kamar zata yi kuka tace yaya it's soo cold here, i am so cold" Murmushi yayi yace "Yeah i know, akwai sanyi sosai, hope you are on ur jacket?" Kallon jacket din MD dake jikinta tayi, ta kara lullube jikinta da shi murya can kasa tace "Yeah" Yace "kina ina yanzu?" Ta kalli babban dakin tace "Gidan Ceo din mu" Da mamaki Maheer yace "Ceo dinku kuma? Why? Where are ur colleagues?" Mayraah tace "Ni kadai ce dai a nan, su ba a nan suka sauka ba, may be they lodge in hotel, kasan duk maza ne" Maheer ya ɗan yi shiru, can kuma yace "But that's weird, why will she keep u in her home? Any way it's fine..." Mayraah tayi shiru, yace "Hope you are comfortable?" Mayraah ta gyada masa kai a hankali tace "Yeah" Yace "To abinci fa?" Tace "Ta bani har na ci" Da damuwa Maheer yace "Gashi har muryarki ya fara nuna alamar sanyi ya kamaki" Tayi murmushi tace "Yaya kasan fa bana son sanyi" Yace "I know Mimi, shi yasa nake tausayinki" Tace "But ta ban heavy duvet" Yace "To better" Tace "Yanzu Yaya tambayar ta inda zan kalla inyi sallah zan je in yi?" Maheer yace "But she is a Christian how will she know? Ke baza ki gane qibla ba?" a hankali tace "Bazan gane ba, i am confuse" Yace "Ohk try asking her... Meye ta baki kika ci?" Mayraah tace "Ta bani hot chocolate da pizza" Yace "Ohk to ki samu kiyi sallan, idan kin idar sai ki kirani" Tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, tana sauka daga saman gadon duk da dumin dakin she was still feeling cold, a hankali ta saka hannunta a sleeve din jacket din MD sannan ta nufi kofa walking slowly ta bude kofar, tana shiga babban parlon gidan ta dinga bin ko ina da kallo sai kuma ta kalli sama, Muryar ceo ta ji ta juya da sauri ta ganta a study room dinta with heap of textbooks a gabanta, tasowa tayi ta shigo parlon calmly tace "You need anything Mary Ann?" Ta gyada kai da sauri tace "I want to pray Ma...." Ceo tace "Ohh kina tambayar gabas kenan ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yes Ma" Kalle kallen Parlon ceo din ta shiga yi, can tace "I can't really tell where Aliyu faces and pray whenever he is around, let me call him on the phone sai ya gaya maki inda zaki kalla" Mayraah tace "Okay Ma" Ta koma ta dauko cellphone dinta ta fara kiran MD, yana dagawa tace "Aliyu zaka gaya mata inda zata kalla tayi sallah" Daga haka ta mika ma Mayraah wayar, Mayraah ta amsa da ladabi ta kai kunne tayi shiru, jin shi ma yayi shiru tace "Ina ji" Sai a sannan yace "Baki da Google a wayarki ne?" Taki ce masa komai saboda ceo dake tsaye, yace "In rashin kunya ne ai ba sai kin jira wani ya gaya maki yanda za ki yi ba, ba ni kika ce ma Quack Doctor ba, za ki sani" Mayraah dai taki cewa komai, Yace "Install Qibla finder on ur phone and stop being a nuisance" Mayraah bata sake tsayawa ta sauraresa ba ta katse wayar ta mika ma Ceo, Ceo tace "Ya gaya maki ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh ya gaya min" Ceo tace "Ae kina da darduma?" Mayraah tace "Ina da shi" Ceo tace "Toh sai kiyi using warm water kiyi performing ablution din so u won't catch cold" Yanda Ceo tace mata haka tayi da ta koma dakin tayi alwala da ruwan dumi bayan ta fito daga bandakin ta bude akwatinta ta ciro darduman da Ammi ta sa mata sannan ta tada sallan, tana idarwa ta kwanta ta kashe fitilar dakin sannan ta lullube da duvet nan da nan bacci ya dauketa ko Maheer din bata kira ba, cikin dare taji zazzabi ya rufeta ga tari da ta dinga yi, wajen karfe uku ceo ta bude kofar dakin ta shigo ta kunna wutan sannan ta karasa ta zauna gefen gadon ta cire duvet din jikinta tana feeling temperature dinta tace "Are you okay?" Mayraah ta mike zaune tana rawan sanyi, Ceo tace "You are running temperature dear" mikewa tayi ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo da magunguna da ruwan gora, bude maganin tayi ta ba Mayraah ta amsa ta hadiye da ruwan sannan ta koma ta kwanta ta takure waje daya, ceo ta lullubeta da duvet tace "Sannu kin ji...." Kafin gari ya waye ceo ta shigo dakin ya fi a kirga, da asuba haka Mayraah ta daure ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta koma ta kwanta…. duvet din da taji an cire jikinta ya sa ta bude ido a hankali, MD ta gani tsaye kanta, ta mike da sauri ta ja duvet din ta wani daure fuska tana kallonsa, sae kuma ta ga CEO tsaye a bayansa, sunkuyar da kai tayi, Calmly yace "How are you feeling?" Ta gyada kai a takaice tace "Fine" Ceo tace "Will u take noodles for breakfast?" Mayraah ta gyada mata kai, ceo ta juya ta fita daga dakin sai da yaji ta kulle kofa sannan yace "Cire min jacket dina" Wani kallo ta jefa masa ta sauka daga kan gadon ta bude akwatinta ta ciro towel din wankan ta da shower gel with sponge sai toothpaste and toothbrush tayi wucewarta bandaki ta bar sa wajen tsaye, ya bi ta da ido har ta kulle kofar ta sa makulli, Bayan kusan minti daya ya gyada kai ya juya ya fita daga dakin, Mayraah na fitowa wanka taji kamar zazzabin ya sake dawo mata, ta ajiye jacket din hannunta ta kwanta ta dukunkune cikin duvet ta fi minti goma a haka daga karshe ta daure ta mike ta shirya, ta dau jacket din tana kokarin sa wa Ceo ta shigo dakin tace "In kin gama ki fito kiyi breakfast" Tana fita Mayraah ta saka jacket din sannan ta fito parlor, dinning area ta nufa ta zauna kujeran dake facing na MD dake kallonta ganin she is still wearing his jacket, garnished noodles with chicken Ceo din tayi mash, MD dai na rike da spoon yana kallon plate din abincin, lokaci lokaci yake satan kallon Mayraah, Mayraah ta fara cin abincin haka ma ceo, bayan some seconds ceo ta kallesa amma bata ce komai ba, mikewa yayi ya wanke fork din da knife din hannunsa a washing hand basin dake dining area din ya dawo ya zauna, Ceo tace "Ya maganar Therapy da nayi maka kwanaki?" Karo na farko da Mayraah ta fara ganin murmushin sa, yace "Soon Ma'am" Ceo ta ci gaba da cin abincin ta a nutse, Mayraah sai kallonsa take kasa kasa without letting him notice, gaba daya he doesn't look comfortable a wajen, kawai ta ga ya jawo wani clean plate din ya goge da tissue ya juye abincin a ciki, Ceo ta kallesa ta ci gaba da cin abincinta, sae a sannan ya fara cin abincin, Mayraah bata ci abincin da yawa ba duk da ɗan manna masu ceo tayi a plate kamar wasu turawa, cikin minti kadan ya gama cin abincin ya mike ya bar dinning area din, duk suka bi sa da kallo, dakin da Mayraah take ya shiga, Mayraah dae sai kallon ikon Allah take, ba a dau lokaci ba sai ga shi ya fito, kallonsa Mayraah ta dinga yi da mamaki ganin Jacket dinta a hannunsa, yana kallon Ceo da ladabi yace "I will take my leave now ma'am” CEO tace “Ohk" Daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita daga Parlon yana rike da jacket din, Mayraah ta mike zata kwashe plates din Ceo tace "Ki bar shi, yanzu mai aikin zata shigo" Mayraah tace "Toh" barin dinning area din tayi ta tafi daki, bayan ta kulle kofar ta dinga kallon akwatinta dake bude, ta wani hade rai, saboda me zai bude mata akwati, is he even okay?? tsaki ta ja ta karasa ta kulle box din, kwanciya tayi ta dau wayarta tayi dialing number Maheer har ya katse bai daga ba, ta ajiye wayar ta rufe jikinta da duvet. Har ta fara bacci Ceo ta shigo dakin cikin sparkling suit da skirt din da iyakarsa gwiwa, sosai tayi kyau kamar wata baturiya, tana kallon Mayraah tace "You just stay back and rest Mary Ann, za mu je conference din yanxu, it's only for today and tomorrow.... if u need anything feel at home ki shiga kitchen" Mayraah tace "Ohk Ma, nagode" Ceo ta mata murmushi sannan ta juya ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da ido har ta fita ta kullo kofar, a hankali ta jawo wayarta tayi dialing number Amminta.... Karfe sha biyu saura kiran Usman ya shigo wayarta, ta mike zaune daga kwancen da take da kyar saboda mugun ciwon da kanta yake mata, picking call din tayi ta gaishesa ya amsa yace "Mura kike ne?" A hankali tace "Eh" yace "Kin sha magani?" Tace "Na sha daxu" yace "Where is ur location?" Tace "Nima ban sani ba yaya" Yace "Ask around you" tace "Ni kadae ce a gida, sun tafi conference, i am not too fine saboda muran da nake...." yace "Hotel ne?" Tace "Aa gidan ceo, idan sun dawo i will ask for the address" ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Gidan Ceo? How comes?" Bai jira tace komai ba ya kara da cewa "Ok then, I will be waiting for the address" a hankali tace "Ohk" katse wayar yayi ta ajiye, gaba daya mura ya sa ta gaba and it's making her feel sick, tana ganin lkcn sllh yayi ta tashi taje tayi alwala, tana idar da slln ta kwanta, cikin bacci ta ji an bude kofar dakin ta bude ido taga Ceo, mikewa zaune tayi, Ceo tace "Baki yi lunch ba Mary Ann" Ta murza ido tace "I slept off" Ceo tace "This is pass 3, ki fito ki ci abinci" Daga haka ta juya ta fita, Mayraah ta sauka daga kan gadon ta tafi parlor. Karfe biyar saura Mayraah ta fito daga dakinta tana kallon Ceo dake parlor tace "Ma ya iso, yana waje" Ceo tace "Ohk, ba kince Yayanki bane?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yayana ne" Ceo tace "Let him in, it's cold outside" Mayraah tace "Ohk Ma" Fita tayi daga parlon, inda ta hangosa tsaye ta karasa, idonsa na kanta har ta karaso ta kara gaishesa tana murmushi tace "Yaya kai ma ashe kana jin sanyi naga ka sa Jacket?" Yace "Kema kika ji sanyi balle ni" Er dariya tayi tace "To ai ni dama kowa yasan bana son sanyi, kai kuma baka bacci sai da AC" Yana kallon rigar jikinta yace "I see, where did u get this designer jacket u are putting on?" Mayraah ta kalli Jacket din MD dake jikinta da sauri, sai kuma ta kirkiri murmushi ta dawo gefensa tace "Ceo ce ta bani" Ya daga kafada yace "Ok, but ai na maza ne, yana da tsada sosai" Mayraah dai sai murmushin karfin hali take, Ya rungume hannunsa yace "But why did she decide to lodge u in her home? Na zata hotel zata biya maku...." Mayraah tace "Eh sauran maza ne duk suna hotel, ni ce kawai a nan, yaya tace fa mu shiga ciki akwai sanyi... She said u are welcome" Ko rufe baki bata yi ba, Ta yi ido hudu da MD da yayi parking ya sauka daga mota wanda da alama tasa ce, Usman ma kallonsa yake ganin he is walking toward them, shi ko bai sake kallonsu ba har ya wucesu, Usman ya bi sa da kallo ganin gidan da Mayraah ta fito zai shiga, sai kuma ya kalleta da sauri yace "Who is he?" Ta ɗan buda ido tace "MD dinta ne, he is the MD of the hospital" Usman yace "MD?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "Shi ma a gidan nata ya sauka kenan??" Da sauri ta girgiza kai tace "Aa fa yaya, kilan ta kirasa ne ta aikesa amma ba nan ya kwana ba wallahi" Usman dai yayi shiru yana kallonta, can yace "Why did u do as if baki san sa ba, shi ma haka?" Da mamaki ta zaro ido tace "Yaya ai ni ban wani san sa ba fa, ka manta ni new staff ce a asibitin? We are not use to each other" Yace "You are never meant to get use to ur boss ai dama, do u know who a boss is? but i am surprise yanda zaki ga boss dinki and not greet him just like that in dai ba akwai wani abu ba, ga dukkan alamu ya sake maki fuska da yawa ko kuma akwai wani abu between u two...." Mayraah ta turo baki tace "Wani abu kuma yaya? To yaushe ma na fara aiki a asibitin, abinda ma zan iya kirga sau nawa na gansa a asibitin, office dinsa ma fa ba kowa ke zuwa ba, and his office is at the last floor of the hospital building, kawai dai ya fiye takura ne da masifa shi sa nake avoiding dinsa, baka ga dauke kai nayi ba kar ma ya gan ni" Usman ya jingina da brick wall din wajen yana kallonta as if not convince, ita dai ta sunkuyar da kanta, bayan few seconds yace "Yaushe tace zaku koma Nigeria?" Mayraah tace "She said gobe ko jibi" Yace "An gama conference din ai?" Tace "Aa gobe ne last day" Yace "Shi kuma da ya zo yanzu sai yaushe zai bar gidan?" Mayraah ta zaro ido tace "Yaya ai nima ban sani ba, kilan aiki zata sa shi.... And na manta tace mu shiga ciki saboda sanyi" A takaice yace "Bazan shiga

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login