Showing 420001 words to 423000 words out of 456519 words

Chapter 141 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70696

a ranta ba, sosai ta kwantar da hankalinta ta saki jiki Maheer na tsumata da salon soyayyarsa me narkar da zuciya, tuni ya rabata da ɗan sauran ɓarbashin kunyarta da ya rage, suka dawo fitsararru a gidan, ita kanta yanzu tasan wani so na musamman take ma Maheer ba na yan uwantaka ba, tun ba yanzu ba ta gano son da take masa ya rikide completely daga na yayanta ya koma na Husband and soulmate, she just can't explain how much she so love and cherish her calm husband, kullum ya fita aiki ta dinga kewarsa kenan har sai ya dawo, she just can't imagine ace ba Maheer bane mijinta, yasan halinta, yasan abinda take so da wanda bata so, yasan me zai ɓata mata rai da wanda zai faranta mata rai, infact he knows her in and out, infact kullum cikin faranta mata yake baya son duk abinda zai bata mata rai, slightest abu zai faru ya bata hakuri even if she's at fault not him, hakan na sa jikinta yayi sanyi sosai, har tayi ta imagining if men like him still exist in this world, it's rare kaga bacin ransa, so da yawa in yana wani abun sai dai ta kafesa da ido tsabar so da kaunarsa da take ji har kasan zuciyarta, wannan yasa a ko da yaushe take hamdala ga Allah with the way things later turn out to be in her life, she now believe every disappointment is truly a blessing in disguise, yanzu kam gidan Ammi dama sai su yi weeks basu je ba. Karfe uku saura Mayraah ta gama girkin da take a kitchen ta fito parlor, kwance ta gansa kan 3 sitter idonsa lumshe yana bacci, ta karasa har kusa da kujeran da yake kwance ta duka tana kallon fuskarsa, babu abinda ya fado mata sai ranan da ta dawo daga gidan yayar Mom dinta da Mama Ladi ta dage wai tana sumbatarsa yana bacci, murmushi tayi ta lumshe ido ta bude, sannan ta daura lips dinta a hankali a nasa, da sauri ya bude ido suka yi ido hudu, ta lumshe ido ta fara kissing dinsa passionately, just 1 minutes kiss tayi masa ta mike zata bar wajen ya jawota ta fado jikinsa sannan ya mike zaune tana dariya ta kwantar da kanta a broad chest dinsa ta lumshe ido a hankali tace "Honey na gama girkin, lkci na wucewa pls ka bari inje in shirya" Yayi kasa da murya yace "But you started first baby" Tana murmushi tace "To yi hakuri mu dawo kaji" Kyaleta yayi ta tashi tana kallonsa tana murmushi ta wuce dakinta, cikin minti ashirin tayi wanka ta shirya sannan ta fito parlon rike da handbag da mayafinta, kallonta Maheer ya dinga yi ganin yanda tayi wani sanyayyen kyau duk da babu make up a fuskarta, sosai atamfar jikinta ya amsheta, gashi ta cicciko ta ko ina... her beautiful shape is so breathe taking, ta nufosa tana murmushi ta wani juya masa gaba daya yana bin ta da ido, daga karshe tayi wani pose tayi fari da ido tace "How do i look Honey?" Maheer ya girgiza kai yace "Ai Hijab za ki sa" Ta marairaice tace "Gidan Ammi fa za mu je Honey, kuma ai ba sauka zan yi daga motar ba, beside a compound za kayi parking ae" Tana gama fadin haka ta wani turo baki ta rungume hannu ta kauda kanta, murmushi yayi yace "Eh haka ne, na tuna a compound zan yi parking kamar yanda kika ce" Ta karasa tana murmushi tayi pecking lips dinsa sannan tace "Bari in dauko abincin lokaci ya wuce" Tana fadin haka ya mike ya bi ta har zuwa kitchen din ya tayata daukan food warmers din ya kai mota, sun dade basu je gidan Ammi ba sai dai su yi waya da ita, yau din ma Mama Ladi za su je gaidawa ta zo tun jiya shine Mayraah tayi masu girki, labari Mayraah ke tayi ma Maheer dake sauraronta har suka isa gida, yayi parking a space da aka tanadar don parking ta bude motar ta sauka, sosai take jin tayi kewar Amminta, ta bar sa da dauko food warmers din a bayan mota ta tafi cikin gida da sauri, tana shiga parlon Ammi ta tafi ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mama Ladi da ta bi ta da kallo tun shigowarta ta bude baki hangangan, Mayraah ta zamo kasa daga jikin Ammi tana murmushi ta kalli Mama Ladi tace "Mama sannu da zuwa, ya hanya" Mama Ladi na gyada kai tace "Ikon Allah, Mera dama za ki yi kumari abubuwa su cicciko maki haka maa sha Allah, ahhh lallai Maheer na kashe kudi ba na wasa ba bawan Allah, waiiii" Mayraah ta dauke kai, Ammi dai kallon Mayraah kawai take don ita kanta tayi mamakin ganin Mayraah a haka, har cikin ranta kuma taji dadi, kana ganinta ka san tana cikin kwanciyar hankali unlike yanda ta rame sosai watannin baya, Ammi tace "Ina yayan?" A hankali Mayraah tace "Yana shigowa" Ammi na kallonta tana murmushi tace "Kyale Mama Ladi she is jealous" Sai ga Maheer ya shigo da abincin, Mama Ladi tace "Ba shakka, shi ta bari da kwaso kulolin ma, ya dai zama mijin ta ce kawai..." Mikewa Mayraah tayi ta shige dakin Ammi tana turo baki ta kulle kofa, Maheer ya ajiye warmers din abincin ya zauna ya gaida Mama Ladi, Mama Ladi na washe baki tace "Ashe ba Mera kadai tayi ƙiba ba, kai ma gashi kayi fes da kai sai san barka" Dariya Maheer yayi yace "Mama kin koma karayen ne?" Nan da nan ɗan fara'an Mama Ladi ya bace tace "Ina ne karaye kuma?" Ammi ta fara dariya tana kallon Mama Ladi, Mama Ladi tace "Dangin uwata ne a karayen ko na ubana da kake tambayata ko na koma saboda neman jifa'i? Haba ai a addinance ma cewa aka yi mutum ya fadi alkhairi ko yayi shiru" Maheer ya sunkuyar da kansa yana dariya, Mama Ladi ta ja wani tsaki ta maida kallonta kan TV, Maheer ya juya ya gaida Ammi, Ammi ta amsa tace "Ya aikin?" Yace "Alhamdulillah" Mikewa Mama Ladi tayi zata fita daga parlon Ammi tace "Ina kuma za ki Mama?" Mama Ladi tace "Ina kuwa zan je banda in dauko plate an kawo abinci" Ammi tace "Toh bari in dauko maki Mama" Mama Ladi tace "Aa bar shi" Tana fadin haka ta fice daga parlon, Maheer na murmushi yace "Na zata fushi tayi zata fita" Ammi tayi dariya tace "Ita Mama Ladin ce zata yi fushi taga an dire cooler din abinci?" Dariya Maheer ma yayi, dai dai nan Mama Ladi ta dawo parlon a gigice ta dafe gwiwowinta biyu tana girgiza kai, da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una" Mikewa Ammi tayi da sauri tace "Lafiya Mama?" Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Wani lafiya? 'ya yan me rasuwa Amina ce na hadu da su a matakalan bene, wallahi Allah ban gane su ba sai da suka matso kusa..." Ko rufe baki Mama Ladi bata yi ba sai ga Eeman ta shigo parlon Ihsaan na biye da ita a baya, sai da kan Ammi ya sara ganin yanda teenagers din suka rame, suka karaso cikin parlon suna tafiya a hankali duk suka zauna nan kasan carpet suna kallon Ammi suka gaisheta, nan da nan hawaye ya cika idon Ammi tayi karfin halin karasawa inda suke zaune tace "Daga ina ku ke Ihsaan?" Ihsaan ta sunkuyar da kanta, sai Eeman ce a hankali tace "Katsina" Mama Ladi ta mike tana kallon yaran da kyau don ta tabbatar kawai sai ta kara fashewa da kuka tace "Amma dai Allah ya tsine ma koma su waye dangin uban nan naku, Allah ya tsine masu tun a gidan duniya, yanzu ina akwatin kayan naku?" Duk suka yi shiru, kasa ci gaba da tsayuwa Ammi tayi ta zauna kan kujeran dake kusa da inda suka zauna, Eeman ta goge hawayen da ya taru idonta a hankali tace "Suna can Katsina" Mama Ladi tace "Basu san kun taho ba kenan?" Eeman ta gyada ma Mama Ladi kai, Ihsaan ta goge hawayen da ke sauka idonta, Mama Ladi ta zauna kan kujera ta rike kai tace "Huhuhu mutuwa me tonan asiri, yanzu a dubi girman Allah a ga yanda yaran nan suka dawo kamar ba farare ba yan gayu, yara sun dawo kamar almajirai ko wata shidda uwarsu bata yi da rasuwa ba, anya wasu za su gama da duniya lafiya kuwa, tirrrrr" Mama Ladi ta fashe da kuka tana girgiza kai, Ammi dai ta kasa cewa komai but deep down controlling kanta kawai take, shi dai Maheer ya kasa cewa komai he was soo heartbroken seeing the twins this way, Mama Ladi tace "Toh zan ga tsinannen da zai kara maida ku katsina, ni dama daga jin sunan garin naji sam bai kwanta min a rai ba, wai Katsina, kai kaji fa wai katsina, to me zuwa katsinan ya tsinano maku banda sharri, daƙuna ne kaca kaca gidan Saminun kaduna, dama can an san shi da rike marayu, tunda ɗa daya Allah ya basa a duniya wato mahaifin Mera, sannan gidan ga gandara gandaran samari 'ya ya da jikokinsa kuma duk 'ya yan yan uwansa ne, suna ganin ku nasan za su kyasa" Da kyar Ammi tayi karfin halin mikewa tana kallonsu Ihsaan tace "Ku taso Eeman" Duk suka tashi suka bi bayan Ammi suka fita daga parlon ta kai su bedroom din Mayraah, wanka tasa su yi sannan ta fita daga dakin, dakin dake kusa da na Mayraah ta shiga ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta fito ta sauka downstairs ta sa Bilkisu ta kai masu abinci da tea dakin, Mita kawai Mama Ladi ke ma Maheer har Ammi ta shigo parlon, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Shi ma Mamudan na da babban kwamasho kuma in bai yi hankali ba sai Allah ya kamasa don zaman mutunci yayi da uwarsu kafin ta rasu bai kamata don babu ranta yayi watsi da lamarin 'ya yanta ba su walakance haka" Mama Ladi na kai wa nan ta fashe da kuka tace "Allah yasani bana son zalunci a rayuwata, sam zalunci bai amsheni ba" Ammi ta zauna cikin karfin hali tace "Amshe wayan yaran suka yi bayan an kai su katsinan wai basu isa rike waya ba, sannan daga karshe ba ma ainahin gidan da shi Mamudan da Usman suka kai su aka bar yaran ba, canza masu wuri aka yi, ta yaya za mu san inda suke da halin da suke ciki, sau biyu Usman na zuwa katsinan gidan yayan mahaifinsu sai ace masa suna Zamfara ai, ta ina zai fara zuwa Zamfara nemansu babu waya? Allah ya sani kullum da yaran nan nake kwana nake tashi a raina, ko shekaranjiya sai da nayi ma Alhaji maganar yaran nan yace min to ya nake son yayi, yayi bakin kokarinsa na bibiyansu amma dangin uban sun ki bude kofar communicating da yaran, a ko da yaushe addu'a nake masu Allah ya dubi maraicin su ya tsare su ya tsare mutuncinsu a duk inda suke" Mama Ladi tace "Kai jama'a, to kuwa in ma suka sake gigin cewa yaran su koma wajensu kawai Usman ya maka su kotu, sannan babban gatansu yanzu shine ace sun auri masu kudi sai su ci gaba da karatunsu a gidajen mazan su, Usman ya auri daya, gidan Alhaji Saminu akwai wani ɗan sa me shegen tsafta, ni dai ina jin aljanun tsafta ne da shi, naji ana ce masa Mendi amma sunansa na gaskiya Aliyu, shima Babban likita ne kamar Mashir, jifa jifa yakan zo gidan, ina yawan jin Hajiya Ramatu na korafin yaki aure duk kanninsa sun yi aure, kuma ko budurwa bai da, to kyau ace na kai dayar yarinya kaduna ya ganta, in Allah ya taimake mu sai mu ga ya kyasa tunda kyawawa ne yaran ga diri ga hanci da manyan idanuwa maa sha Allah, shi Usman ya auri me fara'an shi kuma Mendi ya auri mara fara'an don shi ma ba fara'an ya cika ba ga miskilanci, yana nan wani dogo sambalele kamar Mashir shi ma" Mikewa Ammi tayi duk jikinta a sanyaye ta bude kofar dakinta ta shiga, Kwance ta tadda Mayraah tana danna wayarta, A hankali Ammi tace "Su Eeman ne suka zo Mimi" Mayraah ta tashi zaune da sauri tace "Yanzu wai?" Ammi ta gyada mata kai sannan ta bude press dinta don akwai kayayyakin Mayraah tun tana budurwa a press din nata, Ammi ta dau kala biyu, Mayraah ta sauko daga kan gadon ta bi bayan Ammi suka fita daga dakin, suna fita parlon wayar Mama Ladi ya fara ruri, ta jawo er jakarta ta bude ta ciro wayar ta daga ta kai kunne hade da sallama, kabbara ta saki tace "Alhamdulillah, Allah mun gode maka...." Shi dai Maheer sai kallonta yake har ta gama wayar ta mayar cikin jaka tana washe baki ta mike tace "Hajiya Ramatu ce ta kirani, kaji uwar Mera ta haifo tagwaye duk maza a can kasar waje"
[10/25, 6:54 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah ta bude mota ta sauka bayan Maheer yayi parking, ta juya tana kallonsa tace "Ko dai kawai ka bar shi Dear" Yace "No, let me get it in dawo yanzu, Flight din ai na karfe shidda ne so there is still time" Mayraah tace "Just an hour and a half fa" Yace "Don't worry, am not taking long wife" a hankali tace "Ohk dear, Allah ya tsare" Yace "Ameen my love" Gate ta nufa ta shiga gidan shi kuma yayi reverse, tun da ta bude kofar parlor ta shiga take kallon sa, yana daga kai tayi masa murmushi ta karasa cikin parlon ta zauna tace "Ina yini yaya?" Yace "Lafiya lau, how are you doing?" Tace "Alhamdulillah, ya su Mami?" Yace "They are fine, ina Maheer din?" Tace "Yaje ya dawo yanzu, yaushe ku ka zo yaya?" Yace "Not too long, ke mu ke jira ai" Mama Ladi ce ta sauko parlon daga sama, ta karaso tsakiyar parlon tana washe baki hannunta rike da ledan gyada me gishiri tace "Sannu da zuwa Mendi, yanzu Hajiya Ramatu ke ce min ai tare ku ka zo" ɗaga kai MD yayi yana kallonta, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Mama Ladi ta zauna kujeran dake kallon wanda yake zaune tace "Ashe wai kai zaka raka su kasar wajen" MD yace "Ina wuni Mama" Mama Ladi tace "Lafiya lau Mendi, ya aiki?" Ya ɗan yi murmushi yace "Alhamdulillah" Mama Ladi tace "To madallah" Mayraah ta gaida Mama Ladi, Mama Ladi tace "Lafiya lau, ina mijin naki?" Mama Ladi bata jira cewar Mayraah ba tana kallon sama ta kwalo ma Ihsaan kira, ba a dau lokaci ba sai ga Eemaan ta sauko downstairs ta karaso kusa da Mama Ladi tace "Gani Mama" Mayraah dai kallon Eeman kawai take ganin yanda ainahin haskenta ya dawo, skin dinta sai glowing yake, kwanansu goma kenan da barin katsina amma har sun dawo hayyacin su, Mama Ladi ta daga kai tana kallon Eemaan tace "Kece Ihsaan ko neman magana..." Eeman na murmushi tace "Aa Mama tana can parlon Ammi ne shi sa na zo" Mama Ladi ta dauke kai tana cin gyadar hannunta tace "To ba ke na kira ba, ki tafi kice mata Mama Ladi na kiranta" Eemaan da har sannan fara'a ke kwance fuskarta ta kalli MD dake kallonta ta dan risina tace "Ina yini?" Ya gyada mata kai yace "Lafiya lau" Kallon Mayraah tayi ita ma ta gaishe ta, Mayraah ta amsa mata da murmushi fuskarta, Eemaan ta juya ta koma sama, Mama Ladi na kallon MD tace "Bari yanzu za a zo a kawo maka ruwa Mendi" MD ya daga kai yana kallonta yace "Mama sunana fa Aliyu" Mayraah ta kyalkyale da dariyar da bata yi niyya ba, Mama Ladi tace "Ai nasan sunan ka Aliyu, ba su Hajiya Ramatu naji suna kiran ka Mendi ba, sun ma fi kiran ka Mendin ai akan Aliyu" MD ya jinginar da kansa da kujera after letting out a sigh, bai sake ce mata komai ba, Mama Ladi na mika masa ledar gyadar hannunta tace "Ko zaka ci gyada me gishiri, Halima ce ta bani nima" MD ya girgiza mata kai yace "Alhmdlh" Mayraah dai ta kasa daina dariya, tana son tafiya sama ta gaida Ammi da kakarta da Aunty Halima da ke can bangaren Ammi amma saboda tana son ta ga yanda za a kwashe idan Ihsaan ta sakko ya sa taki tashi daga parlon, Ba a wani dau lokaci ba sai ga Ihsaan ta sauko downstairs ta karaso kusa da Mama Ladi, Kallon Mayraah dake kallonta tayi tace "Ina yini Aunty" Mayraah ta amsa mata tana murmushi, Ihsaan ta juya ta kalli MD that was looking at her a bit confused, a takaice tace masa "Ina yini" Mama Ladi dai sai washe baki take tana kallon MD kasa kasa tace "Naga kamar ka rude ko Mendi, to yan biyu ne ai" MD yayi murmushi yace "Ai nayi tunanin haka..." Mama Ladi ta kalli Ihsaan tana washe baki ba tace "Tafi ki dauko masa lemo da ruwa a kitchen Ihsani, kanin uban Mera ne" Juyawa Ihsaan tayi ta nufi kitchen, MD da ya bi ta da ido sai kuma ya maido da dubansa kan Mama Ladi yace "Aa Mama, na sha ruwa kafin in shigo, dama Mayraah mu ke jira yanzu za mu tafi airport" Ihsaan ta tsaya jin abinda yace amma bata juyo ba, Mayraah dai sai murmushi take tana kallon ikon Allah, Mama Ladi tace "Banda abun ka ko kadan ne ka sha mana Mendi, maza tafi ki dauko ruwan Ihsani" MD ya kalli Ihsaan sai kuma ya kalli Mama Ladi yace "Ai da ta farkon ma kika ce ta kawo min ruwan, naga tafi fara'a" Ihsaan ta juya ta kalli MD dake kallonta, Mama Ladi ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa tace "Toh banda abun ka kai din ma ai ba fara'ar bace da kai Mendi, shi sa nace a kira min ita ta baka

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login