Showing 345001 words to 348000 words out of 456519 words
yunwa kike ji" Tace "Aa ni dai zan yi yanzu, don ina son ka kaini in ga Ammi yau" Ya ɗan buda ido yana kallonta yace "Jiya fa kika ce baza ki je ba, ko kin manta ne" Tace "Aa ni dai kawai in zaka tafi masallaci ka kai ni gidan, yanzu ina son zan je" Yayi shiru, sai kuma yace "Ki bari ranan lahadi...." Ko rufe baki bai yi ba ta marairaice tace "Plss yaya, i am missing Ammi so much, har mafarkinta fa sai da nayi" Yace "Toh ki bari anjima in na dawo masallaci" Ta hade rai tace "Meyasa baza mu fita tare ba sai ka ajiye ni gidan" Yace "Na dai ce ki bari in the evening, dauko min wayata" Ta wani kallesa bata ce komai ba ta bar parlon. Sai wajen karfe shidda saura Maheer ya kai Mayraah gida, har da kukanta da taga la'asar ya wuce bai kai ta ba, wnn ne ma yasa kawai ya kai ta gidan, Bilkisu da Ammi ne kadai a gidan, Omar yaje kai Aunty Mariya da Mama Ladi gidan surkar Dr Khalil za su mata godiya sannan su bata kayan garan da aka debar mata, Sosai Ammi tayi farin cikin ganin Mayraah, Mayraah dai taki barin su hada ido da Ammi sai kallon TV take, Shi kam Maheer danna wayarsa kawai yake tun bayan da ya gaisheta bai sake dagowa ba, as if shi ma dai bai son kallon Ammin tasa, sai suka zama kamar wasu baƙi a parlon, Ammi tayi breaking silence din parlon tace "Amma sai Monday din sama zaka koma aiki ko?" Maheer bai kalleta ba yace "Aa wannan Monday din ne, in sha Allah" Ammi tace "Da wuri haka, na zata sati biyu ka dauka ai" Ya girgiza mata kai yace "Aa, sati daya ne" Mikewa Ammi tayi ta tafi dakinta zata dauko ma Mayraah turaren da Hajiya Amina ta bada a kai mata 3 days ago, Mayraah na ganin Ammi ta shiga daki ta mike ta bi bayanta Maheer ya bi ta da kallo, Ammi ta dauko babban ledan turarrukan tana kallon Mayraah da ta shigo dakin tace "Mimi ga shi Auntynki tace a baki wannan, Mancewa nake ban ba Omar in zai kai maku abinci ya tafi maki da shi ba, in kun koma gida sai ki kirata ki mata godiya" Mayraah ta zauna gefen gadon Ammi tayi shiru, Ammi dai sai kallonta take ganin yanda mood dinta ya canza gaba daya lkci daya, Ammi ta dawo kusa da ita a hankali tace "Lafiya Mimi?" Kamar jira take ta fashe mata da kuka sosai, Ammi ta zauna kusa da ita amma sai ta kasa ci gaba da tambayarta menene don ita inda hankalinta ya tafi daban a lokacin, sosai taji nauyin ci gaba da tambayarta kukan me take don bata san abinda zata bude baki ta ce mata ba, Ammi ta dake, ta jawota jikinta a hankali not knowing what to say to her, dai dai nan Maheer ya shigo dakin da wayar Amminsa da ake kira, ya karasa ya ajiye ma Ammi wayar a kan gadon, Ammi dai bata kallesa ba tana kallon Mayraah tace "Kina waya da Abbanki kuwa?" Mayraah ta girgiza mata kai hawaye na zuba idonta tace "Bani da kati, dama Ammi yaya ne duk inda muka je sai ya dinga ce ma mutane ai ni kanwarsa ce shi bai yi aure ba, shine har da amsan number wata mata lukuta a shopping mall, kullum yayi ta waya da ita da daddare har da ce mata zai aure ta nan da wata daya" Da wani irin mamaki Ammi ta daga kai tana kallon Maheer da ya buda baki yana kallon Mayraah, da kyar Ammi tace "Maheer?? ashe dama kai mutumin banza ne ban sani ba?" Kasa cewa komai Maheer yayi yana kallon Ammin sa, he was so shock, Ammi ta kalli wayarta dake ring ganin Aunty Mariya ke ta kiranta yasa ta dau wayar tace "Ina zuwa yanzu Mimi" Daga haka Ammi ta fita fuskarta a daure, Maheer na kallon Mayraah da kyar yace "Mimi ashe haka kike dama?" Ta wani kauda kai taki kallonsa balle tace komai, ya wani hade rai ce "Ina ce kece kika ce we are still siblings??" Ta wani juyo a fusace tace "To shine nace kaje kana fada ma mutane a titi? Is it not just between us? Duk wanda ya tambayeka kayi aure ba sai kace masa eh ba kawai kayi wucewar ka, har da wani ce mata zaka je gidansu yau bayan magrib, to wllh gwara ka kirata yanzu kace mata ni matarka ce in ba haka ba har Abba sai na gaya ma ba Ammi kadai ba" Maheer was speechless, wato shi yasa ta daga hankali ta dage sai ya kawota gida ashe ita tasan abinda ta shirya, Ammi ce ta dawo dakin tana kallonsa fuska daure ta nuna masa kofa tace "Fita...." kasa ce mata komai yayi ya sunkuyar da kai sannan ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin.
[9/20, 10:21 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer ya koma ya zauna parlon Ammi har sannan bai daina mamakin Mayraah ba, har aka kira Magrib Ammi bata fito dakin nata da Mayraah ba, shi babban fargabansa ma bai san iya abubuwan da take kitsa ma Ammi a dakin ba, jin za a fara sallah ya mike da kyar ya nufi kofa ya fita daga parlon. Ana idar da magrib Aunty Mariya suka shigo gidan da Mama Ladi, Mama Ladi na kallon Maheer dake parlor yana masu sannu da zuwa tace "Ikon Allah, yau kuma ango ne a gidan namu, dazun nan na gama ce ma Ammi ga dai Mera shiru ba ko kiran waya taji halin da muke ciki, kamar ba ita aka dinga kokuwar sa wa a motar Mamuda a kai ta gidanka ba, to har yau bata bi ta kan mu" Ya ɗan yi murmushi ya gaisheta sannan ya gaida Aunty Mariya, Aunty Mariya tace "Lafiya lau Maheer ya gida?" Yace "Lafiya Alhamdulillah" Mama Ladi tace "Mariya kin ga har da wani kumari yayi da haske, abun zar sha'awa, to ina ka baro matar?" Ya kalli sama yace "Tana sama" Mama Ladi tace "Ai ko ran manday muke cewa za mu je da Mariya, don talata za mu tafi kaduna" Maheer yace "Ohk daga kadunan zaki koma karayen kenan" Mama Ladi bata tankasa ba ta amshi ledan abun arzikin da surkar Dr Khalil ta hadota da shi ta wuce sama, Aunty Mariya tayi dariya bayan Mama Ladi ta haura sama tace "Kai meye zaka kawo mata maganar karaye? Karayen da take cewa zata sa a sako mata sauran kayan sakawanta a mota" Maheer yace "Wajenki zata zauna a kadunan?" Mama Ladi tace "Aa ni bata ce min haka ba, ban dai san ko gidan Yahanasu ba" Maheer bai sake cewa komai ba, Aunty Mariya tace "Gida ka baro Mayraan ita kadai?" Ya girgiza kai yace "Aa, tana sama" Aunty Mariya tace "Ohk, da ran lahadi za mu je gidan naku Ammi tace za mu je gidan matar abokin Abba, so in sha Allah Monday muna nan tafe" Maheer yace "Toh Allah ya kai mu" sama ta wuce ta bar sa a parlon, shi dai har sannan bai daina mamakin Mayraah ba he just can't believe she did what she did, amsa gaisuwar Omar da ya shigo parlon yayi sannan ya mike ya shiga dakinsa. Mama Ladi ce ta shigo bangaren Ammi bayan isha, tana kallon Ammi tace "Ita wannan mata da ta bararraje gidan mutane bazata tashi ta samu mijinta a parlo ba su tafi gida ba, gashi har ana neman karfe tara na dare, in dai Mashir ne kinsan bazai bude baki yace ta tashi su tafi ba saboda kara da kawaici" Aunty Mariya dake parlon a zaune ita ma sai da tayi ma Ammi magana amma Ammi tace ai kwana za su yi wannan ne ma yasa bata sake cewa komai ba, Ammi na kallon Mama Ladi tace "Ba yau za su koma ba" Mama Ladi ta kalli Aunty Mariya tace "Kin ji ta ko? Kar fa taje ta kashe ma yarinyar mutane aure mu shiga uku, da Mamuda na nan yaushe za a fara wannan haukan? Kar fa ki dinga fakewa da cewar Mera er ki ce ku dinga cutan bawan Allahn da baya magana, wallahi alhaki bazai bar ku ke da ita ba, gashi tun dazu shi kadai zaune parlor kamar maraya cikin sauro, matarsa ce fa yanzu kuma duu ya fi mu iko da ita, aure ko sati bai yi ba an fara nuna masa yan ubanci, salon ki ja yarinya ta fara renasa ya kasa kwantrol din gidansa" Aunty Mariya dai sai kallon Ammi da ta ki cewa komai take, Mama Ladi tayi kwafa ta fita daga parlon, gun Maheer ta tafi tana kallonsa tace "Amma dai kwana za ku yi ko Mashir, don naga dare yayi har yanzu baku tafi ba" Maheer yace "Aa ita nake jira" Mama Ladi tace "Ahaf, dama ni nasan wannan gurbatattcen shirin na Ammi ne ba na wani ba, sam matar nan bata da ƙan gado, to kuwa wallahi zata kashe ma er nan aure idan aka yi wasa ba, tun wuri ka tashi ka zaga baya ka kira Mamuda ka zayyane masa duk abinda ke faruwa, kace masa daga kun zo ziyara gida taki barinka ka koma da matarka, don ina guje maka yanda uwar ka da makirar yarinyar nan za su hade maka kai a kwanan nan, zugata kawai zata dinga yi wllh, sai ma kaga gaisuwan walakancin da ta min da muka dawo tana zaune kasan kafet wai ina yini Mama, duk uban wahala da sintirin da na dinga yi daga Kaduna zuwa Abuja akan bikinta matar nan bata ce min ya gajiyan biki ba ga tsohuwar banza, ko da yake taga yanxu ta shigo layin manya dole ta billo da sabon fitsara.... Ahaf Mera kuma" Shi dai Maheer kallonta kawai yake bai ce komai ba, Mama Ladi ta juya ta nufi kitchen tana cewa "In kana son tsira da ɗan guntun mutuncin ka kayi abinda kawai nace maka, uwarka dai bata da kai, banda ma abun ka yaushe har ku ka tare da zaka wani kinkimota ku zo gida banda dai yaran yanzu jun zama fitsararru" Daga haka ta shige kitchen. Ammi na parlonta tare da Aunty Mariya, Mayraah kuma na Bedroom a kwance, Ammi bata boye ma Aunty Mariya duk abinda Mayraah ta gaya mata ba, Aunty Mariya dai tayi shiru tana kallonta ta kasa cewa komai, Ammi tace "Ina ga saboda ya sameta a banza bai wahala ba shi yasa har zai fara tsiro da wannan hali da ba tasa ba, duk wannan abubuwan nan da tace yake alamomi ne na cewa bai son auren, tsabar rashin mutunci a gabanta ma yake waya fa, sannan bi yake yana ce ma jama'a ba matarsa bace kanwarsa ce ita, ni dama tun ranan da suka shigo nan da Usman da yake cewa zai saketa tunda bata son auren na sha jinin jikina da shi, alamu sun nuna biyayya kawai yayi ya amshi auren, gani zai dinga yi an makala masa ita ne, don haka bazata taɓa mutunci a idonsa ba, to tun ba aje ko ina ba gwara a san me yiwuwa" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tace "To amma Ammi shi kin basa listening ears kin ji me zai ce?" Ammi tace "Babu abinda zai ce min, Mayraah bazata masa sharri ba kuma ni nasan bazata min karya ba" Aunty Mariya tace "To Allah ya sauwake" Ammi tace "Ameen amma don Allah ko Mama Ladi kar ki fada ma wannan magana, kin dai san halinta" Ko rufe baki Ammi bata yi ba sai ga Mama Ladi ta shigo, tana nuna Ammi da yatsa tace "Ke dai kar ki zama uwar banza uwar hofi Ammi, yanzun nan na samu yaron nan yace min ba da niyyar kwana suka zo ba kika rike masa matarsa wai bazai koma da ita ba, gashi can zaune parlor cikin sauro kamar maraya, me yasa ke duk wani abun ƙaranta daga wajenki yake fitowa? Ji irin sallaman da kika ma kishiyarki me kirki jiya kawai don za su koma Kano tare da mijinta Mamuda...." Mikewa Aunty Mariya tayi ta fita daga parlon, tana sauka downstairs ta tarda Maheer zaune a inda yake har sannan, ta zauna tana kallonsa, tayi kasa da murya saboda Bilkisu dake gyara dinning area, tace "Maheer me ke faruwa?" Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta, ta mike tace "Mu je daki mu yi magana" Babu musu ya mike ya bi bayanta, Maheer bai boye ma Aunty Mariya duk yanda suka yi da Mayraah ba tun daga sanda aka kawota gidansa, Aunty Mariya tace "Ya kamata kasan yarinta ne da wauta kawai ke damun Mayraah, kuma tun farko bai kamata ace ka biyeta ba Maheer, sannan babban mistake dinka wayar da ka zauna kayi a gabanta, that is not proper" Maheer dai bai sake cewa komai ba, Aunty Mariya ta mike tace "Bari in samu Ammi" Daga haka ta nufi kofa ta fita. Ko da Aunty Mariya ta samu Ammi tayi mata bayanin da Maheer yayi mata, Ammi da kusan rabin attention dinta na kan abinda take yi tace "Kin ga Mariya ni babu ruwana da duk wannan bayanin naki, banda yana ganin kamar sadaka aka basa ita har zai zauna yana waya a gabanta? Ke fa mace ce in ke aka ma haka ya za ki ji? Bana son goyan bayan rashin gaskiya, dama ni ban ma so ta tare yanzu ba, don haka duk sanda yasan mutuncinta sai ya dauketa su tafi gida amma ba yanzu ba, ko Mahmud ne ya zo zai daga min hankali wllhi sae in fitar da ita daga gidan in kai ta ajiya" Duk da takaicin da ya ishi Aunty Mariya she couldn't help it but laugh, Ammi ta mike ta bar ta wajen, Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya, Mama Ladi dai dakinta ta wuce da shayinta da bread bayan da ta gano kess din bai shafeta ba take tsoma kanta ciki. Karfe goma saura Maheer ya shigo part din Ammi zai mata sallama ya wuce gida, bai ganta a parlor ba hakan yasa ya karasa Bedroom dinta, yana bude kofa yaga Mayraah zaune gaban mirror dinta tana daure gashinta bayan tayi wanka tayi shirin bacci, tana ganinsa ta dauke kai tana ci gaba da abinda take, ya karasa cikin dakin ya kulle kofar, ta dakatar da abinda take tana kallonsa ta madubi ganin yana sa ma kofar key, dai dai nan Ammi ta fito daga bandaki, jingina yayi da kofa yana kallonta don bai san tana ciki ba, tuni Ammi ta murtuke fuska, yayi kasa da kai yace "Ammi sai da safe" a takaice Ammi tace "Allah ya tashemu lafiya" Ta gefen ido ya kalli Mayraah sannan ya juya kamar munafuki ya bude kofar da ya sa ma key ya fita. Washegari throughout haka Mayraah ta yini a gidan daga dakin Ammi zuwa parlonta ko downstairs bata sauka, abinci ma sai dai a kawo mata bangaren Ammi, Ammi na dakin da su Mama Ladi suke bayan magrib tana harhada souvenirs da za su tafi da shi kaduna don Aunty Mariya tace gobe zata tafi tunda Mayraan ma da za su je wajenta tana gida yanzu, dakinta kuma tun kan ta tare sun riga sun je sun gani, Mama Ladi ta kalli Aunty Mariya tace "To wai Mariya yaushe za mu je kwaso kaya ne? Gashi har za mu tafi kaduna gobe" Ammi da Aunty Mariya duk suka juya suna kallonta, can Aunty Mariya tace "Wani kayan kuma Mama?" Mama Ladi ta gyara zama tace "Na Mera mana, kayan dakinta, ai kamata yayi mu je mu kwaso kayan kar suje su lalace a banza gashi masu tsada dangin ubanta suka mata, kinga ga daki kaca kaca a gidan nan duk sai a zuba su a jera tunda kashe auren ake son yi, ko ke ya kika ga? Shawara ce dama na kawo ba wani abu ba" Ammi ta dauke kai ta ci gaba da harhada abinda take, Ita dai Aunty Mariya bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Ko wani taɓara dai daga pamilyn mu yake samo asali, kafin ya isa pamilyn wasu, tirrrrr" mikewa tayi ta shige bandaki, Aunty Mariya tayi kasa da murya tana kallon Ammi tace "Don Allah Ammi ki bari ya zo su tafi da ita, ran monday fa zai koma aiki" Ammi tace "Mariya ki fita idona in rufe, yaje can ya auri warce zai aura nan da wata dayan da yace, kinga can ai zai fi sanin darajan auren tunda ba sadaka za a basa ba, Mayraah kuwa kinga ai a kyauta ya sameta" Aunty Mariya tace "Amma Ammi kin fi kowa sanin halin Maheer fa, me yasa baza ki masa uzuri ki sauraresa ba...." Ammi ta katse ta tace "Na sani ko canzawa yayi? Ke dai kiyi ta kanki ki rabu da ni da zancen nan" Aunty Mariya ta ja bakinta tayi shiru bata sake cewa komai ba... Mayraah ta shigo dakin Ammi wajen karfe takwas da rabi bayan ta tafi can dakinta ta duba press ta dauko kayan baccinta, yawanci duk kayanta na gidan ba a kai mata gidan Maheer ba, ta ajiye kayan baccin gefen gado sannan ta cire hijab din jikinta ta linke ta ajiye ta karasa gaban madubin Ammi tana daure da towel don ta riga tayi wanka, Humran Ammi ta bude tana shafawa taji an bude kofar dakin, duk tunaninta Ammi ce kamar ance ta daga kai ta gansa ta madubi a bakin kofa, da sauri ta juya tana kallonsa har ya shigo ciki ya kulle kofar, ta kulle Humran da ta bude ta nufi gadon dakin zata dauko Hijab dinta, zaro ido tayi ganin ya rigata isa wajen fizge hijab din, ta wani hade rai ta koma baya tace "Yaya baka yi sallama ba fa, kuma gashi ban saka...." Bata rufe baki ba taga ya fizgota nan da nan ta rikice tana rike da towel dinta gam tace "Wallahi zan