Showing 315001 words to 318000 words out of 456519 words
mu yi ma Mama Ladi ba zata" Mama Ladi tace "Ni ai kin rikita ni, iyayenta da suka ya da ita cikin kwata a kwali ko kuma wasu iyayen kike nufi?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Bari in maki bayani yanda za ki fahimta Mama" Nan Ammi ta fara dauko ma Mama Ladi bayani tiryan tiryan sai dai yawanci duk kwaskwarima tayi ma labarin don bata gaya mata Ceo ba musulma bace, sannan bata gaya mata Ceo bace ta yada Mayraah ta dai ce wata makiyiyarsu ce a gidan tayi hakan saboda tana jin haushin Aaria, sannan still ta boye yanda Abdallah ya auri Aaria cikin sirri don iyayensa where against the marriage, bata kuma gaya mata dangantakar Mayraah da Musharraf ba don kar ma labarin yayi tsayi, haka dai tayi fabricating labarin yanda Mama Ladi bazata samu abun fade ba na har abada, Mama Ladi da ta mike tsaye ta dinga salati tana tsine ma matar da ta yasar da Mayraah, Aunty Mariya dai aikinta kawai take ta yi, Ammi tace "Kakanta sananne ne a kasar nan ma" Mama Ladi ta zaro ido tace "Waye shi?" Nan Ammi ta gaya mata sunansa, Mama Ladi ta saki sabon salati tace "Yo ai na sha zuwa kofar gidansa a Adamawa in amso abincin sadaka in kai gida wajen Hajja, don wallahi wani lokacin sai naje na bi layin karban sadaka muke samun abincin da za mu ci ku duk baku wani girma ba, kinsan babanku sai yayi tafiyarsa ya kwashe wata da watanni bamu gansa ba, haka za muyi ta wahala, sannan shi kakan nata wajen ubansa ya gaji uban dukiyar nan tasa har yayi Gwamna a Adamawa, Innalillahi wa inna ilaihi raji'una yanzu daga wannan tsatsson Mayraah ta fito?? Mahaukacin kudi fa gare kakanta ban dai san uban nata ba, matar kakar tana nan ana ce mata Hajiya Ramatu mata me kirki da faram faram da jama'a, duk sai ta tabbatar mun samu abincin sadaka a wancan lokacin in mun bi layi, kuma ai ɗanta daya tak a duniya bata sake haihuwa ba bayan shi, to ban dai san ko Alhaji Saminun ya kara wani auren ba ko uba Meran ɗan kishiyarta ne" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Wannan ɗan nasa guda dai shi ne mahaifin Mayraah" Mama Ladi ta koma ta zauna tana gwale ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ita Meran? Yau mun shiga uku mun lalace Allah ya so bamu taɓa cutarta ba" Ammi bata sake ce mata komai ba ta ci gaba da aikinta ta bar ta tana ta salallami. Karfe goma Mayraah ta fito daga dakinta, tun da gari ya waye bayan ta gaida su Ammi ta koma daki bata sake fitowa ba, Breakfast ma Bilkisu ce ta kai mata, downstairs ta sauko tana tafiya a hankali, tana hango Mama Ladi zaune bakin kofar shiga kitchen duk ta cika muryarta a parlorn, ta juya da sauri tun kan ta ganta ta koma sama tana zaro ido, sai kuma ta nufi bangaren Ammi, ta bude kofar gently tana leka cikin Parlon, Maheer ne zaune da pepper soup a gabansa da bai fara ci ba, suna hada ido ta juya ta bar wajen ta koma jikin bango ta tsaya, shi dai ya ci gaba da danna wayarsa, har ta fara tafiya sai kuma ta tsaya, ta juyo a hankali ta koma bakin kofar parlon tana makale jikin kofa without looking at him tace "Yaya ina kwana" Shi ma bai kalleta ba yace "Lafiya lau, sai yanzu kika tashi kenan" Sunkuyar da kanta tayi ta karasa ta zauna kasan carpet ɗan nesa da shi tace "Aa" Bai sake cewa komai ba, ita ma tayi shiru, bayan wani lokaci tace "Baka je aiki ba?" Yace "Sai da yamma" Tace "Ohk" Mikewa tayi tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta fita sannan ta kullo kofar. Karfe sha daya da rabi su Alhaji Saminu suka iso gidan Abba, kuma kusan tare ma suka iso gidan da Ceo da Aaria, Mayraah dai na kwance dakinta bata ma san duk sun iso ba, gaba daya ta rasa me ke mata dadi ga shi sai faduwa gabanta ke yi wanda ta kasa gane dalilin hakan, Bude kofar dakinta aka yi ta mike zaune da sauri tana kallon kofar, Usman ne ya shigo dakin ta dinga kallonsa har ya karaso yana kallonta yace "Me yasa kika makale a daki tun safe, ko saboda Mama Ladi?" Tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta tace "Aa, bacci nayi na tashi" Yace "Hope you've taken ur bath?" Ta gyada masa kai yace "Our visitors are around" Sosai gabanta yayi mugun faduwa ta daga kai da sauri tana kallonsa, ya zauna side din gadon calmly yace "You need not to be Tensed Mimi, Musharraf na sonki, kema kina sonsa, beside kun yi ma juna alkawarin aure, so stick to that promise, kar ki ji komai a ranki kin ji Lil sis, be a good gal ki tashi ki shirya ki fito yanzu" Lokaci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, yace "Yeah dress up ki sakko downstairs, everyone is there" Ita dai bata ce masa komai ba, ya mike ya fita daga dakin, da kyar Mayraah ta iya sauka daga kan gadonta ta shirya ta dau veil dinta ta yafa sannan ta fito daga dakin walking slowly, a corridor suka hadu da Maheer da ya hauro sama a lokacin, yana kallonta yace "What happened Mimi? Ba ki zo ki gaishe su ba" Ta sauke idonta tace "Yanzu na gama shiryawa" Yace "Ohk, mu je" tana tafiya a hankali ta wuce sa sannan ya bi bayanta suka sauka downstairs, kanta a kasa ta isa har cikin parlon ta zauna kasan lallausan carpet dake shimfide a kasa ta gaishe da duk occupant din dake parlon, suna hada ido da Mom dinta bata san sanda ta mike ta nufeta ta zauna kasa kusa da ita tana kallonta tayi murmushi a hankali ta kara gaisheta, Ita dai Ammi na zaune kusa da Aunty Mariya, Mama Ladi sai washe baki take ganin Alhaji Saminu da ta saba gani a hoto kawai, banda sai da Ammi tayi mugun kwabarta da yanzu ta cika parlon da zance, yanzu kam ba dama sai murmushi take yi kamar sabuwar amarya, Abba na zaune shi ma tare da ɗan uwansa na lagos wanda shi ya bar ma gidansa na kano dake kurna suke zaune da iyalansa, Alhaji Saminu da brother dinsa wanda shi ne yayi ja gaba wajen amso kudin auren Musharraf wajen Abba, sai sinne kai yake ya kasa hada ido da Abba a parlon tun bayan dai da aka gaggaisa, Abdallah ma na zaune parlon idonsa a kan Mayraah, Hajiya Ramatu da Mamin Musharraf ma duk suna zaune waje daya, Drinks da fruits iri iri ne ajiye tsakiyar parlon sai small chops, a hankali Mayraah ke bin parlon da kallo taga babu Musharraf balle yayansa MD, ta kalli Usman da yayi mata alamar she should be calm don kallonta kawai zaka yi ka gane bata cikin nutsuwa, ta sauke idonta kasa sai kuma ta kalli Maheer, murmushi me kwantar da hankali yayi mata, yayi nodding mata kansa as if giving her assurance, hakan ne ya sa ta ɗan samu nutsuwa a parlon, Alhaji Saminu na kallon Abba yace "To Alhaji Mahmud ni kam ina da flight to catch to Germany zuwa karfe biyu, don haka ku muke saurare mu ji hukuncin da ku ka yanke akan batun auren er ku da ɗan mu" Yana murmushi ya kare maganar, Ceo dake kallon Alhaji Saminu, calmly tace "Ohk i think in za a bani dama i have something to say Alhaji" Abba na kallonta ya gyada kai yace "Yes go on Madam... duk muna sauraronki" Ceo tace "As of 2 days ago na tuntubi Mary ann akan maganar auren nasu da shi yaron, i want to know ko da akwai wani abu dake zuciyarta daban nace ta gaya min tsakani da Allah, sai ta kawo min maganar cewar shi yaron yayi blocking dinta ma a waya, so a ranan yayansa ya zo gidana, sai tayi amfani da wayar yayan nasa ta kirasa...." Ceo tayi shiru tana kallon Mayraah dake kasa kusa da uwarta, tace "Mary Ann say it to everyone now, ya ku ka yi da shi a waya?" Mayraah ta daga kai tana kallonta, nan da nan hawaye ya cika idonta, Ceo tace "Yes say what he told you" Ta sunkuyar da kai tace "Ce min yayi shi ya hakura kawai" Duk kowa na parlon kallonta yake, Ceo ta kalli Alhaji Saminu tace "Babu ta yanda zai ce ya hakura bai yi shawara da ku ba Alhaji, definitely duk kun san da wannan batun, sannan kudin aure ku ke shirin kai masa wani wajen kamar yanda ya gaya mata, let be sincere plss sir is it necessary kuma ku zo jin abinda iyayenta za su ce bayan ku can kun riga kun gama yanke hukuncinku gashi har yaron ya gaya mata, the shocking part of all this is that ya ma riga yayi blocking dinta a waya wanda hakan ke nuni da he have nothing to do with her again, a kaddara ma duk bai sanar maku ba, a wannan era din kun ga ana ma yara dole?" Ceo ta kalli Mayraah tace "Bayan da kika ce min yace maki shi ya hakura, wani hukuncin kema kika ce min kin yanke ta bangarenki?" Mayraah tayi shiru, Ceo tace "Answer me Mary Ann" a hankali tace "Cewa nayi nima na hakura" Ceo ta kalli su Alhaji Saminu tace "So baza mu yi forcing dinsu su yi aure su zauna da juna ba saboda zumunci or anything of such, shi yasa wancan ranan nace kilan an samu changes a zuciyoyinsu baza mu yanke masu hukunci nan take ba, and truly i am right" Kallon Ceo kawai Alhaji Saminu da su Abba suke, ita dai Mamin Musharraf direction daban take kallo a Parlon, alamu sun nuna Alhaji Saminu is totally speechless, quite alright Musharraf ya fada masu hakan amma shi yana da dalilinsa na furucinsa kuma ta wani bangaren da gaskiyarsa baya son a sake breaking heart dinsa ne don gani yake kamar baza a bashi ita ba, su kansu sun yi wannan tunanin duba da yanda aka ki bari a daura auren a lokacin, amma basu yi tunanin zai yi saurin gaya ma yarinyar wannan maganar ba don jira suke su fara jin decision din su Abba tukunna, zai yi magana a parlon Abba ya rigasa bude baki yace "Toh shikenan, Allah Ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi, it's good he spoke out, amma kafin a tashi a nan a matsayina na ubanta, zan daura mata aure da nawa zabin da nasan will be best for her, don tun farko niyyata idan kun zo yau baza mu tashi ba sai an daure auren kamar yanda ku ka so wancan ranan, so now in the absence of Musharraf ni zan aura mata nawa zabin wanda nasan zai zama alkhairi gareta in sha Allah, kai Alhaji Saminu zaka zama waliyyinsa, ni kuma waliyyinta, ga kuma shedu" Kowa na parlon kallon Abba yake with shock, barin Ceo da ta buda baki cause she never saw it coming, Mayraah dai tun da ta daura kanta saman kafar uwarta bata dago ba, kokari kawai take tayi assimilating maganganun Abba amma ta kasa, da gaske bata fahimci abinda yake cewa ba har cikin ranta, Ammi dai gabanta sai faduwa yake tana kallon Abba, Alhaji Saminu da ya hadiye maganarsa da yake kokarin yi na kare Musharraf kafin Abba ya rigasa buda baki, saboda kara da mutuntawa kawai yayi murmushi yana gyada kai yace "To ba damuwa Alhaji, hakan ma dai dai ne, sai a yanke mana sadakin da ɗan namu zai gabatar, in sha Allah sai in bayar...."
[9/9, 5:12 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Abba ya kalli Ammi da ta kasa daina kallonsa, sauke idonta tayi a hankali ta mike tsaye sai kuma ta kalli su Hajiya Ramatu da Ceo tana murmushin karfin hali don har ta fara jin alamar jininta ya hau tace "Mu shiga daga ciki" Aaria ta mike ta dago Mayraah da har sannan ko motsin kirki bata yi tun da taji furucin Abba, duk suka bar parlon gaba daya zuwa sama, Abba dai ya bi Mayraah da kallo har suka haura sama... Mayraah na jikin Mahaifiyarta a parlon Ammi tana sauke numfashi a hankali, sauran baƙin kuma suna parlon dake sama gaba dayansu, Aaria ta dago kan Mayraah tana kallonta ganin hawaye idonta ga jikinta har ya fara zafi, a hankali Aaria tace "Kin san dai Abbanki bazai cutar da ke ba ko Baby?" Mayraah ta gyada mata kai da kyar wasu hawayen na zuba idonta, ga wani mugun faduwa da gabanta yake, rabon da ta shiga irin wannan yanayin da take ciki yanzu tun bayan fasa aurenta da Musharraf bayan ta gano ba su Ammi bane asalin iyayenta, Aaria ta kara rungumeta tana patting bayanta a hankali cikin rarrashi, Mayraah ta lumshe ido still breathing slowly, suna nan a haka da uwarta har bayan minti talatin Ammi ta shigo parlon, Aaria ta daga kai tana kallonta, Mayraah dai taki bude ido gabanta na wani irin bugawa duk da bata san waye ya shigo parlon ba, Ammi ta sauke idonta ta karasa cikin parlon ta zauna tana kallonsu cike da karfin hali tace "Maryam, ana magana da ke a parlon Abbansu" Aaria dake kallonta tace "Ohk" Dago kan Mayraah da ta bude ido tayi, sannan ta mike Ammi na kallonta ta bata direction din inda zata bi taje parlon Abba, Aaria tace "Ohk" Daga haka ta nufi kofa ta fita daga parlon tana waigo Mayraah, bayan Aaria ta fita Ammi ta kalli Mayraah da ta sunkuyar da kanta, mikewa tayi ta koma kusa da ita ta zauna ta jawota bossom dinta tana shafa gashinta tace "ki shiga dakina kiyi alwala kiyi sallah, bari in gama serving baƙi abinci, they will be leaving soon" Mayraah ta gyada mata kai kawai ta mike ta shiga dakinta, Ammi ta bi ta da kallo a sanyaye sannan ta mike ta fita daga parlon, she is just trying to be okay too saboda bakin dake gidan, Tun da Mayraah ta idar da sallah take zaune kan darduma for almost 30 minutes now, har a lokacin kuma gabanta yaki daina faduwa kuma gashi babu wanda taji yace mata komai a gidan, a ranta kawai sai tayi assuming kilan Abba ya canza shawara ne daga karshe yace a bar auren tukunna, wanda tunanin hakan ya sa taji ta dan samu relieve a zuciyarta, probably ceo ta kara convincing Abba a bar batun auren nata tukun, tana ta zaune a dakin Ammu taji an bude kofa ta daga kai da sauri, Aunty Mariya ce ta shigo da abinci ta ajiye mata, Mayraah dai sai kallonta take tana jiran taji ko zata ce mata wani abu amma Aunty Mariya bata ce komai ba da ya wuce "Ga abinci Mayraah" Daga haka ta fita daga dakin, Kasa cin abincin Mayraah tayi duk da ko yunwan ma bata ji, wasu hawayen suka cika idonta taji gaba daya ta rude ta rasa wani tunanin zata yi, kallon wayar Ammi dake gefen gado tayi ta dau wayar tayi dialing number Maheer, yana fara ring with some seconds ya daga, a hankali tace "Yaya" shiru taji hakan yasa tace "Hello Yaya" Calmly yace "Mimi" ta fashe masa da kuka tace "Yaya nobody is saying anything to me, why is everyone not saying anything, don Allah kai kace min wani abu mana" Maheer yace "Me zan ce maki Mimi?" Tace "Abba's Decision" Shiru Maheer yayi, tana kuka a hankali tace "Yaya kayi shiru" A hankali yace "kiyi hakuri Mimi, i pray it's the best for you both in sha Allah" Mayraah ta zaro ido tsabar bugun da zuciyarta ke yi sai da taji kamar zai fito daga kirjinta, ta fashe masa da matsanancin kuka tace "Na shiga uku, Yaya don girman Allah ka gaya min waye Abba ya aura min" a hankali Maheer yace "Ammi zata gaya maki, yanxu dai za mu sallami baƙi za su tafi, stay calm, kiyi ta addu'a a zuciyarki it will help" Daga haka ya katse wayar, Maheer ya dinga kallon screen dinsa kafin ya ajiye wayar a gefen kujeran da yake zaune a dakinsa, jinginar da kansa yayi jikin kujeran zuciyarsa na bugawa yana kallon Ac din dakin baya ko kiftawa, Mayraah ta hade kanta da gadon Ammi ta dinga rusa kuka kamar an aikota, even Ya Maheer ma baya son ya gaya mata mijin da aka aura mata, kasa daurewa tayi ta mike ko dankwalinta da ya fadi kasa bata bi ta kai ba ta fita daga bangaren Ammi gaba daya, parlon Abba ta nufa inda taji Ammi tace Mom dinta taje ana nemanta, tana isa parlon ta bude kofar ta shiga, Aaria na zaune da Abdallah dake mata magana a parlon, duk suka daga kai suna kallonta, Abdallah ya mata alamar ta zo, duk da wajen uwarta tayi niyyar nufa kawai dai ta nufesa hawaye na sauka idonta, zaunar da ita yayi kusa da shi ya rungumeta yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "It's the best for you in sha Allah daughter..." Ta fashe da wani sabon kukan sai ta kasa tambayarsa waye mijin, haka ya dinga lallashinta ita dai Aaria kallonta kawai take bata ko kiftawa nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta. Karfe daya da kusan rabi Abba ya raka Alhaji Saminu bakin mota inda Driver ke jiransa zai kai sa airport immediately, da fara'a Alhaji Saminu ya dinga yi ma Abba godiya sosai yace "Mun gode kwarai da gaske Alhaji, mun gode da karamci, Allah ubangiji ya bar zumuncin mu, nayi farin ciki kwarai da gaske da wannan lamari na yau, Allah ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyaba, mun gode Alhaji, Allah ya kara girma...." Abba na murmushi yace "Ameen ya Allah Honorable, zuwa nan da kwana biyu in sha Allah sai a kai maku ita kadunan tunda tarewan mun saka sai nan da sati biyu in