Showing 387001 words to 390000 words out of 456519 words
jikinsa, ta gama rufe akwatinta ta dau mayafinta da handbag without looking at him zata fita dakin ya Jawota jikinsa a hankali yace "Common Mimi, in dai conversation din da nayi a waya kika ji bai kamata kiyi judging dina ba if you listen to the conversation well" Ta fashe da kuka tace "Conversation da za a kebe a gefe ayi ai ya zama na munafurci, why didn't u pick her call in my presence idan baka son inyi judging dinka?" Sosai jikinsa yayi sanyi ganin hawayen dake zuba idonta, ya rungumeta ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri wife, i accept nayi kuskure, kuma hakan bazai sake faruwa ba in sha Allah, i promise you yau shine last day da zan sake magana da ita ta waya in sha Allah" Lallashinta ya dinga yi hawaye na zuba idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, har cikin ranta bata son komai ya sake hada shi da Haseenah, amma taga kamar hakan ba me yiwuwa bane dole yan biyunsu za su hada su in ma komai bai hadasu ba, a haka Maheer ya lallasheta har ta hakura ta daina kukan bayan sun bar gidan yana driving ya kamo hannunta a hankali yace "Na tura maki kati a wayarki, if there is anything ki kirani" A hankali tace "Nagode" Suna isa gida suka tadda Hajiya Amina da kyawawan twins dinta mata a parlon Ammi, Maheer ya gaisheta ta amsa da fara'a, Mayraah ma ta gaisheta, Maheer ya amsa gaisuwar yan biyun, Hajiya Amina ta kalli Ammi tace "Toh Hajiya tunda sun karaso bari mu tafi kar muyi missing Flight din" Ammi tace "Toh Allah Ubangiji ya tsare, Allah ya kai ku lafiya" Dubu ashirin da turamen atamfa biyu Ammi ta ba Ihsaan da Eeman, Hajiya Amina tayi mata godiya sosai, har downstairs Ammi ta rakosu, Hajiya Amina na rungume da Aymaan, Aryaan kuma na hannun Eeman, tuni dama Bilkisu ta kai akwatunan kayan jariran Booth din motar Usman don shi zai kai su Airport din, Maheer ya fiddo box din Mayraah dake booth dinsa ya sa a na Usman, Mayraah ta shiga front seat ta zauna, Hajiya Amina da yan biyunta suka zauna a baya, Abba dai na bangarensa bai fito ba, Ammi ta kalli Bilkisu tace "Ina pampers da nace ki dauko dazu?" Da sauri Bilkisu ta juya ta koma cikin gidan don dauko pack din Pampers din, Maheer sai kallon Mayraah yake ganin she is moody, kana ganinta kasan tana da damuwa, ya ciro wayarsa ya tura mata text kamar haka "Will miss you soo much my one and only wife, Yesternight was sweet...." Mayraah ta kalli wayarta jin message ya shigo tana karanta abinda ya turo mata ta juya ta kallesa, kashe mata ido yayi, bata san sanda tayi murmushi ba ta dauke kanta kawai ta kife wayar a cinyarta, sosai yaji dadin ganin murmushinta me kyau, Bilkisu na kawo pampers din, Usman na kallon Eeman ta madubi yace "My phone?" Ta ɗan buda manyan idanuwanta tace "I left it upstairs together with mine...." Shi dai Usman kallonta kawai yake ta madubi, Mika ma Ihsaan Aryaan tayi sannan ta sauka a motar ta koma cikin gidan da sauri, Hajiya Amina tace "Da baka tuna ba sai mun je Airport ka tambayeta tayi ta zare maka idanuwa tana maka turanci..." Murmushi kawai Usman yayi, ita dai Ammi na tsaye gefe tana kallon different direction, ba a dau lokaci ba sai ga Eeman da wayarta da na Usman ta bude back seat ta shiga, hararanta yake ta madubi, ita dai tayi murmushi ta amshi Aryaan a hannun twin sis dinta, sai da suka bar compound din sannan Ammi ta juya ita da Bilkisu suka koma ciki, Maheer dama daga nan yayi ma Ammi sallama yace zai tafi Hospital. Karfe sha daya da rabi su Hajiya Amina suka sauka Kano, Driver din gidanta dama na airport yana jiransu, ya daukesu gaba daya sai gidansu Haseenah, tunda suka baro Abuja ko tari yaran basu yi ba har suka iso kano, Sosai Mahaifiyar Haseenah da kawarta suka yi welcoming dinsu bayan sun iso gidan da twins din, Mayraah dai na zaune parlon babu yabo babu fallasa, ko hada ido da Haseenah taki yarda tayi sai danna wayarta kawai take, Haseenah kuwa sai satan kallonta take ta kasa daina satan kallonta, Hajiya Amina na kallon mahaifiyar Haseenah daga karshe tace "In dai wani abu ya taso na bukatar yaran za a iya kiran mahaifiyar Maheer din, ko kuma ni a kirani tunda mun ma fi kusa, zan baki lambata yanzu duk me zai taso kawai ayi min waya in sha Allahu i will deliver tunda ina kanon" Mom din Haseenah tace "Toh in sha Allahu Hajiya, Allah Ubangiji ya saka da alkhairi, Allah ya bar zumunci, mun gode kwarai da gaske" Hajiya Amina tace "Ameen, ragon suna kuma in sha Allahu zuwa anjima za a aiko kamar yanda Abbansu yace, nasan dai an sanar daku sunan yaran" Mom din Haseenah tace "Kwarai kam, ance an samu Alhaji Mamudan da Usman, Allah dai ya masu albarka, Allah ya raya mana su cikin aminci" Hajiya Amina tace "Ameen Ya Allah" Basu wani dade ba a gidan kasancewar driver na waje yana jiran su, Hajiya Amina ta yi ma su Mom din Haseenah da ita kanta Haseenar Sallama sannan suka bar gidan tare da yan biyunta da Mayraah, Hajiya Amina na kallon Mayraah tace "Gobe da safe sai driver ya kai ki har kadunan Mayraah" Murmushi kawai Mayraah tayi, Eeman tace "Momy pls nima zan je kadunan wajen Aunty Khadijah sai in mata kwana daya, dama Ya Usman yace min zai je kaduna gobe daga nan zai zo kano sai kawai mu dawo da shi"
[10/9, 5:17 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah ta dau handbag dinta tana kallon Ihsaan tace "Ke me yasa baza ki bi mu kadunan ba?" Ihsaan dake danna wayarta ta ɗan yi murmushi tace "Kawai haka nan Aunty" Eeman ta ajiye turaren da take fesawa gaban mirror tace "Tana da phobia din shiga mutane" Hajiya Amina ta bude kofar dakin tana kallonsu tace "Baku gama bane har yanzu ga driver can na ta jira?" Mayraah ta nufi kofar tace "Mun gama" Eeman ta dau handbag dinta tana kallon twin sis dinta tace "Baza ki raka mu downstairs ba" Ihsaan ta ajiye wayarta ta sauka daga kan gadon suka fita daga dakin gaba daya.... Sai kusan la'asar Mayraah suka iso garin Kaduna, Mayraah ta kalli Eeman da ta kwantar da kanta jikin kujeran motar tana bacci ga wayarta dake gefenta yana vibrate, Mayraah ta dinga kallon number da tayi saving da Bro Usman, can ta taɓa ta a hankali tace "Eeman" Bude ido tayi, Mayraah ta dau wayar ta mika mata tace "Ana kiranki" Eeman ta amshi wayar tana kallon screen din sai kuma ta koma ta kwanta sannan tayi picking call din, Mayraah dai ta dauke kanta, har ta gama wayar ta ajiye Mayraah bata ji me suke cewa ba, Drivern ya fara dropping Eeman a gidan aunt dinta, Eeman ta sauka motar bayan driver ya dauko mata karamin box dinta a booth din motar, tana murmushi ta daga ma Mayraah hannu tace "Sai anjima Aunty Mimi" Mayraah ma murmushin tayi mata ta daga mata hannu, a haka driver ya ja motar suka bar unguwan. Sosai Hajiya Ramatu da su Aunty Halima suka yi farin ciki da ganin Mayraah, bayan Aunty Halima ta fita Hajiya Ramatu na kallon Mayraah tace "Sallama kika zo yi ma su Maryam hala? Ai sun tafi tun da safe, basu ce maki flight din na safe bane?" Mayraah ta daga kai tana kallonta, can tace "Aa ni daga kano nake" Hajiya Ramatu tace "Ayyo, ai na zata kin san da tafiyar tasu ne kika zo kuyi sallama da su, dazu da safe jirginsu ya tashi zuwa US" A hankali Mayraah tace "Ban sani ba" har cikin ranta taji babu dadi don saboda taga Mahaifiyarta yasa tace zata zo kaduna, Hajiya Ramatu tace "Toh kece baki son kiran mutane Mayraah" Mayraah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Hajiya Ramatu tace "Ina jin yau kwana uku kenan da na kira Amminki nayi mata albarka, Hajiya Ladi tace mana an samu karuwan yan biyu" Bude kofar aka yi Aunty Halima ta shigo tana kallon Hajiya Ramatu tace "Umma bakuwarki zata tafi wai" Hajiya Ramatu tace "Toh gani nan zuwa" Aunty Halima ta juya ta fita, Hajiya Ramatu na kallon Mayraah tace "Ki kai akwatin naki daki" Mayraah ta daga kai tana kallonta tace "Umma yaushe za su dawo?" Hajiya Ramatu tayi murmushi tace "Ai can Baban naki ke aiki Mayraah, sai mu yi wata hudu ma bai zo mana nan ba, kuma kinga tun bayan bikinki tafiya yake yana dawowa, sai yanzu ne zai koma da Maryam din can gaba daya" Sosai jikin Mayraah yayi sanyi ta kasa cewa komai, Hajiya Ramatu tace "Kin yi sallah kuwa?" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Ban yi ba" Hajiya Ramatu tace "Toh ki shiga ciki kiyi, za a kawo maki abinci yanzu" Mikewa Mayraah tayi ta dau akwatinta ta shiga dakin kakarta da shi, Mayraah na idar da sallah ta dau handbag dinta jin wayarta na vibrate, tana ciro wayar taga miss calls din Maheer biyu, kiransa ta shiga yi, yana fara ring ya katse ya kirata, ta daga ta kai kunne yace "Baby Gal" A hankali tace "Ina yini yaya" Yace "Waye yaya? ai na bar ma Usman wannan sunan tun tuni" Ita dai bata ce komai ba sai ɗan murmushi da tayi, yace "Ya hanya Dear?" Tace "Alhmdlh" Yace "Ya su grandma da mutanen gidan?" Tace "Duk suna lafiya" Yayi kasa da murya yace "I miss you so much Mimi" Ta kwantar da kanta jikin gado a hankali tace "Uhm" Yace "Uhm ko?" Murmushi tayi, Yace "Saboda kinsan baza kiyi missing dina ba shi yasa kika tafi kiyi kwana uku ko" Tace "To in dawo gobe ne" Yace "I will gladly come and pick you" tace "Kaga fa zan je har gidan Aunty Mariya, sannan inje in gaida Hajja gidan Baaba Yahanasu" Maheer yace "Duk za ki iya yi a goben sai mu biyo train na yamma" Mayraah tace "Aa ka dai bari jibi pls" Yace "Alright dear, yau din zaki je wajen su Momy?" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Basa kasar" Maheer yace "Yaushe rabon kiyi communicating da su?" Mayraah tayi shiru, Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ya kamata ku dinga communicating a kai a kai don ku saba sosai Mimi" Ita dai bata ce komai ba, yace "Kin ci abinci?" Tace "Yanxu zan ci" Yace "Alright, i will call u back later, nima zan shiga theatre ne yanzu" Sallama suka yi ta ajiye wayar, she is soo sad bata hadu da Mom dinta ba, Shigowar Hajiya Ramatu dakin ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, Hajiya Ramatu ta ajiye mata abincin da ta kawo mata.... Da daddare bayan isha Mayraah na zaune parlon grandma dinta dake sanar mata an sa bikin Farrah er gidan Aunty Halima nan da wata biyu, Mayraah tace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Hajiya Ramatu tace "Ameen, akwai wani kawun ki ma da baki sani ba shi ma zai yi auren, duk rana daya aka sa da na Farrahn" Mayraah tace "Allah ya sanya alkhairi" Hajiya Ramatu tace "Ameen" Mayraah na kallonta tace "Umma, Yaya Aliyu yana nan?" Hajiya Ramatu tace "Aliyu yana Canada, kilan mu ga ya zo bikin" Mayraah ta dau wayar ta dake ringing ganin Maheer ne tayi silencing ta ajiye, Hajiya Ramatu tace "Ba mijinki ke kira ba, tafi daki kiyi wayarki mana" Mikewa Mayraah tayi ta wuce dakin tayi picking call din, bayan sun gaisa a hankali tace "Yaya na mance ban taho da Charger na ba, na bar shi a kano" Yace "How manage? ke da baki da mantuwa, yanzu wayar ba caji kenan?" Tace "Aa nayi using na Aunt dina, but i don't want to be inconveniencing her" Maheer yace "Ohk, Usman zai shigo kadunan gobe zan gaya masa ya siya ya kai maki" Mayraah tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen Baby gal" Tace "Have u eaten?" yace "Wa zai girka min bayan baki nan?" Mayraah tace "Me yasa baka je gida wajen Ammi ka ci ba?" Yace "Let video call" A hankali tace "Ohk" Washegari wajen karfe daya na rana Mayraah ta fito compound ta dalilin kiranta da Usman yayi, ta ɗan buda ido ganin Eeman a motarsa, amsa gaisuwarta tayi tana murmushi, Usman ya dau charger da ya siyo mata ya bata ta amsa tace "Nagode, yaya amma dai ba kanon za ku tafi yanzu da ranan nan ba?" Yace "Kina da sakon da za a kai maki can ne?" Tayi murmushi tace "Aa, am just asking" yace "ke yaushe zaki koma Abuja?" Tace "Tomorrow in sha Allah, yau zan je gidan Aunty Mariya daga can inje wajen Hajja" Usman yace "Ohk" A hankali tace "Yaya ko zaka yi dropping dina gidan Aunty Mariyan kafin ku tafi" Yace "Aa, Driver yayi dropping dinki mu da za mu tafi kano" Tace "Toh shikenan, Allah ya tsare hanya" Sallama tayi ma Eeman sannan ta juya ta koma ciki, tana shiga gidan Usman ya kirata a waya, tana dagawa yace "Did you inform ur husband that u will be going out?" Ta ɗan turo baki tace "Ya sani ae" Yace "Toh fito mu tafi" Sosai Mayraah tayi mamaki, shi da ta riga tasan No dinsa is always No, tasan definitely Eeman ce zata masa magana shine ya canza mind zai kai ta, murmushi kawai tayi, ta tafi bangaren grandma dinta ta sanar mata zata je gidan kanwar Ammi, mayafinta kawai ta yafa ta dau jakarta ta fita, back seat ta bude ta shiga, Usman ya ja motar suka bar layin... Mayraah na shiga compound din gidan Aunty Mariya ta gaida duk mutanen da ta hadu dasu a tsakar gidan, Eeman na biye da ita har suka karasa part din Aunty Mariya, bata yi tunanin Usman zai ce su shiga gidan da Eeman ba, don duk zaton ta suna ajiyeta za su wuce, amma sai yace mata idan yayi sallah zai shigo shi ma, Mama Ladi dake zaune parlon ta tsuke fuska tana fiffita da maficin hannunta duk da fan din dake aiki a sama ta dinga kallon Mayraah bayan sun shigo parlon, can tace "Ikon Allah, ke kuma daga ina haka?" Mayraah na murmushi ta zauna kan carpet tace "Ina yini Mama" Eemaan ta zauna gefen Mayraah ita ma ta gaida Mama Ladi, Mama Ladi na kallon Eeman tace "Wacece wannan kuma, amma ba daga gidan Saminu take ba don duk nasan yan matan gidan" Dai dai nan Aunty Mariya ta fito daga daki, da fara'a tayi welcoming din su Mayraah, tace "Dazu kuwa muka yi waya da Maheer yake ce min kina nan kaduna ai, ya kika baro su Ammi da Bilkisu?" Mayraah tace "Lafiya qlau" Aunty Mariya ta amsa gaisuwar Eeman tana murmushi tace "Sannu yan mata" Duk tunanin Aunty Mariya daga can gidan Alhaji Saminu Mayraah ta taho da Eeman, bude kofar parlon aka yi wata budurwa ta shigo da cooler din shinkafa da miya ta ajiye a parlon, Mama Ladi dai ta kyabe baki ta kauda kai, Aunty Mariya na kallon budurwar tace "An gama rabon abincin ne Hussaina?" Yarinyar tace "Ehh an gama" Aunty Mariya na kallon Mayraah tace "Ku je can ku ci abinci Mimi" Mayraah na murmushi tace "Aa Aunty ni dai na koshi sai dai ko Eeman" Eeman ta girgiza kai da sauri tace "Nima na ci abinci" Aunty Mariya tace "Toh ku je ku dau drink a fridge, kina yin abu sai kace gidan bakon ki ne Mayraah" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta mike Eeman na ganin haka ita ma ta mike ta bi bayan Mayraah, suna fita Mama Ladi tace "Wannan dai tsari na gidan ku tirr da shi Mariya, ace sai yunwa ya ci ya cinye mutum, duk mutum sai ya galabaita sannan a basa abinci a er tsohuwar cooler? Su fa yan kauye in suka yi kudi sama taka za'a ga fi'ili da sanabe iri iri malam, banda haka ta yaya wannan babban gida haka da mutane kaca kaca a cikinsa kamar yan gudun hijira ace lallai sai a tukunya daya za ayi duk girkin gidan, lemon nan dan banza ma sai anje can za a bude katon firiji a dauka, gaskiya kina kokari Mariya, wannan ai rayuwar wahala ce kawai, ga uwar miji da kishiyoyinta uku, ga facalolinki biyar, ga gandara gandaran samari da yan mata a gida sun kusa 30, ga jikoki yarkacee sun kusa arba'in, inaaa.... sam bazan iya ba wallahi, yanzu gashi kinyi baki ace ko lemon da zaki basu a nan babu sai sunje can cikin gida an bude katuwar firiji sun dauka" Aunty Mariya dai danna wayarta kawai take, sai ga Mayraah ta shigo parlon, Mama Ladi tace "Kin samo lemun ko sun wawashe?" Mayraah tace "Aa cokali aka ce in amso sai mun ci abinci a can" Mama Ladi ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa tace "A katon faranti suka zuba abincin ko?" Tuni Mayraah ta tafi ta dauko cokali biyu a kitchen din Aunty Mariya ta fito, Mama Ladi tace "To har ita sadaka yallar da kuka je amso lemon tare suka tilasta ta zauna taci abincin a cikinsu?" Sai kuma ta kara kwashewa da dariya har da kwanciya, Mayraah zata fita Aunty Mariya tace "Daga can gidan ki ka taho tare da ita Mimi?" Da sauri Mama Ladi ta dago tace "Sam, wnn dai ba daga gidan Saminu take ba, abinda duk nasan yaran gidan" Mayraah na kallon Aunty Mariya tace "Aa, kano za su tafi da Ya Usman" Aunty Mariya tace "Wacece ita?" Mayraah tace "Yarinyar Aunty ce" Aunty Mariya tace "Wacece Aunty kuma?" Mayraah tace "Aunty Amina" Mama Ladi ta gwalo ido tace "Ko dai amaryar Mamuda?" Mayraah dai bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Habaa, ni dai ina ta kallon yarinyar naga sak kamar Amina tayi kaki, har dirin irin na uwar