Showing 330001 words to 333000 words out of 456519 words
cewa komai ba. Washegari Surkar Dr Khalil da wata aminiyarta, sai kawayen Ammi biyu da wata matar abokin Abba, da matar ɗan uwansa na kano sai Yahanasu suka tafi kai lefen Mayraah kaduna inda Aunty Mariya zata hadu da su a tafi gidan Alhaji Saminu, kaya ne na gani na fada da suka dame na Musharraf suka shanye, ashe Musharraf bai hada mata komai ba wancan lokacin, set din gold dinta ma kadai ya ci millions, Mama Ladi suna daga cikin masu amsan lefe a parlon sai washe baki take tayi tsumu tsumu cikin dangin Alhaji Saminu ke kya ce er uwarsa ce, Kunya yasa Aunty Halima da yan uwanta da suka yi zugan kwaso lefen Musharraf a gidansu Ammi suka kasa dago kai a babban parlon, Ai ko su Mami da familyn gaba daya suka rasa inda za su sa su Aunty Mariya don tarba, a haka yan kai lefen suka bar gidan da abubuwan arziki da aka basu su ma. Tuni aka fara yi ma Mayraah gyaran jiki a gidan kakanninta, ita dai ta dawo ga ta nan gata nan ne kawai, irin kamar kaga abinda kake dauka wasa ya fara zama gaske gashi har da lefe, har a sannan she is still finding it hard to believe and assimilate da gasken fa Maheer ne mijinta kuma gidansa za ace za a kai ta, Ya Maheer fa? She just wish duk wannan abun kawai mafarki take zata farka soon, wa ennan tunanin ke kara karyar mata da zuciya ya kara jefata cikin damuwa sosai, ta dawo ko abinci bata iya ci ganin kwanakin na ta tahowa a hankali, lkci daya ta rame bata da aiki sai kuka da tunani, babu ranan da zai wuce da bazata tuna irin yanda suka taso a gida daya da Ya Maheer ba da irin relationship dinsu na Yaya with his favorite Lil sis, kawai kuma yanzu ace mijinta, it's so disturbing, daga karshe Mayraah kashe wayarta ma tayi gaba daya don kullum sai Ammi ta kirata Usman ma ya kan kirata to yanzu taji ko magana ma bata so, kakarta duk ta zata normal damuwa ne da ko wace amarya ke shiga idan aka kusa bikinta bata san wannan yafi karfin wannan damuwar ba, a ko da yaushe Hajiya Ramatu cikin kwantar mata da hankali take tana lallabata, Mayraah taji ita dama gun uwarta kawai aka kai ta kilan ta dinga jin saukin abinda take ji a ranta amma ko uwar ta zo gidan bata shigowa Bedroom din Hajiya Ramatu balle ta ganta, kuma da sun zo da sun tafi... Babban gidan ya dawo bai rabo da yan uwa da abokan arziki tunda bikin na ta karatowa, gashi tare za ayi taron bikin da na Musharraf wanda shi a Adamawa za a daura aurensa da Jiddah, duk wani event dinsu ma a can za ayi, kawai iyayensa maza ne za su je daurin aure Adamawa, a mata kuma Hajiya Halima da wasu matan Kannen Alhaji Saminu ne za su je Adamawan biki, Mami kuma will remain in kaduna don su za su kai Mayraah Abuja, duk da Abba ya sanar masu Maheer is not interested in any event sun shirya nasu events din da za ayi ranan bikin... Ana saura kwana uku biki gaba daya familyn suka tare a gidan Alhaji Saminu da Mama Ladi dake cikinsu tsumu tsumu, yan mata kaman Mayraah wa enda duk yan uwanta ne sun kusa goma and they were all by her side kamar da can sun saba da ita, and finally the D day arrived.
I dedicate the whole of this page to *Meenah Parrot, Ummi and Ma'ani.....* Ba sai nace maku komai ba but just know that i have got brand new sisters added to my fanmily list, i love and appreciate you so much sisters 🥰💖
[9/14, 8:44 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Duk wani shagali da ake ta yi tun wayewar garin wannan rana Mayraah na kwance dakin kakarta zazzabi ya rufeta, har sai da aka kira mata wani likita ya zo ya dubata sannan ya aika aka siyo mata magunguna, tunda tasha drugs din ta samu bacci me nauyi, duk bayan ɗan lokaci Hajiya Ramatu ke shigowa dakin dubata don abun ya fara damunta ganin yanda Mayraah ta dau lamarin auren nan, sai a sannan zuciyarta ta fara tunanin to ko dai bata son auren nan ne, don in dai ba auren dole ba babu ta yanda mace zata shiga irin wannan damuwa haka for almost 10 days now, duk da wannan tunanin nata bata dai ce ma kowa komai ba a gidan amma abun ya tsaya mata a rai sosai. Wajen karfe biyu da rabi Mayraah ta bude ido a hankali jin hannu a forehead dinta, MD dake kallonta ya cire hannunsa yace "Ya jikin?" Juyawa tayi taga Kakarta tsaye kanta, daga gefenta kuma Musharraf ne tsaye yana sanye da fararen kaya kal just like MD, kana ganinsu kasan daga daurin aure suke, suna hada ido shi ya fara sauke idonsa kasa, ta gyara Duvet din jikinta a hankali ita ma ta sunkuyar da kai, MD na kallon Hajiya Ramatu yace "Wani magungunan likitan ya bata?" Hajiya Ramatu ta dauko masa magungunan ta mika masa cike da damuwa tace "Har yanzu babu abinda ta ci fa Daddy, shayin ma da kyar ta sha ɗan kadan dazu, jiya ma haka ta wuni ba cin abinci, ga zafin da jikinta yake" MD yace "Ai jikin ba zafi yanzu" Musharraf na kallon Mayraah cikin sanyin murya yace "Allah ya sauke Mayraah" Ita dai bata daga kai ba tana kallon lafiyayyen lallen da aka zanzara mata a hannunta tace "Ameen" juyawa yayi ya fita daga dakin, MD yace "A kawo mata abincin zata ci yanzu" Hajiya Ramatu tace "To Allah ya sa, mu je sai ka taho mata da shi" Tare suka fita daga dakin nata, bayan ta kulle kofar suna tafiya tayi kasa da murya cike da damuwa tace "Anya Aliyu yarinyar nan na son auren nan kuwa? Sai kace warce aka yi ma auren dole? Tun fa da ta zo garin nan a haka take cikin damuwa da ƙunci, ko fa bacci bata yi da daddare, anya lamarin nan ba abun dubawa bane Daddy??" Da mamaki MD yace "Me zai hana ta so auren Umma? Yayanta ne fa, gida daya suka tashi da shi, kuma baki ga shakuwar da suka yi ba wllh, kawai dai kinsan kowa da yanda fargaban aure ke zuwa masa, barin ita da nake ganin kamar a sangarce take she look so pampered, don Allah kar ma ki kara wannan magana wani yaji Umma, beside ta yaya ma za su mata abinda zai cutar da ita, for 22 years basu cuceta ba sai yanzu? Don Allah kar ki bari wani yaji maganar nan" Hajiya Ramatu tace "To in sha Allah, hankalina ne kawai ya tashi wllh, amma ni dama wa zan je in gaya ma, da kai kawai nayi magana" MD yace "Yaushe ne za a kai ta Abujan?" Hajiya Ramatu tace "Gobe da yamma in sha Allah aka tsara" MD yace "Toh Allah ya kai mu, zata warware in sha Allah kar ki ji komai, sangarci ne yayi mata yawa" Hajiya Ramatu bata sake cewa komai ba, shi ya amshi abincin da ta dauko ya tafi yaje kai ma Mayraah, ya ajiye mata saman carpet yana kallonta yace "Sauko ki ci abinci" Ta mike zaune da kyar ta girgiza masa tace "Ni bazan iya ci ba, amai zan yi" Zaunawa yayi saman kujera yana kallonta yace "Mimi kike ko wa? me yasa kike da taurin kai ne, Why are you acting like u are not civilize kamar wata er kauye, Duk maganar da na maki last week ya tashi a banza kenan i just wasted my effort, kin zata ina bada shawara ne nan da kika gan ni? Now tell me what exactly is ur problem da kike sa ma kan ki damuwa haka?" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa babu ko kiftawa, whereas tunanin da take daban a ranta wato imagining Maheer a matsayin mijinta, ya ɗan mata tsawa yace "Malama ba shiru zaki yi ba kina kallona haka, answer my question now" Hawaye cike idonta muryarta na rawa tace "Yaya Maheer fa" Yace "So? Haramun ne aure tsakaninku? Tun watanni nawa baya kika san ba jininki bane shi din? Is it going to take u forever to assimilate that?" Ta fashe da kuka har da daura hannu a kai tace "Na shiga uku, wllhi bazan iya ba, baza ka gane ba" Yace "Ba a kai ki gidan nasa bane.... sanda zaki iya mu muna ina? Kilan ni ina Canada" Ta kara rushe masa da kuka tace "Yayana ne fa, wllh yayana ne, he is my brother...." Dariya ta ba MD ganin she is so serious tsakaninta da Allah take maganar, Yana zare mata ido yace "To yanzu get this stuck to ur head ba brother dinki bane shi, he is ur Husband, Maheer mijinki ne yanzu, ke duk wannan kinibibin da kike kar fa nan da wata hudu mu ganki da cikin Maheer a jikinki" Ai bata san sanda ta sauka daga kan gadon ba ta dawo kasa a rikice tace "Na shiga uku na lalace don Allah ka dena wannan magana, don girman Allah ka rufa min asiri ka daina" Gaba daya ta rikice sai gwale ido take irin ya fadi wani mugun abu din nan, dariya kawai yake yace "Za ki sani, don wallahi sai na tuna maki wannan ranan in dai na ganki da cikin Maheer" Ta hade kanta da gado da sauri tana kara rusa kukan wnn abu da yake gaya mata a kunnenta, MD ya kwantar da murya yace "Mayraah" Ta dago da sauri tana kallonsa hawaye na zuba idonta duk tayi mugun tsurewa da batun da yake mata, nan ya hau kwantar mata da hankali kamar yanda yayi wancan ranan a gidan Mami, for almost an hour he was trying to talk sense into her head, ita dai tana jingine da gado tana kallonsa kai kace she is paying attention, sai dai duk wannan abun da yake bai san her mind is absent ba, ta lula duniyar wani tunanin daban, a haka Babanta da wasu cousins dinsa da suka dawo daga Adamawa daurin aure suka shigo dubata a dakin su ma. Taro sosai aka yi a gidan Alhaji Saminu, don gidan ya dawo ba masaka tsinke saboda jama'a, kudi kam ba na wasa aka kashe ba a wannan biki, matan prominent people daga garurruwa daban daban suka halarci bikin da aka hada har da na Musharraf, komai baja baja, kaji har sai mutum ya ture, duk da babu amarya balle ango amma duk wani events da suka shirya sai da suka yi since Musharraf is also involved, ita Amarya Mayraah anyi considering bata da lafiya... Bayan magrib MD ya shigo babban parlon Alhaji Saminu tare da Maheer dake biye da shi a baya, duk yawan mazan parlon daga kannen Alhaji Saminu sai cousins da kuma abokansa ne, nan MD yayi introducing Maheer da ya zauna saman carpet bayan duk ya gaishesu da ladabi, yawanci duk basu san angon ba sai a lokacin, nan suka masa fatan alkhairi da zuri'a dayyaba, wasu suka masa nasiha akan zamantakewar aure aka dinga basa shawarwari, daga karshe Maheer suka bar parlon da MD, can gun relatives dinsu mata MD ya tafi da shi don ya gaida su, tunda Maheer ya zauna yan matan dake parlon ke kallonsa attentively, wanda yawancinsu sa'annin Mayraah ne, sai wa enda suka girmeta, Maheer dai ya gaida elders din parlon with respect, nan MD yayi introducing dinsa as Mayraah's Husband, duk sai da yan matan parlon suka kalli juna, shi dai Maheer kansa na kasa yana sauraron duk nasihar da tsofaffin parlon ke masa da fatan zaman lafiya, after like 15 mins suka bar Parlon, haka nan MD ya dinga kai sa gun dangi dake gidan yana gaishesu, daga karshe ya kai sa parlon Hajiya Ramatu da yan uwanta, second parlor dinta ta samesu don can suka zauna, da fara'a take welcoming din Maheer ta sa aka kawo masa ruwa har da abinci, Hajiya Ramatu na kallonsa tace "Yaushe ka shigo ne?" Maheer ya daga kai a hankali yace "Daxu da yamma" Hajiya Ramatu tace "Allah sarki, to ya su Amminku suka ji da taro" Yace "Alhamdulillah" Tace "Toh maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya, ya kauda duk wata fitina tsakanin ku" Sunkuyar da kansa yayi, Hajiya Ramatu ta bar masu parlon, MD na kallonsa yace "Ka ci abincin mana" Maheer ya ɗan yi murmushi yace "I am okay, mun ci abinci da frnds dina" MD yace "Oh ok, suna ina frnds din?" Maheer yace "Hotel mu ka yi lodging" MD ya mike yace "Ka shiga ciki ka duba amaryar taka, ba ma ta jin dadi" Da sauri Maheer ya girgiza kai yace "No, ai ina ga ba sai na shiga ba, since, erm i know an dubata ai, ba sai na shiga ba" MD yace "Aa mu shiga ka dubata, kasan tun yaushe ne bata da lafiyan?" Zai yi magana sai ga Hajiya Ramatu da wani warmer cike da kaji, MD na kallonta yace "Umma wai bazai iya shiga dakin ki ya dubata ba" Hajiya Ramatu ta buda baki tace "Ni fa kakarku ce, ka manta kuma ni ce Uwargidan taka" Maheer dai yayi murmushi kawai kansa a kasa, MD yace "To kai ka ji, sai mu je dakin uwargida a duba amarya" Maheer ya ɗan kalli Hajiya Ramatu dake kallonsa tana murmushi don kawai nutsuwarsa ne ya burgeta, kana ganinsa kaga bafillatanin yaro, mikewa yayi ba don ya so har cikin ransa ba ya bi bayan MD zuwa Bedroom din Hajiya Ramatu, Mayraah har ta fara bacci kan darduma daga yin sallan magariba, MD ya tsaya yana kallon Maheer da ya kasa karasawa cikin dakin, Maheer ya kallesa calmly yace "Kaga bacci take MD, pls ba sai mun tasheta ba..." Bai jira me MD zai ce ba ya fita daga dakin, dariya abun ya ba MD yaga kamar shi ma bai son haduwa da ita ne, Maheer's reaction was so funny to him, ya ɗan yi murmushi ya juya ya fita daga dakin shi ma, Maheer bai kara minti ashirin a gidan ba ya koma hotel din da suka sauka da abokansa bayan Hajiya Ramatu tayi masa takeaway din kaji da drinks. Washegari da safe aka ci gaba da shagulgula a gidan Alhaji Saminu, ba laifi yau Mayraah ta fito cikin mutane duk da ba wani dadewa tayi ba kakar ta mayar da ita daki, tsadaddun kayan da aka mata na fitar biki kusan kala 15 uku kawai ta saka a ciki.... Bayan azahar aka fara shirye shiryen tafiya da amarya Abuja nan hankalin Mayraah ya kara mugun tashi ta dinga kuka gabanta na faduwa, tsadadden alkyabba fari da Gold Mayraah ta saka kan kayan jikinta, tayi kyau har ta gaji, kana ganinta ka ga amarya, haka aka bi da ita duk gun tsofaffin dake gidan wa enda duk yawancinsu kakanni suke a gareta suka dinga mata nasiha da yi mata fatan zaman lafiya da mijinta, daga nan aka kai ta gun kakanta shi ma yayi masa nata tare da kannesa dake parlon, shi dai Babanta na zaune a Parlon sai kallonta yake, daga haka aka maido hankali kansa shi ma yayi mata nasa nasihan, bai iya yace komai ba, kawai ya sa mata albarka aka fita da ita, dakin da Aaria take a gidan aka kai Mayraah, Aaria ma dai ta kasa cewa komai sai hawaye. Karfe hudu da rabi yan kai amarya suka sauka a cikin garin Abuja, ciki har da Mama Ladi da sae ka rantse er pamilyn Alhaji Saminu ce, Mayraah dai na jikin Mamin Musharraf ta kasa daina kuka, sai yanzu ta yarda all this while ashe ba mafarki take ba, biyar da yan mintuna convey din yan kai amarya suka iso gidan Abba, duk yawan motocin da suka kawota sai da compound din gidan ya dauke su tas, niyyar su Mami dama bayan an kai Mayraah gidan Ammi in ta mata nata nasihan Abba ma yayi mata sai su kai ta dakinta daga can su kuma su tafi masaukinsu washegari su koma Kaduna, amma sai Hajiya Safiyya da Surkan Dr Khalil ke sanar masu ai za ayi Mothers eve gobe, su yi hakuri goben sai su kai amarya in an gama, haka nan aka bar ma su Mami wani bangare na cikin gidan. Mayraah na kwance dakin da aka sauketa wajen karfe tara na dare, Badiyyah ce zaune kasan carpet din dakin duk ta dawo so calm kamar ba Badiyyah ba, ko maganar kirki yanzu bata cika yi ba sai dai ta bi ka da ido, daga daya side din kuma Farrah ce er wajen Aunty Halima sai cousins dinta uku, Farida da Maimoon sai Rabi'a wanda tare da su aka taho kawo Mayraah kusan sun zama kamar su ne kawayen amarya hiransu suke kasa kasa a dakin, duk yawan mutanen dake gidan sannan ga kuma family din Alhaji Saminu da suka kawo Mayraah kusan su Talatin hakan bai sa Ammi ta ki dinga shigowa gun Mayraah ba, don bi ni bini zata shigo dakin to check on her barin da taji jikinta da zafi tun da aka kawota gashi taki cin abinci, Mayraah dai bacci take restlessly a dakin, Ammi ta shigo rike da cup din shayi da ta hado mata ganin bata ci abinci ba, ajiye shayin tayi saman beside drawer ta cire duvet din jikinta a hankali tace "Mimi" Mayraah ta bude idonta da yayi ja tana kallonta, kasa cewa komai Ammi tayi jin jikinta yayi zafi sosai gashi sai rawan sanyi take, dama kuma Mami tace mata bata da lafiya, Ammi ta mayar mata da duvet din ta fita daga dakin ta tafi bangarenta ta dauko wayar ta, number Maheer tayi dialing, bayan ya daga da damuwa tace "Maheer baza ka shigo ka duba Mimi ba kuwa, zazzabi ne sosai fa jikinta, ga shi sai rawan sanyi take, dama sun ce tun a Kaduna