Showing 321001 words to 324000 words out of 456519 words

Chapter 108 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70657

na rawa tace "Ni dai wallahi bazan iya zama da shi as mijina ba, wanda nake ma kallon yayana fa? that is the last thing i will do on earth" Dariya sosai ta ba Usman amma ya dake bai yi ba, yana murmushi yace "Yanzu dai abinda nake son in gaya maki shine ki kwantar da hankalinki shi ma ai ba so yake ba don yace ke kanwarsa ce, amma kinga it's too early yace ma Abba haka sbda relatives dinki, beside ke da kike wajen Amminki har yanzu... ko kinji wani yace maki ai za a tafi da ke wani waje ne? Iyaka may be next week kije ki gaida grandparent dinki a kaduna ki dawo, so just put in mind that u are still Miss Mayraah ki ci gaba da harkan gabanki har sanda za a san abun yi, but for now, we all are not in support of this" Shiru tayi tana kallonsa tana goge hawayen idonta don abinda yace ya kwantar mata da hankali kam, ya dan buda mata ido yace "Ammi ma tace ai baza ayi haka ba, don haka kinga ta goyi bayanki cewar auren is wrong, so just relax and cheer up" Mayraah ta sunkuyar da kanta a ranta kuwa tana tunanin jiya da take ta tambayar Maheer waye mijin da aka aura mata yaki gaya mata, wani mugun haushin rungumeta da yayi yana lallashinta ta dinga ji, ta kalli Usman tace "To ni dai bana son ma ya sake min magana a gidan nan, nima kuma bazan masa ba" Tana magana ne amma har hawaye ya cika idonta, Usman dai murmushi yayi bai ce komai ba, can ya mike, tana goge idonta tace "Yaya fita zaka yi?" Yace "Zan je in shirya, yau Friday" a hankali tace "Ohk" Ya nufi kofa kafin ya fita ya juya ya kalleta yace "Make sure kinyi breakfast din Mimi" Ta gyada masa kai ya fita daga dakin, sai a sannan Mayraah ta dan ji ta samu relieve a ranta har tayi breakfast din dake gabanta, tana gamawa ta fita da plate din da cup din shayi, tun da ta kallesa sau daya a parlor shi ma by mistake ne don bata san shine a zaune ba, daga haka bata sake kallon inda yake ba ta nufi kitchen fuska daure, shi kam dama ko kallon inda take bai yi ba, ko da ta fito daga kitchen din ma bata gansa a parlon ba. Bayan sallan Juma'ah Maheer da Usman suna parlon Ammi, Ammi na kallon Usman tace "Maheer yace min ka saka masa 5M Allah ya sa afi haka, Allah ya kara maka budi" Usman ya dan buda ido ya kalli Maheer cause bai yi expecting zai gaya ma Ammi ba, shi kuma kawai assisting dinsa yake son yi gun kayan lefen da Ammi tayi magana jiya da daddare, Ammi tace "Allah ya bar zumunci" Murmushi kawai Usman yayi bai ce komai ba, Ammi na kallon Maheer tace "So now what is ur budget na lefen?" Maheer ya daga kai yana kallonta, bayan few seconds yace "I will add 7M to the 5M he gave" Ammi ta gyada kai a hankali tace "To Allah ya kara budi, ni kuma zan siya mata set din Gold da za a sa a kayan, Abbanku ma nasan zai bada wani abu a kara a kudin lefen, though shi ban san me zai mata ba don kakanta yace zai mata furnitures din gida gaba daya, Ceo kuma tace we shouldn't bother about kitchen wares and all electronics, sai a siya akwatuna set uku each with 6 boxes" Usman ya dan buda ido yace "That's much, 18 kenan fa" Ammi ta dan yi murmushi tace "No it's not, Autana ce ai, nima zan mata akwati biyu na kayan sa wa" Usman yayi er dariya, Shi dai Maheer ba abinda yace, Ammi na kallonsa tace "Sai kuma kudin gyaran jiki, nawa zaka bada?" Maheer ya kalleta kamar dai bazai ce komai ba sai kuma yace "Ohk" Usman yace "Shi gyaran jikin nawa ake yi" Ammi tace "Nawa za ku bada?" Usman yace "200k yayi?" Ammi ta masa wani kallo tace "Meye kuma 200k?" Ya Sunkuyar da kai yana murmushi yace "Toh ai ban san kan abun ba" Ammi tace "Ku bada 1M, idan akwai canji sai a ajiye maku" Usman yayi murmushi yace "To ba damuwa" Ammi tace "Yanzu zuwa sunday za a kai ta kaduna zata yi kwana biyu don ina son ta dawo da wuri a fara mata gyaran jikin, in kuma za su mata can din to" Usman yace "Allah ya kai mu" Ammi tace "Ina son zuwa nan da kwana biyar a gama hada komai na lefen tunda kun ga kaduna za a kai masu kayan" Usman yace "A nan Abuja za a hada kayan?" Ammi tace "Eh da zan ma surkar Dr Khalil magana don muna gaisawa sosai da ita, Hajiya Safiya ma zata shigo Abujan sai su hada kayan tare kawai, Mariya kaga yau ta koma sai kuma biki zata dawo" Usman da yayi shiru yana kallon Ammi ya dan yi murmushi yace "But Ammi, Hajiya Amina dake kano ko ita ma zata iya hada kayan cause business dinta ne ba sai in involving outsiders ba" Kallonsa kawai Ammi take, can tace "To sai ka kwashi kudin ka tura mata ta hada" Usman yayi er dariya ya mike yace "Ni akwai inda zan je yanzu, sai na dawo" Ko kallonsa Ammi bata yi ba ya nufi kofa ya fita, Ammi tace "In nasa bikin ya tashi sai ya bata kudi ta hada masa kayan wannan kam bai isa ya gaya mana yanda za mu yi ba" Shi dai Maheer bai ce komai ba, can dai yayi murmushi ya mike, Ammi tace "Ka je ka ci abinci bawan Allah" Usman na fita ya yi knocking kofar dakin Mimi, Yana nan bakin kofar a tsaye har Maheer ya wuce sa ya sauka downstairs, Mayraah ta bude kofar dakin a hankali tana ganinsa tace "Yaya fita zaka kara yi?" Yace "Eh, fito ki ci abinci" Tace "Na ci abinci" Yace "Ammi tace baki ci da yawa ba" Shiru tayi bata ce komai ba, can tace "Yaya don Allah zan iya gaya ma Ammi ina son inje gidansu Ceo?" Usman yace "Ai ina jin Sunday za su tafi can kaduna, next week idan kinje kadunan za ki hadu da su a can" Bata sake cewa komai ba, yace "Fito ki zuba abincin?" Babu musu ta fito daga dakin suka sauka downstairs, ya zauna parlor yana jiran yaga ta zubo abincin kafin ya bar gidan, har ta nufi kitchen ta juyo tace "In zuba maka kai ma yaya?" Yace "Aa sai na dawo" Bata sake cewa komai ba ta nufi kitchen din, wani irin faduwa gabanta yayi bayan ta shiga kitchen din ta ga Maheer, lkci daya ta juya ta fito daga kitchen din fuska daure, Usman yace "Ina abincin?" Kin cewa komai tayi tana tahowa a hankali, yana ganin Maheer ya fito kitchen din da cup din coffee sai da abun ya basa dariya, shi dai Maheer bai kalli inda take ba balle Usman dake zaune ya nufi dakinsa, Usman ya mike kafin yace mata komai ta nufi sama, yace "Mimi" bata tsaya ba tayi wucewarta. Kamar yanda Ammi tace washegari da safe ta shirya ta tafi gidan surkar Dr Khalil bayan ta sanar ma Abba da ya koma kano jiya da yamma, Ammi bata bar gidan ba sai da ta tabbatar Mayraah tayi breakfast sanin bata son cin abincin.... Bayan azahar Usman zai fita Mayraah ta marairaice masa tace "Yaya kai ma fita zaka yi Ammi bata dawo ba" Ya kalleta da mamaki don makullin motarsa da ya bari jiya a dakinta ya shigo dauka yace "Akwai aikin da kika bani ban yi bane Mimi?" A hankali tace "To ni kadai fa a gidan" Yace "Bilkisu na nan ai, even Dr bai tafi aiki ba tukun ai sai da yamma" Bai jira cewarta ba ya nufi kofa, tace "Pls yaya zan rakaka" Sosai ta basa dariya, ya juyo yace "Ki rakani ina?" Ta sauke idonta tace "Inda za ka" Yace "Ni ai ba wani waje zan je ba Client ne ke jirana" Tace "Eh zan bi ka sai in jira a mota" Ya gyada kai yace "To je ki tambayi Dr" Tayi kasake tana kallonsa yace"Yea, in kina son bi na je ki fara gaya masa tukun" Tace "To saboda me?" Yace "Saboda ya kamata a gaya masa" Komawa tayi ta zauna alamar baza ta ba, Usman yace "Sai na dawo" Ta marairaice tace "Don Allah yaya" Ya wani hade rai yace "Ba ki ji abinda nace maki bane?" Shiru tayi tana kallonsa, ya fice daga dakin, a hankali ta mike ta dau gogaggen hijab dinta ta saka sannan ta fito, har zai fita parlon ta gansa da sauri tace "Don Allah ka jirani yaya" Ya juya yana kallonta, ita dai da ya bar ta ita kadai da Maheer a gidan gwara tayi abinda yace kawai, tana tafiya a hankali ta tafi dakinsa, kwankwasa kofar dakin ta yi sannan ta bude fuskarta babu yabo babu fallasa ta shiga, tana kallonsa tace "Wai ya Usman yace za mu fita ka kula da gidan ba kowa" Shi dai danna wayarsa kawai yake, bai daga kai ba balle ya kalleta, ta dinga kallonsa, can tace "Yaya magana nake maka" Jin bai tanka ta ba ta tura baki ta juya ta bar bakin kofar, ta koma ta samu Usman dake bakin kofa har sannan tace "Yaya na gaya masa" Yace "Me kika ce masa?" Tace "Za mu fita da kai" Usman yace "Client din ma sai gobe za mu hadu naji garin da rana..." Daga haka ya koma ya zauna kan kujera, ita babban takaicinta Maheer da yasa taje tayi ma magana gashi ko kula ta bai yi ba yayi mata banza, a hankali ta fara tafiya ta wuce sama, Usman ya bi ta da kallo yana murmushi.....
[9/12, 1:50 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Yau ma dai kamar jiya Mayraah bata samu tayi baccin kirki ba da daddare, Allah Allah kawai take gari ya waye don tun a daren jiyan kafin su kwanta Ammi ta hada mata kayanta wai gobe za a kai ta kaduna, har cikin ranta tayi farin ciki da wannan tafiyar da zata yi don taji gaba daya bata son zaman gidan yanzu, bata jin gidan as her comfort zone anymore kuma sai yanzu taji zuciyarta ya gama amincewa da she is not longer a member of the family, don an nuna mata haka tunda har ake son ta auri Ya Maheer, shikenan sun cireta daga family dinsu, da asuba tana zaune saman darduma bayan ta idar da sallah, Ammi ma na zaune tana azkar dinta, karfe shidda da yan mintuna Maheer ya shigo dakin da sallama, Ammi ta daga kai bayan ta amsa sallamansa, ya karaso ciki ya zauna yana kallonta yace "Ina kwana Ammi?" A hankali Ammi tace "Lafiya lau, how was ur night?" Yace "Alhamdulillah" Ita dai Mayraah bata ko kalli inda yake ba kamar yanda shi ma bai kalli direction dinta ba, bayan wani dan lokaci ya mike yace "Ammi za mu shiga Niger state zuwa anjima, wani colleague dinmu lost his son za mu je masa ta'aziyya....." Ammi tace "Allah sarki, Allah ya gafarta masa" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga dakin, Ammi ta mike ta bi bayansa, har ya bude kofar parlor zai fita ya juya yana kallonta ganin ta fito daga dakin, ta kulle kofar dakin nata sannan ta tafi har inda yake tana kallonsa cikin kwantar da murya tace "Maheer amma nace maka yau za taje kaduna in ji Abban ku ko" Maheer dake kallonta a takaice yace "Eh haka kika ce" Ammi tace "To dama ba kai zaka kai ta ba?" Ko rufa baki bata yi ba ya girgiza kai da sauri yace "Aa ni gaisuwa za mu je, ba ga Usman ba" Ammi tayi shiru tana kallonsa, sai kuma a hankali tace "Ka fi kowa sanin halin Mimi Maheer, kayi hakuri da abubuwan nan da take yi, it is just a matter of time, she was taken unaware we shouldn't blame her" Maheer yace "I am not complaining and i will never complain, beside i was also taken unaware" Ammi tace "To ko baza ka kai ta kai kadai ba ku je tare da Usman din" Da mamaki yace "Ammi gaisuwa fa nace maki za mu je Niger" Ammi tace "Ae naga dai ba da sassafen nan nace maka za a kai ta kadunan ba, kwana za ku yi a Niger din in kun je, do what suit you Maheer" Daga haka ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo, juyawa yayi ya bude kofar parlon ya fita kawai.... Karfe sha biyu Mayraah ta gama shiryawa ta dau handbag dinta, tare suka fito da Ammi da ta tabbatar bata mance komai ba, ta bi ta har parking space, Usman dake tsaye kusa da motar ya karasa ya amshi akwatin hannun Ammi yana kallonsu yace "Da wannan akwatin kawai zata tafi?" Ammi tace "Eh" Bude booth yayi ya saka mata box din, sosai gaban Mayraah ya fadi ganin Maheer zaune gaban motar, ta sunkuyar da kanta Ammi ta bude mata back seat ta shiga, Usman na kallon Ammi yace "Toh sai mun dawo" A hankali Ammi tace "Allah ya tsare, ku yi addu'a" Sai da ya shiga motar sannan Maheer ya daga kai ya kalli Ammi yace "Sai mun dawo" Ammi ta gyada masa kai tace "Journey mercies in sha Allah" Tana tsaye har suka bar compound din.... The journey was silent don har suka bar garin Abuja babu wanda yace komai a motar, bayan wani lokaci Usman ya bar ma Maheer driving din, ita dai Mayraah daga karshe bacci tayi tun da ba wani bacci take samun yi da daddare ba, Sai da suka shigo garin kaduna ta farka daga baccin da ya dauketa, kallon gaban motar take ganin Usman ne ke kadai yana driving Maheer baya motar, saura kadan tace masa ina Yaya don har ta bude baki lkci daya ta rufe da sauri, Usman dake kallonta ta madubi yace "Weldone" Ta dan yi murmushi kawai bata ce komai ba, dai dai kofar gidan Alhaji Saminu yayi parking, Mayraah ta dinga bin unguwan da kallo kafin ta sauka daga cikin motar a hankali, bayan Usman ya sauka ya fiddo mata kayanta a bayan mota, tana tsaye absentminded har ya kawo mata akwatin kusa da ita, kawai ita dai ji tayi bakinta yace "Ina yaya fa" don sai da tayi shock jin tambayar da bakinta yayi, Usman ya daga kai yana kallonta yace "Yaya kuma, baya cikin motar ne?" Sai kuma ya bude motar da sauri yana duba ciki da mamaki a fuskarsa, Mayraah dake kallonsa ta zaro ido ganin facial expression dinsa tace "Ina yaje? Kai baka san sanda ya sauka ba dama?" Usman yace "Ohh oh na tuna, tun a hanya ya sauka ashe, haka ne a hanya ya sauka" Without any thinking tace "To me yasa? Kuma ina yaje?" Usman yace "I don't know too, in ba dai ki kira mana shi da wayarki mu tambayesa ba" Mayraah ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, can ta duka zata dau akwatinta ya riga ta dauka suka nufi gate din gidan a tare, sai da Usman ya shiga har cikin gidan ya gaida Grandmum dinta da Aunty Halima dake gidan, ruwa kawai ya dauka cikin abubuwan da aka kawo masa sannan yayi masu sallama, Hajiya Ramatu tace "Me yasa baza ka sauka a nan ba? They are enough rooms ai" Yana murmushi yace "Ai Abuja zan koma ne yanzu don ina da aiki gobe Umma" Hajiya Ramatu tace "Allah sarki, to Allah Ubangiji ya tsare hanya Usman" Mayraah dake zaune parlor ita dai kallonsa kawai take, ganin ya nufi kofa ta ɗan kalli Hajiya Ramatu da Aunty Halima dake parlon, Aunty Halima tace "To ki je ku yi sallama mana Mayraah" Ita fa duk tunanin Aunty Halima Usman ne mijin, Mayraah ta sauke kanta sannan ta mike a hankali ta bi bayansa, bayan sun fito compound tana kallonsa tace "Yaya dama Abuja zaka koma?" Yace "In sha Allah" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "To a ina zaka samesa shi yanzu?" Duk da yasan wa take nufi sai yace "Wa?" Bata sake ce masa komai ba, ya ɗan yi murmushi yace "Wai Ya Maheer? zan ta duba hanya ko zan gansa, in ban gansa ba sai ya tafi tasha ya hau motar haya" Mayraah dai tayi shiru, yace "So now... Enjoy ur stay and be a good gal Mimi" Tayi murmushi ta gyada masa kai yace "Bye" Ɗaga masa hannu tayi ya juya ya nufi gate sannan ta koma cikin gidan tana tafiya a hankali, Hajiya Ramatu ta kai Mayraah nata Bedroom din da ba kowa ke ma zuwa bangaren ba, har cikin ranta take jin Mayraah, wani irin so take mata kamar yanda take ma Ubanta Abdallah, ta so ace sun samu daman rayuwa tare da Mayraah cikin su, kuma ta so auren nata ma ba yanzu aka daura ba duk don suyi creating bond din da babu tsakaninsu, but they are not in the righful place to tell Abba and Ammi tsarin da za suyi ma Mayraah, tunda aure suke son mata sun ga hakan ya dace ne, but Mayraah is their only grandchild a duniya ta so su ma sun kwatanta nuna mata gata kamar yanda su Abba da Ammi suka mata, suna shigowa dakin Mayraah ta gane dakin kakarta ne, Hajiya Ramatu na kallonta tace "Kin ce baki yi sallah ba, ga bandaki kije kiyi alwala kiyi sallahn, yanzu za a kawo maki abinci" Mayraah tace "Toh" Bayan Hajiya Ramatu ta fita Mayraah ta dinga bin babban dakin da kallo, bayan ta idar da sallah sai ga Hajiya Ramatu ta shigo mata da abinci iri iri ta ajiye gabanta, Mayraah felt loved, and she felt really at home, taji kuma tana son Hajiya Ramatu har cikin ranta, bata taɓa

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login