Showing 339001 words to 342000 words out of 456519 words

Chapter 114 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70588

kuma ana mata allura shikenan sai kuma wani watan, Ya dake yana nuna mata kofa yace "To tashi ki fita" Kallonsa tayi da sauri, sai kuma ta fashe da kuka tace "Ni ka sa min kati a wayata in kira Ammi da Abba ko ya Usman a zo a tafi da ni gida kawai, kullum sai kayi ta min fada da masifa a gidan nan, idan na gaisheka bazaka kulani ba, ranan har cewa kayi zaka mareni" Hawaye ke zuba idonta take maganar, da kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "To na mare kin?" Taki cewa komai tana share hawayen dake zuba idonta, yace "Kuma saboda me zan kula ki ni da kike ma fitsara yanzu" Ta kallesa da sauri tace "Ni yaushe na maka fitsara?" Kallonta kawai yake, ta turo baki ta rungume hannunta tace "Ni kawai dai..." Sai kuma tayi shiru, Yace "Kawai dai me?" Ta daga manyan idonta ta kallesa muryarta na rawa tace "Ni dai kawai kai yayana ne" Yace "To wa ya canza ni daga yayanki dama?" Ta sauke idonta kasa, yayi kasa da murya yace "Ai forever ni Yayanki ne" Ta ɗan kallesa tace "Da gaske" Yace "Da gaske me?" Sunkuyar da kanta tayi tace "Abinda kace mana, kaga ai...." Kasa ci gaba tayi, ya zauna gefen gadon yace "Ae ke ce kika yi complicating issues Mimi, dama ta yaya zan canza ki from my lil sis? It's not possible ai" a hankali tace "To don Allah kayi min alkawari" Yace "Alkawarin me?" Ta sauke idonta tace "Ka min alkawarin we are still siblings" Sauke nasa idon yayi shi ma, can yace "Tun da mu ke dake na taɓa maki karya?" Ta girgiza masa kai, yace "Toh i am telling you the fact Mimi, we will still remain siblings in sha Allah, nothing can ever change that" Mayraah taji sanyi har cikin ranta da abinda yace mata, can ta daga kai a hankali tace "To yaya kayi hakuri da abinda nayi" Ya ɗan yi murmushi yace "To nima kiyi hakuri" Turo baki tayi tace "Bayan har kace zaka mareni" Yace "Ke ma kinsan wasa nake" Marairaicewa tayi tace "You were serious wllhi" Yace "So kike Ammi tayi disowning dina" Tace "Bayan ina ta jiran Ammi ta kirani taki kirana, kuma katina ya kare" Yace "Ta bari ne ki gama koke koken ki, amma yanzu bari in kira maki ita" Daukar wayarsa yayi ya kira Ammi, har ya gama ringing bata daga ba, ya kalleta yace "May be tana downstairs" Tace "Yaya don Allah zaka kai ni in ganta yau?" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "To ai baki da lafiya Yau, ki bari gobe friday" Tace "Toh" Sauka tayi daga kan gadon sai kuma ta duka kasa da sauri ta ɗan kallesa bayan tayi realizing towel ne jikinta, sau daya ya kalleta ya sunkuyar da kai yana danna wayar hannunsa, hijab dinta ta jawo a hankali ta saka tace "Yaya pls ka dauko min Pad da kayana a daki" Yace "Ohk" Mikewa yayi ya fita daga dakin.....
[9/18, 8:55 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer ya daga kai yana kallon Mayraah da ta shigo parlon tana tafiya a hankali, sai kuma ya ci gaba da wayar da yake yi da abokinsa, ta karaso cikin parlon ta zauna kasan carpet shi kuma yana kan kujera, bayan sun yi sallama da abokin nasa ya kalli agogo dake nuna after 4 yace "Cikin yayi sauki?" Ta gyada kai tana kallonsa, yace "Ga abinci ki je ki zuba, you've been sleeping since" ta kalli hanyar dining din sannan tace "Yaya wa ke kawo abincin?" Yana danna wayarsa yace "Omar" Tace "Yaya shine bai tambayeka ni ba?" Yace "Yanzu dai ki je ki zuba abinci ba wani abu da kika ci tun safe" Tace "Yaya kasan me, kawai Ammi kar ta sake bada abinci a kawo mana ni zan yi girkin Dinner yau" Ya kalleta yace "Ke da baki da lafiya" Tace "Aa ni dai na samu lafiya ina son inyi girkin dinner da kaina" Yace "Ohk then" Mikewa tayi ta nufi dinning din ya bi ta da kallo sai kuma ya maida idonsa kan wayarsa dake hannunsa, bayan ta zubo abincin ta dawo tana kallonsa tace "Yaya kai ka ci?" Without looking at her yace "Na ci" a hankali tace "Yaya naga kamar fushi kake da ni har yanzu, pls baka hakura bane?" Ya daga kai ya kalleta sai kuma yayi murmushi yace "Dama can ai ni ba fushi nake da ke ba Mimi kawai i gave u space ne, me za ki girka anjiman?" Ta dan buda ido tace "Ur favorite" Yace "Good, i miss your food Mimi" Murmushi tayi tace "Bari in gama ci sai in maka" lkci lkci yake kallonta tana cin abincin gabanta, har ta gama tace "Yaya har yanzu ban san yanda gidan nan yake ba, kawai bedroom dina da kitchen na sani sai kuma dakin ka" Yace "To mu je sai ki gani yanzu" Mikewa tayi, shi ma ya tashi yana gaba tana biye da shi a baya, bedrooms din gidan kaf ya fara nuna mata, duk dakunan uku where well furnished sannan suna da girma sosai ko wanne kuma da bathroom a ciki, ta buda ido sosai tana kallonsa tace "Sun yi kyau sosai yaya" Ya dan murmushi kawai ya fita daga last dakin da ya shigar da ita, ta bi bayansa, wani hanya taga sun dauka zuwa wani bangare daban, suna isowa ya bude kofar shiga wajen suka shiga wani babban parlor, ta wara ido tace "Waow yayi kyau sosai yaya" Shi dai bai ce mata komai ba ya karasa da ita har cikin babban dakin dake part din, ta wara ido tana kallonsa don sosai dakin ya hadu komai fari a ciki, ya juya ya kalleta yace "I think this the master part" Tace "To wancan dama ba dakina bane?" Yayi murmushi yace " Duk naki ne, har wannan din, in kina son kwana nan ma zaki iya dinga zuwa ki kwana" Bai jira me zata ce ba ya fita ta bi sa a baya, suka dawo main parlor din gidan, kitchen suka shiga ya bude babban store din ciki, nan taga uban garan da aka mata daga kaduna na cin cin da sauransu, daga gefe kuma ga kayan abinci kamar za a bude shago, ta juya ta kalli Maheer dake kallonta, dan murmushi tayi tace "To yaya ni bana son cin cin da dublan kai ma haka, yanzu ya za mu yi da su?" Yace "Kyautar wa mana" Bai jira cewarta ba ya fita ta bi sa a baya, kofar fita daga parlon taga ya nufa ita dai tana biye da shi, har ya fita sai kuma ya juya ya kalleta kafin ta fito yace "Ur hijab" Ta juya ta koma ciki sai ga ta ta dawo da hijab dinta, Mai gadi ne kawai a zaune kusa da dakinsa, Maheer ya zaga da ita bayan babban compound din gidan, wani hadadden garden da shukoki masu kyau ta gani, the back yard has enough space, ya karasa wani kofa ya bude ya shiga ta bi bayansa, zaro ido tayi ta rufe baki da hannunta ganin wani portable swimming pool, sai kuma ta kallesa da sauri tace "Yaya swimming pool??" Yana kallon pool din yace "Ai Abba yasan kina so ne shi yasa aka yi" Mayraah was so happy ta karasa kusa da pool din da sauri ta durkusa ta saka hannuwanta biyu cikin ruwan tace "I love it soo much Yaya" Shi dai kallonta kawai yake, ji tayi har ta kagu ta gama period ta zo tayi wanka a pool din, kallonsa tayi ya dauka kai, tace "Yaya to ai bani da swimming trunk" yace "An sa maki a kayanki" Ta wara ido, sai kuma ta debi ruwan da hannu biyu ta watsa masa, ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta, Kara debo ruwan tayi tun kan ta watso masa ya nufeta ta mike da sauri tana kokarin gudu yayi hanzarin riketa kamar zai sakata cikin ruwan, tace "Wayyo yaya fa wasa nake maka, kai baka san wasa ba...." Saketa yayi nan da nan ta nufi kofar fita daga wajen da sauri tana dariya ya bi ta da kallo, sai kuma ya juya yana kallon swimming pool din, after a minute ya fara tafiya a hankali ya fita daga wajen, dai dai stairs din shiga parlor ya ganta zaune ta marairaice tana kallonsa tace "Yaya ka sa na buge kafana" Ya karaso da sauri yace "Ni kuma? How?" Mikewa tayi tace "Eh mana, na zata ka biyo ni ashe baka biyoni ba" Yace "Where did u hit the leg?" Bai jira cewarta ba ya duka yana kallon kafarta tace "I am fine yaya, dama ba sosai na buge ba" Ya mike yace "Ohk" Ita ta fara shiga parlon sannan ya bi bayanta, kitchen ta tafi don fara girkin da tace zata yi, babu abinda babu a gidan na girki, har nama akwai a deep freezer, ta ciro nama kenan zata fara wankewa ya shigo kitchen din, yana kallonta yayi kasa da murya yace "Are you sure you are not stressing ur self Mimi, kin ga nasan su Ammi sun yi girki da mu, bamu gaya masu tun wuri ba, ki bari in an kawo dinner yau sai in ce ma Omar ba sai ya kawo breakfast gobe ba" Mayraah tayi shiru tana kallonsa yace "C'mon Mimi" A hankali tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu goben" Yace "Ameen" maida naman tayi tace "Amma yaya kai ne ka siyo drinks din cikin fridge?" Ya jingina da kofar kitchen din yace "Noo, bani bane" Tace "To bana son su" Yace "Ohk, bari ayi magrib sai mu je mu siyo wasu drinks din, sai a siya maki har da junk food dinki, cornflakes and golden morn" Tayi murmushi tace "Toh yaya" juyawa yayi ya fita daga kitchen din, ta wanke hannunta ta fito. karfe shidda Omar ya kawo abinci gidan, Maheer ya shigo dakin Mayraah yana kallonta yace "Ki fito ku gaisa da Omar, he is around" Shiru tayi tana kallonsa, can tayi kasa da murya tace "Ni dai yaya kamar bazan iya fita ba fa" Yace "To saboda me?" Kasa cewa komai tayi, yace "To ke da kika ce in kai ki gida wajen Ammi gobe" Mayraah ta kallesa a hankali tace "Kaga su sai su ga kamar we are Husband and wife, na fasa ma zuwa gidan" Dariyar da bai shirya yi ba yayi, yace "Kamar yaya kin fasa?" Sunkuyar da kanta tayi, yana murmushi yace "To amma ai ni da ke mun san we are not husband and wife, So why bother ur self?" Cikin sanyin murya tace "To ai mu kadai muka san haka, su kuma baza su taɓa sanin haka ba, ni fa yaya i see this more like an abomination and i don't know why others are seeing it to be normal, may be because they are not in our shoes" Maheer ya gyada kai, calmly yace "Abomination din ne ma" daga manyan idonta tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Ki fito ku gais" Kwanciya tayi gefen gadonta ta juya masa baya a hankali tace "Ni dai kawai kace masa ina bacci, i can't" Shiru yayi yana kallonta, jin shirun yayi yawa ta juya ta kallesa, sauke kansa yayi ya juya ya fita daga dakin, haka nan taki fita zuwa gun Omar don ita gani take za su dinga tunanin ai ita da Maheer yanzu mata da miji ne, that tot alone ba karamin daga mata hankali yake ba. Bayan magrib Mayraah ta shirya kamar yanda Maheer ya ce mata, ta fito parlor tana kallonsa, Hijab ne har kasa jikinta, ya kalleta yace "Can we" Ta gyada masa kai tana karasowa cikin parlon, kallon kafarta yake yace "Is it paining you Mimi, naga kamr you are limping?" Ta girgiza masa kai tace "Aa ba sosai ba, i am fine" Mikewa yayi ya dau makullin motarsa don dama ita yake ta jira, ya nufi kofa tana biye da shi, sai da ya fara bude mata kofa ta fita sannan shi ma ya fita ya kulle gidan, yace "Mimi dingishi fa kike" Ta langwabar da kai tace "Nace maka zae daina fa yayaaa" A haka suka bar gidan mai gadi yayi masu Allah ya tsare, wani babban shopping Mall Maheer ya kai su, bayan yayi parking sun sauka a motar duk da yanda kafarta ke ciwo haka ta dake tana tafiya a hankali zuwa cikin mall din don kar ya sake mata maganar kafar, cart ya dauka ta amsa a hannunsa tana turawa yana biye da ita ta fara daukan abubuwan da take so, shi dai bin ta kawai yake duk inda tayi idonsa na kanta, ta saki cart din ta tafi zata dau pack din wani chocolate ta juya don tambayarsa ko shima yana so ta daukar masa, kallonta taga yana yi baya ko kiftawa, gani yayi ta kara wani haske tayi kyau sosai, sai glowing take, nan kuma duk gyaran jikin da aka mata a kaduna ne, yana ganin ta juyo lkci daya yace "Oh ok, you want the chocolate?" Ta nufesa tace "In daukar maka Yaya?" Kai kawai ya gyada mata ta juya ta koma wajen, bin ta yayi da kallo sai kuma ya dauke idonsa tun kan ta sake juyowa, bayan ta debi chocolates din zata tura cart din suka ji ance "Maheer" Juyawa suka yi a tare, wata mace ce ta nufo su tana masa kallon mamaki, Maheer ya ɗan buda ido yace "Zeenat" Zeenat tace "OMG Maheer, I can't believe my eyes, is this really you" Yana murmushi yace "Ashe kina Nigeria dama Zeenat" Tace "Ai ni nafi shekara uku a Nigeria yanzu, ya kwana da yawa Maheer? ya bayan saduwa?" Yace "Alhamdulillah" Kallon Mayraah dake kallonta tayi sai kuma da sauri tace "Sorry matar ka kenan Maheer?" Maheer ya kalli Mayraah yana murmushi ya girgiza kai yace "Aa, kanwata ce wannan, her name is Mayraah" Mayraah ta daga kai tana kallonsa, Zeenat tace "Waow maa sha Allah, ai kam gashi naga kuna kama sosai, har dai nose dinku iri daya" Yace "Yeah, autan Ammin mu ce" Zeenat na murmushi tace "Hi Mayraah?" Mayraah ta kalleta kamar bazata ce komai ba sai kuma can ciki tace "Hello" Zeenat tace "My name is Zeenat Abubakar, mun yi karatun Degree tare da Maheer, kin ga yayan nan naki sam baya zumunci, duk yayi watsi da mu wllh, ko an masa magana ta Whatsapp no reply, layinsa kuma ina jin ya rufe ne..." Mayraah dai tayi murmushin da iyakarsa lips bata ce mata komai ba, can ta ci gaba da daukan abubuwan ta tana sakawa a cikin cart a hankali, Zeenat ta kalli Maheer tace "Maheer kar dai kace min har yanzu baka yi aure ba?" Yace "Ban yi ba, ko za ki samar min budurwa that is ready for marriage" Mayraah ta juya ta kallesa, Zeenat tayi dariya tace "Kai haba dai, nima kaga har yanzu ban yi auren ba" Yace "Allah sarki" Er dariya tayi tace "Wa ya sani ko juna muke jira all this while" Maheer couldn't help it but laugh, kamar yanda ita ma take dariya tana kallonsa, Mayraah dai tsayawa tayi tana kallonsu da chocolate a hannunta, Maheer yace "To ke ya kika ga" Zeenat ta ɗan buda ido, calmly tace "Kawai memories ke dawo min kamar ba mu yi rayuwa tare ba Maheer, wa zai ce ko ta Whatsapp za mu daina magana, abun da mamaki" Yace "Ba ni da number ki gaskiya yanzu" Tace "Ai ko ni ina da naka, kwanaki can da dadewa nayi pinging dinka via WhatsApp but no reply, bari ma ka ga" Jakarta ta bude ta ciro wayarta ta shiga contact ta fiddo number dinsa ta nuna masa, Mayraah ta dinga kallonta, Maheer yace "Yeah, that's my number Zeenat, ki kirani sai inyi saving number dinki yanzu...." Mayraah ta ajiye chocolate din hannunta da kyar tace "Yaya kafana ciwo yake min, na gaji i have shop enough....." Maheer ya kalleta yace "Ohk Mimi, za mu tafi yanzu in sha Allah" Zeenat tace "Ayya sannu Mimi...." Dialing number Maheer tayi, ya ciro wayarsa a aljihu yana kallon number nata bayan ya shigo wayarsa yace "I will save right away Zeenat" Nan take yayi saving number nata, a hankali tace "So a Abuja kake aiki kenan?" Yace "Yea nan nake aiki" Tace "As a medical Dr?" Tuni Mayraah ta bar wajen ta bar masa cart din gaba daya, Maheer ya bi ta da kallo sannan ya kalli Zeenat yace "We will talk on phone Zeenat, my sis is sick, za mu tafi gida" A hankali Zeenat tace "Allah sarki to ba damuwa Maheer, am so happy to meet u again after many years, you look more handsome and matured now...." Murmushi kawai yayi yace "Za mu yi waya" Daga haka ya bar ta wajen yana tura cart din da Mimi ta bar masa, Zeenat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, Maheer na isa counter ya biya kudi, ga mamakinsa bai ga Mayraah a cikin mall din ba gaba daya, workers din wajen suka dau siyayyan da ya biya suka kai masa har bakin motar sa, tsaye ya ganta jikin motar ta rungume hannu, yace "Ina ta dubaki ashe kina nan Mimi" Ko kallonsa bata yi ba balle ta basa amsa, bayan an saka masa siyayyan a booth din mota ya duba aljihunsa ya ciro kudi ya basu yana masu godiya, Mayraah ta bude back seat ta shiga ta zauna ta kulle, shi dai bai ce mata komai ba ya zaga ya shiga driver seat suka bar haraban mall din, a hanya yace "Sosai kafar ke ciwo Mimi?" Kyalesa tayi, hakan yasa bai sake ce mata komai ba har suka iso gida, sai a snn ya kunna wutan motar ya juya yana kallonta, hawaye ya gani idonta, da mamaki ya sauka daga motar ya dawo back seat yace "Mimi what happened?" Cikin kuka tace "Ni dai kafata ciwo take min, ka daina tambayata what happened" Yace "Subhanallah,

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login