Showing 318001 words to 321000 words out of 456519 words

Chapter 107 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70699

anyi biki" Alhaji Saminu yace "Kwarai kuwa sati biyu, Allah ya kai mu lokacin lafiya, mun gode kwarai da karamci Allah ya saka da alkhairi" Alhaji yace "To yanzu Kadunan za ayi taron bikin ko ya ku ke son za ayi?" Alhaji Saminu yace "Ai duk yanda ku ka tsara dai dai ne Alhaji, mu ai kun gama mana komai" Abba yace "To in sha Allah za mu yi waya" A haka suka rabu da Abba ya koma cikin gida. Bayan tafiyar Alhaji Saminu su Hajiya Ramatu da Mami duk suka shirya za su bi train zuwa kaduna, tare za su koma Kaduna da Mama Ladi zata je sanar ma su Hajja Mayraah dai an mata aure duk su tarkato su dawo Abuja biki nan da sati biyu, Ammi ta so su Hajiya Ramatu su kwana amma suka ce ai har an siya ticket, Ammi dake murmushi tace "Bari in taso Mayraahn ku yi sallama ina ga bacci take" Mama Ladi tayi karaf tace "Su da za a kai masu ita har kadunan ma meye kuma sai an taso ta, ai kawai bari mu tafi kar jirgin ya tafi ba mu" Hajiya Ramatu tayi murmushi tace "Haka ne Mama a bar ta tayi baccinta kawai" Ita dai Mami murmushi kawai take.... Karfe biyar saura Mayraah taji ana tashinta a baccin da ya dauketa parlon Abba kusa da Mahaifinta, bude ido tayi a hankali ta mike zaune tana bin parlon da kallo ganin bata ga Mom dinta ba balle Baban nata, Ammi na kallonta a hankali tace "Baki yi sallah ba, tashi mu je kiyi" Mikewa tayi tsaye Ammi ta kama hannunta suka fita daga parlon, kasa tambayar Ammi tayi ina mom dinta bayan sun koma can bangaren taga wayam ba kowa, a haka dai taje tayi alwala, bayan ta idar da sallahn ta juya tana kallon Ammi dake zaune tayi nisa cikin tunanin da take, mikewa tayi ta koma kusa da Ammi ta zauna a hankali tace "Ammi sun tafi ne?" Ammi ta mata murmushi tana shafa eyebrow dinta wanda baza ace ba zana mata shi aka yi ba a hankali tace "Duk sun tafi kina bacci Mimi" Mayraah tayi shiru tana kallon Ammi, she is just wondering why Ammi isn't saying anything to her har yanzu, Ammi ta sauke idonta tace "Abincin dazu ma baki ci ba, bari in kawo maki wani ki ci" Bude kofar parlon aka yi duk suka juya, Maheer ne ya shigo parlon, Ammi ta maida dubanta kan Mayraah tace "Let me get the food for you daughter" Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita, Mayraah ta kalli Maheer da ya zauna kan kujera ya ciro wayarsa ba tare da ya kalleta ba, mikewa tayi ta nufesa tayi relaxing jikin kujeran da yake zaune tana kallonsa tace "Yaya" Ya daga kai ya kalleta yace "Mimi" Ganin yanda idonta ya kumbura yace "Kuka kike ta yi kenan?" Ta bata fuska zata fara wani sabon kukan ya mike ganin fita zai yi ta riko hannunsa da sauri cikin rawan murya tace "Yaya ba fa wanda yake son yace min komai har yanzu...." Ya juya ya kalleta yace "Me kike son ace maki Mimi?" Hawaye na sauka idonta tayi shiru tana kallonsa, ya juyo gaba daya yana facing dinta, ganin yanda hawaye ke sauka idonta ya kai finger dinsa yana goge mata hawayen a hankali yana kallonta, ta fashe masa da kuka sosai, ya sauke idanuwansa, sai kuma rungumeta a hankali yana patting bayanta slowly amma ya rasa abinda zai ce mata yana jin kukan nata har cikin ransa, bude kofar parlon aka yi ya saketa da sauri ya koma baya amma tuni Aunty Mariya ta shigo, tayi masu kallo daya ta tafi ta dau abinda zata dauka, daga shi har ita basu yarda sun kalleta ba, ita dai ta fita daga parlon, Juyawa Maheer yayi ya nufi kofa Mayraah ta bi sa da kallo har ya fita daga parlon, zaunawa kasa tayi ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka. Mayraah na zaune parlon Abba bayan magrib bayan Ammi taje ta taho da ita daga bangarenta, banda faduwa babu abinda gabanta yake a inda take zaune duk ta takure waje daya, Abba na kallonta ya nuna mata kusa da shi, ta mike a hankali ta nufesa ta zauna kasan carpet kusa da shi, Bundle din kudin da ta gani gefensa ya kara distablizing dinta gaba daya a parlon ta kalli Usman da Maheer dake zaune kasan carpet waje daya su ma, sai Ammi dake zaune one sitter, babu abinda ya fado ranta sai ranan da Abba ya tara su Parlonsa a kano bayan an kawo kudin aurenta da Musharraf, bayan few seconds Abba ya sauke ajiyar zuciya ya dau bundle din kudin yana kallon Maheer calmly yace "Maheer ga wannan ka ajiye a account dinka" Maheer ya daga kansa dake kasa yana kallon Abban nasa, don wannan shine exact kalmar da yayi masa ranan da aka fara kawo kudin Auren Mayraah da Musharraf, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta hawaye cike idonta, a hankali ya mike ya nufi Abba ya amshi kudin, Ammi dai sai kallonsa take har ya koma ya zauna, Abba yace "Ko ba yanzu ba wani lokaci sai ka tambayeta abinda zata yi da kudin kayi mata, be it in future...." Mayraah ta daga kai ta kalli Abba, sai kuma ta kalli Maheer da yayi shiru bai ce komai ba unlike wancan lokacin da sai da ya tsokaneta ma, murya Abba ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, calmly yace "Mimi" Ta daga kai a hankali ta kallesa, sai kuma ta sunkuyar da kai zuciyarta na bugawa sosai, Abba yace "Kinsan a rayuwar nan bazan yi abinda zai cuce ki ba, a kaf fadin duniyar nan wanda yasan zafinki bayan mahaifiyar da ta haifeki to a bayan ni da Amminki da brothers dinki yake" Mayraah dai ta kasa dago kanta tana sauraron Abba, Abba ya nisa yace "Nasan kuma ko ba a wannan moment din ba cause i believe u might be taken unaware, but wataran zaki yi alfahari da abun nan da na maki, one day one time in sha Allah u will be proud of this, i am quite sure Maheer will be their for you till death do u both apart, he will make a great partner, you have him as a brother and Husband now" a hankali Mayraah ta daga kai tana kallon Abba, can ta juya da sauri ta kalli Maheer that was looking at a different direction, ta kalli Usman da ya ɗan mata murmushi, ta kalli Ammi da hawaye ke zuba idonta, muryan Abba ta sake ji tsakiyar kanta, calmly yace "Allah Ubangiji ya maku albarka, ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba" Mikewa Ammi tayi ta karasa ta daga Mayraah that was soo shock ta fita da ita daga parlon.
[9/10, 7:33 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah na kwance dakin Ammi wajen karfe biyun dare a exact position din da ta kwanta tun karfe taran dare, ko motsin kirki bata yi a inda take kwance, kuma tun da ta kwanta ko gyangyadi bata ji ba idonta a bushe yake, ashe a baya duk ba tashin hankali ta shiga ba yanzu ne take jin ta cikin asalin tashin hankali wanda baya mitsaltuwa, gashi ko digon hawaye ya ki zubo mata ko zata dan ji sanyi a ranta, har a sannan kuma maganganun Abba sun kasa daina yawo a kunnenta, ko tsabar shock din ne yasa ta nemi hawaye ta rasa ita kanta ta kasa ganewa, a hankali ta juya ta kalli Ammi dake daya side din tana bacci, ko da Ammi ta shigo zata kwanta dazu wajen karfe sha daya pretending tayi tana bacci don kulle ido tayi, a hankali ta mike zaune ta sauke kafafuwanta daga saman gadon, sosai taji kanta yayi mata nauyi ga wani ciwo da kanta yake mata, ita tayi mamakin ma da Asthma dinta bai tashi ba yau, Ammi ta juya tana kallonta don slightest motsi ke farkar da ita bacci ta dau wayarta ta kunna fitila, da sauri Mayraah ta fara murza ido kamar a lkcn ta farka, Ammi ta mike zaune tace "Ya aka yi daughter? Kina son wani abu ne?" Bata san sanda ta girgiza kai tace "Ruwa zan sha" Sai kuma ta mike tsaye da kyar tana jin kamar jiri na dibanta, Ammi ta kunna wutan dakin tace "To ki duba parlor ko akwai ruwan, Allah ya sa Bilkisu ta kawo ruwan dazu" Mayraah ta nufi kofa ta fita daga dakin, a hankali tayi switching fitilar parlon tana bin ko ina da kallo, amma tunanin da ya tsaya mata a rai daban, muryar Ammi taji a bayanta tace "Kin samu ruwan" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Zan je in dauko yanzu" Daga haka ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo, bayan ta fita Ammi ta bi bayanta ta bude kofar parlon, Mayraah na jin Ammi ta bude kofa ta nufi downstairs da sauri don da tsayuwa tayi ta jingina da bango a corridor din zuciyarta na bugawa, Tana sauka downstairs gabanta yayi mugun faduwa ganin Maheer zaune duk da ya rage fitilun parlon hasken ba sosai bane a parlon, gaba daya ta daburce ta rasa abinda zata yi don in ta koma sama tasan kilan su hadu da Ammi gashi bata dauko ruwan da tace zata sha a fridge ba, mikewa yayi yana kallonta, sai kuma ya nufeta, tana ganin haka ta wani hade ran da bata taba yi masa irinsa ba ta zagaya ta daya side din parlon ta nufi kitchen tana tafiya da sauri, tsayawa yayi ya bi ta da kallo, ba a dau lokaci ba sai gashi ta dawo rike da goran ruwa nan ma tana tafiya kamar zata tashi ta wuce sama fuska daure, komawa yayi ya zauna. Sai a sannan hawaye ya cika idon Mayraah taji suna gangarowa fuskarta, taji zuciyarta na mata wani irin zafi, da sauri ta goge idon ta nufi bangaren Ammi. Haka nan ta sha ruwan da bata yi niyya ba ta koma ta kwanta Ammi ta rufa mata duvet saboda dakin da sanyi, har aka kira asuba Mayraah ko bacci barawo bai saceta ba bakin ciki da takaici ne kawai cike fal zuciyarta, ana tada sallah a masallaci Ammi ta tasheta tayi sallah, tana idar da sallahn bayan ta gama azkar dinta ta kalli Ammi a hankali ta gaisheta, Ammi dake saman darduma ita ma da carbi a hannunta ta amsa cikin sanyin murya tace "How was ur night dear?" Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "Alhamdulillah" Mayraah tayi nisa tunanin da take zaune kan darduma taji sallamarsa bakin kofar dakin sosai gabanta ya fadi, Ammi ta amsa masa ya shigo dakin ya zauna as usual kamar yanda ya saba duk asuba yace "Ina kwana Ammi?" Ammi na kallonsa tace "Lafiya lau, an tashi lafiya?" Ya sauke kansa yace "Alhamdulillah" Ammi bata sake cewa komai ba shi ma haka, Mayraah dai kanta na kasa kamar sabuwar amaryar da aka kai daki, shi dai bai kalli inda take ba balle ya kalleta, bayan few minutes ya mike ya nufi kofa ya fita Ammi ta bi sa da kallo, sannan ta kalli Mayraah, amma bata dai ce komai ba, bayan fitarsa da wasu yan mintuna Ammi ta sake kallon Mayraah da taki dago kai, a hankali tace "Mimi baza ki kwanta ba" Mayraah ta dago kanta amma bata bari sun hada ido ba ta mike daga kan darduman cikin rashin kuzari ta linke darduman ta ajiyesa inda sauran suke sannan ta tafi ta kwanta saman gado ta rufa da duvet, hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta ta rufe bakinta da sauri don kar ma ta fashe da kukan, bata taba tunanin akwai rana irin yau da zai risketa a rayuwarta ba, how on earth will this happen to her? Ya Maheer fa? Ji take dama ta mutu kawai ta huta, kuka sosai tayi cikin Blanket din duk Ammi dake zaune kan darduma bata sani ba, sai wajen karfe bakwai na safe bacci ya dauketa bayan da zuciyarta ya dameta da ciwo. Karfe goman safe Mayraah na zaune parlon Ammi bayan tayi wanka ta shirya cikin kayan da Ammi ta dauko mata a dakinta, gabanta kuma breakfast ne da Bilkisu ta kawo mata sai juya tea spoon din cikin shayi take absentmindedly, ko appetite din cin abincin ma bata da shi, zuciyarta a tunkushe yake ta rasa inda zata sa ranta taji dadi, Ammi dake zaune parlon duk tana lura da ita amma ta kasa ce mata komai sai kallonta kawai take, ita ma duk jikinta yayi sanyi, Mayraah kam bata ma san tana kallon nata ba tayi nisa tunanin da take, bude kofar parlon aka yi gaban Mayraah ya fadi sosai duk da bata san wanda ya shigo ba don bata dago kanta ba, Ammi dai kallonsu kawai take har suka karaso suka zauna a Parlon, Usman dake kallon Mayraah yace "Sai yanzu kike breakfast Madam" Ta dan daga kai ta kallesa tayi murmushin karfin hali a hankali tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau Mimi, how was your night?" Ta sunkuyar da kanta tace "Alhamdulillah" Satan kallon Maheer tayi suka hada ido tayi saurin dauke idonta shi dai ya ci gaba da danna wayarsa, can ta kalli Ammi a hankali tace "Ammi zan je dakina in ci abincin" Ammi tace "Ohk but make sure you eat much pls Mimi" Mayraah ta gyada mata kai sannan ta mike ta dau breakfast din nata, tashi Usman yayi ya bude mata kofar parlon saboda duk hannunta is occupied, ta dan yi murmushi cikin sanyin murya tace "Nagode yaya" Daga haka ta fita daga parlon sannan ya kulle kofar, dawowa yayi ya zauna yana kallon Ammi yace "Ammi can you hear Maheer?" Ammi ta kalli Maheer dake danna wayarsa tace "Kamar ya?" Usman yace "Wai Abba zai sama yace masa shi a basa izinin warware aurensu da Mimi, just like child's play" Ammi ta juya tana kallon Maheer with mouth open cike da mamaki, shi dai bai daga kansa ba, Ammi tace "Maheer" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, a hankali tace "Duk maganar da na maka baka ji ba kenan Maheer?" Maheer ya sauke idonsa yace "Ammi tun farko ni fa babu wanda yayi shawara...." Katse sa Ammi tayi don tun jiya take fama da shi har ta gaji da magana, a takaice tace "Toh shikenan, kaje ka samu Abban naka, do what suits you" Maheer dake kallonta yayi kasa da murya yace "Ammi ba ina nufin naki hukuncin nan da Abba yayi bane, i don't mean to be disrespectful or disgrace him in anyway, but ina son a dinga yi ana considering Mimi too, she should be place into consideration too, ni ko da ba a gaya min ba ita da an tuntubeta tukun, it will look as if dole aka mata, this is something i never saw coming Ammi..." Ammi ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Maheer, kai ne zaka koya mata zama da kai as partner, beside you two have this bond that i can't even explain, shi yasa kwanaki kaga har na kawo maka maganar da asuba wanda a wancan lokacin ma u were a bit reluctant...." Maheer ya sauke idonsa yace "Ammi this is something that came unexpected, so it will be difficult for me and her, but ban san ko tana tunanin ni nace Abba ya bani aurenta ba" Ammi tayi shiru ta ma rasa abinda zata ce, Usman dake ta sauraronsu ya dan yi murmushi yace "As time goes on, all this shall become history" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa, bayan ya fita Ammi ta kalli Maheer a hankali tace "You have to be patient son, kayi hakuri, dama nasan da farko dole za a fuskanci hakan, but it's just a matter of time, she will learn to accept you soon, kai ma zaka yi accepting dinta as ur wife...." Yace "I am not talking about My self Ammi don ni ban taba tunanin abubuwa za su juye haka ba daga karshe, kawai ni i am after her own feeling, ina ga kamar ba a mata adalci ba since duk mun san abinda take so...." Ammi tace "Amma dai kamar baka parlon Ceo tayi magana akan abinda Musharraf din yace, sannan ita ma Mimin baka ji abinda tace bane" Maheer ya gyara zamansa yace "After all, she is just 22 years, da an bata space da batun aure for now" Ammi dai kallonsa kawai take, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita. Usman na isa kofar dakin Mayraah yayi knocking sannan ya shiga ciki da sallama, har sannan bata fara shan shayin ba ta daga idanuwanta da suka yi ja alamar kuka take tana kallonsa, karasawa cikin dakin yayi yana kallonta cikin kwantar da murya yace "Lets talk Mimi, tell me what ur problem is about Abba's decision?" Ta fashe da matsanancin kuka tace "Yaya wallahi ni dai bana sonsa, imagine fa yaya, wanda nake ma kallon yayana na jini ta ya za ace an mana aure da shi? Why will he tell Abba yana son ya aureni? dama ba kallon kanwarsa yake min ba?" Usman ya dan buda ido yace "Wa yace maki shi yace yana so ya aureki?" Ta kara fashewa da kuka tace "Abba bazai taba yin haka ba idan ba shine yace ba, Abba will never think of this, me yasa bai yi tunanin ni little sis dinsa bace da har zai ce zai aureni, yanzu kenan da gaske ni ba kanwarku bace?" Usman yayi kasa da murya yace "Look Mayraah, ba shi yace ma Abba zai aureki ba, hasalima he was taken unaware too, Billah Dr bai san da batun nan ba kinji na rantse maki, kawai baya son yi ma Abba musu a gaban Dad dinki da Grandpa dinki kuma nasan da tun farko ya sani kafin ayi zaman nan bazai amince ba" Ita dai kuka kawai take don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata yarda bai sani ba, muryarta

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login