Showing 375001 words to 378000 words out of 456519 words
masu a jiki ba, hankalin Ammi ma yafi nawa tashi, wajen duk yayi jan taɓo alamar ƙuna dama ga su farare sol, ai kuwa muka sa muguwar a gaba ta fada mana abinda tayi ma yaran in gaya maka shaidaniyar ba sai ta sakar mana kuka ba wai ta yaya zata cutar da yaran da ta haifa a cikinta, to wai ma wanda yayi niyyar kashe mutum menene ma bazai yi ba Mashir? Tsaf haushinmu da take ji zai sa ta kashe yaran nan biyu mu shiga uku wallahi, sam babu imani a tattare da lamarinta, sabili da hakan nace ma Ammi tun da sauran mutuncinmu a idonta mu dauketa mu maida ta gida gun iyayenta, yaran kuma a bar su gun Ammi ta dinga basu madaran jarirai, ga madaran ma har an siyo za su saba da shi a hankali, in sun yi wayo kuma a daukesu a ba Mera ta rike maka su, wannan shine kawai mafitar mu, yanzu haka Mamuda nake jira..." Mayraah dai kallon Maheer dake kallon Mama Ladi kawai take, Mama Ladi ta kalleta tace "Wallahi Mera da ya zo da safe shi da uwarsa cewa suka yi na toye yaran da ruwan zafi wajen wanka, abun ya min ciwo sosai don sai da nayi kukan bakin ciki suka sa abincin da nake ci ya fita raina" Maheer na kallon gadon yaran dake parlor ga kuma gwangwanin madara da Feeders yace "Ina yaran suke yanzu?" Mama Ladi ta gyara zama tace "Ahaf, shi fa jini mugun abu ne Mashir, dazun nan Ammi ta fita a gigice da dreba bayan taga taɓon jikinsa ta je babban shago ta siyo masu madara me shegen tsada, wai aka kada madaran a feeder da ruwan zafi aka ba yaran nan suka ki sha, sai tsala mana ihu suke a parlon nan, banda sun kwaso munafurci da mugun halin uwarsu yaushe aka haifesu da za su iya banbance Nono da madaran kanti? In gaya maka haka suka kunyata mu tsamo tsamo yanda uwar zata ji dadin mana dariya, dole dai muka sa Bilki ta kai ma uwar ta basu Nono, tun da aka shiga da su tsit kake ji, to tun fa ba aje ko ina ba kenan sun iya munafurci da makirci" Shi dai Maheer shiru yayi bai ce komai ba yana kallon formula din da Ammi ta siyo masu, after a while ya sauke ajiyar zuciya, ya ɗan kalli Mayraah dake kallonsa, sauke kansa yayi ya zauna kan kujera, Mama Ladi ta kalli Mayraah tace "Tashi ki shiga dakin ki dauko masa yaran daya bayan daya" Mayraah bata ce mata komai ba kuma bata tashi ba, Mama Ladi ta rike haɓa, can tace "Ba shakka" Sai kuma ta kalli Maheer tace "Haka fa dazu nace taje dakin ta dubo min wayana sai yarinyar nan Bilkisu ce taje ta dubo min, ilai nayi alwala zan yi magariba nace taje ta dauko min shijabi na da na bari a dakin inyi sallah amma yarinyar nan taki tashi tayi kamar bata ji me nace bata, kai ko ta ga tayi aure ta shigo layin manya tasan komai, bari ta sabunta rashin kunyanta...." A hankali Mayraah ta mike tsaye fuskarta babu walwala, ko kadan bata son Mama Ladi na aiken ta dakin nan, babu yanda ta iya tana tafiya a hankali ta nufi hanyar dakin, Mama Ladi tace "Kawai don dai kakanki Alhaji Saminu mutumin kirki ne kuma ina jin kunyarsa amma da wallahi kema tattara lamarinki zan yi in watsar a kwandon shara, naga kamar tsohon halin Badiyyah kike son ara ki yafa a kanki, ita kuma ga ta can ta koma sak ke lkcn da kike budurwa, Badiyyah ta dawo ba sawa ba hanawa gwanin ban sha'awa, duk tayi sanyi ta dawo mutuniyar kirki sallah baya wuceta, har na fara mata sha'awar Usuman, ina ta son ya dawo in samesa mu yi shawara" Maheer bai san sanda ya juya da sauri ya kalli Mama Ladi ba, dariya sosai ta basa, ita dai ta ci gaba da cin abincin ta, Mayraah na shiga dakin da Haseenah da twins dinta suke, Haseenah ta wani kalleta fuskar nan nata a daure, Bilkisu dai na zaune a dakin bayan Ammi ta umarceta ta zauna tun sanda ta shigo da su Haseenah ta basu Nono, sau uku Haseenah na attempting koranta daga dakin amma cikin dubara, Bilkisu da ta ganota taki fita tunda ga abinda Ammi ta ce mata, Mayraah bata ko kalli Haseenah ba ta nufi gun babies din dake kwance kan gado, tun kan ta dauki wanda ke gabanta Haseenah ta daukesa da sauri fuskarta a murtuke tana kallonta a walakance tace "Ke kika haifa min su? Kema ki haifi naki gobe mana in gani" Bilkisu dai sake baki tayi tana kallon ikon Allah, Haseenah ta ja wani dogon tsaki ta jawo daya babyn ma, Mayraah ta gyara tsayuwa tana mata kallon cikin ido tace "Kema naga ai ba daga zuwa kika haifesu ba, me kike ci na baka na zuba? in my own case daga ni har jaririn uban zai so tamkar rayuwarsa, gata kuwa sai wanda aka manta ne baza a mana ba, unlike you da ake maki favor just because of the babies, tsabar rashin gata irin naki har yau ban ga ko mutum daya daga familynki ya zo maki barka ba, ko akuya ce ta haihu ai sai haka....." Mayraah na kai wa nan ta ja tsaki ta jefa mata wani harara tace "Aikin banza kawai" Daga haka ta juya ta nufi kofa ta bar Haseenah da ta buda baki tana kallonta babu ko kiftawa, Mama Ladi ta juya tana kallon Mayraah tace "Ji jaraba... ina yaran da nace ki dauko?" Mayraah tace "Cewa tayi ba wani ya haifa mata su ba ai" Mama Ladi ta mayar da kwanon abincinta gefe da sauri, har wani ɓari jikinta yake ta mike tace "Mu je" shi dai Maheer kallon Mayraah da ta wani yatsine fuska yake, Mama Ladi na shiga dakin tana huci tace "Shegiya kawai me baƙar aniya, wato don kin samu an ɗosana ki gidan nan saboda albarkacin yaran nan shine har kika samu bakin magana ko? to wallahi ko kwana bakwan baza ki yi ba ni da kaina zan san abinda na gaya ma Mamuda aje tasha a maki shatan mota ki koma can gaban iyayenki tunda ba mu muka haife ki ba kuma babu abinda muka hada dake, su da suke dolenki ma sun guje ki balle mu karere? yara kuma kina ji kina gani Mera ce zata rikesu don mu ba yan iska bane da za mu bar maki yaranmu rayuwarsu ya gurbace mu shiga uku, nononki kadai ma bala'i ne gare yaran nan, banda kaddara me zai sa a hada iri dake Hasinu? matar da tayi yunkurin kashe mutum duk duniya an shaida, to ahir dinki wallahi, zuwa gobe in sha Allah kina hanyar kano" Ammi da hayaniyar Mama Ladi ya sa ta sakko tana tsaye kusa da stairs bata karaso cikin parlon ba duk tana jin me Mama Ladi ke cewa, Mama Ladi ta kwalo ma Mayraah kira tace "Maza zo ki kwaso yaran ubansu ya gansu" Mayraah ta shiga dakin ta dau yaron daya ta fito Mama Ladi ta dau dayan yaron tana cewa "Er iskar mata kawai iblishiya, kin zata Meran a banza take har yanzu ko, to da ne kika santa a banza amma yanzu kam da gatan ta kaca kaca, kije ki tambayi ubanki wanene Alhaji saminu a kaf Najeriya, to jikarsa ce Mera, shi ya haifi ubanta Abdallah, tun asali da Alhaji Saminu ya samu labarin guban da kika sa ma jikarsa a abinci ta ci ai a kasar waje za a yanke maki hukuncin rai da rai... ina za mu sa kan mu in wa ennan jariran suka yo halinki, astagfirullah ai da sai ince mutuwarsu ya fi da dai su yi halinki" Haseenah dai kanta na kasa tana jin duk abinda Mama Ladi ke cewa, Mayraah na dawowa parlon ta nufi Maheer fuskarta daure tana mika masa Babyn hannunta, shi dai kallonta kawai yake at the same time yana kallon Babyn hannunta, deep down him he wish ita ce ta haifo masa cute babies din nan, lumshe ido yayi ya bude still looking at her and the baby, ganin ya ki amsan babyn ta daga kai ta kallesa har sannan fuskarta a daure, sarai yasan dalilin daure fuskar nan da take yi, ya ɗan kalli direction din da Ammi take tsaye yaga kallonsu kawai take, sunkuyar da kansa yayi ya amshi jaririn da Mayraah ke mika masa, Ammi kuwa tuni ta haura sama. Bayan isha Abba ya shigo gidan tare da Usman, sai kuma Maheer da suka hadu bakin gate bayan ya dawo masallaci, a tare suka shigo parlon gaba daya, sai da Abba ya zauna ya gaida Mama Ladi dake rike da jariri daya a parlon, Ammi ma na zaune rike da daya twin din tayi masa sannu da zuwa, Abba yace "Ya aka kashe Ac, bakwa jin zafi ne?" Mama Ladi ta mike ta ba Abba yaron hannunta ya amsa, tace "Kai baka ga yan yaran nan ba, in aka kunna masu Ac ai sai su mutu don sanyi mu shiga uku, dama tun dazu saboda kai nake ta zaune parlon nan, don nasan tunda na ci abinci na koshi ina kishingida bacci zan yi" Abba na kallonta yace "To Allah dai yasa lafiya Mama" Mama Ladi tace "Aa in kaje parlon ka, ka gama duk abinda zaka yi sai inje can in sameka mu yi magana a tsanake" Abba yace "Toh ba damuwa" Mikewa Ammi tayi ta mika ma Usman babyn hannunta ta wuce sama, Abba ya kalli Maheer yace "Ina Mimi fa?" Mama Ladi tayi karaf tace "Tana can kitchen tana hada ma mijinta abinci, tun bayan la'asar take gidan nan yau" Usman dai yayi murmushi, ya mike ya ba Mama Ladi Babyn dake hannunsa, ta amshesa ta kwantar da shi kan gadonsa, Abba yace "Nan kuma aka dawo da su?" Mama Ladi ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tace "Da dalili babba Mamuda, ba haka kawai aka kwaso su aka fito da su ba, kai dai in ka sahirta ko Ammi ka aiko ta sanar min, amma kafin nan don Allah taso ka ga jikin yaran nan" Mikewa Abba yayi ya tafi inda suke kwance, Shi dai Usman kallon yaran kawai yake, Mama Ladi ta bude masu jikin yaran, Abba ya duka yana kallonsu da kyau, haka ma Usman, Mama Ladi tace "Me ku ka gani?" Usman yace "Meye wannan din?" Mama Ladi tace "Dubawa zaka yi da kyau" Kunna fitilar wayarsa yayi yana haska jikin babies din, Abba yace "Konewa suka yi ne?" Mama Ladi tayi kwafa tace "Alhamdulillah, to in gaya maka Mamuda daga mun je kasuwa da Ammi muka dawo muka tarar da jikin yaran nan a haka suna ta tsala ihu zar tausayi, kuma daga su sai uwar muka bari a gidan nan don yarinyar nan Bilkisu girki muka bar ta tayi a kitchen, har yanzu mun rasa gane da me tayi masu wannan izaya a jiki haka, mun tisata a gaba ni da Ammi taki fada" Abba ya juya ya kalli Maheer, Mama Ladi tace "Meye kake wani kallon Mashir ina maka maganar arziki, wannan solobiyon me kake ga zai iya yi? Ai ko bin ta kansa ban yi ba kai kawai nake jira kai me sa Usuman ya wanketa a kotu" Abba yayi shiru sai kallon jikin yaran yake haka ma Usman, Mama Ladi tace "Ka je dai ka huta gani nan zuwa" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh Allah ya kyauta" Daga haka ya juya ya wuce sama, Usman yace "Kuma kun tabbatar ita din tayi masu haka a jiki?" Mama Ladi tace "Aa karya ni da uwarka Hajara muka mata" Usman ya juya ya bar parlon zuwa dakinsa, Maheer dake kallon Mama Ladi yace "Baki masa maganar Badiyyar ba kuma" Da sauri Mama Ladi ta kallesa tayi kasa da murya tace "Kai kuma baka san wasa ba" Shiru Abba yayi yana sauraron Mama Ladi dake zaune a Parlonsa attentively, har dai ta kai aya, sai kuma ta kara da cewa "Sabili da haka gobe da asuba sai mu je da Usuman tasha ayi shatar golf, tana baya ni ina gaba don bazan ma zauna waje daya da ita ba, muna isa garin Kaduna mu tsaya mu dau Mariya sannan mu karasa kano, in ma iyayen sun dubi Allah sun hakura oho, in ma basu hakura ba oho mu dai mun kai ta mun kuma nuna mu manyan mutane ne, idan sun so bayan tafiyar mu su sake korata ta shiga duniya ba ruwanmu" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Shawara ce me kyau Mama, amma kuma abinda bai min ba a duk bayanin nan naki shine da kika ce za a bar yaran nan wajen Ammi, ta yaya za a raba jariran nan da uwarsu, jariran da ko sati daya basu yi ba, ni a ganina hakan bai kamata ba, tamkar an shiga haƙƙinta ne da ma na yaran" Mama Ladi ta katse sa da sauri tace "Wai halan baka ga fatar jikin yaran nan bane da na nuna maka dazu Mamuda? Uwar kirki ce zata ma yaranta haka? Ni fa daga karshe na zargi tawul ta dinga dorawa kan garwashi take nana masu a jiki idan ya dau zafi, A gaskiya Mamuda in kace Hasinu ta ci gaba da zama gidan nan duk ma me zai je ya dawo babu ruwana, babu abinda ya shalli Ladi wllhi, kuma yau da ace abun zai tsaya kan kai da 'ya yanka maza ne, bazai taɓa 'ya ta Ammi ba to da sai ince ku karata, bazan ma sa Mera ba don kakanta Alhaji Saminu ba yarda zai yi ba, wai ma tsaya Mamuda, ko dai ka manta gubar da ta sa ma Mera a abinci ta ci ne har muka fidda rai da Mera? Magana ta domin Allah fa Mamuda" Abba ya ɗan yi murmushi, speaking calmly yace "Mama ina ce har gida an kama mata, ba lallai sai nan gidan zata zauna ba, ga can gidan da aka kama mata sai a samar mata me aiki, ni tausaya ma yaran nake, it won't be fair a rabasu da uwarsu..." Mama Ladi tace "Shi kuma jaririn da uwarsa ta mutu ta barsa sai a tona rami gefen na uwar a saka shi tsabar tausayi ko?" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan, goben sai a yankar maku ticket din jirgin sama zuwa kano in sha Allah" Mama Ladi ta washe haƙora tace "Jirgin sama kuma, toh Alhamdulillah, abinda nake ta son ka fahimta kenan Mamuda, jarirai nawa iyayensu ke mutuwa su barsu wajen haihuwa kuma su girma cikin aminci, ba da son ranmu za mu raba er banzar da jariranta ba sai don muguwa ce, gashi har yaran nata bata bari ba, gwara kakarsu ta rikesu ta kula da su har su yi wayo" Abba yace "Toh Allah ya rufa asiri" Mama Ladi tace "Ameen, kaga kafin jirgin namu ya tashi sai a sanar ma Mariya ta tafi tasha ta hau mota mu hadu a kanon gaba daya" Abba yace "Amma su iyayen nata ya za su ji in suka ga an hanata shayar da yaranta?" Mama Ladi ta mike tace "Mamuda ka daina mayar da hannun agogo baya, ni na ma gaji da magana wallahi, ina ruwanmu da iyayenta da su kansu sun sallama ma duniya ita, yanzun ma kawai sbda dattako da kuma nuna ma iyayen mu yan babban gida ne yasa za mu kai ta, banda haka Hasinu mugun abinda tayi mana ai bai kamata mu sake bi ta kan lamarinta ba, dama bakina bakin iyayen nata zan ce sai dai kuma ayi hakuri mun karbe yaranmu sbda Hasinu bata da halin kwarai da zata rike mana su, snn in labarta masu abinda tayi ma jariran da muka je kasuwa, kamata yayi ma su mikata dawanau don a binciki ƙwaƙwalwarta" Daga haka Mama Ladi ta fice ta bar ma Abba parlonsa. Wajen karfe tara Mayraah na kitchen zata zuba abinci Maheer ya shigo kitchen din, ta ci gaba da zuba abincinta ta ki kallonsa, kulle kofar yayi ya nufeta a hankali yace "Mimi ki zuba a food warmer mu tafi gida it's getting late" Tace "Ni yau a nan zan kwana" rasa abinda zai ce mata yayi yana kallonta, sai kuma yayi kasa da murya yace "Amma fa ba mu yi haka da ke zaki kwana a nan ba Mimi" A takaice tace "To make things easier for you yasa zan kwana a nan yau, kaga ba sai kana sneaking din zuwa nan da sassafe ba, ko kuma ka min karyan zaka je wani waje sai ka zo nan" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, bayan ta bude kofar kitchen din ta juya ta kallesa ta wani turo masa baki sannan ta fita, ɗan murmushi yayi yana shafa kansa, after few seconds shi ma ya fita daga kitchen din. Zaunawa yayi parlor yana kallon Ammi dake rungume da one of the twin, Bilkisu ma na rike da dayan, zuwa sannan babies din sun ɗan fara shan madaran da Ammi ta siyo masu, Haseenah dai na can an bar ta ita kadai a daki gashi an kwashe yaran, ruwan nononta sai zuba yake, Ammi na kallon Maheer tace "Mimi tace kace mata nan za ku kwana?" Ya sauke idonsa a hankali yace "Eh" Ammi bata sake ce masa komai ba, ya mike ya wuce sama. Maheer na murda kofar dakin Mayraah yaji ta sa makulli, ya fi minti daya tsaye bakin kofar, can yayi knocking a hankali, sai da ya sake knocking yaji tace "Waye" Yayi shiru yaki cewa komai, ganin ba bude kofar zata yi ba don da alamar ta gane shi ne, kawai ya juya ya bar bakin kofar. Washegari flight din karfe goma na safe Usman yayi ma Mama Ladi da Haseenah booking, Tuni Mama Ladi ta cakare cikin tsadadden atamfarta da sabon mayafi ga jakarta na yan gayu