Showing 441001 words to 444000 words out of 456519 words
dinta suka iso Nigeria da 1 year old twins siblings dinta, that same day Hajja da Yahanasu suka shigo daga Kaduna, sannan Omar ma ya sauka garin Abuja. Bayan magrib Mayraah na zaune tana cin tuwon da aka yi mata da assorted vegetable soup, Mama Ladi kuma na zaune ta daura kafa daya kan daya ga jariri tana gasa masa cibiya da wutan garwashin dake gabanta, gaba daya Mayraah ta kasa concentrating kan abincin da take ci don duk hankalinta na kan abinda Mama Ladi ke yi ma Babynta, gashi attention dinta sam baya ma kan abinda take labari kawai take ba matar abokin Abba da ta zo barka kai sai ka rantse ta taɓa sanin matar, su uku kadai ne a dakin, aka bude kofa, Mayraah ta daga kai tana kallon warce ta shigo, Mama Ladi ta ajiye towel din hannunta ta matsar da garwashin gabanta tace "Wacece wannan kuma ta afko mana cikin daki?" Sai a sannan Mayraah ta gane Badiyyah ce ta shigo, don kwata kwata bata ganeta ba da farko, salati Mama Ladi ta saki bayan ita ma ta gano ta, Badiyyah ta karaso cikin dakin ta zauna kan carpet tana gaida Mama Ladi, Mama Ladi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Badiyyah?" Badiyya na murmushi tace "Ina wuni Mama" Mama Ladi ta ɗan saci kallon matar abokin Abba, sai kuma tace "Lafiya lau" Mama Ladi bata sake cewa komai ba daga haka, Badiyyah na kallon Mayraah tace "Barka Mayraah, Allah Ubangiji ya raya Baby" Mayraah da duk jikinta yayi sanyi, a hankali tace "Sannu da zuwa sis Badiyyah" Badiyyah na kallon saman gadon tace "Ina Babyn?" Mama Ladi ta mika mata jaririn hannunta, Badiyyah ta amshi yaron tana kallonsa tana murmushi, mikewa Matar abokin Abba tayi tace "Bari in koma can daya parlon Mama" Mama Ladi tace "Toh shikenan, su Ammin ma ai suna can tun dazu" Matar na fita Mama Ladi ta sake kallon Badiyyah da sauri ta gwalo ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Badiyyah baki da lafiya ne? Meye haka ya sameki?" Murmushi kawai Badiyyah take tace "Lafiyata lau Mama" Ammi ce ta shigo dakin don ita ma tunda taga Badiyyah hankalinta ya tashi sosai, sai ga Usman ya shigo shi ma he was so shock at how he saw Badiyyah don shi ma bai ganeta ba da ta shigo at first, Ammi ta karaso ciki tana kallon Badiyyah ta zauna gefen gado tace "Baki da lafiya ne Badiyyah?" Badiyyah ta sauke idonta bata ce komai ba, bayan few seconds ta dago kanta, sai ga hawaye na sauka idonta, shi dai Usman na tsaye bai ma karaso inda suke ba, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Yanzu shikenan don kaddarar rayuwa ta fada ma yarinyar nan sai duk a hadu a gujeta babu wanda ya damu da yasan halin da take ciki a gidan miji, babu me zuwa inda take duk an watsar da lamarinta? marigayiyar uwarta fa er uwar ku ce uwa daya uba daya, shkkn don bata da rai sai er ta ta tagayyara?" Ammi dai ta kasa cewa komai, sosai jikinta yayi sanyi, Badiyyah ta share hawayen dake ta zuba idonta, Mama Ladi na kallonta tace "Matansa nawa mijin naki ne wai?" A hankali Badiyyah tace "Yace min daya, ashe su biyu ne, kwanan nan kuma ya kara wani auren" Mama Ladi tace "Kunji gwaggwon birin banza ko? Ke a ina ma kika samo mummunan halitta irin wannan Badiyyah, anya ma musulmi ne?" Wasu hawayen suka zubo idon Badiyyah a hankali tace "Ashe tsibbu yake bai gaya min ba, ce min yayi Malamin addini ne shi ashe ba haka bane" Mama Ladi tace "Kun ji shege ko, Malamin addinin kafurci yake nufi, ni dama tunda na gansa lkcn bikin na sha jinin jikina da shi, mutum kamar wanda baya alwala kafafuwansa duk wasu lafiyayyun kanta duk sun lalace kamar na kafirin dake zuwa gona, kuma shine har yanzu kike zaune da shi ki ci uban me da shi?" Ta fashe da kuka tace "Yace bazai taɓa saki na ba, gashi matansa gallaza min suke, duk ni ke komai a gidan, har duka sun taɓa yi min kuma ya goyi bayansu, ga girki da itacen da nake yi kullum safe, rana da dare, kullum sai nayi surfe, sannan ga su da manyan yara duk sun raina ni, har karuwa suke ce min, kayan da aka min duk sun sace bani da komai a daki yanzu, dama yace bazan haihu ba don yaransa ashirin da shidda, magani yayi ta ban ina sha har na wata daya daga baya yace min aikin yayi, bazan haihu ba...." Mama Ladi ta daura hannu biyu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shikenan ya cuce ki ya lalata maki mahaifa, yanzu Badiyyah gidan na ubanki ne da baza ki gudo ki bar masu ba? Shkkn ya cuceki" Badiyyah na kuka a hankali tace "Ko nace zan gudu sai inji bazan iya fita daga gidan ba Mama, na sha hada kayana amma sai in kasa fita, kawai sai dai in mayar cikin sif" Mama Ladi tace "Yau nake ganin abinda ya isheni ni Ladi, dama har yanzu akwai sauran tsinannu a duniya? kafe ki fa yayi a gidan da tsafi ta yanda baza ki ji sha'awar fita ba, to garin yaya ya bari kika taho nan yanzu?" Badiyyah tace "Tun da aka yi haihuwan na sanar masa yace bazan je ba, ina ta rokonsa nace kwana biyu kawai zan yi, shine yace sai dai in san yanda zanyi don bai da kudin motar da zai bani, da ya ce haka sai na siyar da akwatuna na shine na samu kudin motar, ya kuma ce kwana daya kawai zanyi" Mama Ladi tace "Zai ci kaza kazan sa kuwa, sai dai ya saka uwarsa a dakin naki amma wallahi baza ki koma gidan nan ba, yo ba gwara gidan gyaran hali ba, kaji min shege arne, mu dau yarinya fara kal mu basa ya maido mana da duna? To wallahi baza ki koma ba, ai kin gama wannan kadararren auren yau, kotu kawai za mu maka Bokan, ai kyan mutumin nan Hasinu" Ita dai Badiyyah hawaye kawai take, Usman ya juya ya fita daga dakin, Ammi was speechless, sosai jikinta yayi sanyi, haka Mayraah da ta kasa cin abincin gabanta.....
Ranan suna da yamma Mayraah ta gama canza kayanta for the countless time, daurewa kawai take don zuwa lkcn ta gaji sosai, sanye take cikin wani tsadadden lace tana tsaye gaban madubi, mai make up ta gama daura mata dankwalinta, sosai tayi kyau kamar wata sabuwar amarya, Maheer ya shigo dakin don Aunty Mariya ya tambaya inda take ta gaya masa, kallonsa kawai Mayraah take kamar yanda shi ma yake kallonta, tun safe bata sake ganinsa ba sai yanzu, Mai make up din ta fita ta bar masu dakin, ya karasa har inda take tsaye ya rungumeta sosai, ta kwantar da kanta kirjinsa ta lumshe ido tana shakan daddadan kamshinsa, juyata yayi leaning his head on her shoulder yana kallonta ta madubi a hankali yace "You look cute Maman Baby" Ta madubin take kallonsa, ya sauke idonsa a hankali yace "Za ku gaisa da wani frnd dina, meet me outside" Tace "Ohk dear" Sai da ya fita dakin sannan ta dau gyalenta ta bi bayansa, har a lkcn gidan cike yake da jama'a, kaf family din dad dinta babu wanda bai zo sunan nan ba, tun safe Mami da matar Musharraf da Ihsaan suka zo gidan, a safiyar ranan Ihsaan suka sauka Nigeria da MD, A haka Mayraah ta fito compound duk ana bin ta da kallo, duban inda zata ga Maheer take a compound din, ta gansa tsaye tare da Umar ta nufe su, Maheer dake jingine jikin wata mota ya dinga kallonta har ta iso inda suke tana ɗan murmushi, tahowa yayi dab da ita ya kamo hannunta a hankali ya saka mata makullin hannunsa yana kallon kwayar idonta yayi kasa da murya yace "Just a little token for you soulmate, thanks for making me a Dad" Umar dai murmushi kawai yake yana kallonsu, Mayraah was speechless and stunned at the same time, it was something she never saw coming, ta juya ta kalli tsadadden dalleliyar sabuwar motar dake parking space, bata san sanda ta rungumesa ba, nan da nan hawaye ya kawo idonta, dai dai nan Musharraf da MD suka shigo compound din.
[11/4, 10:52 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Aunty Mariya ta daga kai tana kallon Ammi bayan Mama Ladi ta fita tace "Kuma gaskiya Mama ke fada Ammi...." Kawai ganin Mama Ladi suka yi ta shigo parlon, ashe makalewa tayi bayan ta fita taji abinda za su ce, duk suka daga kai suna kallonta Mama Ladi tace "Toh ma in ba rashin nutsuwa irin naku ba ai da kun zauna kun nutsu za ku ga dacewar hakan, to babu me gaya maku gaskiya banda ni, ita Hajja ko watse taron suna ba ayi ba ta tattara ta tafi, ban san menene tsakaninta da Mamuda ba banda haka ai yanzu an dena wnn sukurtakan kauyancin, yanzu yarinyar nan Mera surkarki ce ko kin ki ko kin so, kuma tana da dangin ubanta kaca kaca a duk Najeriya, sannan ga uwarta ma a raye, hakuri za ki yi ki ajiye batun ke kika riketa tun tana tsumma ki dena bake bake kan lamarinta, tunda aka watse taron suna lafiya bayan kwana biyu ko ni da Mashir din sai mu kai masu ita kaduna har bayan arba'in, amma bakya riketa a nan kice tayi jego ba, tayi laulayi a gidanki tayi jego a gidanki bayan ga dangin ubanta na kusa ai abun ya zama son kai, suma ai za su so ta kusanto su, banda ma kun aurar da ita da wuri ai da yanzu duk ta saba da yan uwanta, pamilyn ubanta fa pamily ne babba ba irin namu kirgaggu ba, ita Mariya ba haihuwa ta taɓa ba balle tasan yanda ake yi ta dinga nusar dake" Ammi tace "To shikenan Mama, idan Abban nasu ya shigo zan sanar masa" Mama Ladi tace "To ya dai fi, wani abun ya kamata ki zauna ki nutsu ki san abinda ya kamata ba sai ana nusar da ke ba, ga dai jikoki an fara ajiye maki, ni ba ma sai naje ba ko Mariya sai su kai ta da Mashir din don ban cika son gantali ba gaskiya yanzu" Daga haka ta nufi kofa, har ta fita sai ta kuma dawowa tace "Wai ni ita Eemani yaushe zata dawo ne, abu kusan wata daya fa yau, tun da suka kyallara ido suka ga dayar ta samu daukaka gata can a Canada da lafiyayyen mijinta shine suke kokarin shige ma yaran kuma yanzu, har da wani bugo waya a turo Eemani za su yi biki a pamily, kun ga kenan sun ga yaran za su daukaka a duniya bari su lallaba su shige jikinsu, ta yanda in Ihisaani ta haihu sai ace za a biya ma daya a cikinsu tikitin jirgi yaje wajenta, to uban kuturu ma yayi kadan balle na makaho, Allah ne sanadin auren Ihisani da Mendi ni ce sanadi, don ba uban wani ya cusa min ita ba, banda kokari na yaushe Mendi zai wani lura da ita? don haka me zuwa Canada in Ihisani ta haihu a bayana yake wallahi" Daga Ammi har Aunty Mariya kallon Mama Ladi suke, Aunty Mariya na murmushi tace "Amma mu ai haka muke so Mama, ko ba komai za su nuna su su ce dangin ubansu ne, su kuma suce 'ya yansu ne, mu kam haka muka fi so don duk inda za aje a dawo sune dai gatansu, kuma da da matsala in dai Eeman ce tuni zata dawo" Mama Ladi tace "Ki iya bakin ki Mariya, Mamuda ne gatansu sai ni, sai Ammi" Mama Ladi bata jira cewar Aunty Mariya ba ta fice daga parlon, Aunty Mariya ta kalli Ammi, after some seconds Ammi tace "In sha Allahu zuwa Jibi sai ku kai ta kadunan, tun da kinga mahaifiyarta ma na nan kuma tace min za su yi sati hudu nan gaba kafin su koma" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya kai mu jibin" Ammi tace "Ameen" Sosai Mayraah taji dadi har ranta bayan Ammi ta sanar mata zata je kaduna gobe, Aunty Mariya ce ta hada mata kayanta da na baby, da duk wani abu da zata bukata... Ammi na zaune dakin Mama Ladi dake ta linke kayan da Bilkisu ta wanke mata, Mama Ladi na girgiza kai tace "Inaaaa, sam bazan iya gantali ba gaskiya, naga dai ita ma Mariyan ai ba yarinya bace, ko kuma ki yi ma kawarki lauya magana, don dai yini daya ta temaka taje ta mika maki Mera gun dangin ubanta ta dawo ai bazata ce a'a ba tunda ba miji gareta ba, sai su je da Mariyan da Mashir" Ammi tace "Toh amma me yasa baza ki ba Mama Ladi" Mama Ladi tace "Bazan fa je ba, ni ba er iska bace, ko wani tsohuwa na killace gu daya banda Ladi, an maida ni gantalalliyar karfi da yaji bana nan bana can" Linke kayan karshe ta saka a akwatinta ta fita ta bar Ammi a dakin. Wajen karfe tara na dare Maheer ya shigo dakin da Mayraah take tare da Babynta, ya gaida Aunty Mariya dake zaune dakin ta amsa tace "Duk yau shiru baka shigo ba Dr" yana ɗan murmushi yace "Eh na ɗan yi busy ne Aunty" Aunty Mariya ta mike ta fita daga dakin, Mayraah dai kallon Maheer kawai take, ya sakar mata murmushi ya karasa inda take yace "Hello mai jego...." Ya kamo hannunta yace "How are you wife?" Kwace hannunta tayi tace "Shi ne baka zo da safe ba ko..." Zaunawa yayi yana facing dinta yace "I'm so tired Mimi, kuma kin ga naje aiki" Tace "Ohk" Ya kalli Babyn dake bacci ya daukosa ya gyara masa hularsa yana kallonsa, kamar yanda Mayraah ke kallonsa, yana daga kai suka hada ido ya ja hancinta yace "Why are you staring at me that way?" Tayi murmushi tace "Why are you staring at my Baby that way too" Yana murmushi yace "Gaskiya kam Babynki" Tace "Do you have a nickname for him?" Yana kallonta yace "Ke dai da kika sa masa suna za ki nemo nickname, i tot Musharaff din ma zaki dinga kiransa ae" Mayraah dai kallonsa kawai take, ya dau wayarsa dake ringing, Mayraah na kallon screen din taga Abba ke kiransa, ya kwantar da Babyn hannunsa yace "Abba na jirana dear, zan je parlonsa in samesa.." Daga haka ya mike ya fita daga parlon. Washegari Sunday da safe Mama Ladi da Aunty Mariya suka tafi raka Mayraah da babynta kaduna, Maheer ne yayi driving dinsu har can, Hajiya Ramatu tayi farin ciki da zuwansu duk da Ammi ta sanar mata tun kan su taso, dakin dake kusa da na Hajiya Ramatu aka gyara ma Mayraah da Babynta, bayan Azahar Maheer ya kai Aunty Mariya gidanta yayi dropping dinta sannan ya dawo daukan Mama Ladi su koma Abuja, da mamaki Hajiya Ramatu ke kallon Mama Ladi da ta sakale tsadadden jakarta ta gyara yafin mayafinta tace "Dama baza ki kwana biyu ba Hajiya Ladi?" Mama Ladi na girgiza kai tace "Aa tafiya zan yi Hajiya, Mamuda ne ma yayi min magana naji nauyinsa shine nace to bari in rakota, banda haka ai har yanzu gajiyar suna bai gama bin lafiya ba, yanzu haka duk kasusuwa na nukurkusa suke" Hajiya Ramatu tace "To amma ki tsaya ku gaisa da Alhaji sun kusa gida yanzu haka daga airport, yau ya dawo kasar" Mama Ladi zata yi magana sai ga Alhaji Saminu ya shigo parlon da sallama, nan suka gaisa da Mama Ladi, sai ga Maheer ya shigo har parlon don gaida Alhaji Saminu duk da sun hadu a waje, Alhaji Saminu ya amsa da fara'a sosai, Hajiya Ramatu tace "Za su koma Abujan ne" Alhaji Saminu yace "Duk a yau din, toh maa sha Allah, Allah ya tsare hanya...." Hannu ya saka a aljihunsa ya ciro bandir din dubu daddaya ya ba Hajiya Ramatu yace "A ba Hajiya ta sha ruwa a hanya" Ya sake saka hannu a aljihu ya ciro wani bandir din ya mika ma Maheer yace "Ka kara mai" Maheer dai yayi kasa da kai, Alhaji Saminu yace "Amsa mana, fetur nace ka kara a hanya" Maheer ya amshi kudin yana masa godiya, sai da Mama Ladi tayi kame kamenta sannan ta amsa kudin da Hajiya Ramatu ke hada ta da Allah ta amsa, Mama Ladi tace "To Allah Ubangiji ya sa a fi haka" A haka suka bar gidan da Maheer, sai da suka dau hanya Mama Ladi ta ciro rafan kudin a jakarta ta fara kirgawa, shi dai Maheer kallonta yake ta madubi yana driving, ta gama kirga kudin ta mayar cikin jaka tace "Dama nasan dubu dari ce, daga haka kyautarsa ke farawa bai bada kasa da haka, toh shi dai ya sani, ni dai ba saboda Allah na kai masa jikarsa ba" Murmushi kawai Maheer yake bai ce mata komai ba. Days went by, Then weeks, sosai Mayraah ta samu kula gidan kakanninta, tayi jego cikin gata da tarairaya, just 5 weeks da tayi tana jego a gidan tayi wani kyau ta murmure ta dawo kamar ba ita ba, Shi kansa babynta da suke kira Aryaan yayi wayo kamar ɗan wata biyu, duk bayan kwana biyu Mom dinta ke zuwa gidan da twins dinta, a can Abuja kuwa kusan kullum Ammi ke kiran Mayraah to check on her and the Baby, haka ma Abba da kan kirata time to time, a sati hudun nan sau biyu Maheer ya zo kadunan to check on her and Aryaan, kuma siyayya sosai yake masu idan zai je, sai da suka cika 6 weeks Aunty Halima ta dage ma Mayraah da gyaran ciki da waje don Hajiya Ramatu tace next week zata koma dakinta don har ta wuce 40 days, duk wani abu da ya kamata sai da aka ma Mayraah na gyara, ana gobe Mayraah zata koma Abuja Mom