Showing 291001 words to 294000 words out of 456519 words
ina, ina son ya kasance mun binnesa ne a inda muka ji sa har a tashi duniya babu wanda zai kara tada sa after tomorrow, duk da nasan halin yarana maza hakan bai sa na fasa jaddada masu ba" Abba yace "To kafin ki jaddada masu ni na fara jaddada masu, kuma na fi ki sanin muhimmancin binne maganar a inda muka ji sa, fadan ta ma a wani waje bashi da amfani ba kuma shi da fa'ida" Ammi tayi murmushi tace "Toh Allah ya sa mu dace"
[8/29, 10:00 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Washegari da safe wajen karfe bakwai da rabi Ammi ta shigo dakin da Aunty Mariya da Mama Ladi suke, Ammi ta zauna ta gaida Mama Ladi, sannan suka gaisa da Aunty Mariya, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Kin ji fa yau Mariya zata koma, nace mata ina lefin ta ɗan kara kwanaki kafin nan Mera ta ji kwarin jikinta, naga dai ko kwana biyu ba ayi da sallamanta a asibitin ba, ke ba miji ba yana can Legas sai sanda Allah ya kado sa" Aunty Mariya tace "Mama yau satina fa biyu a Abuja, banda muna asibiti ni na so ma mu koma tare da Hajja a sanda ta tafi, Mayraah kuma ai jiki sai dai mu ce Alhamdulillah" Mama Ladi ta kyabe baki ta gyara kwanciyarta, Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima yanzu shigowa nayi in ce maku za mu kaduna amma in sha Allahu yau za mu dawo, kin ga gidan ba kowa Mariya kiyi hakuri ki bari in mun dawo sai ki tafi" Mama Ladi ta mike zaune tace "Me za ku je yi a kaduna kuma?" Ammi tace "Alhaji ne yace za mu je kaduna, ina jin ziyara za mu" Mama Ladi ta gyara zama tace "To wa gareku a Kadunan? shi Mamuda ba mu kadai ne danginsa ba a halin yanzu? waye bai san bai da kowa ba, kullum mu ne dai ke fadi tashi akan matsala idan ta ɓullo a gidansa" Ammi ta mike tace "Bari in je in shirya Mama, jirgin namu na karfe tara ne" Mama Ladi tace "Toh Allah dai ya tsare, kilan wani sirrin za ku je kuyi a can bakin ku alekum, Allah de ya kyauta, dazu ma naga ai kun fita, dama fatanmu Mera ta samu sauki kuma ta samu, nan da kwana biyu in sha Allahu nima sai in san inda dare yayi min, na lura yanzu Mamuda kora da hali yake mana, banda haka ni dai wllhi nasan bashi da kowa a Kaduna" Ammi tace "To ziyara za mu je gidan abokinsa sun samu karuwa, yanzu dai hankalin ki ya kwanta dai ko" Mama Ladi tace "To Allah ya tsare" Ammi tace "Ameen" Kofa ta nufa Mama Ladi tace "Kin dai ji Badiyyah na can ranga ranga asibiti rai a hannun Allah wai ta zame wajen shiga bandakin Yahanasu, kinsan bandakin gidan Yahanasu ko na kasuwa albarka, ga uban gansa kuka, har wani yauki yauki bandakin yake wllh, abun dai ba arziki ko dake duk kun sani ai, ita fa Yahanasu tun muna yan mata take kazanta gashi ya bi ta har tsufa, ko ruwa baka iya sha in ka shiga gidanta sai in kai ma kazamin ne" Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yaushe hakan ya faru?" Aunty Mariya ta numfasa tace "Da asuba aka kirani, ashe tun jiya da daddare abun ya faru" Ammi tace "Amma jikin da sauki dai ko?" Mama Ladi tace "Wuyarta ace mana tayi ɓari, kilan ma da gangan ta zame, ko da yake cikin shege ai kowa yasan naci ne da shi, ba wani zancen barewa" Ammi na kallon Aunty Mariya tace "Wa ke tare da ita a asibiti?" Aunty Mariya tace "Wai babbar jikar Yahanasu, sun kira Hajja tace masu ai ita bata garin ma, Yahanasun ma taki bin su asibitin, dole haka ni nayi masu transfer dazun nan wai za a kara mata jini, sannan she is unconscious, wannan ne ma yasa nake son in koma kadunan yau" Ammi tayi shiru ta ma rasa me zata ce, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Shikenan, in sha Allahu zan karasa asibitin in mun je kadunan" Aunty Mariya tace "Toh Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, wai har su Maheer?" Ammi tace "Eh har su" daga haka ta fita daga dakin. Ammi na kallon Abba bayan ya gama shiryawa, cikin sanyin murya tace "Yallabai ga wani suggestion da ya zo raina yanzun nan" Abba ya juya yana kallonta yace "Na me fa?" A hankali tace "Ni a nawa tunanin Yallabai why not mu bar Mayraah kawai ba sai mun je da ita kadunan nan ba, wallahi bana son abinda zai sake daga mata hankali duk da dai naga tun jiya bata saka damuwa a ranta ba, yau ma naga da walwalarta ta tashi ba wani damuwa, to kar mu je kadunan nan kuma ta samu heartbreak din da ya fi na jiya, i don't want my daughter to be hurt" Abba ya ɗan yi shiru yana kallonta, bayan wasu dakikai yace "Kar ki damu, in sha Allah abinda kike tsoro bazai faru ba, tun da kin ji me asibitin tace mutumin na ta bibiyanta a kasar waje yana tambayarta ita uwar Mayraah din, so wannan ne nima ya bani karfin gwiwan aje da ita, in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, we will go with her" Ammi sai da taji wani rass jin kalman da Abba ya fada wai Uwar Mayraah, sunan da ita ke ta bearing for 22 years now, a hankali Ammi ta sauke idonta tace "Toh shikenan" Abba yace "Hope duk sun gama shiryawa?" Kallonta Abba ya dinga yi jin bata ce komai ba, kuma bata ma san yayi mata magana ba, Abba yayi kasa da murya yace "To meye kuma damuwar? Gaya min menene kuma" Ta ɗan yi yake, sai kuma a hankali tace "And yallabai, sai jiya cikin dare abubuwan da suka faru suka dinga dawo min zuciyata, yallabai gaban wan Musharraf din nan fa aka yi duk wannan maganar? Wallahi da abun nan ya fado min cikin dare kasa bacci nayi, bai kamata ayi komai a gabansa ba, mun yi babban kuskure, kuma wannan kamar kara tona ma kanmu da ita Mayraan asiri muka yi, shi ma ai ba haka ake ba, family issue ne wannan da sai ya fita ya bamu waje, amma yana zaune duk ta bada wannan mummunan labarin shi ma yana ji" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Maheer da Usman sun min wannan maganar tun jiya, but ya muka iya? tunda kika ga tayi duk maganan nan a gabansa kinsan ta yarda da shi ne sosai and suna da kusanci da kyakkyawan alaka da shi, kin ga bayan da muka hau sama zuwa dakin ita wannan matar ai bata fara magana ba sai da tace nurse din ta fita, so she trust him definitely" Ammi ta bata rai tace "Duk da haka dai, yayan fa tsohon saurayin Mayraan ne, yanzu idan ya kwashi duk wannan labarin mara dadin fada ya je ya gaya masu fa? Ni dai wallahi hankalina yayi mugun tashi da abun nan ya fado min cikin dare" Abba yace "In ma yaje ya gaya masu ba abu bane da zai dame mu, it's left for them, don ba mu da wani business da su har a tashi duniya, don su ne musabbabin rugujewan farin cikin Mayraah" A sanyaye Ammi tace "Haka ne Yallabai, lokaci na wucewa kuma airport da nisa daga nan" Abba yace "Ki duba ko sun gama shiryawa" Kofa Ammi ta nufa ta fita daga dakin. Usman ne zai yi driving din na su zuwa airport, Mayraah dake sanye da hijab har kasa tana kallon Maheer tace "Yaya to wa zai dawo da motar" Maheer ya bude mata back seat kafin su Ammi da Abba su karaso yace "Zai bar motar a airport" Mayraah tace "Amma dai biya ake ko?" Yayi murmushi yace "What did u expect" Murmushin tayi ita ma ta shiga motar, Usman dai yana zaune driver seat, Maheer ya zaga ya bude ma Abba front seat don yasan can zai ce zai zauna, karfe takwas da few minutes suka bar gidan heading to the airport. Ko da suka isa airport suka tarar Ceo har ta iso tare da Aaria sai nurse dinta duk suna zaune a lounge, Ceo ta mike tsaye suka gaisa da Abba da Ammi, sannan ta amsa gaisuwar su Maheer, Aaria dai sai kallon Mayraah take, Mayraah ta sukunyar da kanta, bayan ta gaida Ceo ta karasa gunta tana tafiya a hankali, zaunawa tayi tana kallonta ta gaisheta cikin sanyin murya, Aaria bata fasa kallonta ba kuma ta kasa amsa gaisuwar da take mata, Mayraah ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, bayan few seconds Aaria ta sauke idonta kasa, nan da nan hawaye ya fara sauko mata, Ceo ta koma gefenta ta zauna ta jawota jikinta speaking calmly tace "Common My love, where is the promise u made to me" Aaria ta daura kanta saman shoulder din yayarta hawaye na sauka idonta, ita dai Mayraah bata iya ta dago kanta ba, Ammi dai sai kallonsu take, ashe kyan Mayraah ba komai bane a inda kyan uwarta yake, cause her mother is really beautiful, babu wanda zai bata shekarunta ko kuma yace ta haifi kamar Mayraah, A haka suka yi boarding jirgi, shi dai Maheer yayi mamakin da bai ga MD ba don ya zata da shi za su je kadunan, but daga shi har Usman a ransu sun ga hakan ya fi.
Karfe tara da rabi suka sauka airport din garin kaduna, motoci uku na airport din suna jiransu, nan da nan mood din Ammi ya canza bayan taga MD ya sauka daga cikin daya daga motocin, daga Maheer har Usman ma basu ji dadin ganinsa ba, a haka suka karasa har gun motocin, bayan duk ya gaishesu Ceo tace "Ya me jikin? Is she better?" Yayi murmushi yace "He is better Ma'am" Tace "To Allah ya basa lafiya" Cikin ladabi yace "Ameen, ni zan dau taxi in koma gida, idan kun gama za ku taho airport sai ki min waya Ma....." Sosai hankalin Ammi ya kwanta jin abinda MD yace, duk da dai aikin gama ya gama don me ya rage da bai sani ba kuma, Ceo tace "Where are you headed now?" Yace "Malali..." Ceo tace "Ohk to ba damuwa, zan kira ka if we are done"
Bayan sun iso unguwar Malali, su Abba suka ga motarsu Ceo dake gaban nasu sun yi parking a gefen hanya, hakan yasa nasu drivern ma yayi parking, sauka drivern motarsu Ceo yayi ya nufi gun wasu matasa dake tsaye bakin hanya, daga yanda suke communicating zaka fahimci tambayarsu direction din gidan da za su yake su kuma suna masa kwatancen, bai jima tsaye yana magana da su ba ya koma ya shiga mota, Wani hadadden layi suka shiga bayan sun kara tafiyar wasu mintuna, nan ma sai da drivern su Ceo ya sauka yayi tambaya aka sake basa direction, tun da suka baro Abuja sai yanzu Mayraah ta dinga jin zuciyarta na bugawa sosai, kwantar da kanta tayi jikin Ammi da ta rungumeta ta lumshe ido, dai dai gate din wani gida me girman gaske wanda aka yi ma gini irin na zamani suka ga driver din su Ceo yayi parking bayan sun wuce wasu yan sanda kafin su shigo unguwan, motarsu Mayraah ma yayi parking a bayan nasu Ceo, sai da Ceo ta sauko tare da Aaria da nurse dinta sannan Abba ma suka sauka, da kyar Mayraah ta iya saukowa daga motar Ammi na rike da hannunta, her heart is just beating so fast, bayan motocin su akwai wasu tsadaddun motoci biyu a kofar gidan ko wanne kuma da soja daya tsaye jikin motar, Ceo ta nufi babban gate din gidan su Abba na biye da ita a baya, Securities din na kallonsu babu yabo babu fallasa da turanci suka shiga tambayarsu wa suke nema kuma daga ina suke taho, wasu dattawan maza biyu ne cikin shiga ta alfarma suka bude gate din gidan suka fito, security daya ya kulle gate din, gaisawa suka yi da Abba da su Ceo a mutunce, har Abba ya gane daya daga cikinsu don he is a wealthy business man that is well known, kallon securities din bakin gate din daya daga dattawan yayi cikin harshen turanci yake masa magana a ɗan fusace yace "Duk wanda za ku ga ya zo a wannan lokacin to zuwa yayi ya duba mai gidan, so ku barsu su shiga ba sai kun tsaya dogon surutu ba" Da ladabi securities din suka ce "Yes sir" bude masu gate din suka yi duk suka shiga ciki, Ceo dake rike da hannun Aaria tana kallon daya daga securities din tace "Ina ne direction din shiga entrance na gidan?" Nuna mata yayi da ladabi, tana kallon Nurse din dake tare da su ta nuna mata wani waje da aka yi a compound din domin shan iska tace "Farida zaki iya jiranmu a can" Da ladabi Faridar tace "Toh Ma" Daga haka ta tafi can ta zauna, parlor na farko su Ceo suka shiga wanda babu kowa a ciki, hakan yasa ta karasa har second parlor din kanta tsaye su Abba na biye da ita a baya, shi dai Maheer har mamakin courage da confidence dinta yake kuma da alama sam bata da tsoro, Ammi dai gabanta sai faduwa yake kar mai gidan ya masu tijara ko ya koresu, suna shiga second parlor din wata mata da bazata wuce 43 ba ta fito daga wani bangare, tsaye tayi tana kallonsu at the same time tana masu sannu da zuwa, lokaci daya ta buda ido sosai bayan sun hada ido da Aaria, da sauri ta karasa har inda suke tsaye da mamaki tace "Maryam??" Ammi da tayi stiff a inda ta tsaya sai kallon matar take bata ko kiftawa....
[8/31, 11:58 AM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Juyawan da wannan matar da ta kira sunan Aaria zata yi suka yi ido hudu da Ammi dake ta kallonta da wani expression gabanta na faduwa, Matar ma ta dinga kallon Ammi ba ta ko kiftawa alamar tana son tuno inda ta taɓa saninta ita ma, duk da haka dai fuskarta da fara'a take nuna masu kujeru tana welcoming dinsu tace "Bismillahn ku ga kujera...." Ammi ta sauke idonta, hannunta rike da na Mayraah ta karasa kujeran suka zauna tunani iri iri na yawo a ranta, gaba daya she is just confused, Abba ma duk suka karasa can cikin parlon suka zauna kan kujera, Ceo na rike da kanwarta ta zauna tare da ita a gefenta, Dai dai nan wata dattijuwar mata ta shigo parlon zata raka wasu baƙinta biyu, tana ganinsu Abba duk da bata san ko mutum daya a cikinsu ba tayi welcoming dinsu da fara'a, after seeing off her visitors ta dawo parlon ta zauna tana murmushi idonta da attention dinta duk na kan Mayraah tace "Sai dai har yanzu ban wayi kowa a cikin ku ba wallahi" Tana fadin haka ta kalli matar dake tsaye tun shigowarsu Abba parlon tace "Aunty Sadiya a kawo masu ruwa mana ko" Matar da ta kira da Aunty Sadiya ta juya ta bar parlon don duk iya kokarinta na ganin ta tuno inda ta taɓa sanin Ammi ta kasa tunowa, tunanin da take ta yi kenan a tsaye amma ta kasa tuna Ammi, Ceo na kallon dattijuwar nan da ta kasa dauke idonta kan Mayraah calmly tace "Wajen Mai gidan mu ka zo idan babu damuwa pls Hajiya" Matar na murmushi tace "Oh... Allah sarki, to ku karaso parlon nasa ai yana ciki" Tana fadin haka ta mike, ta nufi wani parlon suka bi bayanta gaba daya, wannan din ma wani babban parlor ne that is well furnished, tayi masu iso har ciki duk suna biye da ita a baya, bayan duk sun shigo ta kulle kofar, tsaye Abba da Ammi da su Maheer suka yi ba tare da sun karasa can cikin parlon ba basa ko kiftawar kirki suna bin duk occupant din parlon da kallo, wani Dattijo ne kishingide a saman lallausan carpet ga fruits iri iri a gabansa, daga gefensa kuma Musharraf ne zaune sai MD da shi ma yake zaune kasan carpet din kusa da Mamin sa, daga daya side din wannan dattijon kuma wani mutumi ne da bazai haura shekaru 48 ba, MD ne ya fara mikewa da sauri tsabar yanda ya rikice yana kallon su Abba da Ceo, sai kuma Musharraf da shi ma ya mike yana kallonsu da mugun mamaki, sannan wannan mutumi da yake late forty's dinsa shi ma ya mike tsaye da sauri cikin wani irin yanayi yana kallon Aaria yace "Maryam?" Ita dai Aaria kallonsa kawai take bata ko kiftawa, MD ya ji kafafuwansa sun kasa ci gaba da daukarsa a hankali ya durkusa kan knees dinsa yana repeating Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, Mami was dumbfounded sai bin su Abba gaba daya take da kallo, shi ko Dattijon nan da yayi saurin daidaita zamansa in ya kalli su Abba, sai kuma ya kalli Ceo, sannan ya kalli su Maheer, haka nan dai ya dinga bin su da kallo kana ganinsa kasan shi ma dai ya shiga rudani a wannan lokacin, Matarsa da ta kawo su parlon sai bin kowa take da kallo with confusion, infact everybody in that parlor was more than confused, Ceo ta kama hannun Mayraah dake ta kallon su Musharraf da uwarsu da idanuwanta kamar za su fito don mamaki, ita Ammi tsabar kidimewa haka ta bude baki hangangan tana kallonsu, Ceo na rike da Mayraah ta tafi har gaban wannan mutumi dake tsaye ya kasa daina kallon Aaria, tana nuna masa Mayraah babu yabo babu fallasa tace "Abdallah!! Your Child" Tana fadin haka ta juya ta koma inda su Abba ke tsaye ita ma ta tsaya tana kallon Abdallah wanda ke ta kallon Mayraah da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta kamar an bude pampo, Mikewa tsaye dattijan yayi yana ma Ceo wani kallo yana huci kafin yace