Showing 429001 words to 432000 words out of 456519 words

Chapter 144 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70563

zauna gefen gado ta kira Maheer, yana fara ring ya daga, Ammi tace "Maheer me ya samu Mayraah?" Maheer yayi kasa da murya yace "She is sick for almost a month today" Ammi tace "Why didn't you tell us?" Yayi shiru bai ce komai ba, Ammi ta katse wayarta, Mama Ladi tace "Sam Maheer bai da wayo wallahi, yarinya na jinya yau wata daya yaki gaya mana? So yayi sai ta mutu sannan ya sanar mana mu tafi gidan muna koke koke da iface iface? To kuwa zama bai gan ki ba ki tashi ki sa shijabin ki mu tafi gidan, dama ko hanyar gidan baki sani ba, yau ga dama ta zo" Ko musu Ammi bata yi ma Mama Ladi ba ta shirya, don sosai taji hankalinta ya tashi.... Maheer ya fito daga daki jin ana knocking kofar parlor, yana isa bakin kofar ya bude, ya ɗan buda ido yana kallonsu da mamaki, sai kuma ya fara kame kame, Mama Ladi tace "Dalla gafara ka bamu waje" Yana ɗan murmushi ya shafa kansa ya koma gefe, tuni Mama Ladi ta shige parlon Ammi na biye da ita, ya kulle kofar ya dawo Mama Ladi dake tsaye tsakar parlor tace "Ina Meran?" Yace "Bari in mata magana" Mama Ladi ta rike haɓa ta bi sa da kallo, can ta girgiza kai tace "Da Mashir bai yi boko ba da mun shiga uku mun lalace don sam lamarinsa bazai yi kyau ba Wllhi" Ammi ta nemi kujera ta zauna, tun da Maheer suka fito daga daki tare da Mayraah Ammi ke kallonta ganin yanda tayi mugun rama sai wani haske da tayi pauu, kamar yanda Ammi ke kallonta haka Mama Ladi ke kallonta baki bude, ita dai ta kasa dago kanta ta kallesu ta zauna kasan carpet, ɗan tafiyar da tayi ji take kamar gudu tayi, da kyar ta iya bude baki ta gaishe su, Mama Ladi tace "Toh Allah ubangiji ya raba lafiya" Shi dai Maheer na tsaye bayan kujera yaki kallon direction din su Mama Ladi, Mama Ladi ta nufi Mayraah tace "Tashi mu tafi gida, in ya ga dama ya biyo mu da kayanki" Dagota Mama Ladi tayi Ammi ta mike, Mama Ladi ta nufi kofa tana rike da Mayraah tace "Waiii, sai yanzu na kara tsorata da lamarin Mashir, da Usuman ne tuni zai dawo maki da ita gida ya ajiye maki, amma ki ga Mashir ya ajiye yarinya ciwon laulayi har ya kusa cinyeta ace Allah bazai kama sa ba, to dai Allah ya so mu mun taho da dreba" Ammi dai na biye da Mama Ladi a baya bata cewa komai, Maheer dake tsaye parlon ya kasa bin su har suka fita Ammi ta kullo kofar parlon, tun basu isa gida ba Ammi ta kira Bilkisu tace ta dama mata kunu. Wajen karfe biyar na yamma Mayraah na parlon Ammi a kwance kan bargon da Ammi ta shimfida mata a kasan carpet don tace bata son saman gado, bama ta son dakin gaba daya wai, tun da suka dawo ta samu ta ɗan sha kunu tayi bacci sai yanzu ta tashi, she felt a bit relieve coming back home, Ammi ce ta shigo parlon tace "Sa hijab dinki Mimi" ta mike zaune da kyar ta jawo hijab dinta tana kallon kofar parlon ta ga wanda zai shigo, MD ne ya shigo parlon da sallama tun da suka hada ido sau daya Mayraah tayi saurin sunkuyar da kanta, da tasan shi ne pretending zata yi ma tana bacci, Ammi ta shiga bedroom dinta ta bar masu parlon, ya zauna kan kujera yana kallonta yace "Sannu Mimi" Ita dai bata dago kanta ba kamar munafuka, a hankali tace "Ina yini" Yana murmushi yace "Lafiya lau, Malaria da typhoid ne ko Mimi?" Still bata dago ba ta gyada masa kai alamar eh, jin yayi shiru ta ɗan daga kai ta saci kallonsa taga wani kallo yake mata, turo baki tayi ta koma ta kwanta tana jin kamar ta nutse wajen.
[10/29, 9:19 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: MD yace "Ina drugs din Malaria din da kike sha? Ko yayan bai siyo maki ba?" Mayraah da ke kwance ta ki juyowa tace "Ya kare" Murmushi yayi bai sake ce mata komai ba, ita dai ko da wasa taki juyowa balle ta hada ido da shi, Allah Allah take ya fita ya bar mata parlon, bude kofar parlon aka yi ya juya, Mayraah bata juyo ba balle tasan wanda ya shigo, Ihsaan ce ta shigo parlon, tun da ya shigo gidan sai a sannan ya gan ta, ta ɗan kallesa suka hada ido bata ce komai ba ta tafi inda laptop dinta yake, ya bi ta da kallon gefen ido har ta dau laptop din sannan ta fita daga parlon ta kullo kofa, mikewa yayi yana kallon Mayraah yace "Allah ya sauwake Mimin Yaya me Malaria and typhoid" Ita dai Mayraah bata juyo ba kuma taki ce masa komai sai ma kara runtse idonta da take, yayi murmushi ya juya zai fita sai ga Mama Ladi ta shigo da cup din Custard tana cewa "So fa yayi ki mutu sannan ya bugo ya gaya mana, sai mu kwasa muna kuka mu tafi gidan nasa, tirrr da Mashir...." Mayraah na jin muryan Mama Ladi taji kamar tayi tsuntsu ta ganta a dakin Ammi, Mama Ladi na ganin MD tayi tsit tana ɗan murmushi tace "Lahh, Mendi ashe ka shigo" MD ya gaisheta, tace "Lafiya lau Mendi ya aiki, dazun nan in gaya maka muka yi mota guda muka je kwaso wannan mata a gidan mijin rai a hannun Allah, ashe watan ta kusan biyu kenan tana kwance tana laulayin ciki amma sbda gaɓonci irin na Mashir yaki sanar mana, to kunyar me zai ji oho, ai da ko ni sai ya kira a waya ya gaya min, ga cikin ya zo mata da azababben laulayi in gaya maka ta kirba mana amai yayi sau uku yau, yau duk mun tsorata da halin da muka sameta duk ta fita hayyacinta sai kace cikin jaraba astagfirullah" MD dai sai murmushi yake yana kallon Mama Ladi, Mayraah taji hawaye na zubo mata bata taɓa jin haushin Mama Ladi irin na yau ba, Mama Ladi tace "Atoh, ga dai kwasta nan na dama mata ko zata iya sha, shi dai ba ya cuceta ya hadata da wahala ba, irin wnn laulayin har sai tayi wata hudu kafin ta samu kanta, nayi matukar tausaya mata" Mikewa Mayraah tayi duk da rashin kwarin jikinta bata ko kallesu ba ta shige dakin Ammi hawaye na sauka idonta, Mama Ladi tace "Auu, to ai naga dai kawun ki ne Mendin ba wani bare ba ko" MD dai sai dariya yake yace "Bari in sauka kasa Mama" Mama Ladi tace "Toh maza jeka, Ihisanin ma a kasa na bar ta, yau ita ce zata yi mana girki nace kar a kuskura a ba Eeman in ba so ake mu yi ta gudawa a gidan ba, don ni wllh in ita ce ma tayi bazan ci ba, shekaranjiya fa da ta mana jalop haka muka yi ta tsamo jalop din cikin man gyada, sam tsoron Eemani nake" Shi dae MD ya nufi kofa yana murmushi bai ce mata komai ba ya fita, Mama Ladi ta karasa daki gun Mayraah da Custard din hannunta cikin lallami tace "Naga dai kanin ubanki ne Mendi din ba bare ba balle kice na tona maki asiri" Ko kallonta Mayraah bata yi ba hawaye na sauka idonta. Tun da Mama Ladi da Ammi suka tafi gidan Maheer suka taho da Mayraah kusan sati daya kenan Maheer bai zo gidan ba sai dai ya kira Ammi a waya, shi kansa ya rasa me yasa ya kasa zuwa gidan, ga dai kullum hankalinsa da tunaninsa na kan Mayraah but kawai yana ji bazai iya zuwa gidan ba, he just wish and hope she is getting better now... Mayraah kam ko don shiga da ficen da ake yi parlon Ammi with the numbers of mutanen dake gidan ga draman Mama Ladi na yau da kullum da baya karewa yasa ta ke jin dama dama a jikinta unlike sanda take gidan Maheer, duk da yanzun ma dai sai dai tayi ta bin kowa da ido ko tayi murmushi don ko magana bata son yi, amma she is feeling much better akan gidan Maheer, kusan every evening Usman ke siyo mata Garden egg da Avocado don su kadai take iya tolerating, Mama Ladi kuma ta dama mata kunun masara ta sha babu sugar, duk dare idan Abba ya dawo shi ma ya kan shigo part din Ammi ya duba jikinta... Yau bayan Isha Mama Ladi ta shigo parlon Ammi da sallama ta nemi waje ta zauna tana kallon Ammi tace "Wai ko dai Mashir ba shi da hankali ne?" Ammi ta daga kai ta kalleta, Mama Ladi tace "To naga yau sati daya da dauko yarinyar nan daga gidansa rai kwakwai mutu kwakwai amma bai zo duba ta ba, yana nufin ya hadata da wahala kenan ya kama gabansa ko menene haka?" Ammi dai ta ci gaba da danna wayarta bata tanka Mama Ladi ba, Ihsaan ta shigo parlon da shayin da tayi ma Ammi exactly yanda Mayraah ke yi mata, ta duka gabanta tana kallonta bayan ta ajiye tace "Ammi gashi na gama" Sosai Ammi ke jin Ihsaan a ranta don kusan personality dinsu daya da Mayraah in so many ways, wani lkci in tayi wani abun sai Ammi taga kamar Mayraanta, shi sa take jin yarinyar sosai a ranta, Ammi ta mata murmushi tace "To sannu da aiki daughter, ina Eeman fa?" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Eeman ta shigo parlon fuskarta ba walwala, duk suka bi ta da kallo har ta tafi ta nemi kujera ta zauna tana cika tana batsewa, Mama Ladi tace "Lafiya?" Ko rufe baki bata yi ba Usman ya bude kofar parlon, yana kallon Eeman fuska daure yace "Ke ina maki magana kika wuce??" Eeman dai bata ce komai ba ta sunkuyar da kai, Mama Ladi ta kyalkyale da dariya har da saukowa kan carpet tana kallonsu, nan da nan hawaye ya cika idon Eeman, Mama Ladi tace "Me kika masa hala?" Sai ta kara kwashewa da dariya kamar an aiko ta, Usman na kallon Eeman fuska murtuke yace "Zo ki fita" Mikewa tayi ta goge idonta ta nufi kofa ta bi ta gefensa ta fita daga parlon, Mama Ladi sai kyakyata dariya take kamar taga wawan zama, Usman ya kullo masu kofar parlon ya bi bayan Eemaan, Mayraah dake kwance parlon tayi murmushi kawai tana cin Garden egg din hannunta, Ihsaan ma dai murmushin tayi ta mike ta dau wayarta ta fita daga parlon, Mama Ladi ta hadiye dariyar da take da kyar tace "In kin bibiya wani azababben rawan kan tayi masa, dama na baro ta wai zata dafa masa shayi da kyar in ba gishiri ta lafta masa a madadin sugar ba ko kuma barar masa da shayin tayi a jiki don dai in ba idona ne ba kamar ba kayan nan na gani a jikinsa ba dazu" murmushin da Ammi bata yi niyya ba tayi tana ci gaba da danna wayarta, Mama Ladi ta rike haba tana zare ido tace "Tsorona Allah tsorona yarinyar nan Eeman, tun da ta kona min er sabuwar atamfata wajen guga kuma ta wani zo tana nuna min tana murmushi na sha jinin jikina da ita, ranan har hawaye sai da na zubda, in kun lura sam na dena sa ta aiki, na yarda mu zauna mu yi hira tana baɓɓaka dariya amma ba ruwana da sa ta aiki" Ita dai Ammi bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Dama Usuman din ne dai dai ita, shi zai seta mata zama, shegen rawan kanta ya fi karfinta ga dariya kamar er mahaukata, ni dai ina nan har yau ina kokarin shawo kansa a makala masa ita su je can ya gyara mata zama, duk tsiyar da zata tafka masa dama ko yaki Allah sae dai yayi hakuri, in kuma har yanzu yana kan bakansa to gaskiya sai ta kai kamar Mera za a aurar da ita kar taje ta maida mijin mahaukaci, dama mazan yanzu ba hakuri garesu ba, ba kowa ne zai jure shashancin nan nata ba, haka ranan da Uwar Zainab ta zo da jikokinta yan biyu muna kasa a zaune daga nace Eeman ta dauko min jakata in basu dari biyar su siyi biscuit sai ga yarinya da akwati, kuma jakar fa akan akwatin yake, sai ta sauke jakar ta kinkimo min akwatin, to ina lafiya a nan" Ita dai Ammi bata ce komai ba, Mama Ladi ta mike tace bari dai inje inga halin da suke ciki, Mama Ladi na fita parlon sai da ta tafi dakin yan biyun ta bude kofar a hankali tana leka ciki, kwance taga Eeman tana shesshekan kuka, ta karasa cikin dakin tace "To wai me kika masa ne? Shi fa Usuman din nan dama ya saba cin zalin 'ya yan mutane, ji zamanin Badiyyah haka yayi ta narkarta kamar ya samu er banza, kema dai maganin ki kenan kullum baki da aiki sai makale masa kuna turanci, ai ga irin ta nan" Eeman ta mike zaune tana kuka a hankali, Mama Ladi tace "Gaya min me kika masa?" Zata yi magana aka bude kofar dakin, Eeman ta goge idonta da sauri ganin shi ne, yana tsaye daga bakin kofar yace "Wa kika bar ma sauran?" A hankali tace "Aunty Bilkisu tace in bar shi zata dauke" Ya daure fuska yace "Fito kije ki dauke" Sauka tayi daga kan gadon tana cika tana batsewa ta bi gefensa ta fita, Mama Ladi ta nufo Usman bayan Eeman ta fita tace "Gwara dai ka dinga yi kana seta mana ita kana mata jan ido, sam bata da kai, wani shegen za mu dauketa a haka mu kai masa salon wataran ya koro mana ita, kanta rawa yake kamar kararrawa"

Bayan fitan Mama Ladi parlon Ammi da kusan minti sha biyar aka bude kofar parlon a hankali, Ammi ta daga kai tana kallonsa, karasowa ciki yayi kansa a kasa, ya zauna kan carpet yace "Ammi ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya aiki?" Yace "Alhamdulillah" Tun da Mayraah taji muryansa ta rufe ido kamar tana bacci, Ammi tace "Dazu Mama Ladi ta gama cigiyarka ashe kana hanya" Maheer ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba, after a while Ammi ta mike ta fita daga parlon da cup din shayin da ta sha, tana kulle kofar Maheer ya mike ya tafi inda Mayraah ke kwance ya duka gabanta yana kallonta, sai kuma ya zauna murya can kasa yace "Mimi" Ƙin bude ido tayi still Pretending she is asleep, a hankali ya dagota, amma tana jin kamshin turarensa ta kasa resisting ta bude ido da kyar tana kallonsa, ya ɗan mata murmushi yace "Ya jikin? I am sorry i didn't come all this while, bana son maganan Mama Ladi ne billah, i just have to gather much courage in zo yau in ga jikin ki, Hope kina ɗan cin abincin?" Nan ma ta gyada masa, ya kalli Garden egg ɗake kusa da ita, yace "Shi kike ci?" Still ta gyada masa kai kawai, yace "Are you comfortable here?" kallonsa kawai take babu ko kiftawa, bude kofar parlon aka yi ya juya da sauri sai ga Mama Ladi ta shigo, dauke kai yayi, Mayraah ta zame jikinta ta koma ta kwanta, Mama Ladi tace "Bawan Allah, dazun nan na gama cigiyarka nace ko aikin ne yayi maka yawa kwana biyu shiru" Mayraah ta dinga kallonta tsabar mamaki, Maheer ya ɗan yi murmushi ya gaisheta tace "Lafiya lau Mashir, to da aiki zaka ji ko da zuwa dubiya kullum, ai mu da muke nan duk mun wadatar muna bata kulawa yanda ya kamata, ɗan uwanka kuwa har ya saka adashin Yalo da fiya duk dare, sai dai Allah ya saka masa" Shi dai Maheer bai ce komai ba ya mike ya koma kan kujera ya zauna, Mama Ladi tace "Sai kaji an kara sati biyu bikin Mendi da yarinyar nan Ihsaani ko?" Maheer yace "Eh haka yace min" Mama Ladi tace "To wai me yasa yace a kara sati biyun ne?" Maheer yace "Yana da wani taro da za su yi a ne a kasar waje, a satin bikin" Mama Ladi tace "Ba shakka, to Allah ya sa a cikin sati biyun ita ma er uwar ta samu mijin, ba dadi daya tayi aure ta bar daya" Maheer yayi murmushi yace "To ba ga abokin aikin MD dake sonta ba ku ka ce Aa" Mama Ladi tace "Kaji ka da wata magana, mata fa aka ce garesa da yara biyu, ina Eeman ina me mata? Ai ni ce ma nace ta ce masa an mata miji, Ammi ma ta goyi bayan hakan, gwara ta samu mijinta ita kadae, ranan ma ina zaune a dakin ta gaya masa an mata miji a gida, kaga da yake yana da hankali shikenan ya rabu da ita" Maheer yace "Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi" Mama Ladi tace "Ameen, na fi hango mata Usuman a abinda ya fi zama alkhairin" Shi dai Maheer bai ce mata komai ba, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ni ko zan so in ga irin zaman da Mendi zai yi da yarinyar nan Ihisani in sun yi aure" Sai kuma ta daga hannu sama tace "Allah Ubangiji yasa da ni za aje kai ta Canada din idan an yi bikin" Maheer na kallonta yace "Kamar ya wani irin zama za su yi?" Ta kyalkyale da dariya ta gyara zama zata fara koro masa bayanin abinda idonta ke gane mata duk in MD ya zo gidan wajen Ihsaan, don in dai ta lura ya zo to tayi ta zarya a parlor kenan kamar me nakuda ta shiga kitchen ta fito, taje dakin Bilkisu ta fito, ta tafi dinning ta fito, nan kuwa duk hankalinta na kan MD da Ihsaan, zata fara koro bayani kenan sai ga Ihsaan ta shigo parlon da sallama, ba shiri Mama Ladi ta canza maganarta ta

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login