Showing 282001 words to 285000 words out of 456519 words
jikin?" Tace "Ai naji sauki tuntuni" Ta kalli abincin dake kasa cikin warmer, ta durkusa ta bude tace "In zuba maka abincin?" Yace "Lokacin sallah yayi ai, sallah zan yi first" Zaunawa tayi saman carpet din tace "Ohk i will wait, idan kayi sai in zuba maka" Murmushi yayi yace "Ke baza kiyi sallan bane?" Sai a sannan ta daga kai ta kalli Usman dake kallonsu, sai taki cewa komai kawai ta sunkuyar da kanta ta tallabi chin dinta tana murmushi, shi dai Usman wayarsa kawai yake dannawa, Mikewa tayi tace "Idan an idar da sallah zan dawo Yaya" Yace "Ohk" Usman ya dau wayar Aunty Mariya ya mika mata yace "Ki kai ma Aunty wayarta" Amsan wayar tayi sannan ta fita daga dakin, Usman na kallon Maheer yace "Za ka iya zuwa masallacin ne?" Maheer yace "Let's pray here" Mayraah na komawa daki ta debi abincin da Ammi ta kawo mata dakin, a hankali take cin abincin, lkci daya jikinta yayi sanyi bayan ta tuna incident din da ya sa tayi kusan sati uku a asibiti, duk son ta da abincin sai ta kasa cin da yawa don nan da nan ya fita ranta, daga karshe ta rufe kawai ta mike a hankali ta koma saman gado ta kwanta incident din na dawo mata a kai vividly, bayan minti ashirin taji an bude kofar dakin, juyawa tayi da sauri taga Usman tsaye bakin kofar dakin ta mike zaune kafin tace komai yace "Ya idar da sallahn, ki je ki zuba masa abincin" Ta sauko daga saman gadon tace "Toh" Sai kuma da sauri tace "Yaya kai ka ci abincin?" Yace "Sai anjima" Daga haka ya bar bakin kofar ta fita zuwa dakin Maheer, yana zaune saman darduma ta samesa da counter a hannunsa, ta kulle kofa ta karaso ta durkusa kusa da shi tace "Ka gama yaya?" Yace "Na gama" kallonsa ta dinga yi ganin yanda ya rame, da damuwa tace "Yaya for how long were u sick?" Da fingers dinsa ya nuna mata alamar 2 days, bata sake cewa komai ba ta bude warmer din, same food ne da wanda ta ci dazu a dakinta, ta debar masa ta sa cokali sannan ta koma gefe ta zauna tana kallonsa, sauke idonsa yayi ya dau spoon din ya fara cin abincin a hankali, bayan few minutes yayi breaking silence din dakin yace "I heard MD yayan Musharraf ne ko...." Mayraah ta wara ido tace "Yaya i was very very shock, it was the least thing I expected yaya.... Kuma fa basa kama, kawai dai suna da same thick eye brow with fingers, apart from that i see no resemblance, or may be their noses look alike also, sannan yanayin halinsu ma iri daya wallahi, at times fa idan MD din yayi wani abu sai Musharraf ya fado min, attitude dinsu is almost same, just that Musharraf baya ba irrelevant issues relevant kamar MD, ashe shi MD da Maminsu yake kama, yaya that very day kawai sai nake ganin abun kamar a mafarki wallahi, what a coincidence...." Murmushi kawai Maheer yake yana cin abincin gabansa yana sauraronta, don kanta tayi shiru, ya daga kai ya kalleta yace "Kamar dama kina jiran wannan tambayar ki fara amayar da abinda ke ranki?" Mayraah tayi er dariya tace "Wallahi na rasa da wanda zanyi labarin, i was so shock and confused at the same time, sai nayi regretting abubuwan da na dinga masa a asibitin" a hankali ta karasa maganar, Maheer na kallonta yace "Wasu abubuwa kika dinga yi masa?" Mayraah ta ɗan langwabar da kai tace "Ko da yake shine ai ya janyo duk abinda nayi masa" Maheer yace "Gaya min abinda kika masa" Zata yi magana aka bude kofar dakin, duk suka daga kai, Ammi ce tsaye bakin kofar dakin, mamakin abincin da Maheer yake ci tayi, don for the pass 5 days sai dai ya sha tea kadan ko kuma ya sha fruits amma ba dai abinci ba, ko da ta tilasta sa ya ci abincin to cokali biyu zai yi da kyar, yanzu kuma taga ya ci da ɗan yawa, Mayraah zata mike Ammi tace "Yi zaman ki, ke kin ci abincin ne?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na ci" Rufe kofar Ammi tayi ta bar wajen, Maheer ya kalli wayarsa dake vibrate ya dauka yana kallon screen din, can ya kalli Mayraah yace "Shi yake kirana" Mayraah ta buda ido sosai tace "MD din?" Maheer ya gyada mata kai sannan yayi picking call din ya kai kunne tare da sallama, gaisawa suka yi sannan Maheer yayi shiru yana sauraron sa, can yace "Ohk zuwa yaushe kenan?" Daga karshe dai Maheer yace "Alright, ba damuwa" Katse wayar yayi, Mayraah dai sai kallonsa take eagerly taji abinda MD yace masa, bayan ya ajiye wayar da sauri tace "Yaya me yace maka?" Maheer ya ja hancinta yace "Cewa yayi akwai sauran drip uku da za a saka maki a asibitin da kuma allurai 5, wai a maido ki yanzu" Mayraah bata san sanda ta hade rai ba tace "Aa ko ba drip ba, sai dai ya sa ma kansa, ni dai kowa yasan na warke" Dariya Maheer yayi, tana ganin haka ta marairaice tace "Pls be serious mana yaya, nasan ba haka yace maka ba, don Allah ka gaya min me yace maka?" Maheer ya ajiye spoon din hannunsa a hankali yace "Cewa yayi zai zo gida mu hadu, he wants to discuss an issue with me" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa a ranta kuwa sai nanata issue din take, bude kofa aka yi duk suka juya, Usman ya shigo ya ajiye ma Mayraah leda a kusa da ita yace "Wash the fruits for him" Ta bude ledan tana lekan ciki sai kuma ta kallesa tace "Yaya ni fa?" Yace "Au zaki sha ko?" Ta wani turo baki tana kallonsa, yayi murmushi yace "It's for the both of you" Ta washe baki tace "Toh mun gode yaya" Tare suka fita dakin da shi, ita ta wuce kitchen zata wanko fruits din shi kuma ya haura sama.
Bayan isha Maheer ya fito parlor bayan MD ya kirasa ya sanar masa yana waje, Ammi na zaune parlor tare da mai aikinta, Ammi ta bi sa da kallo tace "Ina kuma zaka?" Ya dawo yana kallonta yace "Dr Aliyu ne ya kirani, yace za mu yi discussing wani issue, so yana kofar gida" Da wani expression Ammi tace "Waye kuma Dr Aliyu?" Maheer yace "MD...." Da mamaki Ammi tace "MD kuma? Discussion akan me kenan?" A hankali Maheer yace "Shine zan fita in ji, bayan magrib ya kirani zai zo, so he is around now" Ammi da taji hankalinta ya tashi ta mike, kafin tace komai Maheer yayi saurin cewa "Look Ammi, ni nafi tunanin discussion ne akan abinda ya shafi lafiyar Mayraah ba wai wani abu bane...." Shi kansa bai san sanda ya fada mata haka ba ko hankalinta zai kwanta, bai san furucin nasa kara daga mata hankali yayi ba, cike da damuwa tace "Na shiga uku, kar dai sun ga wani abu ne Maheer, dama wannan farin likitan na ta exaggerating akan liver, wai ko poison din ya taɓa nan..." Maheer ya ɗan yi murmushin karfin hali yace "Ni nasan ba haka bane kar ki wani daga hankalinki, zan je in ji koma menene in dawo yanzu" Daga haka ya fita daga parlon, Bilkisu na kallon Ammi tace "Ki kwantar da hankalinki Ammi in sha Allahu babu komai" Ammi dai bata ce komai ba ta koma ta zauna zuciyarta na bugawa. Maheer was confuse, ya dai kafe ido kan result din DNA test da MD ya basa a cikin motarsa, bayan wasu yan dakikai ya kalli MD yace "I am confuse na meye wannan din, naga sunan Mayraah, and dayan babu suna, ban fahimci komai ba, meye ma'anar hakan?" MD yace "I am also confuse just like you, CEO dinmu ce zata warware mana komai... All i know is that 8-9 days back ta kai ni gidanta da daddare ta sa na dau sample din jinin wata mata, muka dawo asibiti tasa na debi jinin Mayraah, ta kuma umarce ayi Genetic testing, dazu result din ya fito and this is what i am seeing" Kallonsa Maheer yake babu ko kiftawa, MD kamar yasan abinda ke ran Maheer yace "Look da ace bani na dau sample din jinin ba nima it won't make any sense to me, but i am telling u ni na dau jinin nasu da hannuna...." Maheer da kansa ya gama kullewa yace "Then what does this mean? It's showing postive, who is the woman?" MD yace "Shi yasa nace maka Ceo ce zata warware koma menene don matar na gidanta, and from the look of things she is not mentally stable" Maheer ya sake kallon results din hannunsa da mamaki, he was totally speechless, MD yace "Naga kafi wancan ɗan uwan naka hankali da sanin ya kamata shi yasa na amshi number gun Dr Khalil na kira ka mu hadu" Maheer ya dago kansa yace "Ni fa na rikice, yanzu me Ceo din ke cewa?" MD yace "You know what will happen now?" Maheer ya girgiza kai, MD yace "May be u should talk to ur dad about this Asap, sai aje gidan Ceo don ita ce zata yi bayanin wacece wannan matar wanda DNA test ya nuna ita ce mahaifiyar Mayraah, you are a Dr, and i am also a Dr, mun san babu karya a DNA test, although i know this isn't enough evidence a wajenka da ma family dinka tunda ba a gabanku aka dau jinin ba, kuma ni nasan dole za a sake wani test din don clearing doubt din kowa wanda kai da kanka zaka debi both samples ka kai duk inda ka yarda ayi test din" Maheer yayi nisa tunanin da ya fada lokacin, sai a sannan maganganun Ammi suka dinga dawo masa yanda ta dage bata yarda da ceo akan kulan da take ba Mayraah ba, kullum zancenta kenan tun kan wannan incident din ya faru na poisoning Mayraah, Maheer ya girgiza kansa don har sannan shi fa ya kasa assimilating lamarin yace "To amma me ita ceo din ke cewa akan result din?" MD yace "Kuka kawai take ta kasa min bayanin komai, ban kuma zo nan gidan ba sai da saninta, kaga she is willing to reveal who the woman in her house is" Maheer yace "Gobe da safe Abbanmu zai dawo, zan masa duk wannan bayanin, nasan kuma a goben za mu je har gidan Ceo din, amma pls ita matar da ka debi jinin ta muslma ce?" Zuciyarsa na bugawa yayi tambayar, a hankali MD yace "I can't really tell, don nace maka she is not mentally stable" Maheer ya kasa cewa komai ya jinginar da kansa da kujeran motar. Har Maheer ya shiga gida kansa a kulle yake, ya zama so confuse nan da nan kansa ya fara ciwo, Ammi dake ta jiransa ta mike da sauri gabanta na faduwa tace "Ya aka yi Maheer?" Yayi yake yace "Ba komai fa Ammi, kawai wasu magunguna wai za a daurata a kai na yan watanni" Ammi ta fashe da kuka tace "Dama ba na fada ba, kilan sun hango wani mugun abun ne" Maheer yayi dariyar karfin hali yace "Kai Ammi, amfanin maganin fa kawai wanke duk wani system dinta zai yi ne tunda poison din me karfin gaske ne, amma wallahi basu ga komai ba, kuma a likitance haka ya kamata su dorata kan magani, ina jin sun mance basu rubuta maganin bane da suka sallameta" A haka dai ya samu ya kwantar ma Ammi hankali, sannan ya wuce dakin Usman, shi ma ya sanar masa duk yanda suka yi da MD, Usman was also speechless ya dinga kallon Maheer, Maheer yace "Yanzu zan koma daki in kira Abba in sanar masa tun kafin ya dawo, don wannan issue ne da ya kamata a daukesa da muhimmancin gaske" Usman yace "But how are we to believe this bayan ba a gabanmu aka debi jinin da aka yi test din ba" Maheer yace "Duk za a zo wajen, kai ma kasan dole ne za a sake wani test din to clear everyone's doubt" A hankali Usman yace "Amma ita matar da ya debi jinin nata musulma ce?" Maheer ya sauke idonsa kasa yace "He said she is not even mentally stable" Usman ya dinga kallonsa babu ko kiftawa. Washegari Abba Flight din safe ya biyo daga kano zuwa garin Abuja, Ammi tayi mamaki sosai don da yamma ya kamata ai ya dawo ba da sassafe haka ba, ta dai yi welcoming dinsa, ko zama bai yi ba yace "Ki shirya za mu fita ne Hajiya" Da mamaki tace "Zuwa ina Yallabai?" Yace "Za mu je gidan Ceo din nan ne mu yi mata godiya kafin ta bar kasar" Nan da nan Ammi ta hade rai tace "Godiyan me kuma Yallabai? Ina ce biya muka yi..." Abba yace "Wa yace maki an biya? Au wai dama baki san bata amshi ko sisi a hannunmu ba? To a kaddara ma mun biya din laifi ne don munje mun ma warce ta ceto ran er mu godiya? Daga kasan waje fa ta taho da manyan likitoci, me yasa kike yin haka Madam?" Ammi dai ta kauda kai bata ce komai ba, Abba yace "Ina parlor ina jiranki" Daga haka ya fita ya koma downstairs, Ammi babu yanda ta iya haka ta shirya ta sauko downstairs din ko su Aunty Mariya bata sanar ma ba, da mamaki take kallon Mayraah tace "Ke kuma ina za ki?" Abba yace "Ni nace ta shirya mu je tare" Ammi tace "Haba yallabai, duka duka yaushe ta farfado ai yayi wuri ta fara fita yanzu nake ga" Maheer dai sai kallon Ammi yake, haka ma Usman dake parlon, Usman yace "Abinda mota ne Ammi, zama kawai fa zata yi a mota" Abba yace "Shi dai na gani, ku tashi mu tafi" da mamaki Ammi tace "Su kuma ina za su?" Abba ya kwantar da murya yace "Kina bata mana lokaci ranki shi dade" Daga haka ya fita, Usman ya bi bayansa, Mayraah dai ta mike tsaye tana kallon Ammi dake ta kallon Maheer, rai bace Ammi tace "Wato har da ku kenan za aje? To wai meye ma'anar haka? Haka duk sauran patients din asibitin suke idan sun warke su je gidan Ceo yi mata godiya?" Maheer yayi kasa da murya yace "Ke dai don Allah tunda yace mu je kawai mu je Ammi, ai ina ga ba wani abu bane don anje an mata godiya duba da yanda aka bamu full attention a asibitin kuma saboda Mayraah staff dinta ce ta taso tun daga kasar waje da wasu likitoci, relax plss Ammi" A haka dai ya lallabata suka fita zuwa motar Abba dake jiransu, tun asuba Maheer ya kira MD yayi sending masa address din gidan Ceo kamar yanda Abba ya bukata, suna shiga motar Abba da kansa ya ja motar suka bar gidan zuwa gidan Ceo.
[8/27, 9:50 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: A cikin babban compound din gidan Abba yayi parking bayan mai gadi ya bude masa gate, MD yayi leading dinsu har cikin parlon gidan don tun basu iso ba Maheer ya kirasa ya sanar masa suna hanya, Ammi dai ta rasa dalilin da yasa gabanta ke ta faduwa tun da suka baro gida, MD ya kara gaida Abba a parlon, Abba ya amsa da fara'a yana kallonsa, ita dai Mayraah na zaune kusa da Ammi sai da suka hada ido da Ammi ta sauke idonta ta gaishesa, amsawa yayi ya tambayeta ya jiki, tace "Alhamdulillah" Kamar yanda MD bai kalli direction din Usman ba balle su gaisa haka shi ma Usman ko kallon inda yake bai yi ba, ita dai Ammi ta kagu ayi godiyar da Abba yace su koma gida, ba a wani dau lokaci ba Ceo ta sauko downstairs sanye da doguwar riga sai rosary dake wuyarta, Mayraah dai sai kallonta take har ta karaso cikin parlorn tana tafiya a hankali, tun da Ammi ta kalleta sau daya ta dauke kai, cikin sanyin murya Ceo ta gaisa da Abba sannan suka gaisa da Ammi ma, Maheer da Usman ma suka gaisheta ta amsa da murmushi fuskarta, tana hada ido da Mayraah, Mayraah ta gaisheta, Ceo ta sauke idonta ta amsa cikin sanyin murya sannan ta zauna parlon, tana kallon Ammi tace "Ya ta kara ji da jiki?" Ammi tace "Alhamdulillah, ta ji sauki" Ceo tace "Toh Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Ammi tace "Ameen" Ceo tace "Ko a kawo breakfast, since it's still early" Da sauri Ammi tace "Alhamdulillah, mun yi breakfast" Ceo tayi shiru bata sake cewa komai ba, daga Abba har su Maheer da MD kallonta suke, ita kuwa Ammi tana ta jira ayi godiya su fita parlon, kuma taji duk an yi shiru, Bayan few seconds a hankali Ceo tace "Nasan Aliyu ya kai maku wata magana me ban al'ajabi ko kuma ince that is confusing but not hard to believe, don da hakan bai yi making any sense a wajen ku ba baza ku fara zuwa gidana ba, amma it made a lot of sense because..." Sai kuma tayi shiru kanta a kasa Abba da su Maheer dai kallonta kawai suke, Ammi taji gabanta ya yanke ya fadi ita duk zaton ta zargin da tayi jiya na cewa ko an gano wani illan da poison din yayi ma Mayraah ne ya tabbata, ita kanta Mayraah jin abinda Ceo tace sai da ya daga mata hankali a lokacin, Calmly Abba yace "Muna bukatan more highlight on that, yes it made sense but we need explanation" Ammi ta kalli Abba hankali tashe tace "Yallabai me ke faruwa?" Abba na kallonta cikin kwantar da murya yace "Ki kwantar da hankalin ki, kuma ina nema alfarman kar ki sake cewa komai a parlon nan, just listen" Ammi ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Ceo na kallon Abba a hankali tace "Ranan 5 ga watan 5 a garin Adamawa, shekaru ashirin da biyu da suka wuce an