Showing 432001 words to 435000 words out of 456519 words
marairaice tace "Yanzu yaya kake yi da abinci in ka dawo daga gun aiki ba mata a gida?" Murmushi Maheer yayi ya mike ya fita daga parlon bayan ya amsa gaisuwan Ihsaan. Tun daga ranan duk bayan kwana biyu sai Maheer ya zo gida duba Mayraah, duk in zai zo kuma abinda yaga take iya ci yake siyo mata, a gefe guda kuma ana ta shirye shiryen bikin Ihsaan da MD, Eemaan kuwa ta tsiri avoiding Usman a gidan, dama tana jin shigowar motarsa zata shige dakin Ammi wani lkcn ma nan take bacci, da safe kuwa sai ta tabbatar ya fita take fitowa, duk Mama Ladi na kula da ita.... Mayraah na zaune parlon Ammi ita kadai tana cin shinkafa da mai da yaji bayan magrib don haka tace take son sa, zuwa yanzu kam jikinta da sauki ba laifi, har Ammi nata mamakin ita laulayin na wata biyu kacal tayi, komai yanzu tana iya ci, Maheer ne ya shigo parlon da sallama, ya karaso kusa da ita yana kallonta yace "Me kike ci haka?" Kallonsa tayi ta ci gaba da cin abincinta, ya ajiye ledan yoghurt din hannunsa da tace ya siyo mata, ya zauna yana kallon abincin ganin yajin da ta lafta yace "Baya maki yaji ne Dear?" ajiye cokalin tayi don dama ta gaji da cin abincin, yace "Ina su Ammi fa?" Tace "Sun je dubiya da Mama Ladi da Eeman" Yace "Dubiya kuma? Waye ba lafiya?" Tace "Ummi, anyi admitting dinta a hospital daxu" Yace "Allah ya sauwake, driver ne ya kai su?" Mayraah ta gyada masa kai, A hankali ta matsar da abincin daga kusa da ita, yace "You need anything?" Ta kallesa cikin sanyin murya tace "Kamar ice cream nake son sha ba yoghurt din ba" Yayi kasa da murya yace "Ko muje in siya maki ice cream din mu dawo kafin su Ammi su dawo daga hospital din" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike ya dagota yace "Come on Baby, ai ba dadewa za mu yi ba" Daki ya tafi ya dauko mata Hijab dinta don dama dogon riga ne jikinta tayi wanka kenan ta fara cin abincin da Bilkisu ta kawo mata, dakansa ya sa mata Hijab din, ta marairaice tace "In su Ammi suka dawo fa?" Yace "I assure you za ma mu riga su dawowa, nearest ice cream spot za mu je in siya maki" Daga haka ya kama hannunta suka fita daga parlon.
[10/30, 10:03 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: A hankali Mayraah ta bude ido ta dalilin yunwan da ya dameta cikin bacci, da mamaki take tattaba gadon da take kwance duk da duhun dakin, how did she manage to get here, tunda ta dawo gidan Ammi bata kwanta saman gado ba, dakin ma gaba daya bata so a parlor take kwanciya kan shimfida, garin yaya kuma take jin ta kamar a kan gado, da sauri ta mike zaune tana zaro ido trying to figure out where she is, Maheer dake zaune saman darduma ya idar da sallah ya juya yana kallonta duk da ba wani haske ne da dakin ba, can ya mike ya kunna wutan dakin, he can see how shocked she was tana kallonsa kamar idanunta za su fito, ya karasa kusa da ita ya zauna gefenta yace "Baby kin tashi" kamar zata yi kuka cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku yaya, idan su Ammi suka dawo fa?" Ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Nayi ta tashin ki in maida ke gida kika ki tashi Baby, at the end kika ce in kyaleki" Mayraah ta fashe da kuka tana kokarin sauka daga saman gadon, sai kuma ta rufe jikinta da sauri da duvet ta wani kallesa, kuka ta fara rera masa kamar er yarinya, muryarta na rawa tace "Don girman Allah ka rufa min asiri kai maida ni gidan kafin su dawo" Maheer ya ɗan yi murmushi ya dauke kai bai dai ce mata komai ba, ta lallaba ta sauka daga kan gadon ta jawo clothe dinta cikin few seconds sai ga ta ta shirya ta saka har hijab dinta tana kallonsa tace "Ni ka tashi ka maida ni gida plss" Ya juya ya kalleta, calmly yace "Kin san karfe nawa kuwa?" Ta wani zaro ido ta nufo sa ta duka gabansa cikin tashin hankali tace "Karfe nawa?" Ya dau wayarsa dake kan bedside drawer ya kunna ya nuna mata agogo, bata san sanda tayi wani kara ba ganin karfe biyu da rabin dare, Maheer yace "Ke, baki san dare bane Mimi?" Tayi zaman dirshan kan carpet tace "Na shiga uku na lalace" Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana rusa kuka, shi dariya ma take basa, ganin da gaske take kukan ya dawo kasa ya zauna kusa da ita yayi kasa da murya yace "Wallahi na tasheki kika ki tashi Mimi, har masifa kika min in kyale ki" Ita dai kuka kawai take kamar an aikota, babu warce ta tsaya mata a rai lokacin kamar Mama Ladi, da ta tuno Mama Ladi sai ta kara sautin kukanta, shikenan ta shiga uku ta lalace kuma wajen Mama Ladi, Maheer ya dukar da kansa dai dai fuskarta cikin kwantar da murya yana murmushi yace "Kawai ba sai mu ce baki da lafiya bane na kai ki hospital aka sa maki drip karami, zan iya sa maki Cannula ma a hannu da sassafe sai mu tafi can gidan mun ce daga hospital muke, dama ga sauran magungunanki a nan da ban kai maki ba sai mu tafi da shi like wanda aka baki a hospital" Sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta cikin rawan murya tace "Baza su gane ba?" Ya gyara zama yace "Ba wanda zai gane mana, ga dai cannula zan sa maki a hannu, infact sai mu tafi da karamin drip ince ai ance karfe tara na safe a kara sa maki wani drip din, kawai around 9am sai in koma in sa maki drip, no body will suspect anything" Mayraah ta fara shara hawayen idonta a hankali alamar she is convinced with his plan, sai kuma ta wani kallesa kamar zata fashe da wani kukan tace "Da naki tashi ba sai ka daukeni ka kai ni motar haka ba, ai in dai na ji ni a mota dole zan tashi" Yayi kasa da murya trying hard not to laugh yace "Billah dubaran hakan bai zo min ba wife" Tace "To yanzu karfe nawa za mu tafi can gidan?" Yace "As early as 7am in sha Allah" Ta cire hijab dinta ta ajiye gefe tace "Toh ni yanzu yunwa nake ji" Yace "Ohk za ki ci Indomie?" Shiru tayi tana tunanin ko zata iya cin Indomie, tun da ta fara laulayi bata ci Indomie ba don sam ji tayi bata son ko kamshinsa, yanzu kuma da yace Indomie sai taji tana sha'awarsa, ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake babu ko kiftawa, ya sakar mata murmushi yace "In dafa maki Indomie din?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Amma ina son yayi yaji" Yace "To ai ba Fresh pepper a gidan wife" Tace "Akwai dakakke a kitchen din mana ka duba sai ka sa min a Indomie din" Yace "Ohk dear, how about egg? Should i fry or cook it for you" Tace "Just cook 2" Yace "Alright baby, but kafin in gama kije kiyi wanka pls" Bai jira cewarta ba ya dagota ya fara undressing dinta ya kai ta har cikin bathroom din sannan ya baro ta ya fito ya tafi kitchen don dafa mata Indomie din. Mayraah na kwance ta dukunkune da bargo bayan ta fito daga wanka, har bacci ya dauketa Maheer ya shigo dakin da plate din Indomie da ya dafa mata a kan tray da bottle water da fork, ya karaso ciki ya ajiye tray din kan carpet sannan ya nufeta ya zauna kusa da ita ya yaye duvet din yana kallon lallausan jikinta, a hankali ya kai forehead dinsa saman nata yana shafa chest dinta yayi kasa da murya yace "Ur food is ready Mimi" Baccinta kawai take, ya ɗan yi murmushi ya dagota yace "Tashi ki ci abincin Baby" Bata bude ido ba tana kokarin komawa ta kwanta yaki barin ta ta kwanta yace "Baby ga abincin fa na gama" Kamar dazu da ya dinga tashinta ya maidata gida yanzun ma ƙin tashi tayi, baccin take as if her life depends on it, da ya takurata ta tashi ta sakar masa kuka tana tura sa, hakan yasa kawai ya kyaleta yana murmushi ya rufa mata duvet din ya tafi kitchen ya dauko plate ya rufe Indomie din sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta gefenta. Bude kofar dakin da aka yi ne ya farkar da Maheer ya bude ido yana bin ta da kallo har ta fita daga dakin, ya mike zaune yana kallon tray din abincin da ya ajiye mata, tas ta cinye Indomie da kwan, ruwan goran ma ta shanye, ya dau wayarsa yana duba agogo yaga karfe hudu da rabi, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo dakin rike da bread da ta gani kan dinning, ta karaso ciki, yana kallonta yace "Baki koshi bane?" Ta ɗan yatsine fuska tace "Kawai ina son in ci bread din ne" Yace "Ohk, should i get u jam or butter?" Ta girgiza masa kai ta zauna kan carpet ta fara cin bread din, basu sake komawa bacci ba har aka yi sallan asuba. Mama Ladi na zaune wajen karfe bakwai da rabi na safe a parlon Ammi, Ammi dai laziminta kawai take tana kallon Mama Ladi da tun da gari ya waye ta shigo mata take zance daya, bude kofar parlon aka yi Bilkisu ta shigo da tray dauke da shayi da bread sukutum, sai soyayyen kwai a kan plate, tunda Mama Ladi ta xo gidan dama Bread dinta babba daya ne babu me yaga a ciki, kuma tas take cinye kayanta in ma ta rage zuwa take ta ajiye sauran saman akwatin ta, Ammi ta sauke boyayyen ajiyar zuciya kilan yanzu da taga kumallo zata hakura da zancen da take tun daren jiya, Bilkisu ta ajiye tray din gaban Mama Ladi sannan ta zauna ta gaisheta, Mama Ladi bata amsa ba ta dau spoon ta debo ruwan shayin ta kai baki don tabbatar da kaurinsa, ta gyada kai jin komai yayi dai dai tace "Lafiya lau Balki, to ke a jiyan sanda za su fita a kitchen kika hangosu ko daga cikin dakinki kika hangosu?" Bilkisu tayi murmushi tace "Aa fa Mama, na fito kitchen kenan" Mama Ladi tace "Ikon Allah, kuma baki tambayesu inda za su ba?" Bilkisu har snn murmushi take bata ce ma Mama Ladi komai ba, Mama Ladi tace "Je ki kawai, dama ke me aiki ina ke ina tambayarsu inda za su" Bilkisu ta fita ta kullo masu kofa, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Mu dai ai saboda Allah mu ka yi ba don wani shege ba, kuma Allah shi zai bamu lada, amma don ta munafurce mu ta kira mijinta bayan fitarmu tace ya zo ya dauketa ai kanta tayi ma ba mu ba, sanda take ganiyar laulayi ai har lambarsa mantawa tayi, matar dake kwance kamar ba rai a jikinta sai in kai ka ji tausayinta ka muskutata, wato sakayyar da zata mana kenan, mutumin da ina jin sai da ɗan uwansa ya zaga ya kirasa yayi masa fada tunda ba lissafi ke garesa ba snn ya fara zuwa dubata a gidan nan, don ranan da nayi ma Usman kwamfulan da safe ke kuma na maki da yamma sai gashi sumui sumui kamar agwan da aka yi ma satar shanu ya shigo mana parlor kai a kasa, bazan boye maki ba in nace raina bai baci akan abinda yaran nan suka mana ba nayi ma Allah karya, ko baccin kirki ban yi daren jiya ba, duk fadi tashin da muka dinga yi akan munafukar yarinyar nan kamar mu muka mata cikin bata gani ba, ni ce dama kunun masara ba dare ba rana a gidan nn har sai da fuskata ta fara canza launi sbda zafin wutan gas, na dawo kamar wata me blitting amma da abinda Mera zata saka min kenan, ke ko kullum cikin wanke amai a bandaki da kin wanke da ta kirba, wallahi don dai naka naka ne amma da Allah ya isa kawai zan ja masu bakina alekum...." Bude kofar parlorn da aka yi yasa Mama Ladi tayi shiru ta juya, sosai gaban Mayraah ya fadi bayan sun yi ido hudu da Mama Ladi, ji tayi kamar ta juya, can dai ta dake ta sunkuyar da kai tana tafiya a hankali ta karasa cikin parlon, juyawa tayi ta kalli kofa tana jiran Maheer ya fara koro bayani taga wayam ashe bai shigo ba, bata san sanda ta gwalo ido ba cikin tashin hankali, muryar Mama Ladi taji tana cewa "Shimfidan naki kika dawo dauka, yana can dakin ki an linke an kai an ajiye maki, ga sauran yalonki ma can an kulle a leda an cikin firij sai ki hada da shi" Mayraah ta fara matsar kwalla cikin sanyin murya tace "Daga asibiti fa muke" Ammi dake kallonta tace "Asibiti?" Mayraah ta gyada mata kai da sauri tace "Dama ai jiya da safe nace maki ina jin jiri, shine da ya zo sai muka je asibiti, ko gama kara min ruwan ba ayi ba yace zai sa min kawai a gida" Ammi tace "Amma me yasa bai kira yace kuna asibiti ba?" Mikewa Mama Ladi tayi ta dau tray din kumallonta ta nufi kofa ta yanda rainin hankalin bazai shafeta ba ta fice ta bar masu parlon, Ammi na kallon Mayraah tace "Ina Maheer din?" Ta juya ta kalli kofa kamar zata yi kuka tace "Dama ashe bai shigo ba" Ammi tace "To kin ci abinci?" Mayraah ta girgiza mata kai, Mikewa Ammi tayi ta fita daga parlon, Mayraah ta sauke wani ajiyar zuciya ta tafi ta zauna kan kujera, wato dama wayo yayi mata ba shigowa zai yi ba, ta wani hade rai kamar yana wajen yana ganinta, Ammi bata dade da fita daga parlon ba Mayraah taji an bude kofa ta juya da sauri, Eeman ce ta shigo parlon ta nufi dakin Ammi da sauri tana gaida Mayraah da ta bi ta da kallo har ta shige dakin, ko minti biyu ba ayi ba sai ga Usman ya shigo parlon, Mayraah ta gaishesa ya amsa yace "Eeman ta shigo nan?" Mayraah ta kalli kofar dakin Ammi, bai jira cewarta ba ya karasa cikin dakin yaga bata ciki alamar ta shige bandaki, ya juya kawai ya fita, Mayraah ta bi sa da kallo har ya fice daga parlon.
[11/1, 2:00 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah ta bude kofar kitchen tun kan ta fito ta hango Mama Ladi zaune a parlor har ma sun hada ido da ita, da sauri ta juya ta koma kitchen din tana wondering yaushe ta sakko downstairs, Mama Ladi ta kalli Eeman dake kusa da ita tace "Maza je ki gano ko abinci ta zuba" Eeman ta mike ta nufi kitchen din da sauri, Mayraah ta fara cin abincin hannunta tana kallon Ihsaan dake girkin don bai ma dahu ba ta sa ta zuba mata, tace "Idan na fita don Allah ki kawo min abincin sama, in ma Mama Ladi ta tambayeki na wanene kice ke za ki ci" Ihsaan na murmushi tace "Toh Aunty" Sai ga Eeman ta shigo kitchen din, ta gefen ido ta kalli Mayraah sai kuma ta nufi fridge ta bude ta dau ruwan gora ta dauko cup ta ɗan debi ruwan kadan ta sha ta mayar da sauran cikin fridge, ko da wasa bata bari ta hada ido da Mayraah ba balle Ihsaan, ta juya ta fice daga kitchen din ta kullo kofa, Mama Ladi sai jiran fitowarta take, Eeman ta karaso ta zauna kusa da ita tayi kasa da murya tace "Shi ta zuba" Mama Ladi ta saki salati tace "Shi ta zuba? Duk ita ta cinye abincin dazu da bai ishi jama'an gida ba fa, tun bai sauka ba ake ta zuba mata take ci, duk yau babu wanda ya koshi a gidan nan tsabar yanda tayi ta narkan abinci kan a raba ma kowa hakkinsa, a gaskiya Mashir ya zo ya tafi da matarsa kuma haka tunda ta samu lafiya, mata tana ta ci da haƙƙin jama'a a gidan nan, in kuma bazai dauketa ba to ya kamata yayo cefane na kayan abinci ya kawo gidan nan, idan ya so sai a dinga kara rabin kwana a kan yanda ake girkin, shi yanzu ba don auren gida bane ya isa ya kai ta gidan iyayenta a halin da take ciki bazai yi masu guzurin kayan abinci ba, shi ko tausaya ma ubansa bai yi, a rana sai Mera ta sha shayi sau biyar a gidan nan duk muna zaune daga na safe sai na safe, ai ko ni dai zan kirasa in basa shawaran ya siyo kayan abinci kar uban yaga rashin hankalinsa ya kawo yarinya ya ajiye masa ba ko kwayar hatsi" Fitowar Mayraah ne ya sa Mama Ladi tayi shiru, Mayraah dai bata kalli direction dinta ba ta wuce sama da goran ruwa a hannunta, Mama Ladi ta bi ta da kallo murya can kasa tace "Ikon Allah" Eeman dai sai murmushi take kamar wata sabon kamu, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Naga ma har wani mazaunai tayi, to yaki halal yaki haram, ta ci nata ta ci na wani" Da sauri Eeman ta kwanta kan kafar Mama Ladi ta rufe ido jin sallaman Usman, Mama Ladi ta amsa tace "Sannu da zuwa Usuman" Ya karaso ya zauna parlon ya gaisheta ta amsa tace "Ya aikin? Ko ba aiki kaje ba" Bai ce mata komai ba yana duba wayarsa da kira ya shigo, Ihsaan ce ta fito kitchen rike da plate din abincin Mayraah da ta rufe da wani plate din, Ihsaan ta gaida Usman sannan ta wuce sama, Mama Ladi tace "Yau dai Allah ya sa abincin nan