Showing 456001 words to 456519 words out of 456519 words

Chapter 153 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70653

jin bai sani ba da zai gaya mana, shi ma zan ce ya kira uwar yayi mata gaisuwa" Sosai jikin Mayraah yayi sanyi, a hankali tace "Allah Ubangiji yayi mata rahama, ya yafe mata kurakuren ta" Ammi da Badiyyah suka ce "Ameen" Badiyyah na kallon Ammi tace "Ammi kuna waya da Mama Ladi kuwa?" Ammi tayi dariya tace "To ko daxu da safe sai da muka yi video call da ita, ai in gaya maki Mama Ladi na can ta zama wata bukekiya tayi fresh abun ta, da Glasses ma take yawo yanzu" Badiyyah ta zaro ido tana dariya tace "To ya take operating Babban wayar?" Ammi tace "Kinsan Mama Ladi bata da duhun kai, wai ɗan mijin nata ke nuna mata yanda zata dinga amfani da wayar kan kace me har ta haddace, bini bini kya ga ta doka maka Video call, ta ce min ma jiya suka dawo daga New york da me gidan nata" Dariya Badiyyah ta dinga yi tace "Haka tace New york?" Ammi na dariya ita ma tace "Yu york tace min, ni kuma na fahimci me take nufi...." Sai da Mayraah tayi dariyar da bata yi niyya ba don tun da taji mutuwar Haeeenah jikinta ya mutu, Badiyyah ta dinga dariya Ammi na taya ta. Maheer da Mayraah sun bar Nigeria zuwa US da sati uku Eeman ta haifo yan biyunta kyawawa duk mata, kwana biyu ne tsakaninsu da Ihsaan da ta haifi santalelen ɗan ta namiji a Canada, labari na zuwa ma Mama Ladi cewar Ihsaan din Mendi ta haihu tace ma Attajirin me gidanta Alhaji Ahmadu a samar mata Bisan Canada, ai ko aka fara mata processing cikin gaggawa.....



*Littafin Mayraah na kudi ne ba free book ba, ayi kokari a sauke min hakkina don da ni da ku bamu san gobe ba.*

07087865788

Drop 8 concrete lessons of the book Mayraah, the best goes home with 10k
Drop via 07087865788

_ALHAMDULILLAH a nan na sauke littafin *MAYRAAH* darussan dake ciki Allah Ubangiji ya sa mu amfana da su, kura kuren ciki kuma Allah ya yafe mana..... I am thanking my fans Wholeheartedly for being patient with me from the beginning of the book Mayraah to the end, nasan kun min kokari sosai..._

Na kuma sadaukar ga littafin *MAYRAAH* zuwa ga Lovely Mom dina Hajiya Hajara with her ɗan auta Umar Farouk (Papi) 🥰 Allah Ubangiji ya dafa maki, ya jibanci lamarinki, ya raya maki mu cikin aminci.....
*Ya Allah ya Ubangiji kaji ƙan Abbana kayi masa rahama, ka Kyautata makwancinsa, ka yafe masa kurakuransa tare da duk sauran musulman da suka riga mu gidan gaskiya, ya Allah ka kyautata namu zuwan bayan nasu*😓


My special greetings goes to you Oga Barrister, thanks for always borrowing me little of ur time to do what makes me happy, Allah Ubangiji ya ci gaba da kara mana hakurin zama da juna,😂 Allah ya kara maka budi Ameen....


*To all Readers of Mayraah, thanks soooo much for patronizing me, Allah Ubangiji ya maku albarka ya raya maku zuri'a, marasu aure kuma Allah ya kawo babban rabo, Allah ya sa kafin karshen shekaran nan za ku aiko mana da cingam din sa rana...* 😁

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login