Showing 411001 words to 414000 words out of 456519 words

Chapter 138 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70652

wayarta da ta jona mata a caji ganin Abba ne ke kiranta, Hajiya Amina ta amshi wayar sai bata daga ba har ya katse, miss calls dinta ta hau dubawa bayan kiran Abba ya katse, Mama Ladi tace "Ba kiranki ake ba Amina?" Hajiya Amina ta kalleta tace "Ai kam har ma ya katse" Ita dai Ammi na zaune suna hira da surkar Dr Khalil da ta zo yi masu gaisuwa tare da er ta Zainab, Ita Mayraah dariya ma Zainab din ke bata don abu kusan wata nawa amma bata wani son hada ido da Mayraah sai tayi ta kame kame, ita kam Mayraah har cikin ranta taji ta yafe mata abinda tayi mata amma Zainab still taki sakin jiki, wayar Hajiya Amina ne ya fara ring, Mama Ladi tayi karaf ta ce "To gashi an maido da kiran" Hajiya Amina ta daga kiran ta kai kunne hade da sallama, lkci daya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta mike tsaye da sauri tace "Lafiya??" Su Ammi duk suka juya suna kallonta su ma, Aunty Mariya ta mike ta dawo kusa da ita tace "Hajiya Lafiya?"
[10/20, 9:28 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Sai da Hajiya Amina ta gama wayar da take sannan ta ajiye wayar a gefenta, Mama Ladi tace "Lafiya? Me ke faruwa?" Aunty Mariya ta wani kalli Mama Ladi, tare fa duk suka ji communication din da take a waya kuma still Mama Ladi na tambayar me ke faruwa, Hajiya Amina tana kallon Mama Ladi tace "Gwaggon su Ihsaan ce ta kira ni wai basu da lafiya tun da safe" Mama Ladi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, naji kamar tace maki har da suma ko?" Hajiya Amina tace "Eh wallahi" Mama Ladi ta zauna gefen kujera cike da alhini tace "Dama basu da lafiya ne?" Hajiya Amina ta girgiza kai tace "Lafiyarsu kalau suka bar kano wllhi" Aunty Mariya tace "Allah Ubangiji ya basu lafiya" Ammi da Mom din Zainab su ma duk suka masu fatan samun lafiya Hajiya Amina tace "Ameen" Mama Ladi tace "To amma banda abun gwaggwan tasu meye sai ta kiraki ta gaya maki ko er yarinya ce dai, banda haka sai ta masu abinda ya kamata tunda ita ma uwa take garesu" Hajiya Amina tace "Tun safe ne ai abun ya faru kuma kinga sai yanzu take gaya min" Mama Ladi tace "To an kai su asibiti dai ko?" Hajiya Amina tace "Eh suna asibitin ma yanzu haka" Mama Ladi tace "Amma dai magana ta domin Allah bai kamata ta kira ki ta daga maki hankali ba kina gidan mutuwa, kuma duk su biyun ne ba lafiya?" Hajiya Amina tace "Eh wai Eeman ce ta fara, to dama su haka suke daya baya rashin lafiya daya bai yi ba" Mama Ladi tace "Amma dai dama can sun saba suma ko?" Ammi dai ta dauke kai, Aunty Mariya tayi tagumi cike da takaici, yanda Mama Ladi ke jero tambayar one by one zaka zata retired er jarida ce, Hajiya Amina tace "Aa basu taɓa ba gaskiya, shine ma yasa har ta kirani yanzu" Mama Ladi tace "To ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sai alkhairi, kawai ina jin canjin ruwa ne kilan ruwan pampo suke sha a gidan, nima nan da girmana farko farko kafin in saba da zaman Kaduna haka na dinga zazzabi sama sama sbda rashin sabo, to gashi yanzu zaman garin ya zame min jiki ina zaune lafiyan Allah, ba ko ciwon kai, kwana nawa za su yi a Katsinan ne?" Hajiya Amina dai duk bata san abinda Mama Ladi ke cewa ba don gaba daya tunaninta yayi wani wajen daban, sosai taji hankalinta ya koma kan yan biyunta, it's very rare su yi rashin lafiya kuma wai har da suma, abinda basu taɓa yi ba, muryar Mama Ladi da taji a tsakiyar kanta ne yasa ta daga kai da sauri tana kallonta, Mama Ladi tace "Kwanan su nawa a katsinan?" Hajiya Amina tace "Kwanan su biyu kenan" Mama Ladi tace "Ahaf zuwa anjima duk za su warware canjin ruwa ne" Hajiya Amina ta ɗan yi murmushi tace "Allah ya sa" Mama Ladi tace "Haba ai jini ba wasa ba, dama tun da kika shigo na lura baki da kuzari karfin hali kawai kike, ashe tagwayenki ne kwance ba lafiya kike ji a jikin ki, Allah Ubangiji dai ya basu lafiya, mu dai gashi an kashe mana namu tagwayen har lahira don mugunta, Allah dai ya ji kansu kawai yasa masu ceto ne" Mama Ladi na kai wa nan ta fara matsar kwalla, a hankali Hajiya Amina tace "Ameen ya Allah" Nan Mama Ladi ta dinga bata labarin ta yanda su Aymaan suka rasu, shidda saura Ammi ta fita raka Ummi, Aunty Mariya kuma ta mike ta tafi kitchen don ita ke assisting Bilkisu suna girka Dinner, Mama Ladi na kallon Hajiya Amina tace "Bari dai in je in ga yau kuma me ake dafa mana ga magariba ya gabato har yanzu ban ga an sauke tukunya ba..." Tashi tayi ta nufi kitchen, tana shiga ta tsallake Aunty Mariya ta tafi inda Mayraah ke yi ma Maheer girki tana murmushi tace "Ikon Allah, abincin kala biyu za a mana kenan yau" Aunty Mariya tace "Aa ga nan namu ina yi, wancan kuma mijinta take ma girki" Mama Ladi ta kalli abinda su Aunty Mariya ke dafawa sannan ta sake kallon wanda Mayraah ke dafawa tace "Ikon Allah, wato ke me miji bazai ci wanda aka dafa ma yaku bayin dake gidan ba, to ni dai bari in taya ki yanka koren tattasan" Aunty Mariya dai ta girgiza kai tana ci gaba da juya stew din dake kan wuta... Bayan barin Mama Ladi parlon Ammi ta dawo daga rakiyar da tayi ma baƙinta zuwa compound, tana kallon Hajiya Amina tace mata ta taho sama tayi alwala lkcn sallah yayi sannan ta tafi sama, Hajiya Amina ta sake kiran Aunt dinsu Eeman, tana dagawa tace "Aisha can i speak to them?" Aunt dinsu Eeman ta sanar mata sun samu bacci, Hajiya Amina tace "Ki tada Eeman ki bata waya let her talk to me" Hakan Aunt din nasu tayi, Hankalin Hajiya Amina ya kara tashi sosai hearing Eeman's voice, kawai ji tayi she just have to go to her girls, this is so unusual of them tunda ta haifesu basu taba wani abu wai shi suma ba, shi yasa duk take jin ta wani iri tun da ta fito gida a kano har ta iso Abuja, katse wayar tayi tana kokarin dialing number Abba Usman ya shigo parlon, ya karaso ya zauna yana kallonta ya gaisheta, ta amsa da murmushi tace "Ai na zata ma kana Kaduna" Yace "Aa ina nan..." Tace "Ya karin hakuri?" Yace "Alhamdulillah" After few seconds ta daga kai ta kallesa tace "Usman za a samu flight going to Kano da daddaren nan kuwa?" Yace "Komawa kanon za ku yi Aunty?" A hankali tace "Wallahi kirana aka yi su Ihsaan basu da lafiya suna asibiti, it's so unusual of them..." Usman yace "Subhanallah, me ya same su?" Hajiya Amina tace "Wai sun ma fita ne da safe za su je kitso and Eeman pass out on their way, kafin ma a isa hospital da ita Ihsaan did same too, not long ago aka kirani ake gaya min" Usman ya ɗan yi shiru, can yace "Allah ya basu lafiya, amma da ki bari sai ki bi Flight din safe Aunty" Tace "Duba min dai ko za a samu" Usman bai sake cewa komai ba ya ciro wayarsa zai duba mata if their is any available flight to kano that evening, ta mike tace "Before then bari in ɗan yi magana da Abbanku" Yace "Ohk" wayarta ta dauka ta fita compound, tayi dialing number Abba hoping bai shiga Masallaci ba don lkcn sallahn magrib yayi, Abba na dagawa bayan ta gaishesa ta sanar masa zata koma kano da dalilin komawar nata, Abba da yayi shiru yana sauraronta yace "To su kuma da suke katsina ko kin koma kano a daren nan ba wani difference da zai yi making ba ai, ki bari kawai sai Allah ya kai mu gobe sai ki bi morning flight" Shirun da tayi ne yasa Abba yace "But if kinga hankalinki zai fi kwanciya idan kin koma kanon yau it's fine, in an samu Flight din sai ki sanar min" Hajiya Amina tace "Alright thank you ranka shi dade" Komawa cikin parlor tayi tana kallon Usman tace "Ka samu Flight din" yace "Ehh na samu but nan da 30mins jirgin zai tashi, bai ma cika ba za su tashi" Hajiya Amina tace "Toh bari in sanar ma Ammin ku" Sama ta tafi zuwa parlon Ammi, bayan ta sanar ma Ammi, Ammi tace "Toh Allah Ubangiji ya basu lafiya cikin gaggawa" Hajiya Amina tana kallon Ammi tace "Ameen ya Allah" Ammi tace "An samu jirgin ne yanzu?" Tace "Ehh Usman yace min an samu, ya ma kusa tashi" Ammi tace "Toh Alhamdulillah, sai ya kai ki airport din da wurwuri, amma dai ba a yau din zaki karasa katsinan ba in kin sauka kano saboda dare ga hanya sai addu'a" Hajiya Amina tace "Zan bari da safe in sha Allah" Ammi tace "Toh Allah ya kai mu" Hajiya Amina tace "In ji dai baki yi fushi ba, ba za ayi sadakan uku da ni ba" Ammi tace "Haba dai, ba komai wallahi ai lalura ce ta taso, Allah dai ya basu lafiya" Hajiya Amina tace "Ameen" Sai da Hajiya Amina tayi sallahn magrib sannan ta sauko downstairs tare da Ammi, Mama Ladi da ta fito daga kitchen kenan ta saki baki ganin Hajiya Amina da karamin jakarta a hannu, tace "Ina kuma za ki Amina? Kaddai kano za ki koma da daddaren nan?" Hajiya Amina tayi murmushi tace "Mama ai jirgi ne" Mama Ladi tace "Ikon Allah yanzu dai in ba dora ido kika yi kan yaran nan ba kika ganki kusa da su baza ki taɓa samun sukuni da nutsuwa ba, ko da yake da gaskiyarki mu da muka yi sakwa sakwa da namu yan biyun ba gashi an kashe mana su har lahira ba, gwara ki je gun kayanki bakinki alekum, Allah dai ya basu lafiya cikin gaggawa, kuma duk kice muna masu sannu, in na samu sarari har kanon zan zo dubasu idan Allah ya yarda" Ita da Hajiya Amina murmushi kawai take, Mayraah ta karasa ta amshi jakar hannunta, nan duk suka rakata compound, don Usman na can parking space ya tada mota yana jiranta, Hajiya Amina na kallon Mama Ladi tace "To mama ayi min hakuri ban zauna ayi sadakan uku da ni ba" Da sauri Mama Ladi tace "Haba dai ai duk mun san lalura, ke dai Allah ya kai ki kanon lafiya ya ba yan biyun ki lafiya" Hajiya Amina tayi ma Ammi da Aunty Mariya sallama sannan ta juya tana kallon Mayraah ta amshi jakarta a hannunta, Mayraah tace "Allah ya tsare Aunty" Hajiya Amina tace "Ameen Mayraah, ai ta hakuri a zauna lafiya kin ji, duk da nasan Maheer ba shi da matsala be a good wife to him, Allah ya baku zuri'a dayyaba" Mayraah dai ta sauke idonta kasa, Hajiya Amina ta shiga motar, suka dau hanyar airport da Usman. Suna isa airport Hajiya Amina tace ma Usman ba sai ya shiga ba don har ciki ya so rakata, tana rike da karamin jakar hannunta tace "Ka tura min ticket din ai ta WhatsApp ko?" Yace "Eh na tura" Tace "Nawa ne kudin ticket din?" Yace "Kawai ganin alert nayi Abba ya turo 150k, but the ticket is 110k" Hajiya Amina tace "Ohk to, sai mun yi magana" Yace "Allah ya tsare" Tace "Ameen" Sai da ya ga shigarta airport sannan ya juya motarsa, Hajiya Amina na shiga airport din aka sanar mata ko minti uku ba ayi da tashin jirgin ba, zaunawa tayi tana tunanin yanda zata yi, hankalinta bazai taɓa kwanciya ba in ba ganinta tayi gun yan biyunta ba don so tayi jirgin na sauka kano ta dau hanyar kt, tana ta zaune airport din tuna nazarin yanda zata yi, tasan tana ce ma Abba babu jirgi zai ce ta dawo, ta ciro wayarta ta saka Flight mode ta mayar cikin handbag dinta. Karfe takwas da yan mintuna Maheer ya shigo parlor bayan ya raka colleagues dinsa da suka zo yi ma Ammi gaisuwa, bai tadda Ammi a parlon ba, hakan yasa ya tafi sama don tunda ya dawo bai ga Mayraah ba, bude kofar dakinta yayi ya ganta kwance kan darduman da tayi sallah har ta fara bacci, ya karasa kusa da ita ya duka yana kallonta yace "Mimi" a hankali ta bude ido, sai kuma ta mike zaune da sauri tace "Yaya ka dawo?" Yace "Kin gaji ko?" Ta marairaice masa tace "Kaina ke min ciwo, amma na sha magani naji ma yayi sauki" Ya dafa goshinta yace "Allah ya sauwake Baby Gal, gobe za mu tafi gida in sha Allah" Tace "In kawo maka abincin yanzu?" Yace "Wanka zan fara yi tukun" Tace "Ohk" Mikewa tsaye tayi ta dauke darduman tace "Ko zaka shiga bathroom dina kayi wankan?" A hankali yace "Sai mu yi tare?" Turo baki tayi ta masa wani kallo, yace "Toh shikenan an fasa wankan ma, abincin ma an koshi" Ta marairaice masa tace "Wallahi ka fiye wayo yaya" Yace "I will take off ur clothe, and then you retaliate" Ta masa wani kallo ta fara unbotton din masa shirt din jikinsa a hankali yana kallonta..... Abba na zaune parlonsa wajen karfe goma na dare, Ammi ta shigo masa da black tea da ta dafa masa, ajiye masa tayi ta nemi waje ta zauna tana kallonsa tace "Nayi ta kiran layin Maman su Ihsaan ban samu ba har yanzu, fatan dai ta isa gida lafiya, sannan ya jikin su Ihsaan din?" Abba yace "Nayi trying line din nata nima ban samu ba probably network...." Ammi tace "To ka kira mai gadin gidan mana" Mikewa Ammi tayi ta fita daga parlon zata dauko masa water melon da ta saka masa a fridge yayi sanyi, Ammi na fita ba dadewa wayan Abba ya fara ring, ya duba ganin Hajiya Amina ya daga kiran ya kai kunne.....



[10/21, 9:31 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Abba ya ajiye mug din black tea din hannunsa a hankali ya mike tsaye har a sannan wayarsa na kare a kunnensa, jin the person on the other line na ta cewa "Hello, Hello..." Abba ya koma a hankali ya zauna saman kujera still not responding kuma har a sannan bai cire wayar a kunnensa ba, ji yayi an katse call din ya dinga kallon screen din wayar, a haka Ammi ta dawo parlon ta samesa, ta ajiye watermelon din hannunta ta zauna gefensa tana kallonsa sai kuma ta kalli wayar hannunsa tace "Is anything the matter?" Abba ya juya ya kalleta amma ya kasa cewa komai, Ammi sai da taji gabanta ya fadi, ta dake tace "Wai lafiya Yallabai?? Me ya faru?" Abba ya dauke kansa, after few seconds wayar hannunsa ya fara ringing again, Ammi ta kalli wayar ganin Hajiya Amina, ta daga kai ta kalli Abba, mika mata wayar yayi, da mamaki Ammi dake kallonsa taki amsan wayar tace "I don't understand? for what reason?" Hakan yasa Abba ya daga kiran ya sa handsfree ya ajiye wayar a hankali kan kujera, muryar namiji Ammi taji yayi sallama, sosai taji faduwar gabanta yafi na da, ta daga kai da sauri tana kallon Abba, can tayi karfin halin amsa sallaman da mutumin ke yi, a takaice mutumin yayi introducing kansa sannan ya fara sanar mata me wayar sun samu accident a public transport that was heading to kano from Abuja, and the accident occurred a kusa da Kaduna, Ammi bata san sanda ta mike tsaye da sauri ba cikin kidimewa ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mutumin ya ci gaba da sanar mata an kawota hospital din 44 dake garin kaduna with 2 other passengers that survive the accident for intervention, Ammi bata fasa nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ba cikin tashin hankali, Shi dai Abba was just short of words, mutumin na katse wayar Ammi ta koma ta zauna tana facing Abba a rikice tace "Yanzu kadunan za mu tafi?" Abba ya sauke ajiyar zuciya, calmly yace "Sai dai gobe, it's already late now" Ammi na girgiza masa kai tace "Har sai gari ya waye yallabai? tunda Usman kan yi driving din dare ba sai ku je kadunan da shi ba yanzu, in yaso sai mu mu taho gobe" Abba dai bai ce komai ba, Ammi tace "Incase ko da bukatar wani abu shi yasa ya dace ku tafi yanzu ba har sai gobe ba" Bata jira cewar Abba ba ta fita daga parlon da sauri, ta tafi dakin Usman, bata samesa ba a dakin nasa ta sauka downstairs, Maheer ya fito daga dakinsa kenan rike da magungunan da ya siyo ma Mayraah jiya zai kai mata ta tasha don she is running temperature, Tsayawa yayi yana kallon Ammi da ta nufosa cikin tashin hankali, sosai ya ji gabansa ya fadi tun bata karosa ba, tana isowa inda yake ta sanar masa abinda ke faruwa, Maheer yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani asibitin a kaduna?" Ammi tace "Wai forty four mutumin yace, ina Usman?" Dai dai nan Usman ya fito daga kitchen rike da cup din lipton, Ammi ta nufesa shi ma tana gaya masa, he was soo shock and speechless yana kallon Ammi, da kyar yace "Accident kuma?" Ammi tace "Yanzu aka kira Abban ku, shine nace ku tafi Kadunan tunda naga wani lkcn kana tukin dare" Usman sai da ya nemi waje ya zauna tsabar yanda batun ya dakesa, sai ga Abba ya sauko downstairs din, makullin mota kawai Usman ya dauko a dakinsa da Atm card, Maheer da shi ma duk jikinsa yayi sanyi ya mika ma Ammi ledan maganin Mayraah yace "Ammi na Mimi ne, she is running temperature, let me go with them..." Ammi ta amshi maganin tace "Toh Allah

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login