Showing 276001 words to 279000 words out of 456519 words

Chapter 93 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70613

da kallo kafin ya fita a hankali tace "Ko da ba a mata Birth certificate ba ina bukatar garin da aka haifeta, da ranan da aka haifeta, da kuma lokaci" Abba ya juya ya kalleta, shiru yayi na ɗan dakikai, sai kuma da sauri yace "Toh zan tambaye ta" Daga haka ya fita ya kulle mata kofa, mamaki ne ya cika Abba, don ya kai second talatin a tsaye bayan ya fito daga office dinta, to me kuma zata yi da birth certificate din Mayraah, ai it's something that is not necessary shi dai a tunaninsa, to ko saboda a saka a file dinta ne take tambaya, amma gaskiya shi kam bai taɓa jin asibiti sun bukaci birth certificate ba in ba dai kilan shi ne bai sani ba, a haka dai har ya isa dakin da su Mayraah suke.... Zaunawa yayi yana kallon Ammi dake lallaba Mayraah ta ci abincin da Aunty Mariya ta girka mata, yace "She is asking for her birth certificate" Ammi ta juya ta kallesa tace "Birth certificate kuma? What for?" Abba yace "Ni ma dai shine na kasa ganewa, dama idan an kwantar da mutum a asibiti ana tambayar Birth certificate dinsa ne? Ina ce iya shekarunsa ake tambaya" Mayraah dai kallonsu kawai take, Ammi ta ajiye plate din abincin hannunta bata sake cewa komai ba, Abba dake kallonta yace "Ya naga mood dinki ya canza, lafiya kuwa? is there anything wrong?" A hankali Ammi tace "To ai ban taba jin haka bane, why is she asking for her birth certificate, ita dai ba iyaka ta fadi bill dinsu mu biya su kudinsu su sallamemu mu wuce gida ba, ai jikin nata ya ma yi sauki tun da yamma kawai a sallamemu gaskiya..." Abba zai yi magana Usman ya shigo da sallama, Ammi na kallonsa da sauri tace "Usman ka taɓa jin inda aka tambayi patient birth certificate a asibiti? ba iyaka shekarunsa ake tambaya ba ko date of birth dinsa? Then why the certificate gaba daya?" Usman yace "Birth certificate kuma? Me za ayi da shi" Abba yace "To haka dai tace, har cewa tayi in ma babu birth certificate din to tana bukatar garin da aka haifeta, ranan da aka haifeta da kuma lokaci, amma bari dai Maheer ya shigo sai mu tambaye sa ko haka ake yi" Ammi tace "Aa kawai kace mata ba a taɓa mata certificate din haihuwa ba, kuma a kano aka haifeta a gida ba a asibiti ba...." Abba dai bai sake cewa komai ba. Ana kiran isha shi da Usman suka tafi masallaci, Ammi dake ta zaune ta kasa motsawa daga inda take tun maganar da Abba ya kawo mata ta juya a hankali ta kalli Mayraah, cikin sanyin murya tace "Ina ke maki ciwo yanzu kuma Mimi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Yanzu dai babu ko ina Ammi, kawai dai jikina ba kwari ne har yanzu" Ammi tace "Kin gaji da zaman asibiti ko?" A hankali Mayraah ta gyada mata kai tace "Na gaji Ammi" Ammi ta bude handbag dinta ta ciro dubu biyar sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta mike tsaye tace "Mu tafi gida kawai nasan baza su yarda su sallamemu ba sai suce sai nan da wasu kwanaki..." Daga haka ta kama hannun Mayraah ta sauko da ita daga kan gadon dama an riga an cire mata drip tun dazu da ya kare kuma ba a sake saka mata wani ba, Ammi ta dauko mata takalmanta ta ajiye mata, Tana rike da ita ta saka takalmin, sai da Mayraah ta ga wani jiri bayan ta tsaya, Ammi bata damu da hakan ba tana rike da hannunta suka nufi kofa suka fita daga ward din, suna shigowa reception ta ki kallon ko wace nurse ta nufi kofar fita, daya daga nurses din ta mike tace "Ma'am... Za ku ina?" Sai a sannan Ammi ta kalleta da sauri ta kirkiro murmushi tace "Aa za mu ɗan zaga premises din asibitin ne tayi exercise ko zata ji kwarin jikinta" Nurse din ta koma ta zauna tace "Ohk Ma" Daga haka Ammi ta fita rike da Mayraah, direct gate suka nufa Ammi na waige waige har suka fita daga asibitin gaba daya, da kyar Mayraah ke tafiya don har strength dinta ya kare, Ammi dai na rungume da ita a jikinta har suka iso bakin titi ta tsayar masu da adaidaita sahu suka shiga ta gaya masa inda zai kai su.
[8/23, 9:03 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mikewa Aunty Mariya dake zaune parlor tayi da mamaki tana kallon Ammi da suka shigo parlon tana rungume da Mayraah, ta karasa kusa da su da sauri tace "An sallameku ne Ammi?" Ammi bata amsan tambayarta ba, hakan yasa Aunty Mariya ta taimaka mata wajen rike Mayraah da ko tsayuwan kirki ta kasa suka wuce sama zuwa Bedroom din Ammi, Ammi ta kwantar da ita a hankali saman gadon sannan ta rufa mata duvet tana kallonta cikin sanyin murya tace "Sannu" Mayraah dai ta kasa cewa komai don ji take kamar an kara mata ciwon da take ji a kirjinta tun da suka fito asibitin, ga wani sabon ciwon kai, Aunty Mariya dai na tsaye ita ma sai sannu take mata ganin yanda take sauke numfashi, Mayraah ta lumshe ido don baza ma ta iya amsawa ba, mikewa Ammi tayi ta fita daga dakin, Aunty Mariya ta bi bayanta ta sameta zaune parlor tayi tagumi, Aunty Mariya tace "Wai an sallameku ne Ammi? naji jikin nata da zafi fa, numfashin ma kamar da kyar take yi" Ammi ta kalleta a fusace tace "To ya bazan dawo da ita gida ba Mariya? Ban san me matar take nufi da ita ba...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka, Aunty Mariya that is confuse ta zauna kusa da Ammi tace "Ban gane ba Ammi, me ke faruwa? wace mata?" Cikin rawan murya Ammi tace "Tun fara aikinta a asibitin dama hankalina bai kwanta ba Mariya, har cikin raina naji ban yarda da CEO din asibitin ba, in baki manta ba ai har kiranki nayi na gaya maki tafiyar da ta sa aka yi da ita zuwa UK, ban san meye manufarta akan Mayraah ba, yanzu kuma ana zaune kalau kawai ta kira Abbansu wai tana bukatar birth certificate, to me zata yi da birth certificate din Mayraah? Dama ana haka a asibiti ne? Me yasa tun kwantar da mu ba a bukata ba sai yanzu?" Da damuwa Aunty Mariya tace "Kai Ammi, shine zaki fito da yarinya babu izininsu bayan kin san halin da ta tsinci kanta a kwanakin baya da kyar kuma aka samo kanta, what if jikin nata ya kara rikicewa Ammi? Sannan meye a ciki don an tambayi Birth certificate dinta? This is not enough reason na dawo da ita gida Ammi, ni damuwata kar ciwon nan ya dawo sabo mu shiga uku" Ammi na hawaye tana girgiza kai tace "In sha Allahu hakan bazai faru ba, kawai Alhaji ya dawo a canza mana wani asibitin gaskiya don bani da kwanciyar hankali a asibitin nan, ban san meye manufarta akan yarinya ta ba, wa ya sani ma ko er Cult ce, wallahi duk fargaban da nake kenan" Aunty Mariya dai ta kasa cewa komai tayi tagumi tana kallon yayar tata, Ammi dai hawaye sai sauka idonta yake, bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Abba ya shigo Usman na biye da shi a baya, Abba sai kallon Ammi da ta wani hade rai yake, sai kuma ya kalli Aunty Mariya yace "Ina Mayraahn take?" A hankali Aunty Mariya tace "Tana daki" Wucesu yayi ya shiga dakin, Usman ya karaso kusa da Ammi ya duka yana kallonta yace "Ammi meyasa za ki taho da ita gida a halin nan da take ciki?" Ammi ta fashe da kuka tace "Wallahi Usman ban yarda da Ceo din nan ba, da kyar in ba er shan jini bace" Usman ya ma rasa abinda zai ce mata sai kallonta yake, Abba na shiga Bedroom din yaga wani sabon zazzabi ya rufe Mayraah, sai sauke numfashi take da kyar, ya fito parlor a fusace yana kallon Aunty Mariya yace "Kin dai ga karamin tunani irin na yayarki ko? Ina ce kin dai gani? Yarinyar da dakyar aka samo kanta shine saboda rashin tunani baiwar Allahn nan zata fito da ita asibiti bata duba halin da take ciki ba? Wani me hankalin ne zai yi wannan abun da tayi?" Aunty Mariya ta mike da sauri bata bar sa ya ci gaba ba ta dinga basa hakuri, Ammi dai ko kallonsa bata yi ba hawaye na sauka idonta, Abba da ransa yayi mugun baci yace "Zan maida ita asibitin kuma wallahi bana son ganin kafarta a can, gwara ke Mariya ki je ki ci gaba da jinyarta" Ammi ta mike tace "Wallahi bazaka maida min yarinya asibitin matar nan ba, ai asibitoci kala kala ne a Abuja kuma masu kyau, wanda ma suka fi wancan kyau, me yasa baza a canza wani asibitin ba..." Ko kallonta Abba bai yi ba ya shige dakin Aunty Mariya ta bi bayansa, Usman ya kama hannun Ammi da ke kuka suka fita parlorn ya maidata wani parlor yayi kasa da murya yace "Ammi bai kamata ki fito da ita asibitin ba, har yanzu fa ba wai samun sauki tayi ba kuma kema kin sani..." Katse sa tayi tana kuka tace "Me yasa baza ku fahimce ni ba ne wai Usman??" Usman ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Na fahimce ki Ammi, birth certificate dinta da ta bukata ka'idar asibitinsu ne za ayi photocopy a saka cikin file din patient, kinsan ko wani asibiti da rules din su, so baki tsaya kin fahimci dalilin tambayar certificate din da tayi ba kika yi saurin yanke hukunci" Ammi dai bata fasa kukan da take ba, Usman ya dinga kokarin kwantar mata da hankali. Aunty Mariya na rike da Mayraah suka sauka downstairs Abba na biye da su a baya, gaba daya jikin Aunty Mariya yayi mugun sanyi, bata san sanda Abba ya dawo mafadaci haka ba cikin kankanin lokaci, da da ne a yanda ta san sa uffan bazai ce ma Ammi ba sai dai kawai ya maida Mayraah asibiti, amma yanzu sam ba haka ba, ya daina mata uzuri kwata kwata, Mayraah na rungume jikin Aunty Mariya har suka isa asibitin a motar Abba, zuwa sannan kam gaba daya jikinta ya rikice don sai sarkewa numfashinta yake, hakan ya sa aka shiga Emergency da ita. Duk yanda Ammi ta so zata koma asibitin bayan tafiyar su Aunty Mariya Usman bai yarda ya bar ta ta koma ba ganin yanda ran Abbansu ya baci, cikin kwantar da murya yace "Ammi pls ki bari gobe da safe sai ki je tunda tare suka koma da Aunty Mariya kuma kinsan zata kula da ita sosai, don Allah kiyi hakuri ki bari gobe, nima yanzu bazan koma ba, idan ya so gobe da sassafe sai mu je" a haka dai ya dinga kwantar mata da hankali har ta hakura da komawa asibitin amma ba can cikin ranta ba, su Hajja da Mama Ladi suna can dakin visitors basu ma san me ke faruwa ba a gidan. Karfe sha biyu saura aka cire ma Mayraah oxygen da aka sa mata bayan numfashinta ya dawo dai dai, MD da Dr Hamid ne tsaye Emergency ward din watching her closely, MD ya karasa kusa da ita ganin kamar magana take son yi, dukawa yayi yana kallonta bai dai ce komai ba, da kyar tace "Ina son zan sha ruwa pls" Yayi shiru bai ce komai ba kuma bai fasa kallonta ba, hakan yasa ta dauke kanta tana kallon direction din Dr Hamid kilan shi zai taimaketa, shi ma da yaga magana take son masa ya isa kusa da ita ya duka yace "Ya aka yi?" Murya can kasa tace "Dr ruwa nake son zan sha" Calmly Dr Hamid yace "Za ki sha zuwa anjima, be patient" Ta marairaice tace "I'm very thirsty" Yace "I know, za ki sha anjima kadan" Daga haka ya juya ya fita ward din, Abba dake bakin Emergency din a zaune tun dazu ya mike yana kallon Dr Hamid, Dr Hamid yace "Numfashinta is stable yanzu, zuwa karfe daya za a maida ta ward" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh
Alhamdulillah" Barin wajen Dr Hamid yayi.... Mayraah ta kara kallon MD kamar zata yi kuka tace "Don Allah ku bar ni in sha ko kadan ne" Shiru yayi da farko, sai kuma yace "Zan baki anjima" Hawaye ya cika idonta tace "To ka kira min yayana nasan shi zai bani" Ya kafeta da ido, a hankali yace "Wani yayan naki?" Tace "Ya Maheer" a hankali yace "Ohk..." Juyawa yayi ya fita daga ward din, bayan wani lokaci ya dawo rike da disposable cup karami da ya debi ruwa kadan cikin Dispenser din dake reception, tana ganin ruwan zata mike zaune amma ta kasa don duk jikinta is weak, ya ajiye karamin cup din, helping her to seat on the bed gently, sannan ya dau ruwan da kansa ya bata very little a ciki, zai mayar ya ajiye a hankali tace "Kadan fa na sha" Sake bata sip daya yayi dai dai nan Dr Balogun ya shigo, da mamaki yake kallonsa da ruwan hannunsa, MD yayi saurin ajiye sauran ruwan sai kuma ya fita ya bar ward din, Dr Balogun yayi disposing ruwan da cup immediately, Aunty Mariya dai na zaune reception tayi tagumi kamar ance ta juya taga Ammi kamar an jefota, mikewa tayi da mamaki ta nufeta da sauri tace "Ammi? Meyasa kika taho cikin daren nan" Ammi da idonta ya kumbura don kuka cikin rawan murya tace "Bazan iya bacci ba Mariya" Aunty Mariya ta kasa ce mata komai, a ranta kuwa fata take Allah yasa kada Abba ya sake wani fadan in ya ganta, can ta kama hannunta suka tafi suka zauna tana kallonta tace "Kin shiga kin duba Maheer?" Ammi na share idonta tace "Ina? Me ya samesa?" Aunty Mariya tace "Ai yana gidan, yana dakinsa baya jin dadi" A hankali Ammi tace "Ai ban sani ba" Aunty Mariya tace "Da ku ka dawo dazu bacci yake ne, saboda shi ne ma nake zaune parlor sai ga ku kun shigo" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba. MD na komawa office dinsa ya tadda Musharraf zaune yana duba wani littafi to distract him daga damuwar halin da Mayraah take ciki, tun da ya fito daga Emergency da aka shigar da Mayraah ya dawo office din yayansa ya zauna, kallo daya Musharraf yayi masa ya maida idonsa kan littafin hannunsa, MD ya ajiye stethoscope dinsa ya zauna kan sofa din office din without looking at Musharraf yayi kasa da murya yace "Now tell me, are you still interested in getting married to her" Musharraf ya daga kai ya kallesa, sai kuma ya ajiye book din hannunsa yace "Who?" MD ya jinginar da kansa da kujera yayi kasa da murya yace "The Girl" Musharraf ya sauke idonsa yace "Why the question?" MD ya kallesa yace "I will make sure...." Shiru yayi ta dalilin wayarsa dake vibrate, ya dauka yana kallon screen din, ganin Ceo ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, bata taɓa spending din night a asibitin ba a iya saninsa sai gashi yau har karfe sha biyu da rabi na dare bata tafi gida ba, bayan yaji abinda tace a wayar a hankali yace "Ohk Ma'am" Daga haka ya mike ya nufi kofa Musharraf ya bi sa da kallo har ya fita. MD na isa office dinta ya sameta zaune kan 3 sitter ta lulluba da karamin duvet kamar me jin sanyi tana jiransa, tun da ya shigo yake kallonta ganin yanayinta ya dawo kamar mara lafiya, da ladabi yace "Are you really okay Ma'am, is anything the matter?" Kujera ta nuna masa alamar ya zauna without looking at him, ba musu ya zauna yana kallonta, bayan few seconds ta sauke idonta kasa cikin sanyin murya tace "Tambaya nake son maka Aliyu" Yace "Ohk Ma ina ji" Calmly tace "What did you know about Mary Ann" Ya sauke idonsa kasa, ya ma rasa ko mamakin tambayar nata yayi ko akasin haka, duk da ya jima yana mamakin dalilin da yasa ta sake haka da Mayraah har aka je da ita UK kuma ta sauketa gidanta bayan yasan tana da trust issues, wanda a duk ma'aikatan asibitin nata shi kadai yasan gidanta both UK, Abuja, and Lagos, bayan few seconds ya dago kansa yace "Ma'am ni ban santa ba, ban taɓa ganinta ba sai a asibitin nan, sai dai a yau i was also shock bayan da naga Mamina da Younger brother dina sun zo dubata all the way from kano, and i get to know that fiancee din brother na ce ita da na ce maki an fasa aurensu kwanaki" Ceo dai kallonsa kawai take, can tace "Brother din ka kuma?" MD ya sauke ido a hankali yace "Nima sai yau na sani" Ceo na kara wrapping din duvet din jikinta tace "Ko zan iya sanin me yasa aka fasa auren?" MD ya ɗan yi shiru, a ransa yaji bai kamata ya tona ma Mayraah asiri ba, this is supposed to be her secret in this hospital, yana jin ko Dr Khalil bai san wacece ita ba from the look of things, and bai kamata ya ce ma Ceo ai ita din ba a san asalinta ba, CEO ta dafa shoulder dinsa a hankali tace "Akwai wani abu da zaka boye min ne Aliyu? Talk to me kar ka ji komai" MD ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya san dai ko ya gaya ma Ceo wacece Mayraah yanda yaga take jinta a ranta ba raguwa zai yi ba, lumshe ido yayi ya bude bayan ya gama nazarin yanda zai sanar ma Ceo wacece Mayraah ba tare da yayi tarnishing image dinta ba, Murya can kasa yace "Uncles dina sun gano foster parent kawai gareta...." CEO dake ta kallonsa babu ko kiftawa ta sauke idonta ta dalilin hawayen da ya ciko mata, shi

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login