Showing 270001 words to 273000 words out of 456519 words
ward ya zauna yana kallonta don tada masa bala'i tayi sai ya kawo ta, ko su Aunty Mariya basu san ya taho da ita ba, Usman na kallon Mayraah da taki amsan shayin yace "Ya isheki?" Ta gyada masa kai, ya ajiye sauran shayin ya gyara mata pillow din bayanta ta kwanta, can dai ya kalli Mama Ladi da taki yin shiru ga kukan da ta cika kunnensu da shi yace "Don Allah Mama ki yi kasa da muryarki asibiti ne nan akwai marasa lafiya, shi yasa ba a barin mutane su shigo anyhow" Ta juya da sauri tayi facing dinsa ta wani tsuke fuska kafin tace komai aka bude kofar ward din, Maheer ne ya shigo da sallama duk suka juya suna kallonsa har ya karaso ciki, da mamaki Ammi ke kallon warce ke bayansa da hijab dinta har kasa, Mama Ladi har da kifta ido don ita ma ta tabbatar da warce take gani a bayansa, Mayraah ma ta dinga kallonta har ta karaso cikin ward din, gun Ammi ta fara zuwa kanta a kasa ta gaisheta a hankali, Ammi ta amsa tana kallonta, daga haka ta karasa kusa da gadon ta kalli Usman tace "Ina yini Yaya" Yace "Lafiya lau" ta maida dubanta kan Mayraah, Mayraah ta sunkuyar da kanta, a hankali tace "Ya jikin Mayraah?" Mayraah ta gyada mata kai kawai, Mama Ladi da abun duniya ya isheta ta ja Kujera ta zauna tace "To yanzu fisabilillahi ke kuma uban wa ya maki kwatancen nan? Salon a ganki cikinmu a gano baki da aure mu bar abun fadi a asibitin nan ayi ta nuna mu da hanci in muka zo wucewa, me yasa baki yi zamanki a inda kike Badiyya, yanzu domin Allah meye amfanin zuwanki nan ki bar mana abun fade" Badiyyah dai kallon Mama Ladi kawai take bata ko kiftawa, Mama Ladi ta kyabe baki tace "Ni yanzu ban ma san yanda zan bi in fita asibitin nan ba gashi ban sa Shijabi ba, tunda nasan duk yan asibitin sun san nan dakin kika shigo, wannan ai sai ayi tunanin kema pamilynmu ce bayan ba haka ba" Badiyyah da har hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kai, a hankali ta fashe da kuka ta durkusa gaban Mayraah tana kallonta cikin kuka tace "Nasan ni ce silan duk wani abu da ya sameki saboda son zuciya na, i wish i never did all what i did to you Mayraah, nasan ban yi deserving yafiyarki ba kuma bazan ce ki yafe min ba, amma ina maki fatan Allah ya baki lafiya, Allah ya ci gaba da daukaka ki a rayuwar ki, i wholeheartedly regret all what I did Mayraah, nayi ruining happiness dinki for my selfish interest..." Mayraah dai kanta na kasa hawaye na sauka idonta, Mama Ladi ta fashe da matsanancin kuka tace "Wayyoo Allahnaa, wayyoo" Badiyyah dake kuka sosai ta mike da sauri ta fita daga ward din, sai a sannan Mayraah ta daga kai hawaye na sauka idonta, Ammi dai ta rike kanta daga inda take zaune, a hankali Mayraah ta jinginar da kanta jikin kafadar Usman dake gefenta tana kuka a hankali, shi dai idonsa na kofar ward din baya ko kiftawa, jin yanda take kuka ya juya ya kalleta, sauke idonsa yayi ya mata side hug trying to comfort her without saying anything, da sauri ta fada jikinsa tana kuka sosai, Maheer ya sauke idonsa ya juya ya fita daga ward din yana jin kukan nata har cikin ransa..... Dr Hamid ne ya shigo ward din, yana kallonsu yace "Plss plss bata bukatar duk wannan hayaniyar a kanta duba da condition dinta, mutum daya ya isa ya zauna tare da ita ba sai an cika daki haka ba, ka'idar asibitin nan kenan kuma lokacin visting ya wuce tun dazu" Mama Ladi ta share hawayenta tana kallonsa tace "Amma dai asibitin yan iska ne asibitin nan, yau naga bala'i da neman fitina, ta yaya za a dinga mana walakanci ana hantaran mu kamar wasu en banza, ko basu san waye Mamudan bane a garin nan, ba fa a banza muke ba don ka ganmu bama cikin hayyacinmu mun yi wujiga wujiga sbda tashin hankali, wallahi ba yan banza bane, meye haka kamar in an mutu a nan din aljanna za aje? Ni tunda uwata ta haifeni ban taɓa jin wannan ka'ida ba sai a shegen asibitin nan, yau kwanana takwas a garin nan anki bari in shigo nan ana ta mana iya shege, na samu da kyar an kawo ni yau kuma kace daga ina na fito? To wallahi ka fita idona in rufe" Dr Hamid dake ta kallonta ya juya ya fita, tuni Ammi ta mike ta kasa tsaye ta kasa zaune taji kamar ta nutse wajen don kunya, Usman dama kauda kai yayi, Mama Ladi ta ja tsaki tana huci tace "Yau ga figaggen likita kawai zai kawo min fi'ili, ko dai asibitin na ubansa ne ne" Dr Hamid na fita office din MD ya tafi, bakin office dinsa ya samesa ya fito kenan, MD yace "Pls karfe nawa ne injection din nata?" Dr Hamid yace "MD pls talk to her family su bar yarinyar nan ta yi recovering yanda ya kamata kar su yi traumatizing ƙwaƙwalwarta, me yasa ma security za su dinga barin suna shigowa haka, ina ce tun karfe uku aka gama visting, noise din wata tsohuwa naji har corridor fa kamar ana cin kasuwa, what if Ceo ta shigo yau...." MD dake ta kallonsa yace "I will talk to the mother, no more visitation till she recovers completely, Ceo din ma na hanya yanzu haka...." Dr Hamid yace "Gaskiya hakan zai fi Sir, talk to the mother" Daga haka ya juya ya bar wajen, MD ya sauka downstairs zai je duba wani patient da suka yi ma aiki dazu da safe kafin ya je ya samu Ammi a ward din da Mayraah take, tun daga nesa yake kallonsa babu ko kiftawa kamar yanda shi ma yake kallonsa har ya karaso cikin reception din, ya cire face cap dinsa zai wucesa without looking at him yace "Good evening" MD ya bi sa da kallo yace "Daga ina kake?" Bai tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Kano" MD ya bude ido sosai ganin matar da ta shigo Reception din, ya karasa wajenta da sauri, cike da mamaki yace "Mami, daga ina ku ke haka?" Mami na kallonsa daga sama har kasa tace "Daddy you told me u are in Adamawa da na kira ka dazu...." Yana shafa kansa yace "Eh na dawo ne Mami, me ku ke yi a nan?"
[8/21, 10:00 AM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Dubiya muka zo Daddy, i was surprise da naji asibitin nan ne ma, shi yasa na kira ka dazu nake tambayar ko kana Abuja kace kaje Adamawa" MD ya shafa kansa yace "Mu je office ki sha ruwa Mami" Mami dake kallon Musharraf da ya zauna reception yana dialing number Maheer tace "Aa bari mu fara duba ta tukunna Daddy" MD yace "Ohk wani ward number suka ce maku suke?" Mami tace "Shi zai kira yayan nata mu ji, da kyar ma aka bari muka shigo wai visting sai nan da kwana biyu, sai da Musharraf yace masu za mu ga likita ne sannan suka bari, ya kira wayar ka kuma baka daga ba" MD ya ɗan kalli Musharraf Yace "Ohh wayar na office ne Mami, ashe dai yana da numberta har yanzu" Mami tace "Wani irin magana ne wannan Daddy" MD yace "To yaushe rabon da ya kirani? Duk ya kullaceni tun akan aurensa da aka fasa kamar ni na hana auren, me ya hanasa fara bincike kafin ya nemi yarinyar? Kinga we are not to be blamed ai" Mami tace "Kaga ba a nan ya kamata mu yi wannan maganar ba, kuma koma dai meye ɗan uwanka ne you can't change that fact, and you were suppose to sympathize with him during that period, amma yace min baka taɓa kiran sa ba tun bayan faruwan abun which is very bad of you, yana da wani ɗan uwan ne da zai tsaya masa bayan kai?" MD zai yi magana sai ga Maheer ya karaso Reception din, tafiya Maheer yayi gun Musharraf dake zaune yayi kamar baya jin discussion din Mami da yayan nasa, ya mike yana kallon Maheer ya basa hannu, Mami tace "Ina jin yayan nata ne wannan" MD dai ya dinga kallon Maheer a bit confused, Maheer ya karasa gun su bayan Musharraf yace masa tare suke da Mamin sa, Gaisheta yayi da ladabi Mami ta amsa masa, da damuwa ta kara da cewa "Ya me jikin?" Maheer yace "Alhamdulillah da sauki, mu karasa ciki" Mami ta kalli MD da gaba daya kansa ya ƙulle sai bin su yake da kallo with confusion, tace "Bari mu je...." Daga haka Maheer yayi leading dinsu zuwa ward din da Mayraah take, MD ya bi su da kallo still confuse, can dai ya bi bayansu shi ma da sauri, Maheer na shigowa ward din Mayraah ta dinga kallon Musharraf dake bayansa bata ko kiftawa, a hankali ta mike zaune har sannan kuma bata daina kallonsa ba kamar yanda shi ma yake kallon ta, MD dai na tsaye bakin kofar bai karasa ciki ba, anya ma ya taɓa zama confuse haka a rayuwarsa banda ranan da ya kawo Mayraah asibiti, Mikewa Ammi tayi ganin Mami ta fara welcoming dinta da fara'a, Mami ta karaso cikin dakin Ammi ta ajiye mata kujera tana mata sannu da zuwa, Mami sai da ta fara gaida Mama Ladi da tayi bake bake kan kujera, Mama Ladi na kallonta daga sama har kasa tace "Sannun ku da zuwa... Ai kun ma ci sa'a da aka barku ku ka shigo don lokacin ziyaran marasa lafiya ya wuce, duk da dai sun san wa enda suke raina ma hankali" Mami na murmushi tace "Ai kam da kyar suka bar mu Mama, ya me jiki?" Mama Ladi tace "Aa Alhamdulillah jiki yayi sauki, gashi har tana tashi zaune da kanta duk da maganar tata har yanzu sai an kasa kunne ake ji, da yake asibitin me tsada ne sun san kan aikinsu da karamin asibiti ne da yanzu gaisuwa ku ka zo ba dubiya ba" Mami tace "Gaskiya kam, Allah Ubangiji ya kara mata lafiya ya sa kaffara ne, Allah ya tsare gaba" Daga haka Mami ta karasa gun Ammi dake kallonta, da fara'a suka kara gaisawa Ammi na nuna mata kujera tace "Ki zauna Hajiya" Mami na murmushi tace "To nagode" Sai da ta fara karasawa kusa da gadon dakin tana kallon Mayraah cike da tausayinta tace "Sannu kin ji Mayraah, ya jikin?" A hankali Mayraah ta gaisheta, Mami ta amsa tace "Ya karfin jikin?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Da sauki" Kallonta kawai Mami da ta dafa gadon take, don bata taɓa ganinta ba sai yau, ita dai Mayraah kanta na kasa, Mami kam bata fasa kallonta ba, Ammi ta amsa gaisuwar Musharraf da murmushi fuskarta tace "Ya hanya Musharraf?" Da ladabi yace "Alhamdulillah Ammi, ya me jiki?" Ammi tace "Jiki Alhamdulillah da sauki" Usman ya mike ya gaida Mami, sannan suka gaisa da Musharraf ya fita ward din, Umar ma ya gaishesu daga inda yake zaune, Musharraf ya karasa kusa da gadon yana kallon Mayraah dake kallonsa ita ma, Mami ta zauna kujeran da Ammi ta ajiye mata, Musharraf ya sauke wani ajiyar zuciya yayi kasa da murya yace "Ya jikin?" Ta sunkuyar da idonta ta kasa cewa komai, nan da nan hawaye ya kawo mata, shi ma ya sauke idonsa kasa, Ammi ta nufi MD da ta gani tsaye bakin kofa ya kasa shigowa, tayi kasa da murya tace "Don Allah ku yi hakuri Dr nasan ba haka ka'idar asibitin yake ba, amma su daga kano suke ne, in dubata zaka yi ka shigo kawai sai mu mu fita tunda su baki ne" MD ya sauke idonsa ƙasa ya kasa ce mata komai, Ammi ta koma cikin dakin zata ce ma Mama Ladi da Umar su ɗan fita su je reception, Sai a sannan Mami ta lura da MD a bakin kofa, tace "Oh ashe ka biyo mu Daddy" Bai ce komai ba ya karasa ciki, Mami na kallon Ammi tace "He is my son, he is working here" Da sauri Mayraah ta daga kai tana kallon MD kamar yanda Maheer har ma da Ammi ke kallonsa da mugun mamaki, MD ya sauke idonsa, Sai a sannan Ammi ta lura da mugun kaman da suke, ta ja kujera ta zauna da mamaki tana kallon Mami tace "Don Allah fa?" Murmushi kawai Mami tayi, Ammi na jinjina kai tace "Ji wani ikon Allah kuma" Mayraah dai ta kasa daina kallon MD babu ko kiftawa zuciyarta na wani irin bugawa, MD ya daga kai ya kalleta, da sauri ta sunkuyar da kai, ya juya ya fita daga ward din, Musharraf ya bi sa da kallo, Ammi da ta kasa daina mamaki tace "Allah me iko, ai kam ya mana kirki sosai, tun da aka kwantar da mu yake tsaye kan mu, always making sure she is better...." Musharraf ya maida dubansa kan Mayraah da jikinta yayi sanyi sosai ga tunani kala kala dake yawo a ranta infact ta ma rasa wani irin tunani zata yi, yayi kasa da murya yace "Ya jikin?" Ta gyada masa kai amma ta kasa cewa komai don duk a daburce take, a hankali Musharraf yace "Pls say something" Tayi karfin halin cewa "Alhamdulillah" Bai iya ya sake ce mata komai ba saboda yasan duk kallonsu ake a dakin barin Mama Ladi dake ta kallonsa tana kokarin tuna inda ta taɓa ganinsa. MD na komawa office dinsa ya zauna kan office chair dinsa ya tallabi chin dinsa looking so confuse zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri, at the same time he was trying so hard to understand something, to a ina su Mami suka san Mayraah da family dinta kenan? Or are they family frnds? Kawai sai yayi convincing kansa da hakan wato they are just family frnds shine dai bai san da haka ba, ya kai minti sha biyar a yanda yake wayarsa da ke kan table ya fara vibrate ya sauke idonsa kan screen din a hankali ya ga Mami ce ke kiransa, dagawa yayi ya kai kunne murya can kasa yace "Mami" Tace "Na fito ward din yanzu, kana ina?" Ya sauke idonsa yace "Ina office, ai kin san office din Mami" Tace "Ohk gani nan zuwa" Mami ta kalli Musharraf da ya zauna reception don allura za ayi ma Mayraah shine yasa suka fito daga ward din har Mama Ladi da tace kora da hali kawai ake masu meye kuma za a ce su fita don za ayi mata allura kamar wasu bare, Mami tayi kasa da murya tace "Mu je office din Daddy Musharraf" Musharraf ya kalleta yace "Ki je ni zan jira a nan Mami" Mami tace "Saboda me? Wai kana da wani ɗan uwa da yafi Daddy ne a duniyar nan, me yasa ku ke haka Musharraf?" Shiru yayi bai ce komai ba, ganin yanda take kallonsa sai kuma ya mike, ta fara tafiya yana biye da ita har suka haura sama zuwa office din MD, Mami ta ɗan yi knocking kofar sannan ta bude ta shiga ciki Musharraf ma ya shiga, kallonsu kawai MD yake har suka karaso ciki sannan ya mike, Mami ta zauna kan kujera tace "Ka rage Ac din nan don Allah" Musharraf ya zauna ya dau remote din AC din dake kan karamin table dake gaban sofa din da suka zauna ya rage karfin AC din ya mayar da remote ya ajiye, MD ya nufi fridge dinsa ya bude ya dauko masu can drink biyu da goran ruwa biyu ya karasa ya ajiye kan table din, Mami tace "Kwanansu nawa kenan a asibitin yau?" MD ya tafi ya jingina da table din office din ya rungume hannunsa yana kallon Mami yace "Sati daya, amma a ina kika san su Mami? Ko family friends?" Mami tace "Wani family friends kuma? Ita ce fa yarinyar da Musharraf ya nema da aure aka fasa" Sai da MD ya dafa table din bayansa da sauri tsabar yanda zuciyarsa ya buga, Mami na kallonsa da mamaki tace "Are you okay?" Shi dai Musharraf idonsa na kan TV dake kunne a office din duk da yana sauraron conversation dinsu, MD ya dago da sauri yana girgiza kai ganin Mami ta mike yace "I'm fine Mami, just that tun safe muke wani aiki ne, i am exhausted..." Mami da ta tsaya tana kallonsa tace "To ko dai kwanciya zaka yi" Ya girgiza kai da sauri ya zauna kan kujeran dake kusa da shi ya jinginar da kansa jikin kujeran yace "I will be fine, it's just stress" Mami ta koma ta zauna tace "Sannu...." Sai a sannan Musharraf ya juya ya kallesa, Mami na kallon MD tace "I heard she was poisoned?" Gyada kai kawai MD yayi bai iya yace komai ba, Mami tace "Allah sarki, yarinyar nan na ganin jarabawa iri iri" Sai kuma da mamaki Mami tace "Wait... Amma ai da kai aka kai kudin auren nata Daddy ko ka manta ne? Ai zaka gane yayyinta maza da ma Abban nata...." Girgiza kai kawai MD that was speechless and confuse yayi yana kallon Mami amma ya ma kasa magana, Mami bata sake ce masa komai ba cause she can see he is tired don taga hakan a idonsa, bayan few seconds ya lumshe ido kansa na jingine da kujera zuciyarsa na ci gaba da bugawa, Musharraf ya dau can drink din gabansa ya bude ya fara sha, Mami kuma ta dau bottle water ta bude, Lkci daya MD ya bude ido bayan kusan minti biyu jin wayarsa na vibrate, yana dubawa ya ga Ceo ce ke kiransa, gaba daya yaji kamar an zare masa laka ne a jikinsa, Musharraf ya mike bayan ya kusa shanye drink din Mami na kallonsa tace "Zaka koma ward din ne?" Yace "I want to get something for her outside first" Mami