Showing 360001 words to 363000 words out of 456519 words

Chapter 121 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70622

bubbuga kafa tace "To ka fada in ji mana" shagala yayi da kallonta baya ko kiftawa, zata kwace nikab din a hannunsa yayi saurin mayar da shi bayansa, yana magana can kasa yace "You are not ready" Kofar parlor ya bude yana shiga ta bi bayansa da sauri, turus tayi a parlon tana kallon Haseenah dake zaune kasan carpet da tsohon cikin ta a gaba wanda kai sai kayi tunanin yan uku zata haifa, Maheer tun da ya kalleta sau daya shi ma by mistake yayi saurin dauke kansa, tayi wani irin baƙi kamar na zunubi, kai baka ce ta taɓa haske ba a rayuwarta ga uban ramar da tayi, ga ciki ya tsufa sosai, tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Ina wuni" Fuskarsa a murtuke yayi hanyar stairs without looking at her for the second time balle ya amsa gaisuwan, Mayraah dai ta sauke idonta kawai ta bi bayansa ita ma bata sake kallon Haseenah da ta sunkuyar da kanta ba, ko da Mayraah ta haura sama taga Maheer bangaren Ammi ya nufa, tana tafiya a hankali ta nufi dakinta ta bude ta shiga, lkci daya mood dinta ya canza ta zauna bakin gado tana kallon windan dakin. Maheer na shiga Parlon Ammi ya sameta zaune ita da Usman, Maheer ya karasa ciki ya zauna sannan ya gaisheta, ya kalli Usman shi ma suka gaisa, duk wannan abun bai kalli idon Ammi ba, infact rabonsa da gidan ma tun last friday bayan ya tafi da Mayraah, sai dai suna waya kullum, A hankali Ammi tace "How is Mimi?" Yace "She is downstairs" Ammi bata sake cewa komai ba, amma tana kula da how moody he is kuma tasan hakan bazai rasa nasaba da kiran da tayi masa dazu ba, bayan wani ɗan lokaci Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni dai ina ga Abban ku kilan don ba shi ya ci poison din bane shi yasa har ya nemi a wanke yarinyar nan, tunda gashi har anyi granting mata bail jiya, duk wannan bai ishe sa ba sai gashi ya sake ce mata ta zo min nan, wai ta je kano mahaifiyarta ta koreta sannan ta hanata zuwa gun yan uwanta gaba daya, to uwar me ni zan mata da ya sa ta taho min nan?" A fusace Ammi ta kare maganar, Maheer dake ta kallon Ammi a hankali yace "Ni dai nasan babu aure tsakanina da ita balle a kawo min wani batu can, imagine relatives dinta wa enda su ne dolenta sun yi disowning dinta sun koreta balle mu, i don't think she is suppose to be here, Barrister ya kamata tun farko yayi ma Abba maganar rashin dacewar haka, don nasan Abba bazai ce ta zo gidan nan ba without his knowledge" Ammi tace "Ni fa don takaici wllhi har yanzu ban sauka parlon ba balle in ganta, tun da Bilkisu ta shigo nan tace min ai ga wance ta zo na kira Abbanku nan take, sai yake ce min wai shi yace tazo nan kafin a san yanda za ayi idan ya dawo, Idan haka ne me yasa bazai kai ta wajen matarsa a kano ba? Ina ce can ma gidansa ne ko? To ai sai ya kai ta can ta zauna, don Wllhi in har gidan nan yarinyar nan zata kwana to barin gidan zanyi bazan kwana a ciki ba, duk wanda zai iya saka ma mutum poison don ya ci ya mutu to babu mugun abun da bazai iya aikatawa ba a rayuwa, tsaf zata iya yin komai, zuciyarta ta riga ta kekashe komai zata iya aikatawa, don haka in dai bata bar gidan nan yau ba to ni zan bar gidan" Usman dake ta sauraron Ammi ya daga kai yana kallonta, calmly yace "Abba fa ba wai yace nan zata zauna bane, mu ma ai baza mu yarda ta zauna mana a nan ba, Abba is just being considerate because of her pregnancy, and she just have 6 weeks remaining to put to bed...." Ammi tace "Sai aka ce lallai lallai sai a wajenmu zata haihu? In uwarta ta koreta to ta tafi dangin ubanta mana, wlh daga kai har Abban naka kuna bani mamaki, ku a ganin ku wannan shawaran da ku ka yanke a tsakaninku dai dai ne ko? Mu kuma bamu da right da za aji namu opinion din tunda kun gama shawara ko" Murmushi kawai Usman yayi, Ammi ta mike tace "Ina nan ina jiran Abban naku ya dawo in ji abinda yake nufi" Daga haka ta fita daga parlon rai bace. Bayan Magrib Mayraah na zaune parlon Ammi da plate din abinci a gabanta tana ci a hankali, har sannan taki sakin jikinta kai kace bakuwa ce ita a gidan, sai da ma Ammi ta bi ta har dakinta dazu kafin ta iya fitowa bayan tayi pretending kamar sallah ta shiga dakin tayi, ko da taje gaida Abba a bangarensa bata dade ba on like before ta dawo bangaren Ammi ta zauna, duk Ammi na lura da ita abun ma dariya yake bata, tana gama cin abincin ta mike zata fita da plate din Ammi tace "Ya isheki?" Gyada mata kai tayi, sai ga Bilkisu ta shigo da sallama, plate din ta amsa hannun Mayraah sannan ta dau warmers din abincin ta fita. Karfe takwas da yan mintuna Abba na zaune parlon parlon Ammi, sai Haseenah dake kan carpet ta sunkuyar da kanta, daga kusa da Ammi Mayraah ce zaune sai Maheer da Usman da su ma duk suna parlon, Ammi dai fuskarta babu yabo babu fallasa a parlon don ko kallon Haseenah taki yi, da Haseenar ma ta gaisheta a takaice ta amsa mata babu yabo babu fallasa without looking at her, da ta tuna irin wahalan da Mayraah ta sha sai taji they have nothing to do with Haseenah, cikin jikinta ma kawai fata take kar ya kasance na Maheer, don sam bata son su hada zuri'a da irin Haseenah, duk kawaicinta da hakurinta tunda har ta kasa yi ma Haseenah wnn kawaicin to ba karamin kullatar ta tayi ba a ranta, Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa ya fara magana yace "Da farko dai nasa an daukaka karan wannan yarinya ne ba don komai ba sai don albarkacin juna biyun da take dauke da shi, sannan Allah ma muna masa laifi mu nemi gafararsa ya yafe mana, ko ma ba don haka ba iyayenta mutanen kirki ne, duk da suna da damar daukan lauya da zai kareta tun farkon shari'a amma basu yi hakan ba, they neva supported her deed, sai ta dawo kamar mara galihu a lokacin, anyway all that aside, ban sa a daukaka karar nan don yarinyar ta dawo cikin rayuwarmu ba, Aa ina son mu yi considering condition dinta, sannan Maheer is suppose to take her responsibilities har zuwa sanda Allah zai sauketa lafiya, in ta yarda zata shayar da yaron it's left for her, idan kuma bazata shayar ba shi ma it's okay" Ammi dake ta kallon Abba zuciyarta na tafarfasa tace "So yanzu me kake nufin zai faru?" Abba ya kalleta, shi dai Maheer kansa na sunkuye bai taba jin zai bijire ma umarnin parent dinsa ba amma wnn umarnin kam baya jin zai iya because he have nothing to do with Haseenah, ko ganinta ma bai son yi har cikin ransa yaji yana mugun tsanarta, Abba ya katse masa tunaninsa ta hanyar cewa "Abinda zai faru, kawai wajen da zata zauna har zuwa sanda zata haihu Maheer zai samar mata a cikin garin nan, ko da self contain ne, sannan zai dau duk wani responsibilities nata tun daga ciyarwa har zuwa magani da abubuwan bukatan yau da kullum" Ita dai Haseenah kanta na duke hawaye na ta sauka idonta, A takaice Ammi tace "Na ga dai duk wannan responsibilities din da kake fadi za a iya mata a ko ina ba lallai sai an samar mata waje a Abuja ba, don't she have relatives? Ta tafi wajensu mana, sai lallai tana nan ne za ayi taking responsibilities dinta" Abba dai kallonta kawai yake, Haseenah ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "Don girman Allah Ammi kiyi hakuri ku yafe min, wallahi ban san inda zan je ba kuma daga nan, Mum dita ta koreni kuma ta hanani zuwa gun yan uwanta gaba dayan su, dangin babana duk yan Nijar ne, bayana ciwo yake min bazan iya zaman motar zuwa can ba wllh, don Allah ku rufa min asiri ku tausaya min..." Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Abba na kallon Maheer yace "Get her a self contain apartment, zan tura maka kudin" Abba na kai wa nan ya mike, Ammi ta bi sa da wani irin kallo, har ya kusa kofa ya sake juyowa yace "Kafin a samu gidan, ka biya mata hotel ko na 3 days ne ta zauna a can, so in za ku tafi gida sai ku tafi tare da ita ka samar mata hotel a hanya ka ajiyeta" Bude kofar parlon Abba yayi ya fita, Ammi da ranta yayi mugun baci ta mike ta wuce dakinta, Sai a sannan Mayraah da gaba daya mood dinta ya canza ta dago kanta a hankali sannan ta mike ta nufi kofa ta fice daga parlon Maheer ya bi ta da kallo, Usman ya mike shi ma ya fita daga parlon, Haseenah na kuka ta hade hannunta biyu tana kallon Maheer cikin rawan murya tace "Don girman Allah ka yafe min Maheer, wallahi nayi nadamar duk abinda na aikata, son zuciya ne ya kai ni ga aikata abubuwan da nayi, ka dubi girman Allah in ci albarkacin cikinka da nake dauke da shi ka yafe min ko zan samu sukuni a rayuwata..." Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, Maheer da ko kallonta bai yi ba ya mike ya wuce dakin Ammi, Ammi na zaune gefen gadon ranta a bace, Maheer ya zauna kan kujeran dakin a hankali yace "Ammi this time around i am sorry zan yi abinda ban taba yi ba a rayuwata, which is ignoring Abba's order, gaskiya bazan iya yin duk abubuwan nan da Abba ya lissafa ba don i can't withstand the sight of her" Ammi dake kallonsa ta kwantar da murya tace "Hakuri zaka yi kawai Maheer, yanzu yana ganin ka kiyi cewa zai yi ni ce na zugaka barin yanda yaga nayi reacting a parlon, don haka kawai kayi hakuri kayi abinda yace, kai din me biyayya ne na sani, kuma baza ka taɓa tabewa ba, ba dai nan da sati shidda bane zata haihu, Allah ya kai mu lokacin, in ta haihu sai ayi DNa test din da aka ce" Shi dai Maheer bai ce komai ba amma sam ransa bai so haka ba, wani mugun tsanar Haseenah yake ji har cikin ransa, Ammi ta katse masa tunanin da yake tace "Dare nayi baza ku tafi gida ba?" Yayi kasa da murya yace "We will be spending the night here" Yayi hakan ne don baya jin zai iya daukan Haseenah a motarsa, Ammi tayi shiru tana kallonsa, can tace "Tsoron yarinyar nan fa nake ji Maheer, bamu san da wani kulalliyar ta zo ba kuma, don duk wanda zai iya sa ma mutum guba a abinci yaci don ya kashesa to babu abinda bazai iya aikatawa ba, sam zuciyarta babu alkhairi a cikinsa, gwara dai a kai ta can hotel din" Maheer yace "Babu abinda zai faru in sha Allah Ammi... Gobe da safe idan muka fita zan kama mata hotel din sai ta tafi can" Ammi tace "Toh gaskiya sai dai a bude mata Chalet taje can ta kwana, don ni hankalina bai kwanta da ita ba" Maheer bai sake cewa komai a dakin ba, ita ma Ammi tayi shiru, da ta tuna irin wahalar da Mayraah ta sha a hospital sai taji wani sabon tsanar Haseenah a ranta, mikewa Maheer yayi daga karsh ya nufi kofa, Ammi ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle mata kofa, bai ga Haseenah a parlon ba alamar ta sauka parlon downstairs, walking slowly ya nufi dakin Mayraah, a hankali ya bude kofar dakin ya ganta kwance kan gado, ya shiga ciki ya kulle kofar gently sannan ya karasa kusa da ita ya zauna yana kallonta, ita dai bata yarda ta kallesa ba, ya kamo hannunta yace "Are you okay?" Shiru tayi bata ce komai ba, Yace "Mimi" Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa suka hada ido, sosai gabanta ya fadi don har ta mance rabon da ta hada ido da shi, Ya daura forehead dinsa kan nata as if counting his words yace "Should we spend the night here or we should go home?" Kokarin mikewa zaune take hakan yasa ya dagota ta sauke kafafuwanta daga kan gadon tace "I want to take my bath" Ya bi ta da kallo har ta tashi tsaye ta nufi bandaki, tana shiga ta kulle kofar ta jingina da bango ta fashe da kuka a hankali, wanda ita kanta bata san dalilin kukan ba, Maheer ya fi minti goma zaune dakin kafin ya mike tsaye da kyar ya fita daga dakin ya sauka downstairs, Bilkisu ce tsaye kan Haseenah bayan ta bata sakon Ammi kan cewar ta je Chalet ta kwanta, Bilkisu ta kara da cewa "Kinsan duk anyi occupying dakunan nan, zaki fi sakewa a can bangaren idan kin je" Cikin sanyin murya Haseenah tace "Toh, amma bayana ya rike bazan iya tashi yanzu ba sai zuwa anjima, kafafuwana ma sun min nauyi sabda benen da na hau, ki bani makullin idan naji dama dama sai in je can" Bilkisu tace "Toh" Mika mata makullin tayi, Maheer da ko kallon inda suke bai yi ba ya wuce dakinsa. Wajen karfe goma Mayraah ta sauko kasa sanye da hijab har kasa don kayan bacci ne jikinta, Bilkisu na zaune parlon har sannan tana jiran fitan Haseenah sannan ta kulle kofa kamar yanda Ammi ta umarceta, Lkci daya kamshin Mayraah ya zagaye parlon bata kalli direction dinsu ba ta wuce kitchen, Ta shiga kitchen ba dadewa Maheer ya fito daga dakinsa, bin parlon ya dinga yi da kallo as if trying to figure out something, can ya nufi kitchen Haseenah dake sauke numfashi a hankali ta bi sa da kallo, Har sannan bata san da auren Mayraah da Maheer ba, Mayraah ta juya jin an bude kofar kitchen din, ganin shi ne ta maida dubanta kan abinda take yi, ya karasa har bayanta ya tsaya, leaning against her, zuciyarta ya fara bugawa da sauri, as if whispering yace "Har da ni shayin?" Kai ta gyada masa da sauri don tsoro ma take kar wani ya shigo ya gansu a haka, still a hankali yace "To a kawo min nawa daki idan an gama" nan ma kai ta gyada masa, ya juya ya fita daga kitchen din, wani ajiyar zuciya ta sauke jin kafafuwanta sun mata nauyi ta juya ta jingina jikin cabinet din kitchen din. Mayraah na kai ma Ammi shayinta ta dawo ta dau nasa ta fito zata kai masa, har a sannan Bilkisu na zaune parlon tana jiran sanda Haseenah ta fita, Haseenah ta bi Mayraah da kallo har ta dau hanyar dakin Maheer, Mayraah bata kulle kofar ba gaba daya ta karasa ta ajiye masa shayin, gani tayi ya sauka ya tafi ya kulle kofar har da sa makulli, ta zaro ido gabanta na faduwa tace "Yaya wllhi Ammi fa na jirana zata sa ni wani aikin..." Yace "Na wa aikin ai ya fi na Ammi lada yanzu" Marairaice masa tayi tana komawa baya.... Ashe dama ba shayin zai sha ba don at the end they ended up spilling the whole cup of tea a kasan tiles din dakin.... Wajen karfe biyun dare Mayraah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi sbda bacci, duk da baccin bai isheta ba haka ta zame jikinta a hankali from his, ta sauke kafafuwanta kasa, sai da ta laluba inda zata ga ribbon dinta kan gadon bayan ta gani ta dauka ta daure gashinta.... After dressing up ta dau hijab dinta ta saka sannan ta nufi kofa, har wani rurrufewa idonta suke sbda bacci, a hankali ta bude kofar dakin ta fita ta kullo masa, ido hudu suka yi da Ammi da saukowarta parlon kenan, Mayraah ji tayi kamar ta nutse a wajen, nan da nan baccin ya bace idonta, Haseenah dake zaune idonta biyu don bata iya yin bacci, sai kallon Mayraah take bata ko kiftawa, Bilkisu kuma bacci ya ɗauketa kan kujera a parlon, Ammi dai tun da ta kalli Mayraah sau daya ta dauke kai tace "Mimi baki yi bacci ba dama" Mayraah da ta kasa kallonta tana kame kame tace "Eh Ammi, yanxu na sauko kasa, ina kallo ne a laptop" Daga haka tayi saurin barin wajen ta wuce sama ba tare da ta jira me Ammi zata ce ba, bandaki Mayraah ta shiga tayi wanka sannan ta shige cikin duvet dinta amma ta kasa bacci sai juye juye take, ta rasa me yasa moment din dazu ya makale mata a rai haka, daga karshe ta rufe har kanta bayan ta takure kusa da second pillow dinta, a haka ta samu bacci ya ɗauketa.
[9/28, 9:41 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Washegari da asuba Mayraah na idar da sallah ta tafi bangaren Ammi don gaisheta, Ammi dai kallonta kawai take bayan ta amsa sallamarta, har ta zauna kan carpet kanta a kasa tace "Ammi ina kwana?" Ammi tace "Lafiya lau Mimi, how was ur night" Tace "Alhamdulillah" Ammi tace "Maa sha Allah" Daga haka Mayraah bata sake cewa komai ba a dakin, ko minti 5 bata yi da shigowa ba Maheer ya shigo dakin da sallama, Ammi ta amsa masa sallaman, zaunawa yayi yana kallon Ammi yace "Ina kwana" Ammi tace "Lafiya lau, an tashi lafiya?" Yace "Alhamdulillah" Mayraah ta ɗaga kai suka hada ido da shi, sunkuyar da nata kan tayi tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" Bata sake ce masa komai ba, Ammi na kallonsa tace "Likita za a kira ne ya dubata ko asibitin zaka kai ta?"

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login