Showing 399001 words to 402000 words out of 456519 words

Chapter 134 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70700

A hankali yace "Ohk, bari mu karasa gida sai kiyi wanka ki huta" Ita dai bata kallesa ba balle ta basa amsa, a wani eatry ya tsaya ya siya mata abinci sannan suka nufi gida... Bayan sun isa gida duk moodiness din Mayraah sai da Maheer yasan yanda yayi ya dawo da ita lively, tuni taji zuciyarta ya wanke babu wani abu dake damunta sai abu daya da ya makale can ƙasar zuciyarta, bata taɓa jin damuwar abinda ke ranta ba sai yau, duk da haka bata bari damuwar yayi tasiri a fuskarta ba. Bayan kwana biyu Mayraah na kitchen da daddare tana hada ma Maheer fruit salad, bayan ta gama ta fito parlor da shi, bata gansa a parlon ba, bayan ta ajiye fruit din kan center table ta nufi master bedroom nan ma bata gansa ba, fitowa tayi ta tafi Bedroom dinsa still baya ciki, ta dawo parlor tana mamakin inda yaje, an yi sallan isha balle tace masallaci ya tafi, karasawa windan parlor tayi tana duba compound, tsaye ta gansa yana waya a Balcony amma bata jin abinda yake cewa don widunan a kulle suke gaba daya, ta fi minti biyu tsaye tana kallonsa ko kiftawa babu, a hankali ta juya ta bar jikin window din ta wuce dakinta, dama ta riga tayi shirin bacci ta kashe wutan dakin tayi kwanciyarta ta rufa da duvet, ko minti biyar bata yi da shigowa ba taji ya bude kofar dakinta, kunna wutan yayi yace "Kwanciya kika yi Baby" Ta juya tana kallonsa a hankali tace "Dama ai nace maka ina jin bacci tun dazu" Karasawa yayi ya zauna kusa da ita ya sauke duvet din yace "Baza ki sha fruit salad din ba?" Tace "Na sha wanda zan sha" Yace "Me yasa baza ki kwanta a dakina ba?" Ta ɗan yi murmushi tace "I don't want to stain ur white bedsheet" Ya wara ido yace "But ai flow din ya ragu wife, in ma kin bata ba sai in wanke ba" ta make kafada tace "I want to sleep here today pls" Yayi kasa da murya yace "Ohk... sleep tight wifee" Pecking din forehead dinta yayi ya ja mata duvet din, sannan ya tashi ya kashe mata wuta ya fita daga dakin... Kasa bacci Mayraah tayi daren nan, har karfe biyu ta nemi bacci ta rasa gashi ba tsarki gareta ba balle tayi ta sallah, sosai take jin damuwa a ranta, a hankali ta sauke kafafuwanta daga saman gadon ta mike tana tafiya slowly ta kunna wutan dakin sannan ta bude kofa ta fita, wutan corridor a kunne yake amma wutan parlor a kashe, duk da haka sai da ta hangosa kwance kan 3 sitter yana bacci, tana tafiya a hankali ta karasa shiga parlon, wayarsa da ta gani a ajiye side dinsa ta tafi ta dauka, ta koma dakinta ta bar kofar a bude ta zauna gefen gado, last call dinsa ta duba taga wani number ne, kawai ta shiga text message taga message da aka tura masa tun karfe hudu na yamma kamar haka, "Assalamu alaikum Good evening Maheer, na shigo Abuja da yaran na zo wani interview na aiki a wani Company, it's raining heavily, gashi an sace min jakata dauke da wayata da atm card dina da kudade a tasha, yanzu haka ina motor park na fake a wani rumfa da yaran, am using a borrowed phone to text you don na kikkira baka daga ba, niyyata dama in biya hotel na kwana uku, plss i am waiting for ur response Maheer, i am stranded, gashi ruwa ake sosai, ko kuma zaka taimaka ka amso min makullin gidan da aka min renting tunda rent din bai yi expire ba in zauna a nan har in gama abinda ya kawo ni ba tare da su Ammi sun san na ma zo garin ba" Mayraah na gama karanta text din ta koma call log, gani tayi immediately da ta tura masa text din ko second bai kara ba ya kirata, and they spent 5 minutes speaking on phone, daga yamman zuwa yanzu sun yi waya sau uku, a hankali Mayraah ta ajiye wayar a gefenta, wato shi yasa ya fita dazu ana ruwa har take tambayansa inda zai je cikin ruwa yace mata home service aka kirasa kuma Emergency ne, Mayraah ta goge hawayen da taji ya gangaro mata, haske taga wayar yayi ta juya tana kallon screen din taga ita ke kiransa, Mayraah ta dinga kallon wayar, can tayi picking ta kai kunne amma tayi shiru, daga daya bangaren cikin tashin hankali Haseenah tace "Maheer har yanzu fa basu daina ba, kuma nayi duk abinda kace, gashi baza mu samu abun hawa ba da na kai su asibiti, pls ya zan yi?" Katse wayar Mayraah tayi ta mike a hankali ta fita ta mayar masa da wayarsa ta ajiye gefensa ta dawo ta kwanta, kuka taji ya taho mata ta rufe fuskarta da pillow tana jin zuciyarta na mata zafi.... Wajen karfe hudun asuba Maheer ya shigo dakinta har ta samu bacci ya dauketa ya tasheta, yayi kasa da murya yana kallonta yace "Mimi zan je in duba patient dina, i will be back before 7am in sha Allah" Mayraah tace "Ohk" Daga haka ta juya masa baya ta rufe idonta, ya mike ya kashe mata wutan dakin ya fita... Ammi ce zaune parlon Abba bayan sallan asuba, magana Abba ke mata amma idonta na kan Usman dake zaune kan carpet, at the same time tana sauraron duk abinda Abban ke cewa, bayan Abba ya kai aya tayi wani murmushi har a sannan idonta na kan Usman, Calmly tace "Usman" Usman ya daga kai ya kalleta, tace "To sai ka zabi ko ni ko yarinyar...." Tana kai wa nan ta mike ta fice daga parlon, kallon mamaki Abba that was speechless ya bi ta da shi, after few seconds Usman ya daga kai yana kallon Abba yace "Abba na hakura kawai, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi"
[10/15, 4:18 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer ya mike bayan ya kwantar da Aymaan dake bacci a hannunsa yana kallon Haseenah dake rungume da Aryaan shi ma yana baccin yace "In kinsan haka zaki dinga biyowa hanya da yaran nan suna wahala i am assuring you za mu amshe su a wajenki, since you don't have conscience" Haseenah ta daga kai ta kallesa tace "I don't Understand I don't have conscience Maheer, yaushe da yaushe na biyo hanya da su? Amarya fa muka kai kaduna kuma a gidan aunt dina yarinyar da aka aurar take, nima kuma a gidan nake, so meye laifi don mun kai ta kaduna, sannan tare da mai aikin aunt dina muka taho kadunan saboda ta taimaka min da renon yaran, Abuja da na zo kuma nace maka interview na zo na aiki, in banda dalili me zai biyo da ni hanyar Abuja, ko shikenan saboda ina da 'yan biyu bazan nema ma kaina mafita ba a rayuwa kar in nemi aikin yi? Allowance din da ku ke turo min duk wata ai na 'ya yanku kawai ku ke lissafi ku turo ba wai har da ni uwarsu ba, so i have to look for work, kuma da na bar yaran a gida waye zai kula min da su bayan nace maka Aunt dita bata da lafiya saboda gajiyan biki" Maheer yace "Shi 250k din ne kike cewa na babies kadai ne?" Haseenah tace "Of course, kasan babban gwangwanin cerelac kwana nawa yake masu? Sannan common pampers a rana sai in canza masu yafi sau biyar, suna cin Noodles da kwai and even biscuits, so what is 250k that u are calling" Maheer bai tankata ba ya dau makullin motarsa, tayi kasa da murya tace "To yanzu in zan je interview din a ina zan bar yaran, i tot u will be with them har in dawo Maheer" Maheer yace "Ki kai su gida gun Ammi" Haseenah ta dinga kallonsa ta rasa abun cewa, yace "Shi wayar da kika ce min kin ara a park bar maki shi aka yi kenan" Haseenah tace "Na Coursemate dina ne, kuma tare muka yi applying aikin da shi, tare kuma aka kira mu interview, wayace karama ba wai babba ba" Tana kai wa nan ta jawo jakarta tace "Pls zan dan fita in siyo masu Noodles da kwai da zan dafa masu idan sun tashi, naga akwai sauran gas sai in dafa masu" Hijab dinta ta dauka ta saka ta fita, shi dai Maheer na tsaye yana kallon yaran dake bacci, Haseenah na fita ta dinga waigen gate din gidan don ta tabbatar Maheer bai fito ba.... Sai bayan minti sha biyar ta dawo da ledan Indomie da kwai a hannunta, Maheer ya nufi kofa ya fita without saying anything to her, bin bayansa tayi ya juya yana kallonta, tace "Kulle gate din zan yi" Shi dai bai ce mata komai ba har ya fita daga compound din... Karfe tara saura na safe Maheer ya iso gida, hadari ne sosai a garin, bayan yayi parking ya sauka daga motar yana kallon wayarsa dake ringing, ganin Ammi ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, sallama yayi mata hade da gaisheta, ko amsa gaisuwar bata yi ba ta hau jero masa jawabi rai bace, a hankali Maheer ke tafiya zuwa entrance din shiga gidan yana sauraron duk abinda Ammi ke cewa a wayar, yana shiga parlor ya zauna kan kujera ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ya kwantar da murya yace "Don girman Allah Ammi kiyi hakuri ki daina irin wannan maganar, duk bai kai haka ba plss, ni nasan barrister in dai kika ce baki son abu to ya bar shi har abada komin son da yake ma abun nan, kema kuma kinsan da haka so bai kamata kina wannan maganar ba, kiyi hakuri don Allah" Hakuri Maheer ya dinga ba Ammi yana kokarin calming dinta down amma taki sauraronsa, daga karshe ta kashe wayar, ya fi minti uku zaune a Parlon ya ma rasa tunanin da zai yi don Ammi ta dau lamarin da zafi, after a while ya mike ya nufi dakin Mayraah, yana bude kofar dakin tana fitowa daga bandaki daure da towel tayi wanka, sau daya ta kallesa ta nufi gaban mirror dinta, ya kulle kofar ya karasa ciki yayi kasa da murya leaning against her body yace "Good morning Better halve" Tana goge jikinta without looking at him tace "Good morning My man" Yana tsaye a bayanta yace "Are you just waking up Baby gal?" Tace "Yeah" Yace "Kin yi breakfast?" Ta girgiza masa kai tace "Zan dai yi yanzu" Duk a takaice take basa amsan tana shafa lotion dinta, a hankali yace "Ohk, bari in je inyi wanka, yau dama bazan je aiki ba, we have all day to cuddle baby gal" Ya kai bakinsa wuyanta yace "Don ma akwai interruption..." Hada ido suka yi ta madubi ta sakar masa murmushin da bai kai zuciyarta ba tana ci gaba da shafa cream dinta, yace "Ko ya dauke ne?" Er dariya tayi tace "Yana nan tukunna" Yace "Ohk let me take my bath" Yana fadin haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo ta madubin gabanta har ya fita ya kullo mata kofa, sosai take jin zuciyarta na mata zafi, ita kanta tayi mamakin ta yanda aka yi ta iya dakewa haka take basa amsa, tayi karfin halin yakice kukan da taji na kokarin zuwa mata ta gama shafe shafen da zata yi ta dau kayanta ta saka, gefen gado ta zauna, ta dade zaune kan gadon tayi nisa tunanin da take, kawai saukan ruwan sama ta ji, a hankali ta mike ta tafi ta kulle window din dakinta da ta bude sannan ta fita daga dakin ta tafi parlor, kitchen ta tafi ta dauko breakfast din da tayi ma kanta, tana fitowa parlor sai gashi shi ma ya fito, kallo daya tayi masa ta karaso parlon ta zauna kan carpet da breakfast dinta, ya nufeta ya zauna gabanta yana kallonta yace "Nawa fa?" Ta ɗan buda ido tana kallonsa tace "Ai na zata za kayi kafin ka dawo, i wasn't even expecting you, all my thought daga can zaka tafi Hospital sai yamma kuma" A hankali yace "Shiyasa baki yi breakfast da ni ba?" Ta gyada masa kai, yace "Toh yanzu da na dawo ya za kiyi da ni?" Ta langwabar da kai tace "Sai ka jira idan anyi na rana, kaga wannan dai bai da yawa" Kallonta kawai Maheer yake ganin she is so serious, ita dai ta sauke kanta ta fara cin abincinta, daga kai tayi taga har sannan kallonta yake tace "Ko kuma ka hada shayi ka sha kafin inyi girkin rana" Ya ɗan yi murmushi yace "Zan jira na ranan kawai" Yana fadin haka ya mike ya koma kan kujera yayi powering Tv, tsaf Mayraah ta cinye ɗan dankali da kwan da ta soya ta tafi ta kai plate din kitchen ya bi ta da kallo, tana fitowa daga kitchen din ta karaso ta zauna gefensa tana kallonsa tace "Zan yi bacci idan karfe biyu yayi ka tasheni zan girka lunch" Yace "Ohk dear" Mikewa tayi ta nufi dakinta, tana shiga ta kulle kofarta, wani mugun haushinsa take ji har cikin ranta, ta kwanta ta rufe har kanta da duvet jin hawaye na sauka idonta. Ammi ta fito daga dakinta wajen karfe hudu jin kamar Mama Ladi ce ke rafka sallama a parlonta, ai ko ta ganta tsaye duk ta jike da ruwan sama, Ammi tace "Mama kece cikin ruwan nan?" Mama Ladi tace "To ba kya gan ni cikin ruwa ba, daga kaduna fa nake, wllhi idan nace ban gaji da froblem din pamilyn nan namu ba nayi ma Allahn da ya halicce ni karya, Allah ma ya gani na gaji, ace daga wannan sai wannan kamar mun tafka babban sabo a duniya, Al-qur'an a pamilyn Alhaji Saminu ban ga suna haka ba, in kin gaji da zama da Mamudan ne ba sai ki kama kanki ba cikin mutunci da mutuntawa, wallahi shayi me ƙauri na hada zan sha da burodi da kwai Mamuda ya kirani a fusace wai babu abinda kika mance baki gaya masa ba har kina kiransa da butulu me manta alkhairi, yace min gori sai wanda kika mance ne baki masa ba, shayin da ban sha ba kenan na kamo hanya kamar tababbiya ko rigar mama ban sa ba, ai ko rabin tafiya bamu yi ba ashe rubabbiyar mota na shiga motar ta lalace mana a tsakiyar daji, an fi awa uku ana kokarin dawo da ran motar duk muka zazzauna a gefen titi da ma Allah ya rufa mana asiri ba a kwashe mu anyi cikin daji da mu ba, yanzu haka duk hanjin cikina sun galabaita da yunwa, ga dukan ruwan sama, wannan wani irin jaraba ne ni Ladi, yaushe kika lalace kika tambade haka Hajaru?" Ammi tace "Sai kuma bai gaya maki nace ya tattara ya bar min gidan ya koma gun amaryarsa ba?" Mama Ladi tace "Au, wato kin yanke shawaran zaki sallama ma mai mazaunan mijinki tun auren saurayi da budurwa? Ashe baki da seti ban sani ba, a kanki aka fara kishiya ne wai? To bari dai in canza kayan nan in dawo kada mura ya kamani a banza a hofi ku bar ni da jinya ni ba tsinana ni ku ke da komai ba, shi ma Mamudan yace min yana gida tsabar bacin rai ko fita bai yi ba yau, bari dai in sauya kaya in dawo...." Mama Ladi na tafiya dakin da ta saba sauka ta canza kayanta sannan ta nufi bangaren Abba, tare suka dawo parlon Ammi da Abba, Mama Ladi ta shiga daki ta kira Ammi, Ammi ta zauna kan one seater fuskarta a daure bayan ta fito, Mama Ladi ta zauna tana kallonta tayi kasa da murya tace "Yanzu fisabilillahi Hajara gaki da yara gandara gandara har kin aurar da biyu ana harin na uku amma ace abinda baki yi da kuruciyarki ba shi zaki fara yanzu na rashin yi ma miji biyayya? Duk kin bi kin maida kanki fitinanniyar bafillatana?" Ammi tace "Mama ba fa sai an kai zancen nan da nisa ba, kawai Mamuda ya sauwake min ya tattara ya koma gun matarsa ya bar min gida, bana auren kuma, idan na masa rana zai sani wataran, in ma ban masa ba duk zai sani, haka kawai a dakeni a hanani kuka, akan me? to wallahi na gaji kawai ya sauwake min... naga dai duk maganar da yayi ban tanka sa a parlon ba da ɗana nayi magana na tashi na fita, still ya biyoni bangarena zai min tijara akan nace ɗa na bazai auri er matarsa ba, to na gama aurensa yaje can ya zauna da warce ta fi masa alkhairi" Mama Ladi ta saki salati ta dafe kanta tace "Huhuhu, yau ga abinda ya isheni ni Ladi" Abba dai kallon Ammi kawai yake, Mama Ladi ta sake kanta tace "To ai in ke mahaukaciya ce shi Mamudan ba mahaukaci bane Hajara, kuna zaune lafiya na kusan shekara arba'in babu wanda ya taɓa jin kanku sai da ku ka manyanta za ku fara abubuwa irin na yara, yanzu haka ku ke so Mera da Maheer su kwaikwaya?" Ammi ta katse Mama Ladi tace "Ai wallahi da raina dai Maheer bai isa yace zai ma Mayraah kishiya ba sai in bana numfashi, ba ma Maheer ba duk 'ya yana basu isa su ce za suyi ma matansu kishiya ba, don ina tsoron kada suyi gadon rashin adalci irin na ubansu Allah ya tambayesu, kinga kuwa ai na taimake su" Abba har sannan bai daina kallon Ammi ba, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Mamuda bai hanaki ci ba, bai hanaki sha ba, bai hanaki sutura ba, bai kai ma amaryarsa kwananki ba, ga ki a muhalli me kyau na nuna ma sa'a gida duu Ac, to wani rashin adalci kike fadi in za ayi batu na tsakani da Allah? Sannan ke dai naga ba gida daya kike da Aminar nan ba balle ki ga ana fifitata a

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login