Showing 267001 words to 270000 words out of 456519 words
Khalil ba ya karasa kusa da Mayraah yana kallonta, can ya juya ya kalli Dr Khalil dake kallonsu, yace "I think da safe relatives dinta can come in one at a time to check on her..." Dr Khalil ya gyada kai yace "Haka ne, Allah ya kai mu goben, Allah kuma yasa kafin goben improvement din yafi haka...." Daga haka ya juya ya fita, MD ya bi sa da kallo, a hankali ya juya ya kalleta, sai kuma ya duka ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Can you hear me Mayraah?" A hankali ta bude lumsassun idonta, he was astonished seeing her open her eyes, Bai san sanda yayi mata murmushi ba, murya can kasa yana massaging hannunta yace "You will get well sooner, you are already doing great, be strong...." Rufe ido ta sake yi, tun kafin magrib ta ke making different movement of discomfort as a result of the breathing tube and that's a very good sign of recovering slowly, amma duk bata bude ido ba sai a yanzu, murza hannunta ya sake yi therapeutically, ta bude ido a hankali, yayi kasa da murya yace "Can you hear me...." Kallonsa kawai take looking so pale and weak, ya sauke idonsa daga kallonta, bai sake ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa, har a sannan Maheer na zaune bakin ICU, MD na kallonsa yace "You can check on her, speak to her" Mikewa Maheer yayi yace "Thank you Dr" MD ya bar wajen, Maheer ya shiga unit din, yana isa bakin gadon ya duka ya kamo hannunta a hankali yace "Mimi..." Bude ido tayi, Maheer couldn't believe that, ya kalli Ventilator Machine din da sauri ya ga an ma rage karfinsa, ya matsa dab da ita yace "Get well pls Mimi, we all miss you, i know you to be a strong baby gal, stay calm and relax... You will get better very soon, we love you Mimi" sweet words haka is also a sedative therapy dake improving mental and psychological well being na patient in ICU, it really helps patient to be relaxed and comforted, bin sa kawai Mayraah take da ido, yana massaging mata hannu gently yana kallonta giving her a warm smile yace "Be strong for me, ur Ammi, Abba and barrister..." Lumshe ido tayi, ya sauke ajiyar zuciya feeling so much relieve now. Karfe tara Usman ya shigo IC unit din tare da Dr Khalil, Dr Khalil na kallonsa yace "Speak calmly to her" daga haka ya juya ya fita, nurse daya ce zaune tana monitoring din Mayraah, Usman ya karasa kusa da gadon, idonta na lumshe, ya zauna kan kujeran dake kusa yana kallonta, kasa ce mata komai yayi ya sunkuyar da kansa, bayan few seconds ya riko hannunta ta bude ido, still bai iya yace mata komai ba yana rike da hannunta for almost 10 mins, sake dago kai yayi ya kalleta, yayi pecking hannunta ya lumshe ido da kyar ya iya cewa "Come back soon Mimi" Daga haka ya mike ya fita waje. Sha daya saura Dr Hamid ya shigo Unit din, da mamaki yake kallon nurse din dake kokarin canza ma Mayraah hospital gown dinta da blanket yace "Madam sau nawa za a canza gown din nan ne?" Nurse din zata basa amsa sai ga MD ya shigo, Dr Hamid ya duba abinda zai duba sannan ya juya ya fita, MD ya kalli nurse din yace "What are you waiting for?" Nurse din tace "Dr Hamid just came in to check on her, yanzu zan canza" Juyawa MD yayi ya fita. Washegari da safe Abba ya shiga ICU din tare da Maheer, sosai hankalin Abba ya kwanta ganin state din Mayraah, don yanzun ma ta bude ido duk tana kallonsu, Maheer dai ya duka gabanta yana rike da hannunta yayi mata murmushi yayi kasa da murya yace "Good morning Mimi" Kallonsa kawai take, mintinsu sha biyar suka fita, Abba ba kallon Maheer yace "To yaushe za su yi disconnecting abubuwan nan da suka sa mata?" Maheer yace "Ana jiran aga ko zata iya numfashi da kanta babu matsala sai a cire in sha Allah, nasan zuwa anjima kilan a cire tunda an rage karfin machine din sosai" Abba yace "Toh Alhamdulillah, mun gode ma Allah, nayi farin ciki da abinda wannan asibitin suka mana na nuna concern dinsu, ko nawa suka bukata a biya nasan they deserve it" Maheer yayi kasa da murya yace "Ammi zata iya shiga ta dubata ita ma?" Abba yace "A dai bari a cire abubuwan nan da aka sa mata tukunna" Maheer yace "Haka ne" Ceo ce ta shigo asibitin leaving her securities outside, MD da ya fita dauko mata laptop dinta da wasu abubuwa yana biye da ita a baya, tana ganin Abba maimakon ta wuce sama sai ta tsaya suka gaisa tace "Ka shiga ka dubata ko Alhaji...." Abba yace "Eh bamu dade da fitowa ba, na kuma ji dadin yanda muka sameta, jiki kam Alhamdulillah" Ceo tayi murmushi tace "Mun gode Allah" Daga haka ta wuce sama MD na biye da ita har zuwa office dinta, ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga ya kulle kofar ya kunna AC, ajiye handbag dinta tayi ta zauna tace "I left early yesterday, wani family issue ne ya taso shi ne naje nayi intervening, tun daga gidansu nayi niyyar kiran ka in baka samples din nan...." Tana fadin haka ta warware karamin towel din hannunta ta ajiye kananun bottles biyu dauke da blood samples kan table dinta, sai kananun ziploc nylon biyu each dauke da strand of hair tace "I need genetic testings on this, commence it immediately" MD ya dauka yace "Ohk Ma'am" zai fita tace "Yauwa ya jikin Mary Ann? Zuwa yaushe za ayi disconnecting dinta daga Machine din?" Da ladabi yace "Har yanzu numfashin isn't steady so we are still watching over it" Ceo ta sauke ajiyar zuciya tace "Idan na sha coffee zan sauko in duba ta yanzu" Yace "Ok Ma'am" Daga haka ya juya ya fita, duk da Abba bai so Ammi ta ga Mayraah ba sai an cire mata Ventilator Machine, amma saboda yanda ta mugun daga hankali haka likitocin suka saka a barta ta shiga kawai ta ganta, ai ko ranan kwana Ammi tayi kuka har da karin drip, don ita yanda taga an jojona mata wayoyi a jiki duk da idonta biyu tana kallon kowa gani take kamar fa babu sauki kwata kwata, in da sauki ai baza a makala mata wayoyi ba, haka nan aka ci gaba da kula da Mayraah a asibitin, a duk sanda Maheer ko Usman or Abba wani zai shiga wajen ta ya ganta babu hinderance, tunda Incident din nan ya faru MD ke zaman asibiti 24/7 don dama Bedroom babba garesa a office dinsa, Surkar Dr Khalil da inna da ita kanta Zainab duk sun zo asibitin duba Mayraah, duk da basu shiga ICU ba iyakarsu wajen Ammi. Aunty Mariya na kitchen yau ma kamar kullum tana dafa abincin da za a kai ma Ammi asibiti, kwanansu na shidda kenan a Abuja amma Abba yace ba sai sun je asibitin ba tukunna, hakan na damun Aunty Mariya amma bata masa musu ba duk suna gida sai dai tayi girki ita da Bilkisu Usman ko Maheer ya zo ya dauka ya kai asibiti, Mama Ladi ce ta shigo kitchen din tana yafa gyale tace "Sai na dawo Mariya" Aunty Mariya na kallonta tace "Ina kuma zaki Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Ina kuwa zan je banda asibiti? Ko a kasashen waje ban taɓa jin inda aka ce baza a shiga asibiti a duba marasa lafiya ba in ba a tsinannen asibitin can ba, in haka ne meye amfanin zuwana? yau fa kusan kwana shidda mun tare a katon gidan nan sai dai mu ci abinci mu kwanta kamar wasu mayunwata" Aunty Mariya tace "Amma dai Alhajin da kansa yace ba sai mun je ba ka'idar asibitin kenan ko, kuma dazu da muka yi magana da shi yace ko zuwa jibi sai mu je" Mama Ladi tace "Amma ai katuwar matarsa Amina ita dai taje kuma an bar ta har ta shiga, tun da har nan ta zo ta mana jaje, naga ma ta kara narka wani uban kiba matar, kuma kwanan ta uku a garin nan yau, Shi kansa Umar da ya dawo shekaranjiya yayi sintirin zuwa asibitin ya fi a kirga kuma duk ana barin sa ya shiga, to sai mu ne za a raina ma wayo ace baza mu je asibiti ba? Ko dai wari muke ne?" Hajja dai ta tabe baki don ita ma hakan sam bai mata ba, to meye amfanin zuwan su Abujan kenan har yau basu ga marasu lafiyan ba, Mama Ladi tace "Ko ya zata cin abinci ya kawo mu Habujan, ni wallahi ban da yanda Hajja ta kirani tana kuka, da nayi ma kaina alkawarin ko gwal ake rabawa gidan Mamuda bazan sake tako kafata ba, don ba shi da mutunci mutumin, amma wannan ya zama dole ne kawai babu yanda na iya, don haka kin ga tafiyata asibitin idan kuwa ba haka ba idan zuciya ta debeni wallahi sai in dau jakata in koma karaye, iyaka duk wanda ya mutu in bugo waya ince Allah ya ji kansa ya gafarta masa" Tana kai wa nan ta fice daga parlon tana sakale da wani jaka a hammata, Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Ae gaskiya ne Mariya, mu muna nan sai dai ayi ta ce mana jiki da sauki an ki barinmu muje mu duba su, a ina aka taba haka?" Aunty Mariya dai bata ce komai ba ta ci gaba da girkinta a ranta kuwa tasan Abba gudun su bar abun fade a asibitin yake ne, barin ma Mama Ladi... Mayraah na kwance bayan an maida ta ward jiya, sai da tayi kwana biyar da Ventilator Machine kafin aka cire, kuma duk da haka wani lokacin sai taji numfashin ta na mata gardama, gaba daya ta rame sosai, sai haske da ta kara ba kadan ba, har a sannan she is having difficulty in saying anything sai dai tayi ta bin mutane da ido, kana ganinta kasan tana jin jiki, Ammi na zaune gefenta tana rike da hannunta trying to comfort her kamar yanda take yi tun da suka fito ICU, wani lokacin kuma Usman ne ke zama by her side, Maheer dai sai dai ya tsaya jikin window yana kallonta, yana jin kamar ya maida pains dinta gaba daya jikinsa ta samu relieve, ganin tana son mikewa zaune Ammi ta zaunar da ita tana mata sannu cike da damuwa, da kyar Mayraah ta bude baki a karo na farko tun da suka fito ICU tana kokarin yi ma Ammi magana, Ammi ta kasa kunne don jin abinda take cewa, Maheer ya karaso kusa da su, Ammi ta kallesa bayan ta fahimci abinda Mayraah ke cewa, dukawa yayi yace "What did she want Ammi?" Kasa cewa komai Ammi tayi, ta kara kallon Mayraah dake sauke numfashi a hankali, Maheer yace "Pls me tace Ammi?" Ammi dai tayi shiru.
[8/19, 10:00 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer ya karasa kusa da su ya duka yana kallon Mayraah ya kwantar da murya yace "Me kike so Mimi?" Shiru Mayraah tayi tana kallonsa tana sauke numfashi a hankali, Mikewa Ammi tayi ta bar wajen ta koma jikin window ta tsaya tana kallonsu, gaba daya damuwa yasa ita ma duk ta rame ba kadan ba don ko abincin kirki bata iya ci ganin halin da Mayraah take ciki, jin Mayraah tayi shiru Maheer ya rike hannunta yace "Talk to me Mimi, what is it? Me kike so?" Hawaye na sauka idonta cikin rawan murya tace "Yaya i just.... want to ask Musharraf for forgiveness, kilan mutuwa zan yi wallahi..." sai da Maheer ya sa kunne sosai sannan yaji abinda take cewa, ya dinga kallonta ya ma kasa cewa komai, da damuwa ya girgiza kai yace "No Mimi, baza ki mutu ba, ki daina kira ma kanki mutuwa pls, you will heal completely nan ba da dadewa ba in sha Allah, i know u are strong" Ta daura kanta a shoulder dinsa tana kuka a hankali tace "I am always finding it difficult to breathe, I can't do anything my self, my body is getting weaker everyday, bana iya tsayawa da kaina.... ina jin kamar mutuwa zan yi, ina son kowa ya yafe min..." Nan da nan hawaye ya cika idon Ammi tana kallonsu daga inda take tsaye, Maheer dai ya kasa cewa komai yana rungume da ita maganganunta na yawo a kansa, bata san he is just acting strong because of her ba, don a yanda yake ji kullum da yanzu an kwantar da shi shima amma bai bari abinda yake ji yayi weighing dinsa down ba cause he wants to be by her side always, kuka kawai Mayraah take tana jin kirjinta ya mata nauyi, shi kam he was trying all possible means to control him self yana patting bayanta a hankali, after many seconds da kyar ya dake yace "Za ki samu sauki Mimi, in sha Allah..." Ta girgiza kai da kyar tace "Amma ina son in masa magana pls Yaya, even Hamidah" Maheer bai sake cewa komai ba, ya kasa ci gaba da sauraronta yayi karfin halin kwantar da ita ya mike ya fita daga ward din, Ammi dai sai kallon Mayraah take ta kasa karasawa kusa da ita, ji take ina ma zata iya dauke duk wani ciwo da take ji a jikinta, hawaye ya kasa tsaya mata, tasan duk za su cinye wannan jarabawar ma kamar yanda suka cinye na baya, Bude kofar ward din aka yi MD ya shigo da sallama, ya kalli Ammi dake share idonta, ya kalli Mayraah dake kuka ita ma saman gadon, yayi kasa da murya yana kallon Ammi yace "Ma'am za mu ɗan yi magana a waje" Ba musu Ammi ta bi sa tana share hawayen da yaki daina zuba idonta, suna fita waje MD na kallonta da damuwa yace "Kukan nan da kike a ko da yaushe isn't helping her, you need to be strong, she will recover fully in sha Allah nan ba da dadewa ba" Ammi ta fashe da kuka tace "Dr dole inyi kuka, ko da yaushe sai tayi ta ce mana zata mutu, ta yaya hankalina zai kwanta, wallahi she is all i got, ita kadae ce macen da Allah ya bani" Tana kai wa nan ta kara fashewa da kuka sosai, MD ya jingina jikin bango yana kallonta bai iya yace komai ba, bayan few seconds a hankali yace "Bazata mutu ba in sha Allah, she will heal completely, i know it's not going to be easy, she is experiencing all this because she stayed too long in ICU, gradually jikinta zai dawo dai dai in sha Allah.... Abinda ya kamata yanzu idan akwai ko aunt dinta sai ta dawo nan ke ki koma gida, you need rest too, kema ba lafiya gare ki ba" Da sauri Ammi tace "Aa zan iya, i will be with my daughter" MD ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Toh shikenan, let me speak with her now...." A hankali Ammi tace "Toh" Kujeran dake corridor din ta tafi ta zauna tayi tagumi, shi kuma ya shiga ward din ya kulle kofar, karasawa yayi gaban gadon yana kallonta, ta sauke idonta daga kallonsa tana sauke numfashi a hankali, ya dafa gadon cikin kwantar da murya yace "Akwai inda yake maki ciwo ne bayan chest dinki da kuma weakness da kike ji?" Girgiza kai tayi ba tare da ta kallesa ba, yayi kasa da murya yace "To ina za ki mutu ki je?" Sai a sannan ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, Ya sauke idonsa yace "Yea, mutum baya mutuwa sai lokacinsa yayi, tun da baki mutu a ICU ba, a nan ma in sha Allah baza ki mutu ba, you won't die until ur creator is pleased with your soul, you are going no where in sha Allah, think about ur parent, brothers, relatives, friends, And...." Shiru yayi, ita dai kallonsa take, ya mike a hankali yace "And ur new pesky...." ita dai share hawayen dake makale idonta kawai take, yayi kasa da murya yace "You will get married, make babies... And fulfill all ur beautiful dreams in sha Allah" Ta daga kai ta kallesa, sunkuyar da kai yayi ya juya ya fita daga ward din, Ammi na ganin ya fito ta mike, ya karasa kusa da ita yace "Pls Ma'am ki rage kukan da kike a gabanta, always say encouraging words to her, it will really help" a hankali Ammi tace "Toh Doctor Nagode" Ya ɗan yi murmushi ya juya ya bar wajen, Ammi ta shiga ward din. Da yammacin ranan wajen karfe biyar Mayraah na zaune Usman dake gefenta yana bata shayin dake cikin cup din hannunsa, Ammi na zaune kan kujera tana azkar dinta, Umar da Mama Ladi suka shigo ward din, Mama Ladi ta cire gyalenta ta jefar kan kujera ta karasa kusa da Mayraah da sauri tana kallonta tace "Sannu Mera, wallahi yau satina daya a garin nan an ki bari in zo in duba halin da kike ciki yanzun ma zagawa nayi na biyo Umar babu wanda ya sani" Tana kai wa nan ta fashe da kuka ta rike kai tace "Allah ya isa tsakaninmu da Sanisa, Allah ya saka mana cikin gaggawa, Allah yayi mata abinda tayi mana, kuma naji dadi da Mashir yayi dubaran mikata hannun hukuma bakinsa alekum, da wa'e ne kilan kasheta da duka zai yi kinga sai laifin ya koma kansa dumu-dumu" Ita dai Mayraah bata dago kanta ba don hayaniyar Mama Ladi har cikin brain dinta take jin sa, yanzu gaba daya bata son hayaniya ko wani iri ne nan da nan sai kanta ya fara mata matsanancin ciwo ta fara ganin jiri, Ammi ta mike tana son ce mata ta rage murya amma ta rasa ta yanda zata fara gaya mata hakan, Umar dai tun da suka shigo da ita ya tafi far end of the