Showing 288001 words to 291000 words out of 456519 words
will be a forever trauma.... da bazan ma fara rabata da er ta ba, ina ta zaton bayan yan watanni zata dawo dai dai amma abun sai gaba yake, sallah da bata wasa da shi tun shiganta boarding school ta dawo bata yi ma kwata kwata and i was a bit happy with just that because i was against her practicing Islam Hajiya Amina ce ta ce in rabu da ita tayi addinin da take so, ranan farkon da naga tayi sallah bayan ta dawo wani hutu da suka yi i was so angry at her for trying to practice islam ashe makarantar ma a musulma suka san ta she was bearing Maryam Ibrahim that was our fathers name, duk da ni da sunanta na Christain nayi registering dinta, sai nake ga kamar kawaye ne suka ja ra'ayinta na yin addinin musulunci whereas ba haka bane don kanta ta zabi addinin, ta bi religion din mahaifinmu ne don sanda yake da rai she was his favourite, bayan yan watanni nayi jamb na shiga jami'a still with Amina's assistant, all this while kuma muna zaune gidan bawan Allahn nan Alhaji Ayuba, gradually kanwata ta zama mara cikakken lafiya don in zan fita makaranta ma kulleta nake a daki in na dawo in bude" Ceo ta goge idonta cikin sanyin murya tace "Hajiya Amina is the reason i am where i am today, sai dai Allah yayi mata rasuwa yau shekara bakwai kenan kuma bata taɓa haihuwan rayayyu 'ya ya ba, ranan da na fara ganin Mary Ann, kawai gani nayi tana min kama da wannan Hajiya Aminar, amma ni dai nasan Hajiya Amina bata taɓa haihuwa ba ta dai yi adopting yara uku a orphanage kuma duk tayi sponsoring dinsu kamar yanda nima ta min tun ma bata san zata auri me kudi danginsa su sa ta gaba ba, wanda bakin cikinsu ne ma ya kasheta, da farko saboda yanayin da take min da Hajiya Amina yasa naji ta shigar min rai, ina kuma sonta har cikin zuciyata, sau tari sai in shigo asibiti duk don in ganta, i usually have a feeling that i cannot even explain akan Mary Ann, even after i left for UK tana rai na, rana daddaya ne idan muka yi magana da Aliyu bazan tambayesa ita ba, she wasn't suppose to go for that UK conference but saboda kawai ina son ganinta na sa a taho da ita, sannan babu staff da ya taɓa sauka gidana amma ita na sauketa gidana, zamanta gidana na just 2 days din nan ne nayi noticing wasu abubuwan da suka girgiza ni game da ita, first nayi noticing yanda take kwanciya bacci just exactly like my sister Aaria, kafin nan ma i notice how she behaves when sick, don da suka sauka bata jin dadi har cikin dare, and all through the night ina shigowa dubata, in the morning i noticed the way she eats, muna dining din still sai na lura da irin kallon da ta ma Aliyu sak na kanwata, i was tensed and confused at the same time, bayan ta gama cin abincin ta bar dinning area, her walking steps took my attention.... Haka nan dai na kawar da komai a raina na ci gaba da harkokin gabana su kuma suka koma Nigeria tare da Aliyu, sun koma da kwana hudu aka yi poisoning dinta, ban yi tunanin hankalina zai yi irin tashin da yayi ba bayan Aliyu ya kirani ya sanar min abinda ya faru, and immediately nayi communicating da wasu Dr which were my colleagues muka taho Nigeria babu bata lokaci tare da su, bayan ta fara farfadowa ne na debi jininta da gashin kanta just to clear my unnecessary doubt that i my self don't understand, ban ma san menene damuwata game da ita in particular ba, ni dai har cikin raina ban taɓa tunanin ita din yarinyar kanwata ce da nayi deserting ba, amma na kasa samun sukuni a kanta, na rasa inda matsalar take, result din DNA test da na bada ayi na fitowa kuma i got the shock of my life, still na sake kawo Aliyu gidan nan ya debi jinin kanwata da kansa muka koma hospital ya debi na Mary Ann, and behold the result was still the same....." Shiru Ceo tayi tana share idonta tana kallonsu, su Abba dai kallonta kawai suke su ma, kuma babu wanda ya iya cewa komai, Maheer dai sai kallon Mayraah da ta rufe fuskarta jikin Ammi yake, he was soo heartbroken, he wish ba da ita aka zo gidan ba, Bayan some minutes Ceo ta mike da kyar tace "Aaria is upstairs, za ku iya bi na yanzu mu je wajenta, wani lokacin tana magana sama sama, though ni kadai ma take yi ma maganar, wani lokacin kuma sai dai ta bi ka da ido kawai, babu kasar da ban fita da ita ba don nema mata lafiya but all my effort prove abortive, babu wani improvement, kuma a haka yanda take har sallah tana yi, masu kula da ita da na dauka ma duk musulmai ne...." Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ya mike, sauran ma duk suka mike tsaye, Ammi ta dago Mayraah a hankali tana kallonta, hawaye ta gani kwance fuskarta, Ammi ta goge mata hawayen murya can kasa tace "Kar ki sake kuka daughter" Mayraah ta gyada mata kai, duk kallonsu ake a parlon, Ammi ta dagota suka mike, Ceo na gaba suka bi ta har sama zuwa inda Aaria take, bude kofar dakin tayi ta shiga, Mayraah dai na makale jikin Ammi ta ma ki kallon kalan dakin, Nurse din dake zaune tare da Aaria tana nuna mata hotunan flowers masu kyau a Tablet din hannunta ta mike tsaye daga gefen gadon ganin su, Ceo tayi murmushin karfin hali tace "You can leave Farida" Nurse din tace "Alright Ma" Daga haka ta fita daga dakin, Aaria dai sai bin dukkansu take da kallo kamar bata saba ganin mutane da ɗan yawa ba, Ceo ta karasa ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta tace "Do not be afraid my love, you know what i bring to you today?" Aaria ta girgiza mata kai, Mayraah dai har sannan taki kallon matar dake dakin sai makalewa jikin Ammi take, Cikin sanyin murya Ceo tace "I brought to you ur baby gal, kin tuna dama na taɓa ce maki na kai maki ita ajiya ne?" Aaria dai sai kallonta take, Ceo na kokarin danne kukan da ke taho mata tace "To yau naje na amso maki ita, ur 22 year old baby girl that u named after you.... remembered you try telling me that her birthday is in few weeks time? You remembered? To yau naje na amso ta tare da bayin Allahn da suka rike maki ita har ta girma" Aaria dai bata ce komai ba kamar tana kokarin processing maganganun yayar tata, Ceo ta mike ta juya tana kallon su Ammi babu ko kiftawa, karasawa tayi kusa da Ammi tana tafiya a hankali tana share idonta kafin tace komai Ammi ta janye Mayraah daga jikinta a hankali, cikin sanyin murya tana kallonta tace "Go to her daughter...." Mayraah ta gyada ma Ammi kai, trying hard not to cry, sai kuma ta kalli Ceo wasu sabbin hawayen da take ta avoiding na taruwa idonta, Ceo ta sauke idonta ta kama hannunta ta nufi kusa da gadon da ita, sai da suka isa gadon Mayraah ta iya kallon matar dake zaune tana kallonta ko kiftawa babu, Ceo tace "Aaria this is ur baby gal, this is ur Maryam" Zaunawa Mayraah tayi kusa da ita tana kallonta, bata san sanda ta fashe da kuka ba a hankali ta daura forehead dinta saman shoulders dinta hawaye na sauka idonta, Aaria ta dinga kallon ceo dake hawayen ita ma, gently Aaria ta dago kan Mayraah tana kallonta, rungumeta Mayraah tayi sai a sannan ita ma ta rungumeta gam tana kallon yayarta, as if counting her words tace "Maryam dita ce?" Ceo ta gyada mata kai tana murmushin karfin hali tace "Maryam din ki ce" Kuka ta fashe da tana kara rungume Mayraah jikinta, Ammi ta sunkuyar da kanta tana share hawayen dake sauka idonta ta juya ta fita daga dakin Abba ya bi ta da kallo, bin bayanta Usman yayi, Maheer dai ya jingina jikin bangon dakin, cikin kuka Aaria dake kallon yayarta tace "Don Allah kar ki sake rabani da ita Aunty, na ce maki ina sonta a haka, wallahi ina son ta" Ceo ta zauna kusa da su tana girgiza kai tace "Bazan sake rabaki da ita ba Aaria, amma su ma wanda suka rike maki ita ai iyayenta ne, kin ga su ma baza ki rabasu da ita ba" Aaria dai kuka kawai take tana rungume da Mayraah tana kallon yayar tata, juyawa Abba yayi ya fita daga dakin MD ya bi bayansa, Maheer kam kukan da yake jin Mayraah take ne ya sa ya kasa fita daga dakin, after a while dai kawai ya juya ya fita. Abba suna zaune parlor yana kokarin calming Ammi dake kuka duk da bai ma san takamaiman kukan abinda take, Usman da ya zauna gefenta dai kansa na kasa, Maheer na zaune tare da MD ko wannensu da tunanin dake ransa, after a While sai ga Ceo ta sauko downstairs tana rike da hannun kanwarta sai Mayraah dake tare da su, Mayraah na shigowa parlon ta nufi Ammi tana tafiya a hankali, ta zauna daya side dinta ta jinginar da kanta jikinta ta lumshe ido, Ammi ta ja ta jikinta, Ceo ta sa kanwarta ta zauna two sitter sannan ta zauna gefenta, gaba daya idanuwan Aaria da hankalinta na kan Mayraah, Ceo na kallon Aaria tace "Say hi to them, su ne iyayenta da suka rike maki ita" Aaria ta dinga bin su da kallo wasu hawayen na taruwa idonta, sai kuma ta kalli yayarta cikin rawan murya tace "Yanzun ma tafiya za su yi da ita? Amma kin ce min watarana za ki dawo min da ita gaba daya" Ceo ta kasa cewa komai, kuka sosai Aaria take tana bin su da kallo gaba daya a parlon, Ceo ta goge hawayen idonta cikin sanyin murya tace "Appreciate them Aaria, they look after ur Maryam for 22 years now, in ma sun tafi da ita ai tun da har suka kawo maki ita nasan zata dinga zuwa ganinki, kema zaki dinga zuwa ganinta ko da yaushe, kin san karatu take yanzu..." Aaria dai sai hawaye take tana kallon Mayraah da taki bude ido a jikin Ammi, Calmly Abba na kallon Ceo yace "Sai dai baki karasa mana labarin ba...." Ceo tayi murmushin karfin hali tace "Mary Ann's father ko?" Abba ya sauke ajiyar zuciya don abinda yake son ji kenan, gaba daya su Maheer kallonta suke, Ammi ma kallonta take, A hankali tace "I will prefer in dauke ku gaba daya mu je har gidansu a garin da yake, kuma har da Aaria za mu je..." Abba yace "Me yasa kika ce haka?" Ceo tace "Hakan zai fi Alhaji, zan yi booking flight for us gaba daya, gobe da safe za mu je har gidansu, i don't want to call his name" Abba ya sauke ajiyar zuciya thinking if hakan dai dai ne, Bayan few seconds yace "Amma kina tunanin hakan bazai haifar da wata matsalar ba? Do u think it's necessary sai mun je har gidansu" Girgiza kai tayi tace "Not at all, ai har bibiyata yake a Uk, he wants me to connect him to Aaria ban kuma san dalilinsa ba, sai da na kira masa police wani lokaci suka ja masa boundary da ni sannan ya hakura ya daina bi na, don can kawai muke haduwa, tun bayan Incident din bamu kara haduwa da shi ko family dinsa a nan Nigeria ba" Abba yace "To shikenan, Allah ya kai mu goben" Aaria dai sai kallon Mayraah take bata ko kiftawa, Ceo ta kamo hannunta a hankali tace "Za su tafi da Maryam don za ta je makaranta yau, amma na maki alkawari zaki kara ganinta gobe" Aaria ta fashe da kuka a hankali tace "But that wasn't what u promise Aunty" Ceo na shafa girarta murya can kasa tace "I know my love, for now allow her to go to school, za ku kara haduwa gobe"
Har suka Isa gida babu wanda ya iya cewa komai a motar, Mayraah dai na rungume jikin Ammi, bayan Abba yayi parking Ammi ta bude motar ta sauka tare da Mayraah suka nufi cikin gida, Daga Usman har Maheer dai na cikin motar basu sauka ba kowa da tunanin dake yawo a zuciyarsa, Calmly Abba yace "Ina son duk abinda muka ji yau ya zamana sirri a tsakaninmu duka, duk da nasan halin ku, nasan abinda za ku aikata da wanda baza ku aikata ba, da Umar na nan nasan shi ma bazai taɓa fitar da maganar nan ba har a tashi duniya, amma duk da haka tunda baya nan ko shi bana so ya ji, ita ma mahaifiyar ku zan mata magana idan mun shiga ciki" Ammi na komawa bangarenta ta nufi Bedroom dinta direct tare da Mayraah ta kulle dakin ta zaunar da ita gefen gado ita ma ta zauna tana kallonta a sanyaye, Mayraah ta sauke idonta hawaye masu zafi na zubo mata, Ammi ta share mata idon muryarta na rawa tace "Bana son kina kukan nan daughter, this is our destiny altogether, don ba jarabawanki bace ke kadai, har mu, kuma dole mu amshesa hannu bibbiyu" Mayraah ta dake tace "Kawai kukan farin ciki nake Ammi, na kuma amshi kaddarata hannu biyu don being a muslim is one of the greatest thing that have ever happen to me in my life regardless of ta yanda aka sameni, ni nasan bazan taɓa iya canza kaddarar yanda Allah yayi zan zo duniya ba, who am i ti change that? it's already written, kuma ina farin cikin da Allah ya kaddara min rayuwa tare da ku har na zama cikakkiyar musulma, ina alfaharin kasantuwar ku iyayena da bazan taɓa replacing ba no matter what, Alhamdulillah ala kulli haal.... Alhamdulillah ala ni'imatil Islam.... Don da ace na tashi tare da warce ta haifeni duk da ance tana musulunci probability dina na zama musulma will be very low don yayarta zata iya fin karfinta a kai na, ko wannan kadai na tuna zan ci gaba da godiya ga Allah, and now i will have rest of mind nasan wacece ni...." Rungumeta Ammi tayi tana kuka tace "That is just it daughter, Allah Ubangiji ya maki albarka, and i am proud of ur faith, In sha Allahu daga yau kin daina kuka" murmushi Mayraah tayi tana rungume jikin Ammi. Bayan azahar Mayraah na zaune kan darduma a dakinta Usman ya shigo da sallama, ta daga kai tana kallonsa bayan ta amsa, kasa kallonta yayi ya karaso cikin dakin ya zauna, ita dai kallonsa kawai take, bayan few seconds ya sauko kusa da ita ya zauna saman carpet din a hankali ya kamo hannunta murya can kasa yace "You know what Mimi?" Tace "Sai ka fada yaya" Ɗan murmushi yayi jin reply dinta, a hankali yace "I want you to know that no matter the situation, no matter the circumstances you still remain our little Mimi, we still sees you as our blood" murmushi kawai take tana kallonsa, Bude kofar dakin aka yi duk suka juya, Maheer ne ya shigo dakin da sallama, yana ganinsu ya wara ido yace "Really?? What are my siblings up to?" Yana fadin haka ya karaso kusa da su shi ma ya zauna ya tankwashe kafa yana kallonsu both yace "Me ake yi babu ni?" Usman na kallonsa yace "I am just reminding her that we still sees her as our little cute sis, we still sees her as our blood... And all in all, we still love her as our lovely intelligent Mimi" Maheer ya daura hannunsa kan nasu yana murmushi yace "Ayi reminder din da ni" Er dariya Mayraah tayi cikin sanyin murya tace "And i see u both as my shield! today, tomorrow, next tomorrow, and forever.... I am proud to have u both and Ya Umar as my big brothers, ina alfahari da ku yayyina a ko da yaushe" Duk murmushi suke suna kallonta, ita ma tayi murmushin tayi pecking din hannunsu gaba daya. Sosai Ammi tayi mamakin yanda Mayraah ke ta harkan gabanta throughout ranan a gidan kamar babu abinda ya faru, hakan ya sa hankalin Ammi ya kwanta, sai dai fa can kasan zuciyar Mayraah tana jin tausayin mahaifiyarta amma ba wai don tana son kasancewa tare da ita ba. A ranan da daddare MD ya tura ma Maheer Flight ticket na Business class da Ceo ta sa yayi har kujeru takwas na tafiyar da za su yi washegari, flight din kuma na karfe taran safe ne, Mayraah na tare da Maheer da Usman a dakinsa tana basa labarin yanda ta ji a sanda ta ci poison, Usman dai danna wayarsa kawai yake yana sauraronta, Maheer dake kallonta attentively ya dau wayarsa jin shigowar message, ganin wanda ya turo masa message din ya shiga WhatsApp dinsa, Mayraah ta hade rai tace "Yaya kai ma danna wayar zaka yi baza ka saurareni ba" Dariya ta ba Maheer bayan yaga ticket MD ya turo masa ya mayar da wayar ya ajiye gefe yanw murmushi, Usman ya daga kai yana kallonta yace "Wa yace maki bana jin abinda kike cewa" Ta turo baki tace "Toh gaya min me na fada last in ji" Yace "Oho"
Abba ya gama shan shayin cup din hannunsa ya kalli Ammi, sai kuma ya ɗan yi murmushi yana girgiza kai yace "Sai kuma nace maki zan je in gaya ma Hajiya Amina wannan magana" A takaice Ammi tace "I don't know, and I don't even care to know, kawai ni dai nace maka in ma kana da niyya kayi hakuri kar ka fara, don wannan babban sirrin daughter na ne da ma mu kan mu gaba daya, bana kuma son zancen nan yaje ko