Showing 408001 words to 411000 words out of 456519 words
sauri tace "Ba Haseenah bace wannan?" Usman dai was speechless yana kallon Ammi da ita ma ta bude baki, Aunty Mariya ta amshi wayar hannun Ammi tana kallon screen din tace "Me ya faru" Lkci daya Aunty Mariya ta ajiye wayar tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta maida kwanon abincinta gefe ta tashi da sauri ta nufesu tace "Wani lafin ta kuma tafkawa?" Bata jira a bata amsa ba ta dau wayar tayi mici mici da ido tana kallo.
[10/19, 8:19 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Gaba daya kowa na parlon yayi shiru ko wanne da tunanin da yake a ransa, Mama Ladi dai shinkafar gabanta take ci tana korawa da lemon fanta me sanyi, Ammi ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Maheer tace "Amma tun yaushe aka kira ka Maheer?" Maheer dake zaune parlon ya daga kai yana kallon Ammi, a hankali yace "Tun kafin magrib, but before then anyi ta kirana da rana i wasn't responding, da naga kiran yayi yawa ne na daga dazu da na fita" Mayraah dai kallon Maheer kawai take, he look so stressed and tired, Ammi tace "To su a ina suka samu Number ka?" Mama Ladi ta dago kai da sauri tace "Wallahi abinda ya fi ƙona min rai kenan, duk lambobin danginta a rasa wanda za a kira sai nasa, meye gamin sa da ita da za a kirasa in ba neman magana ba?" Maheer yace "Tun wajen karfe sha daya na safe tayi accident din, ba a samu wayarta a scene din accident din ba shi yasa har aka dorata yanan gizo ana neman yan uwanta dazu wajen karfe shidda, ina jin daga baya ne ta farfoda sai ta bada lambata...." Mama Ladi tace "Kaji er iska, toh me zaka mata da ta bada lambarka? Ai tunda aka dorata a yanar gizo har mu nan mun gani to danginta ma duk sun gani wllh, don haka kar shegen da ya sake kiranka a bar mu muyi zaman makokin mu a nutse cikin kwanciyar hankali, har yanzu babu ɗan iskan da ya kira mu daga pamilynta yayi mana gaisuwa ko ta'aziyya ba, ko basu san ta kashe yaran bane ohon masu" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya kyauta, amma da ka kira ko mahaifiyarta don ba lallai sun kai ga gani a social media din ba tunda ba a dade da dorawa ba...." Mama Ladi ta daga kai tana kallon Ammi tace "Yau ni nake ganin jaraba, to ko dai shiryawa za kiyi ki je Zari'an nan ne naga duk kin bi kin damu? haba duk kin bi kin ishe yaro da tambaya a kunnensa baza ki bar sa yaji da mutuwar yaransa har biyu ba, meye hadinsa da Hasinu kuma yanzu da har za a damu don tayi hatsari a hanyar Zari'a, wa gareta a Zaria da ta kama hanyar can din ayi magana ta domin Allah, banda ma dai ma'aikatan asibitin en sharri ne akan wani dalili za su kira Mashir? Meye hadin Maheer da ita yanzu? Dama can wannan yaran ne kuma Allah ya kashesu ba shikenan ba, kilan ma wani mugun abun ta je zata yi a Zari'a Allah ya nuna mata iyakarta, Al-qur'an ban gane ta ba da farko da Usuman ya mika min wayar, kai kace daga bakin ƙura aka kwato ta, da kyar in bata rasa ido daya ba a yanda na ga hoton nan, Usuman da yaga abun bai shafesa ba ai kinga yayi wucewarsa bayan ya nuna mana ita a hoto ya tafi ya ci gaba da harkokin gabansa, ni ma dai wllh bai shafeni ba haka Mashir da Mera, ban dai san ko ke da Mariya ya shafeku ba irin wannan sanyi da jikin ku yayi sai ku shirya ku tafi Zari'a" Ammi ta dau wayarta ta hau kiran Mahaifiyar Haseenah, mikewa Maheer yayi ya ajiye ma Mayraah ledan maganin da ya siyo mata, ita dai kallonsa kawai take har ya fita daga parlon, Mama Ladi tace "Atoh dai ya fi maka gwara kaje kayi abinda zai fissheka, tunda uwar taka ita ta kawo tausayi duniya ba sai ta tashi ta tafi asibitin da aka kwantar da Hasinun ba, mu dai Allah ya isa yan biyun mu da tayi mana sanadin mutuwarsu, gashi tun a duniya ta fara ganin karshenta, Shari'ar mu da ita kuwa sai mun hadu a lahira" Aunty Mariya dai ta ma rasa abun cewa a parlon, sosai jikinta yayi sanyi ganin critical situation din da Haseenah take a hoto, abun ba kyan gani, after a while Mayraah ta mike ganin Mama Ladi ta gama cinye abincin gabanta ta tafi ta dau plate din, Mama Ladi tace "Atoh dai, maza fita ki je kiji da mijinki kiyi ta kwantar masa da hankali kina basa baki Allahn da ya basa su shi zai kara basa wasu nan ba da dadewa ba in sha Allah" Mayraah ta kasa daga kanta, tun da Maheer ya fita take son ta bi sa amma ta kasa tashi a parlon sai yanzu da ta samu opportunity sai gashi Mama Ladi ta mata handsfree, tana rike da plate din ta fita daga parlon, bayan ta kai plate din kitchen ta nufi dakin Maheer, zaune ta samesa a dakin yana deleting pictures din su Aryaan da Aymaan wanda Aunty Mariya ta turo masa few days back a wayarsa, daga kai yayi yana kallonta, ta sunkuyar da kai har ta isa kusa da shi har a lkcn idonsa na kanta yace "Have you eaten dear?" Mayraah ta duka gabansa a hankali tace "What should i make for you?" Yace "I just took tea now" Ta daga kai tana kallonsa, murmushi ya sakar mata ya dagota ta zauna gefensa yayi kasa da murya yace "Ko mu tafi gida, naji ma jikinki da zafi, ina maganin da na siyo maki" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Talk to me baby gal" Ta daga kai tana kallonsa yace "Kin sha maganin?" Ta girgiza masa kai, yace "Yana parlorn Ammi har yanzu? Let me get it for you" Saketa yayi ya mike ta bi sa da kallo har ya fita, ta goge hawayen da ya cika idonta, tun safe har zuwa yanzu bata samu sukuni a ranta ba, gani take kamar ta bada nata contribution din wajen rasuwan yaran, sosai ta shiga damuwa wanda ko abinci ta kasa ci, ta rufe fuskarta da pillow hawaye na sauka idonta, she wish zata iya maida hannun agogo baya da bata yi abinda tayi ba, a haka Maheer ya dawo dakin ya sameta, ya ajiye ledan maganin hannunsa da ruwan goran da ya dauko, ya zauna gefenta ya dago ta yace "Mimi" Ta daga kai hawaye na sauka idonta, rungumeta yayi a hankali yace "Kina son ki gan ni cikin damuwa ne Mimi? Bana son wannan kukan da kike yi, erase every thinking that is making you to cry off ur mind, i believe and have faith that hakan da ya faru shine mafi Alkhairi garemu baki daya, so plss let move on, su kuma Allah ya sa masu ceto ne" Ita dai tayi shiru tana jin duk abinda yake fada, dago kanta yayi yace "Me za ki ci let me get it for you?" Ta girgiza masa kai a hankali tace "I am not hungry" Yace "No dear, you are" Ta girgiza masa kai tace "Da gaske, i am okay" Shiru yayi yana kallonta can ya cire mata hijab dinta yace "To kiyi wanka sai ki sha maganin ki kwanta" Ita dai bata ce komai ba, yace "Let me get u your sleeping dress a dakin ki" Daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, ba a wani dau lokaci ba ya dawo dakin, har a sannan tana zaune yanda ya bar ta, ya ajiye rigar baccin gefen gado ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi kasa da murya yace "Ko mu yi tare Baby?" Ta daga manyan idanuwanta tana kallonsa, ɗan murmushi tayi ta rufe fuskarta a chest dinsa ta lumshe idonta, duk sakewar da tayi da shi this pass month bata yarda su yi wanka tare ba saboda kunya, zata iya komai da daddare cikin duhu amma da zaran da haske to bata iya yin komai sbda kunya, but if that will please him today zata cire duk kunyarta ta yarda da request dinsa, ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace "Kin yi shiru Baby" kai ta gyada masa ba tare da ta bude idonta ba, tana ji ya fara taking off every single cloth that is on her, ita ko tayi nisa tunanin da take na yanda suka taso gida daya seeing their selves as siblings from the same parent, those beautiful memories of them as siblings keep on coming to her mind and how things later turn out, and now the Maheer she sees as her favorite elder brother, the Maheer she cherish soo much as an understanding and lovely elder brother is now a husband to her, they made love... katse tunanin tayi da sauri daga ranta tana girgiza kai a hankali, who could have ever imagine this between the two of them, bata ankara ba kawai sai jin bakinsa tayi a neck dinta ta bude ido da sauri tana kallonsa, shi ma kallonta yake da lumsassun idanuwansa ya dagata heading straight to the large bathroom with her.... Ba su suka fito daga bathroom din ba sai after an hour, ko kayan baccin bata sa ba bacci ya dauketa sai shi ne ya sa mata kayan baccin covering her with duvet, wajen karfe dayan dare taji yana tashinta, ta bude ido da kyar tana kallonsa, kunna wutan dakin yayi mara haske yayi kasa da murya yace "I am hungry wife" Mikewa zaune tayi tace "Toh me zaka ci?" Yace "Ba akwai abinci da aka dafa ba a gidan" Ta sauka daga kan gadon ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita daga dakin ta nufi kitchen, ganin da akwai abincin tayi microwaving din masa, ita kanta sai da ya tasheta taji tana jin yuwan don tun safe ta kasa cin abincin kirki, ta daura ruwan da zata hada masa shayi, bayan ta gama ta tafi masu daki da abincin da tea. Washegari da safe wajen karfe tara da rabi bayan Mayraah tayi wanka ta fita daga dakin Maheer ta tafi sama dakinta ta shirya sannan ta nufi bangaren Ammi tana tafiya a hankali, kunya ma take ji ace sai yanzu zata je gaishesu, kuma duk shi yasa suka makara, tana shiga parlon ta zauna kan carpet ta gaishesu, Ammi da Aunty Mariya suka amsa, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ke kuma daga fita da plate din da na ci abinci kitchen shiru bamu sake jin duriyarki ba, ni na zata ma tafiyar ku kuka yi gida kuka bar mu da zaman makoki" Mayraah dai bata ce komai ba, bude kofar parlon aka yi Maheer ya shigo da sallama, Ita dai Mayraah bata dago kanta ba ya zauna kan carpet ya gaishesu, tunda yake bai taɓa kai wa har wannan lokacin in dai yana gida bai shigo gaida Ammi ba, infact da asuba ma yake shigowa gaisheta idan ya dawo masallaci, Mama Ladi tace "Kai dai in gaya maka Mashir Ammi dai tayi waya da mahaifiyar Hasinu, ashe iyayen basu ma san ta kamo hanyar Habuja ba tun daga kano, karya ta lafta ma kanwar uwar cewar zata gidansu tayi kwana biyu don gidan kanwar uwar ta dawo da zama da yan biyun, kaga ai ita ba yarinya bace da kanwar uwar zata hanata zuwa gida kamar yanda ta ce mata, to fa tana lafta wannan karya shine ta nufi tasha ta hau mota ta kamo hanyar Habuja da yara biye raɓe raɓe, sam iyayen basu san abinda ke faruwa ba sai ganin hotonta suka yi yana yawo a yanar gizo ana neman yan uwanta tayi mummunan hatsarin mota a hanyar Zari'a, uwar tace abun sam ba kyau, ta samu lafiyayyun karaya a duk kafafuwanta biyu, hannunta daya ma ya karye sosai, tun daga hancinta zuwa haɓarta kuwa dama sai dai a yanki wani sashi na jikinta ayi mata joni idan zai yiwu kenan, idonta daya ma ana zargin ya tsiyaye abun sai dai iyayenta su ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'una don mu kam bai shafemu ba muji da zaman makokin da ta ja mana muke yi ma, amma dai hatsarin na ya sauya mata halitta" Daga Ammi har Aunty Mariya kallon Mama Ladi suke, kai kace taga Haseenah da idonta irin wannan bayanin da take badawa in details, Mama Ladi ta gyara zama tace "Uwar na ta kuka tana Allah wadai da er da Allah ya bata, nace ba kuka zata yi ba tayi ta nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, haba jama'a da wannan wahalan da ta jajibo masu na kashe kudi ai gwara ace mutuwa tayi a hatsarin bakinta alekum, ni dai wallahi ko digon tausayinta ban ji ba a raina, karshenta ne Allah ya kawo, don Hasinu kam ba er arziki bace, kawai mata sbda kin ga yara sun shiga ran mu sai ki kashe mana su da ruwan sama duk da mutuwar tasu tafi alkhairi gare mu, kaga da bata nufi Mera da sharri ba ko Alhaji Saminu sai inyi ma magana a fitar da ita kasar waje ayi mata aiki cikin gaggawa, ban taɓa neman wani abu gun Alhaji Saminu na rasa ba, yanzu ma ba sai na tambayesa ba yake min wllh, sai dai kawai in ga ya min, gida kuwa dama har an siya...." Sai kuma tayi shiru tana gwale ido kamar warce tayi ma sarki karya, Aunty Mariya tace "Wani gidan Mama?" Sallaman da aka yi bakin kofar parlon yasa Mama Ladi ta amsa da sauri duk don ta kawar da tambayar da Aunty Mariya ke mata tace "Bismillah shigo muna nan gaba daya a zaune" Hajiya Amina ce ta shigo parlon, Mama Ladi na murmushi tace "Aa Amina ce ashe, sannu da zuwa Amina" Hajiya Amina ta karaso cikin parlon Aunty Mariya na mata sannu da zuwa, Ta zauna kan carpet ta fara gaida Mama Ladi, Mama Ladi tace "Hau kujera abun ki Amina" Hajiya Amina ta maida dubanta kan su Ammi su ma ta gaishesu, Ammi ta amsa tace "Ya hanya" Maheer ya gaida ta haka ma Mayraah, Hajiya Amina tace "Ya mu ka ji da karin hakuri?" Mama Ladi tayi karaf cikin sanyin murya tace "Hakuri ai sai ma'aiki, mu kam mun dau dangana ma, Allah ya sa hakan shine mafi Alkhairi gare mu baki daya" Hajiya Amina tace "Ameen ya Allah" Ammi tace "Ya su Ihsaan?" Hajiya Amina tace "Suna nan lafiya" Mama Ladi tace "Ya aka yi baki zo da su ba, tun da gaisuwa ce ai da sai ki taho da su mu ma za mu ji dadi" Aunty Mariya dai sai kallon Mama Ladi take, Hajiya Amina tana murmushi tace "Sun je gidan kanwar babansu ne a Katsina" Mama Ladi tace "Maa sha Allah, dama tun da na gansu kyawawa nasan marigayin ubansu bakatsine ne, Allah dai ya ji kansa yayi masa Rahama" Murmushi kawai Hajiya Amina take a hankali tace "Ameen ya Allah" Maheer ya mike ya fita daga parlon. Bayan wani lokaci Hajiya Amina ta mike tace "Bari mu je can parlon, naga da mutane" Mama Ladi tace "Ehh gaskiya can ma yafi iska, tashi mu je can kawai" Mama Ladi ta dau carbinta ta mike ta bi bayan Hajiya Amina suka fita daga parlon, Ammi na kallon Mayraah tace "Kin yi breakfast Mimi?" Mayraah ta girgiza kai sannan ta mike ta fita daga parlon, Aunty Mariya na kallon Ammi tace "Amma dai Ammi ya kamata a samu me ƙwabar Mama Ladi akan shisshige ma kakannin Mayraah da take, haba abun ai yayi yawa sam ba tsari" Ammi tace "Wa kika ga ya isa ya kwabeta Mariya? Nima abun na damu na wallahi, a ina aka taɓa yin haka? Allah ne kadai yasan irin abubuwan da take masu a can, wannan ai sai mutunci ya zube" Aunty Mariya tace "Ai ko zan kira Hajja in gaya mata tayi mata magana gaskiya, zagi dai ne na san za mu sha shi kwando kwando amma aje a haka, haba tun ana mata abu na marmari har sai ta tsire ma mutane" Ammi dai tayi tagumi bata ce komai ba, Aunty Mariya tace "Amma Ammi don Allah ki saki ranki ki tashi mu sauka downstairs mu zauna, wannan baiwar Allahn da ta zo yanzu naga alamar er siyasa ce sannan ta san kan zama da mutane, yanzu fa a rayuwar nan komai siyasa ne wallahi Ammi" Ammi tace "Siyasa ko munafurci? Ke kanki kin san ban iya munafurci ba kuma bazan fara ba da sunan siyasa, don yanzu munafurci ake dangantawa da siyasa, though ni bani da wani issue da ita right from beginning, sannan ni babu abinda ya taɓa hada ni da ita, the issue i am having is with my husband, ya kuma gano laifinsa and he promise to amend his ways that is if he can keep to that promise, amma ban taɓa ce maku ina da matsala da matarsa ba kuma bana fatan in samu matsala da ita after all a ina zan ganta ko kuma ita a ina zata gan ni in ba da kwakkwaran dalili ba kamar irin wannan wato zuwa taya farin ciki or otherwise which we don't pray for" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tace "Haka ne kam" Ammi tace "Sai kuma da yake kokarin hada ɗan sa da er ta ta karfi da yaji, that i will never approve and i told him bluntly..." Aunty Mariya tace "Allah ya sa mu dace" Ammi tace "Ameen" Throughout ranan Ammi da Aunty Mariya suna downstairs tare da Hajiya Amina warce zata kwana a gidan saboda sadakan uku da za ayi na yan biyu gobe, yanda Mama Ladi ke jan ta a jiki kai kace wajenta ta zo, hatta abinci ita ta debo mata da manyan kaji sannan ga lemo kala uku... Wajen karfe biyar na yamma Mayraah ta kawo ma Hajiya Amina