Showing 342001 words to 345000 words out of 456519 words
bari mu je ciki sai in duba maki, za ki iya sakkowa kuwa?" Taki cewa komai ta sauka daga motar hawaye na sauka idonta, yayi kasa da murya yace "Ko in dauke ki??" Banza tayi masa ta fara tafiya da kyar, ya kalli bakin gate ganin mai gadin ya fita waje bayan ya rufe gate din, kawai ya dauketa kamar er yarinya, zaro ido tayi tace "Na shiga uku, ni fa zan iya yaya, ka ajiyeni plss" Yace "Toh shikenan" Zai sauketa ta wani turo baki tace "To mu je" Dariya sosai ta basa amma bai yi ba yana dauke da ita jikinsa suka shiga cikin gidan, dakinta ya kai ta ya ajiyeta kan gado sannan ya durkusa yana duba fararen kafanta, ya daga kai a hankali yace "Bari in dauko man zafi in shafa maki" Da kyar tana harhade rai tace "Sai nayi wanka ni dai...." Yace "Toh je kiyi, let me pray isha too" Ya bi ta da kallo har ta shiga bandakin sannan ya mike a hankali ya fita daga dakin. Mayraah na fitowa daga wanka har ta gama shirin bacci bata ga ya shigo dakin ba, har sannan abinda yace ma Zeenat na makale ranta ta rasa dalili, ta karasa saka hair net dinta tana kara jan sabon rigar baccin jikinta da ya kusa knee dinta kasa, ta nufi kofa a hankali ta bude ta fita yanda bazai yi making noise ba, dakinsa ta nufa ta jingina da kofar ta kasa kunnenta don jin abinda yake, dai dai nan ya bude kofar dakin, da sauri ta koma baya kamar munafuka lkci daya ta birkice, yana kallonta daga sama har kasa, a hankali yace "Mimi..." Ta marairaice masa tana langwabar da kai tace "Yaya ciwo fa kafar yake min sosai kuma naga baka zo ka shafa min ba, kilan ma waya kake yi a ciki" Ya sauke idonsa don ko kadan bai ma fahimci abinda take cewa ba, juyawa yayi kawai ya koma dakin ta bi bayansa.
[9/19, 9:55 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah ta bi sa da kallo ganin ya shiga bandaki, juyawa tayi ta kalli wayarsa dake ajiye kan gado, ta karasa kusa da gadon ta dau wayar tana dubawa, mamaki ne ya cika ta ganin wayar da password, shi da baya sa ma waya password ko pin, ta dinga kallon wayar babu ko kiftawa, can ta zauna gefen gadon ta ajiye wayar tana jiran ya fito ta tambayesa yaushe ya fara sa password a waya bata sani ba, wanka taji yake yi a bandaki wanda hakan ya bata mamaki don ko da ya bude kofa taga alama he just took his bath, ita dai bata fita ba tana zaune tana ta jiran fitowarsa, bayan kusan minti goma sha biyar ya fito daga bandakin, jallabiyar jikinsa ya mayar ya kalleta sau daya ya dauke kai yana goge kansa da karamin towel, Mayraah dake kallonsa tace "Ba naga kamar kayi wanka ba Yaya?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban gama ba dama" Zata yi magana wayarsa dake kusa da ita ya fara vibrate, ta juya tana kallon wayar taga Dr Zeenat jikin Screen din, tuni ya karaso kusa da gadon ya dau wayar, Mayraah ta dinga kallonsa, yayi picking call din yace "Hi Zeenat, i will call you back" Daga haka ya katse kiran ya ajiye wayar yana kallon Mayraah, sai kuma yace "Ohh bari in dauko man zafin...." Ƙin cewa komai tayi, ya tafi inda first aid box dinsa yake ya bude ya duba yaga babu man zafi a ciki, dawowa yayi yana kallonta yace "I think i will have to go out and get it, babu a nan" Still taki ce masa komai, ya tafi ya dau makullin motarsa da wayarsa ya fita daga dakin, hawayen da bata san dalilinsa ba ya cika idonta, sai kawai ta fashe da matsanancin kuka ta fada kan gadon ta rufe fuskarta da pillow, tayi kukanta me isarta.... Har ta fara bacci Maheer ya dawo gidan, yana shigowa dakinsa yayi mamakin ganinta don bai yi tunanin zai dawo ya sameta a dakin ba, karasawa yayi ya zauna gefen gadon yana kallonta from head to toes, bayan minti daya ya mike a hankali ya koma kusa da kafarta still yana kallonta, yana kai hannu kan kafar ta bude ido, da sauri yace "Erm, zan shafa maki lotion din ne" Yana fadin haka ya nuna mata tube din hannunsa, ita dai ta wani hade rai bata ce komai ba, ya sauke idonsa yace "Wani kafar ne?" Nan ma taki ce masa komai, duba kafar ya fara yi da kansa, yana kai hannu inda ke mata ciwo ta janye kafar da sauri tana turo baki tace "Ni dai bana so" Kasa kallonta yayi yace "A hankali zan maki ai" Saboda yanda ya san ta da shegen raki kawai shafa mata lotion din yayi kamar yana shafa mata mai a kafar bayan ya tabbatar ba dislocation bane, duk da haka har da kukanta, ita dai tasan kukan me take don shi kam gently ya shafa mata lotion din balle tace zafi taji, yana kallonta ya mike ya koma kusa da ita ya zauna yace "Amma dai ba saboda man zafin da na shafa maki kike kuka ba?" Ta kara fashewa da kuka tace "Don baka san zafin da kafar yake min bane shi sa zaka ce haka, kuma sai da kaje ka gama wayarka zaka wani zo ka shafa min saboda ba kai ne ke jin ciwon ba" a fusace ta fara kokarin sauka daga kan gadon shi dai idonsa na kan lap dinta, tun kan ta sauka yayi saurin rikota da murya yace "C'mon Mimi, daga pharmacy fa nake wllhi, nasan ai yana maki ciwo shi sa har na fita da daddaren nan...." Ta kara rushewa da sabon kuka, ya jawota kusa da shi yayi kasa da murya yace "To yi hakuri Mimi" Ta daura kanta saman chest dinsa tana sheshekan kukan, lumshe ido yayi, sai kuma ya rungumeta a hankali yayi kasa da murya yace "It's okay" Bai yarda ta dade a jikinsa ba ya ɗan ja baya, bayan few seconds yayi karfin hali yace "Za ki je ki kwanta Mimi?" Ta daga kai ta kallesa, sauke idonsa yayi not wanting to have eye contact with her, yace "It's late yanzu, ki je ki kwanta" Tace "Saboda kana son zaka yi waya ko?" Ɗan murmushi yayi still shi dai bai kalleta ba yace "To idan ban yi waya ba me kike son inyi Mimi? Ni ba namiji bane? ko haka kike son inyi ta zama baki son yayanki yayi aure? Ko kina da budurwar da za ki min nima kamar yanda MD yace min kin masa" Mayraah dai bata ce komai ba ta sauke kanta, dai dai nan wayarsa ya fara vibrate, ita ta rigasa juyawa da sauri tana kallon wayar taga Dr Zeenat a saman screen din, yace "Ki je ki kwanta, let me pick a call, ko nan zaki kwanta?" Ita dai bata ce masa komai ba, kwantar da ita yayi saman gadon yace "Toh kiyi kwanciyarki a nan" Daga haka ya dau pillow daya ya ajiye kan carpet ya dau wayarsa sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta kan carpet din, dialing number Zeenat yayi, yana fara ring ta daga, duk da ba a handsfree ya sa ba amma saboda silence din dakin Mayraah na jin maganarta radau, bayan sun gaisa Mayraah taji tace "So what are ur plans now Maheer?" Maheer that was speaking calmly yayi murmushi yace "Aure, and setting up a family" Zeenat tace "Really? Kamar zuwa yaushe kai kake son kayi auren kuma kana da budurwar da zaka aura ne yanzu?" Yace "Not at all, i am single, ni ko gobe na samu warce ta shirya i am ready nan da wata daya" Zeenat tace "Amma dai da mamaki kamar ka kace min baka da budurwa Maheer, naji zuciyata ta kasa yarda da hakan" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ba budurwa ba har aure na taɓa yi Zeenat, but auren bai yi 6 months ba muka rabu da matar" Zeenat tace "Subhanallah, garin yaya Maheer, in dai ba canzawa kayi ba kai din na san mutum ne me hakuri, kawaici da kauda kai, wacece wannan tayi ma kanta asaran miji kamar ka?" A hankali Maheer yace "Bata son family dina Zeenat, and she poisoned my Lil sis warce kika ganmu tare a mall, duk da ni tayi niyyar poisoning...." Zeenat tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to yanzu tana ina?" Maheer ya ɗan sauke ajiyar zuciya yace "Ai nace maki na saketa babu aure tsakaninmu" Zeenat tace "I mean ba ayi mata wani hukunci ba akan abinda ta aikata ko ba kuyi involving hukuma bane?" Maheer yace "I did, ni ne ma na mikata gun yan sanda, Unfortunately she is pregnant for me as she said, so bayan abinda tayi which i have evidence, an yanke mata hukunci yanzu haka tana gidan yari, amma saboda cikin dake jikinta my dad had pity for her, yace babu aure tsakanina da ita amma ta ci albarkacin yaron cikinta duk da idan an haifesa dama za ayi DNA test ne, so my dad had to persuade my brother Barrister Usman, sannan ya biya wasu manyan lauyoyin don ayi appealing din case din just for the sake of her pregnancy, we were all against that even our mother, but we had no choice, let it not be as if we are noncompliance to our dad, so ranan monday din nan za a fara zaman court.... And hopefully da irin lawyers da Abbanmu ya daukar mata sannan ga brother na, za a wanketa daga laifin da ta aikata, amma hakan ba yana nufin ni da family dina mun yafe mata bane" Zeenat tayi wani ajiyar zuciya tace "Abun dai bai yi dadi ba Maheer, sorry about that...." Yace "Thank you Zeenat" Tace "Toh yanzu da gasken aure kake son ka sake?" Yace "I am serious Zeenat, i am tired of staying single" Zeenat na murmushi tace "Gashi ka saba da mace" Duk wannan conversation din nasu Mayraah na jin su, A hankali Zeenat tace "Amma in tambayeka?" Yace "Ina jin ki" Tace "Tell me the truth za ka iya aurena Maheer" Sai da Mayraah ta daga kai ba tare da tasan tayi hakan ba, Maheer yayi murmushi yace "Me zai hana, in dai baki canza daga Zeenat din da na san ki ba" A hankali tace "Ina nan yanda ka san ni ban canza ba Maheer, kuma son ka ma bai canza ba a raina" Maheer yace "In dai haka ne me zai hana to, barin in zaki so wannan lil sis dina da kika gan ni tare da ita dazu don a duniya bayan Ammina babu wanda nake ji a raina sama da ita, sannan kuma zaki so family dina da relatives dina" Zeenat tace "Wallahi baka da matsala Maheer, nima fa ina da kannin nan, sannan ai zan so kyautata ma relatives dinka don kai ma ka kyautata ma nawa" Maheer yace "Then we are good to go Zeenat" Zeenat tace "Yanzu yaushe zaka zo mu yi magana?" Yace "Kina ina ne a nan Abuja?" Tace "Gidan aunt dina, ina aiki a wani Private hospital ne" Yace "Ohk gobe friday zan zo after magrib" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah dai ya sa da gaske kake Maheer" Er dariya yayi yace "Ba dai ni nace maki zan zo ba? Just text me the address" Mayraah bata san sanda ta fashe da kuka ba, kawai ita ma ganin kanta tayi tana kuka, Maheer ya mike zaune da sauri yace "I will call u back Zeenat, ina zuwa" Daga haka ya katse wayar ya mike ya hau saman gadon ya zauna kusa da ita da mamaki yace "Mimi what happened? Baki yi bacci ba ne?" Kuka kawai take taki ce masa komai, ya dafa shoulder dinta yace "Talk to me plss Mimi, me ya faru" Buge masa hannunsa tayi ta cire daga kafadarta tace "Ni ka kyaleni cikina ne ke min ciwo" Yace "Subhanallah, yanzu ya fara?" Taki ce masa komai ta fada kan gado ta dinga rusa kuka kamar an aikota, yace "Toh bari in maki allura" Daga haka ya sauka daga kan gadon da sauri, kunna wutan dakin yayi ya juya ya kalleta lkci daya yayi saurin dauke kai don duk rigar baccin ya tattare, har ya gama hada alluran bai sake juyawa ya kalleta ba, yana tafiya a hankali ya nufeta.... Ya zauna kusa da ita yace "Toh bari in maki alluran" Taki ce masa komai, ya dagota yayi mata alluran a lap, ita dai bata fasa kukan da take ba, bayan ya gama mata alluran ya dinga massaging mata wajen yana kallonta ya jawota jikinsa ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Pls ki daina kukan haka, zai daina in sha Allah" he was so carried away da abinda yake yi da har shi kansa bai sani ba, lkci daya ta cire hannunsa daga cinyarta fuska daure tace "Ni ya daina" Da sauri ya saketa ya koma baya, yana kame kame yace "Dama ai nace maki zai daina, let me go and take coffee" Ita dai share idonta kawai take taki ce masa komai, kasa tashi yayi daga inda yake zaune, bai yarda ya kalleta ba yace "Ko zaki je dakinki ki kwanta" Bata tankasa ba ta ja pillow ta kwanta, a hankali yace "To tashi ki kashe wutan dakin sai ki kwanta" Tace "Na fi son sa a kunne" Yace "Ohk, ni bazan iya bacci da shi ba" Tace "Ba coffee zaka je kayi ba" Bai ce komai ba ya zamo kasa daga kan gadon ya kwanta kasan carpet yayi backing dinta, har kusan 12 Maheer bai yarda ya juyo ba, yayi pretending yayi bacci, wajen sha biyu da rabi ya juya a hankali ya daga kai yana kallonta, yaga tayi bacci, tashi yayi da kyar ya fita daga dakin. Can cikin dare Mayraah ta farka, da sauri ta mike zaune ganin baya dakin, idonta na sauka kan wayarsa da ya bari kan carpet kawai ta koma tayi kwanciyarta nan da nan ta ci gaba da baccin ta... Karfe hudu ta sake tashi taje tayi fitsari bayan ta fito ta dau wayar tasa, can dai ta ajiye karkashin pillow, kofa ta nufa ta bude a hankali ta fita har zuwa parlor, kunna wutan parlon tayi ta gansa kwance kasan carpet yayi rub da ciki, ta karasa tana kallon cup din dake kusa da shi, ta dau cup din ta ajiye gefe, sannan ta duka gabansa tace "Yaya" Da sauri ya dago kansa, tace "Yaya me yasa ka kwanta nan? Are you okay?" Ya maida kansa kan throw pillow yace "I am having stomach pain amma na sha magani da sauki" Ita dai kallonsa kawai take, sai kuma da sauri yace "Kin san ban cika son ginger drink ba, i think shi ne ya sa min ciwon ciki" a hankali tace "Allah ya sauwake yaya, to ka sha magani ne?" Ya kalli cup din gefensa yace "Yeah na sha, ai da sauki" Tace "Toh kaje daki ka kwanta" Yace "Aa ai asuba tayi, don't worry je kiyi kwanciyarki, switch off the light for me" Tace "Ohk" Mikewa tayi tace "Bari in kawo maka bargo naji parlon da sanyi" Bata jira me zai ce ba ta tafi ta dauko masa bargon, lulluba masa tayi yace "Thank you" Ta ɗan yi murmushi sannan ta mike ta kashe wutan parlon ta wuce dakinsa ta dau wayarsa sannan ta tafi nata dakin da wayar. Ana idar da sallan asuba Maheer yayi kwanciyarsa kan 3 seater ya fara baccin da bai samu ba sosai jiya, soye soyen da Mayraah take a kitchen ne ya tashesa bacci wajen karfe takwas na safe, da kyar ya mike zaune don kansa yayi masa nauyi ga kuma ciwon da yake masa, har a sannan cikin nasa bai daina ciwo ba, tashi yayi ya wuce dakinsa, yaga ta gyara masa gadon banda kamshi babu abinda dakin yake, bandaki ya shiga yayi wanka, bayan ya fito wanka ya lura wayarsa baya dakin kuma shi yasan bai kai parlor ba, shiryawa yayi yana son fita ya siyo magani tayi knocking kofar dakinsa sannan ta bude tana kallonsa tace "Yaya ina kwana?" Ya sauke idonsa yace "Lafiya lau Mimi, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah, cikin ya dena maka ciwon?" Yace "I told u ginger drink ne da na sha, i am fine now" Tace "Toh na gama mana breakfast" Yace "Ohk i am coming" Juyawa tayi ta fita ya bi ta da kallo, yana tafiya a hankali ya fita zuwa parlorn ya tarar har ta hada masa tea ta debar masa abubuwan da ta soya, ya ja kujeran dinning din ya zauna yace "Weldone Mimi" Tana murmushi ta bude wani tsadadden warmer dinta tace "Nayi har da pepper soup" Yace "Thanks Mimi" Haka nan yake breakfast din amma shi kadai yasan abinda yake ji, ganin ya bar abincin tace "Yaya naga baka ci da yawa ba?" Yace "Yeah, i am having headache zan je in siyo magani in dawo yanzu" A hankali tace "Ba maganin ciwon kai a gidan?" Yace "Aa babu, i will be back immediately" Tace "To ko in raka ka?" Yace "Yanzu fa zan dawo" Tace "Toh" Makullin motarsa ya dauka da Atm card, shi dai har sannan bai tambayeta wayarsa ba... Bai wani dade ba ya dawo gidan bayan ya siyo drugs din, a nan cikin motar ya sha maganin da bottle water da ya siyo a hanya, sannan ya ajiye maganin da ya sha a cikin motar, ya dau ledan sauran drugs din ya shiga gidan, zaunawa yayi kan kujera yana kallonta, atamfa ne jikinta dinkin yayi mata kyau sosai, ta karaso ta dau ledan magungunan ta fiddo da su tana dubawa, ya ɗan yi murmushi bai dai ce mata komai ba, bayan ta gama ganin maganin ta tafi ta dauko masa ruwa, ya dau paracetamol din ya sha, tace "Yaya me zan dafa mana da rana?" Yace "Ki bari later mana, ko