Showing 303001 words to 306000 words out of 456519 words

Chapter 102 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70671

ma Ammi shayin a karamin flask, sannan ta gama yi masa coffee din, zata fita kitchen din Usman ya shigo tana kallonsa ta mika masa flask din hannunta a hankali tace "Yaya pls ka ɗan taya ni kai ma Ammi upstairs" Yana kallon coffee din hannunta yace "Wancan kuma na waye?" Tace "Yaya" Yace "Ke bakya differentiating yayas din, which of the Yaya" Murmushi tayi tace "To kace in maka coffee ne? Beside ai kai baka shan coffee ai naga" Ya ɗan buda ido yace "Sai kice min Doctor" Daga haka ya amshi flask din hannunta ta fita daga kitchen din, ya dau cup ya tafi sama zuwa bangaren Ammi dama daga can din yake, Mayraah na zuwa kofar dakin Maheer tayi knocking a hankali, sannan ta bude kofar ta shiga, har ya sa Pajamas dinsa zai kwanta ta karasa ta ajiye masa Mug din tace "Gashi Yaya" Yace "Ohk thank you" Ta daga kai tana kallonsa sai kuma ta marairaice tace "Yaya yaushe na murguda maka baki?" Maheer ya ajiye wayar hannunsa yace "Kin kai ma Ammi shayinta?" Ta turo baki tace "Ai ba ruwan ka da wannan kuma" murmushi yayi yace "Tunda haka kika ce let me go and check for my self" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da ido, tana ta durkushe inda take bayan fitar sa, can ta mike ta dau Coffee din da ta ajiye masa ta fita daga dakin ta koma kitchen ta zubar a sink ta wanke mug din ta kife sannan ta fita daga kitchen din ta wuce sama, a stairs ta hadu da shi yana saukowa, taki kallonsa zata wuce ya ɗan bi ta da kallo, can yace "Mimi" Ta ki juyowa balle ta tsaya, hakan yasa ya kamo hannunta yace "Are you angry?" Kamar jira take ta fashe da kuka, ya zaro ido yace "Me kuma ya faru Mimi?" Taki cewa komai tana kuka sosai, ya jawota kusa da shi yana bin ko ina na stairs din da kallo, sai kuma ya daura kanta saman kirjinsa a hankali yace "Ohk, i am sorry...." Muryarta na rawa tace "Ni yaushe na maka masifa na murguda maka baki?" A hankali yace "A dakin ki mana, yanzu ma a dakina ai kin min" Ta daga kai hawaye na zuba idonta tana kallonsa, ya ja dogon hancinta yana murmushi yace "Baki san kin yi ba ko?" Sauke idonta tayi tana tunani, sai kuma ta fara sabon kuka tace "To me nace maka ka tuna min" Getting her more closer to himself yace "Shikenan, ya wuce...." Muryar Usman suka ji duk suka juya da sauri, Mayraah ta matsa daga kusa da Maheer, yana tsaye jikin rail din stairs din supporting himself with his hands yace "Ammi's wrapper or Aunty Mariya's Wrapper?" Maheer that was confuse yace "Wrapper?" Usman yace "Eh, wai ka goyata yanda zata ji lallashin da kyau mana tunda bata da aiki sai kuka" Turo baki Mayraah tayi tana kallonsa kamar zata fashe da kuka, Maheer dai ɗan murmushi kawai yayi ya fara sauka downstairs, Usman yace "Silly gal" Daga haka ya juya ya bar wajen, Mayraah ta bi Maheer da kallo sai kuma ta bi sa downstairs da sauri tace "Yaya na fa shanye coffee din sai dai in maka wani" Ya juya yana kallonta yace "Kin dai zubar Mimi" Ta zaro ido tana kallonsa, sai kuma da sauri tace "Ba wani nan, let me make u another one in just 2 minutes" Yana ci gaba da tafiya yace "Tun da kika zubar kawai kije ki kwanta don't bother ur self" Ta marairaice tace "Plss ni dai bari zan je in maka wani" Still bai juyo ba yace "Kwanciya zan yi, kawai ki bari tun da kin zubar" Tsayawa tayi ta bi sa da kallo har ya wuce dakinsa ya kulle, a hankali ta juya ta wuce sama lkci daya duk jikinta yayi sanyi, sai tayi da ta sanin zubarwan da tayi. Washegari da safe wajen karfe goma da rabi Ammi ta shigo dakin Mayraah, ta zauna gefen gado tana kallonta a hankali tace "Mimi ki hada kayan naki, in kin gama sai ki zo in gyara maki gashinki" Mayraah ta sunkuyar da kai ta kasa cewa komai, Ammi ta mike tace "Be careful kar ki manta komai" Daga haka ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita, nan da nan hawaye ya cika idonta, sai bayan kusan minti talatin ta mike ta fara hada kayan nata a akwati, bayan ta gama ta fita, tana tafiya a hankali ta nufi part din Ammi, sai kusan azahar Ammi ta gama yi mata gyaran gashin, Ammi na kallonta tace "Kije ki fara cin abinci sai kiyi wanka kiyi sallah...." Mayraah tace "To Ammi" Mikewa tayi ta nufi kofa, Ammi ta kalli Usman da shigowarsa kenan a hankali tace "Wa zai kai ta?" Usman yace "I will drop her" Ammi tace "Ohk, zuwa karfe uku sai ku tafi" Yace "In sha Allah" Kamar yanda Ammi tace karfe uku Usman suka bar gidan tare da Mayraah, ko sallaman kirki Ammi bata iya tsayawa sun yi ba ta shiga dakinta, tun da suka baro gidan Mayraah ke hawaye, lkci lkci Usman ke kallonta yana driving dinsa, can ya ɗan yi murmushi a hankali yace "Ke da za ki yi aurenki ki koma Familyn Dad dinki shine za ki fara kuka tun yanzu" Mayraah ta kallesa da idanuwanta da suka yi ja bata taɓa tunanin akwai ranan da zai zo a kira wani ba Abba ba da Dad dinta, Usman yayi kasa da murya yace "Mimi zaki yi aure kiyi nesa da Ammi da mu kanmu gaba daya, may be say once in a blue moon za mu dinga ganin ki" Mayraah dai sai kallonsa take, Calmly yace "Gradually bond din mu zai ragu, daga karshe ma ya zama tarihi.... that beautiful bond of 22 years.... gradually za ki mana nisa and we will have no lil sis to look upon, Ammi will have no daughter to show to the world anymore" Mayraah na share hawayen dake zuba idonta ta ɗan yi murmushi tace "You think so yaya?" Shi dai bai ce mata komai ba, ta girgiza kai cike da karfin hali kar ta fashe da kuka tace "Har cikin zuciyata nasan bani da familyn da za su fi min ku a duniya, a cikinku na taso na ga kaina, nothing can ever change the fact that ku ne family members dina a ko da yaushe, and i am sorry to say any other family member will only be a counterfeit" Usman yace "I need a favor from you Mimi, nasan tunda mu ke ban taɓa tambayarki wani abu ba sai dai ke ki tambayeni ko?" Mayraah ta juya tana kallonsa, haka kawai taji gabanta na faduwa ta rasa dalili, yace "Bazan samu favour din ba kenan" Ta hadiye abu da kyar tace "Zaka samu in sha Allah" Yace "Ohk bari in samu waje in tsaya sai mu yi magana" Mayraah bata sake cewa komai ba gabanta dai sai faduwa yake, har dai ya samu wajen wani siyar da Ice cream me kyau ya shiga yayi parking, ya juya yana kallonta yace "Let go in" Bata iya ta ce komai ba ta bude motar ta sauka kamar yanda shi ma ya sauka, tana biye da shi suka shiga cikin wajen, direction din da babu kowa ya nufa Mayraah ta bi sa har ya nemi waje ya zauna ita ma ta zauna, yayi order din masu ice cream duk da he is not a fan of ice cream, ita dai Mayraah ta kagu taji wannan favor din da yake so daga gareta, yana facing dinta gently yace "Mayraah" Ta daga kai da kyar tana kallonsa cikin karfin hali tace "Na'am" Yace "Tell me a little about Yaya Maheer" At this point Mayraah was confuse, tana kallonsa tace "Ban fahimta ba"
[9/4, 8:47 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Usman ya kafe ta da ido waiting for her response, ta langwabar da kai a hankali tace "Allah yaya ban gane abinda kake nufi ba" Usman yace "Meye baki gane ba? am i speaking french?" Ta ɗan yi murmushi tace "Kace i should tell u a little about Ya Maheer..." Shi dai bai ce mata komai ba yana kallonta, ta kara yin wani Murmushin tace "To yaya naga dai kai ma kasan sa, duk gida daya muke, then what should i tell you about him?" Usman ya zare mata ido yace "Kee bana son iskanci" Ta ɗan turo baki tace "Toh wai tarihinsa zan baka?" Sunkuyar da kai yayi yana murmushi ba tare da ya shirya ba, hakan ya sa ta fashe da dariya, nan da nan ya hade rai yana kallonta, ta kasa daina dariya tace "To an haifi yaya Maheer in the year...." Dakatar da ita yayi yace "Ina wasa da ke ne Mimi?" Ta marairaice tace "Yaya to ba sai ka min straightforward question ba, duk wanda kace ma he should tell you a little about himself or someone ai tarihi zai fara baka, or are using law terminologies for me?" Usman yace "Ohk tarihinsa kawai kika sani kenan?" Mayraah ta girgiza kai tace "No bayan tarihinsa nasan personalities dinsa mana" Usman yace "What are his personality" Mayraah tayi murmushi tana kallon ice cream da aka ajiye masu, bayan matar ta tafi ta fara shan nata tana kallon Usman tace "Yaya yaushe ka fara shan ice cream?" Ya dau na gabansa ya ajiye mata, ta fadada murmushin fuskarta tace "Thank you" Shi dai bai ce mata komai ba, ta sauke idonta a hankali tace "One of Ya Maheer's best personality is selflessness, it is always others first before himself, sannan he is soo caring yana kuma damuwa da damuwar wani, baya son hayaniya, tun da nasan kaina ni bai taɓa min fada ba sai dai yayi min nasiha a hankali, it's hard a ga ya ɓata ma mutum rai...." Usman na murmushi yace "Fada sai ni ko?" Ta fashe da dariya tace "Ni yaushe nace haka?" Yana gyada kai yace "Ina jin ki, go on" Tana shan ice cream dinta tace "Sannan Ya Maheer yana iya hana kansa abu for anybody's happiness, ba shi da rowa, infact he is so lovely and sweet to be with, as far as i am concern ban taɓa ganin wani fault dinsa ba, he is 10/10 minus nothing" Usman na gyada kai yace "Do u pray to get married to someone with all this qualities you mentioned?" Da sauri ta gyada kai tace "Sure" a takaice Usman yace "Why not get married to him then" Shiru Mayraah tayi tana kallonsa as if trying to assimilate what he just said, shi ma kallonta yake baya ko kiftawa, a hankali ta sauke idanuwanta, bayan few seconds cike da mamaki tace "How can i get married to my brother? That's weird" Tana fadin haka ta rufe ice cream din gabanta, Usman that was watching her closely yace "You think so?" Ta daga kai da kyar ta kallesa da wani expression tace "Ya Maheer fa? Me yasa zaka ce haka yaya?" Bata jira cewarsa ba tana girgiza kai da kyar tace "No that is the last thing i should do on earth" Usman yace "What are ur reasons? I need concrete reasons" Ta sauke idonta lkci daya har mood dinta ya canza, duk da ice cream da ta fara sha ga sanyin ac dake wajen ji tayi zafi kawai take ji, yace "I am listening" Ta girgiza kai kawai tana kallon outside tace "Yaya yamma fa yana yi" Yace "Kee, bani amsa ta" Nan ma dai tayi shiru, can ta kallesa tace "But yaya me yasa zaka kawo wannan tunanin a ranka? How on earth? Ko ka mance tsakaninmu da ya Maheer ne?" Usman yace "Na manta, tuna min" Ta ɗan hade rai tace "Yayana ne fa, senior brother dina ne fa yaya" Usman yace "Ko? I see... Shi Ammi ta fara haifa sannan ta haifeni, aka haifi Umar after that aka haifeki ko?" Mayraah ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta, muryarta na rawa tace "I am no longer part of the family right?" Usman ya sunkuyar da kansa ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, sai kuma ya kwantar da murya yace "Ba haka bane Mimi, ba haka nake nufi ba, you are and will always be part of the family, but with the way things are going now kina aure shikenan an raba mu dake zaki yi nisa sosai da mu, ki duba yanda Ammi ke jin ki Mimi, u are her only baby now, bata da kowa a gabanta, idan kika yi aure kika koma relatives dinki sai sanda Allah yayi za mu ke ganinki tunda ba gari daya bane, what if kika yi aure cikin gidan da kika tashi tunda Allah ya halasta hakan? Won't we be together forever?" Ita dai hawaye ne kawai ke zuba idonta sosai, Usman yayi kasa da murya yace "I am sorry if i hurt you Mimi, yanzu baza ki iya auren Ya Maheer ba kika ce ko?" Still ta ki cewa komai tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Yace "Fine... Ni za ki iya aurena?" Da sauri ta daga kai tana kallonsa bata ko kiftawa with so much shock, bata gama recover daga first shock din ba ya sake hitting dinta da wani, kawai sai ta fashe masa da kuka sosai, Usman ya dau makullin motarsa yace "Ina jiran ki a mota" Yana kai wa nan ya mike ya bar wajen, ta bi sa da kallo tana kuka a hankali, da kyar ta iya composing kanta daga karshe bayan kusan minti biyar ta goge idonta ko bin ta kan Ice cream din bata yi ba ta bi bayansa walking slowly ta fita waje, Zaune ta samesa cikin motarsa yana jiranta, bata yarda ta hada ido da shi ba bayan ta bude motar ta shiga, shi ma bai kalleta ba suka bar haraban wajen, har suka iso gidan Ceo Mayraah bata dawo daga duniyar tunanin da ta fada ba, bata taɓa tunanin akwai ranan da zai zo da wani zai mata wannan maganar ba, she never expect it, it was something she never saw coming, ganin maganar take kamar wani gagarumin Taboo, How zata iya zama gida daya da Ya Maheer ko Ya Usman a matsayin mijinta, a ina aka taɓa haka? infact na Ya Maheer din ma ne ya fi tsaya mata, people she looked upon as her senior brothers na jini tun tasowarta, girgiza kai tayi har da astagfirullah a zuciyarta, bayan yayi parking yace "Sai anjima" Sai a sannan ta iya juyawa ta kallesa, da kyar tace "But yaya pls me yasa zaka kawo wannan tunanin a ranka? Dama ba kallon kanwar ku ta jini kake min?" Usman yace "In haka ne Musharraf din ma ai ya kamata ki ji baza ki iya aurensa ba, do u know the kind of relationship that is between u and him now? Musharraf is ur uncle, he is ur Dad's cousin" Mayraah dake ta kallonsa tace "To amma ai aurenmu ba haramun bane naga" Usman yace "Oh haka ne fa, sai auren ke da Ya Maheer ne Haram ko? Look.... don't even bring me into the picture kawai da kika ce ke baza ki iya auren Maheer bane yasa nayi involving kaina because our mothers Happiness is our priority, ban san ko shi kina masa kallon yaya ba saboda shakuwar ku ni kuma otherwise tunda quite alright nasan ni dake bamu yi shakuwar da kika yi da Maheer ba, shi yasa nace maki how about me, if not bazan kawo maki maganata ba, Maheer went through alot just like you too, and he deserves peace and happiness now, he is still not himself har yau tun bayan faruwan abubuwan nan, he is feigning smile always, i will love to see him happy once more, but u can do what suits you Mimi" Mayraah kallonsa kawai take hawaye na zuba idonta, why is he saying this comfortable kamar babu komai, wai ta yaya zata auri Ya Maheer?? Usman yace "Akwai inda zan tafi, lokaci na wucewa" A hankali ta bude motar ta sauka ta kulle tana kallonsa ya bude mata booth yace "Ur box" Sai kuma ya bude motar ya sauka ya ciro mata akwatin a booth ya kai har gabanta, ita dai bin sa kawai take da kallo, bayan ya ajiye mata ya zaga ya shiga motarsa ya bar wajen Mayraah ta bi sa ido, da kyar ta iya composing kanta ta goge idonta sannan ta nufi gate din gidan da Akwatinta. Sosai Ceo tayi farin ciki da Abba ya bar Mayraah ta zo gidan, don ko gaya mata bai yi tana zuwa ba, Mayraah dai sai murmushin karfin hali take, ta bi ta har suka je sama zuwa part din da Mahaifiyarta take, zaune suka sameta saman darduma a dakin don karfe hudu har ya gota, Aaria ta dinga kallonta don ita ma bata taɓa expecting ganinta a sannan ba, Ceo ta juya ta fita daga dakin, Mayraah na tafiya a hankali ta karasa har kusa da ita ta zauna tana kallonta tana murmushi a hankali tace "Ina yini" Aaria ta sauke idonta daga kallonta nan da nan hawaye ya kawo idonta, jikin Mayraah yayi sanyi, ita ma ta sunkuyar da kanta, can dai tayi karfin halin dagowa tace "Ain't you happy to see me" Aaria ta daga kai da sauri tana murmushi hawaye na zuba idonta tace "I am..." Daga haka ta rungumeta jikinta, Mayraah ta lumshe ido, sai a sannan taji ta samu relieve din abinda take ji a zuciyarta, they were like that for more than 5 minutes, a hankali Aaria tace "How is ur Mom and everybody?" Mayraah ta daga kai tana kallonta tana murmushi tace "They are all fine, sun ce suna gaisheki" Aaria tace "Ina amsawa" Mayraah ta sauke idonta tace "Ina son zan yi sallah" Aaria ta nuna mata bathroom, Mayraah ta mike ta cire Hijab din jikinta sannan ta nufi bandakin, Aaria ta bi ta

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login