Showing 372001 words to 375000 words out of 456519 words
babies might be the only reason da zai sa ya yafe mata har ma kilan su dawo su zauna tare as husband and wife for the sake of the babies, don taga alamar har cikin ransa yana son yaran nan, bayan ya gama ba babyn hannunsa maganin ya kwantar da shi kan bed dinsa, ta mika masa na hannunta tana kallonsa, ya amshe sa ya basa maganin shima, duk idonta na kansa ta kasa daina kallonsa, daukan babyn da ya ajiye tayi ta daurasa kan kafadarta kamar yanda taga yayi ma dayan, after few minutes yaran duk suka koma bacci.... Sai wajen karfe daya su Ammi suka dawo daga kasuwa, har sannan kuma Maheer na gidan bai tafi ba, a parlor Mama Ladi ta jefar da gyalenta ta baje tana kallon Bilkisu tace "Ke zubo min abinci ko bai dahu ba" Bilkisu ta tafi kitchen don kawo mata abincin, Ammi kuma ta shiga dakin da Haseenah take da jariran, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Tirrr, akan wata er iska shegiya za ayi ta gantali da ni cikin azababben ranan Habuja kamar mara makabuli, dubi yanda na ƙode kamar ban taɓa haske ba a rayuwata, to akan me? Kai ko matar kirki ce Hasinun ai kayan da aka siyo mata tun na farko ya isa ba sai an ce za ayi cacan wasu kudaden a karo wasu kayan ba, balle duk mun san er iska ce shaidaniya mara tsoron Allah, in na sake bin kowa kasuwa shegiya nake wallahi, amma dai mu je zuwa in ta sake tafka masu wata tsiyar ni dai ina kaduna kuma ko jaje wallahi, don ta haifo en biyu sai a rufe ido a shashantar da mugun abun da ta aikata a pamily, gashi nace kar a bari ta basu nono mu siyo Madara amma anki saurarata an maida ni er banza sai dirka masu nononta mara tsarki take, to su suka jiyo in yaran suka kwaso mugun halinta ni dai ba ruwana ina Kaduna, Mera dai ce abar tausayi, don hadata da uban nasu za su yi ta yi ya dinga jin haushinta" Tuni Mama Ladi ta gyara zama ganin Bilkisu na tahowa da babban plate din abinci da kwalin lemo... Ammi ta dinga kallon jikin twins din da Maheer ya nuna mata, ita dai Haseenah kanta na kasa, Ammi ta kalli Haseenah tace "Yaushe jikin nasu yayi haka?" Haseenah ta dago kanta a hankali tace "Tun bayan da Mama Ladi ta masu wanka ta shirya su" Maheer dai kallon Ammi kawai yake, Haseenah ta mike daga kan gadon ta dau pad ta wuce bandaki, Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Zan mata magana yanzu, ruwan wanka ya masu zafi da yawa ne" Maheer dai bai ce komai ba, Ammi ta kwantar da babyn kan gado sannan ta mike ta nufi kofa har ta fita sai kuma ta dawo tana kallon Maheer tace "Ina Mayraah?" Yace "Tana gida" Ammi tace "Ohk" daga haka ta fito parlor ta tadda Mama Ladi dake cin abincin da aka kawo mata, Ammi ta zauna kan kujera tana kallonta tace "Dreban bai shigo da kayan ba" Mama Ladi dai sai tura abincin gabanta take bata dago kai ba balle ta kalli Ammi, cikin kwantar da murya Ammi tace "Mama ina jin fa ruwan da kike ma yaran nan wanka da shi ya masu zafi da yawa" Mama Ladi ta daga kai ta kalleta, can tace "Haka yaran suka buda baki suka gaya maki?" Ammi ta ɗan yi murmushi tace "Aa nunawa yayi a jikinsu, duk jikin nasu yayi tabon ja" Mama Ladi tace "Kamar ya?" Ammi tace "Gama cin abincin sai ki gani Mama" Mama Ladi ta maida abincin gefenta ta mike tace "Aa mu je dai in gani, sai kace yau na saba yi ma jarirai wanka za ace ruwan yayi masu zafi, a takaice dai so ake ace na kone su, ina ce har ubansu na yi ma wanka ban kona sa ba balle su" Ita dai Ammi bata ce komai ba, dama tasan dole sai Mama Ladi ta juya zancen nan, ganin Mama Ladi ta nufi dakin da Haseenah take Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta bi bayanta, Mama Ladi na shiga dakin ta nufi kan gado ta daga kayan jariran tana kallon jikinsu, can tace "Ikon Allah, shi kuma ruwan wankan saboda neman magana sai yayi masu dabbara dabbara a jiki maimakon duk jikin nasu gaba daya yayi ja, to ko Mariya da bata taɓa haihuwa ba bazata ce ruwan wanka ne yayi ma yaran nan tabo a jiki ba balle ke me yara uku ga Mera ta hudu, wato ga Ladi er banza da bata san abinda take ba ko? to wllhi ku tuhumi makirar uwarsu ita kadai tasan me ta masu jikinsu yayi wannan tabon, kada wani shege ya sa ni a bakin duniya sai in tattara sabon akwatina in koma kaduna tunda ba kanwar uwata bace ta haihu, ban da ma zuciyar musulinci ina ruwana da abinda Hasinu ta haifa da har za a gayyato ni Habuja, matar da ta wargaza mana pamily ta sa ma Mera guba a abinci ta ci, ai ko don wannan bai kamata ma ku bari ta haihu a gabanku ba, uwar da ta haifeta ta mutu ne? In ma uwar ta mutu bata da dangin uwa da na uba ne a duniya? yarinyar da ta tafka mana lafiyayyen barna amma ace duk mun manta sai nan nan ake da ita don ta haifo maza biyu? Ko da yake ku dai ku ka manta amma ni ban manta ba wallahi, kuma daga yau ma bazan sake ma yaran wanka ba ke ki dinga masu tunda jikokin ki ne, kece dolensu" Mama Ladi na huci ta sake kallon jikin yaran tace "Wannan dai da kyar in ba izaya ta dinga masu da abu me zafi ba a jiki tunda ba imani ne da ita ba duk mun sani, to meye bazata aikata ba in har zata iya saka ma mutum guba a abinci ya ci, wallahi Hasinu ba abar yarda bace er jikar firauna ce" Daga haka Mama Ladi ta fice daga dakin ta koma gun abincin ta, duk wannan abun Haseenah dake ban daki na jin Mama Ladi don ba a hankali take maganar ba, gabanta sai faduwa yake jin maganganun Mama Ladi na karshe, tunanin abinda zata yi ta dinga yi a bandakin, Maheer dai kallon Ammi kawai yake, Ammi ta sake kallon jikin babies din.... Bayan wani ɗan lokaci Haseenah ta fito daga bandakin tana rike da cikinta ta karaso ta durkusa kan carpet ta sunkuyar da kai tana yarfe hannu hawaye na zuba idonta, Ammi dake ta zaune tana jiran fitowarta tace "Lafiya?" Da kyar tace "Cikina ke ciwo sosai" Da haka Haseenah ta samu tayi distracting din su daga tabon dake jikin babies din don kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita tana durkushe a dakin, Shi dai Maheer fita yayi kawai daga dakin ya bar Ammi dake bin ta da sannu, Mama Ladi na ganin fitowarsa tayi masa alamar ya zo, ya nufi inda take ya zauna, Tayi kasa da murya tace "Yanzu fisabilillahi Mashir nan ya kamata yarinyar nan ta zauna tayi jego? Bata da pamily ne? Mu fa ba yan iska bane Mashir, kuma me hali bai fasa halinsa, iyakar kokarin da za ayi mata a gidan nan an mata tun da har gashi an bari ta haihu a nan, to sai kuma ta koma pamilynta su ma su yi dawainiya da ita ai hannunsu bai rubewa su yar, kuma don ta koma pamilynta hakan ba yana nufin duk abinda kai da uwarka ya kamata ku yi mata baza ku mata ba a can, don haka ni a gaskiya ban goyi bayan zamanta a gidan nan ba, in kuma Meran er banza ku ka mayar da ita ne to sai in ji, don ko domin abinda ta aikata ma Mera na kisan gilla bai kamata ko gate din gidan nan ta sake shigowa ba" Maheer dake ta sauraron Mama Ladi ya sauke ajiyar zuciya yace "Dama Ammi tace kawai kwana arba'in zata yi ta koma gun iyayenta" Mama Ladi tace "Wato har sai tayi kwana arba'in kafin nan ta kara tafka mana wani tsiyar ko? Da ace ita Ammin ce ta ci guban da Mera ta ci ai bazata fara cewa Hasinu tayi kwana daya a gidan nan ba balle kwana arba'in, kun dai mayar da Mera er banza, yarinyar nan fa gata gareta kaca kaca ta ko ina, ko kakanta Alhaji Saminu yaji wnn abun da ku ka yi sai ya kullace ku wllh, kun nuna bara da balu kenan, duk mutumin da zai iya yunkurin kashe wani fa babu abinda bazai aikata a duniyar nan ba, ina ta fada kun sake fahimtata amma ba komai" Maheer ya jinginar da kansa da kujera yace "Ba gidan nan zata zauna ba Mama, nan da kwana bakwai zata koma can gidan da aka kama mata, a can za su yi arba'in din" Mama Ladi tace "Oho dai ni ba ruwana duk abinda zai je ya dawo ni dai nawa ido..." Kallon agogo dake nuni da karfe biyu saura Maheer yayi sai a snn ya tuna lunch da yace zai siya masu shi da Mayraah, mikewa yayi ya bar parlon, Mama Ladi dai ta taɓe baki, ta mike ta tafi tayi sallah. Ammi zata fito daga dakin da Haseenah take kenan Maheer ya bude kofar, hanya ya bata bayan ta fita ya shiga dakin, Haseenah na kwance ta rufe ido kamar me bacci amma ba baccin take ba, Ya karasa kan gadon yana kallon jariran dake bacci, kasa kasa Haseenah ke kallonsa yanda bazai gane ba bacci take ba, ya fi minti uku yana kallon yaran and she could see their love in his eyes, daga karshe ya mike bayan ya gyara masu lallausan blanket din dake jikinsu sannan ya nufi kofa ya fita ya kullo, ɗan murmushi Haseenah tayi adding more hope to her self. Karfe uku saura Maheer ya isa gida, tun da ya shiga parlon gabansa ke faduwa don bai ma san me zai ce ma Mayraah ba, shi dai yasan ko da wasa bazai ce mata daga gida yake ba, ya ajiye takeaway din abincin hannunsa a hankali, yana tafiya slowly ya isa kofar dakin Mayraah, sai kuma ya kasa bude kofar, after standing for a while a bakin kofar ya bude a hankali yana kallon cikin dakin, bin dakin ya dinga yi da kallo ganin bata ciki, ya fito ya duba dakin dake kusa da nata nan ma yaga bata ciki, mamaki ne ya cikasa, komawa yayi parlor ya tafi kitchen ya duba nan ma bata ciki, duk da yasan baza ta shiga dakinsa ba still dai haka ya tafi dakin nasa nan ma yaga bata ciki, he became confused at once, ya fito ya tafi master bedroom nan din ma bai ganta a ciki ba, compound ya sake fita da sauri ya nufi mai gadi, yana kallonsa yace "Don Allah ta dade da fita gidan ne??" Mai gadi dake kallonsa yace "Aa gaskiya bata fita ba, ina jin ko ta zaga can baya ne, amma ina nan ban ga fitar ta ba" Maheer ya sauke wani ajiyar zuciya sannan ya zaga bayan gidan, zaune ya ganta a garden din wajen tana danna wayarta, ya nufeta yace "Mimi" Ta daga kai ta kallesa sai kuma ta ci gaba da abinda take, a takaice tace "Good evening" Zaunawa yayi gefenta yace "Baki ci abinci ba har yanzu ko?" Tace "Aa na ci" Ya ɗan buda ido yace "Kuma gashi na siyo maki abinci a eatry" Tace "Sai ka ci, don ni na riga na ci abinci" Yayi shiru yana kallonta, after few seconds a hankali yace "Kinsan har ina muka je yau kuwa?" Mayraah tace "Aa how will i know" Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "I am so exhausted, inda muka je da nisa sosai, yanzu ki tashi mu je ki kara cin abinci, sai mu shirya mu je can gida, Ammi har ta fara kira tana tambayar me yasa ba mu zo ba yau" Sai a sannan Mayraah ta daga kai ta kallesa, ya sakar mata murmushi ya ja dogon hancinta yace "Yes, ko kuma ni in zauna ke kadai ki je gidan kiyi representing the 2 of us, dama na gaji sosai bacci nake son in yi.. " Mayraah dai bata ce komai ba ya mike ya dago ta, yana rike da hannunta suka bar wajen, da kansa yaje kitchen ya dauko masu plate ya juye masu abincin, ita dai tana zaune tana kallonsa.... Bayan La'asar Maheer na dawowa masallaci yace "Let me order a bolt da zai kai ki can gidan Mimi, cause ina son inyi bacci ne i am so tired, idan na tashi ko zuwa 6 ne sai in je in dauko ki mu dawo gida..." Maheer bai jira opinion dinta ba ya tashi ya shiga dakinsa, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya dau wayarsa don mata ordering bolt din, sai dai fatansa Allah sa garin maganganun Mama Ladi bazata ce ma Mayraah ai yaje gidan da safe ba, haka nan Mayraah ta tafi dakinta ta shirya ba don ranta ya so ba, after some minutes Maheer ya shigo dakin nata don ganin ko ta gama shirin cause Bolt din na kofar gida, kallonta ya dinga yi ta madubi baya ko kiftawa, don wani kyau na musamman tayi cikin tsadadden atamfar jikinta, she look so beautiful and stunning, daga dankunne har tsarka da zobunan hannunta gold ne, ita dai tun da ta kallesa sau daya ta ci gaba yafe gyalenta, ya karasa har bayanta ya tsaya, hakan yasa ta juyo amma taki kallonsa, ya lumshe ido ya rungumeta jikinsa, yayi kasa da murya yace "You look so cute wife" dukawa yayi ya mata Light kiss a lips dinta, ta ɗan yi murmushi still bata bari sun hada ido ba, ba karamin kashe masa jiki murmushin nan nata yayi ba, a haka ya rakata har bakin gate yana rike da handbag dinta cikin rashin kuzari, ya bude mata back door yana kallonta har ta shiga sannan ya ajiye mata jakarta, ya daga mata hannu cikin sanyin murya yace "Till i come later Dear" Sai a sannan ta daga kai suka hada ido, still smiling at him ta daga masa hannu, kallonta ya dinga yi babu ko kiftawa har sai da motar ya bar wajen.... Mayraah na isa gida wajen karfe biyar saura ta gaida securities dake bakin gate ta shiga cikin compound, tana isa entrance din parlor ta bude kofa ta shiga, dai dai sanda Mama Ladi ta fito kitchen rike da kettle din ruwan zafi, Mama Ladi ta kalleta daga sama har kasa tace "Wacece wannan kuma kamar dai Mera" Mayraah na murmushi ta karasa har kusa da ita ta gaisheta, Mama Ladi tace "Wannan ai sai ki sa Mashir din ya dinga rashewa kugunki yaki tabuka abun arxiki a rayuwarsa, irin wannan kwaliyya haka kamar wata jikar sarki, ko da yake meye banbancin Alhaji Saminu da sarkin, shime sarki ne a fadarsa ai" Mayraah dai murmushi kawai take zata amshi kettle din hannunta Mama Ladi tace "Aa bar shi kawai mu je dakin, ruwan zafi ne zan ma wa en can jariran er iskar matar can wanka, duk da ance na toyesu dazu da safe, amma dai albarkacin ubansu bazan ki masu wanka ba don Mashir mutumin kirki ne duk duniya mun shaida" Mayraah tace "Ammi tana sama ne Mama?" Mama Ladi tace "Wani sama? matar da ji take kamar za a gudu mata da jikokin nan nata idan ta matsa daga wajensu, ke dai mu je ki bude min kofa kawai" Mayraah na tafiya a hankali har suka iso dakin da Haseenah take ta bude kofar, Mama Ladi ta fara shiga sannan ita ma ta shiga ta kulle kofar, kallonta Haseenah ta dinga yi ko kiftawa babu don da farko bata ma gane ta ba, Mayraah dai tun da ta mata kallo daya ta dauke kai, Ammi na ganin Mayraah tayi murmushi, Mayraah ta karasa har inda take ta zauna sannan ta gaisheta, Ammi ta amsa tace "Ya gidan Mimi?" Mayraah tace "Alhamdulillah Ammi, ya twins" Ammi ta dauko mata daya babyn ta mika mata, Mayraah ta amshesa tana kallonsa, har sannan Haseenah bata daina kallon Mayraah ba lkci daya duk mood dinta ya canza ga hawayen dake kokarin cika idonta, Mama Ladi ta ajiye ruwan zafin hannunta tana kallon Ammi tace "Ni fa da farko ban gane Mera bace ta shigo parlor, lallai Mashir ya iya kiwo, kuma da kyar in ba sabon ciki ne da ita ba wannan tsantsan kyan da tayi haka, shi ma Mashir din naga yayi kiba, haskensa ya kara fitowa alamar yana cikin kwanciyar hankali Mera na kula da shi sosai yanda ya kamata, bawan Allah sai yanzu zai san yayi aure amma da ai wahala yake bai san dadin aure ba" Haseenah ta sunkuyar da kanta cikin dubara take goge hawayen da ya cika idonta, Ammi dai jin maganganun Mama Ladi sun fara fin karfinta ta mike ta shiga bandaki don dauko baff din babies din, Mama Ladi ta kalli Mayraah da ta sunkuyar da kai tace "To ina Mashir din?" Mayraah ta daga kai a hankali tace "Yana gida yana bacci" Mama Ladi tace "Ahaf, da ina ya samu kwanciyar hankalin yin bacci miko min yaron in cire masa kaya" Mayraah ta mike ta mika ma Mama Ladi jaririn hannunta.
[10/3, 7:45 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Bayan magrib Mayraah na zaune parlor tare da Mama Ladi dake cin abinci Maheer ya shigo gidan da sallama, idonsa na kan Mayraah har ya karaso cikin parlon ya gaida Mama Ladi, Mama Ladi ta ajiye cokalin hannunta tana kallonsa da kyau tace "Dazu da safe kiri kiri kai da uwarka ku ka titsiyeni wai na toya yara da ruwan zafi, to wallahi dazu da zan masu wanka ni da Ammi muka kare ma jikinsu kallo da kyar in ba abu me zafi makirar uwar ta dauka ta dinga dangwala