Showing 336001 words to 339000 words out of 456519 words

Chapter 113 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70595

kallon Abbanta cikin sanyin murya tace "Abba ina yini" Yana murmushi yace "Lafiya lau my daughter, ya gajiya?" Mayraah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Ammi ma na zaune parlon, Nasiha sosai Abba yayi mata tare da Maheer, daga ita har shi babu wanda ya dago kai a parlon, ita dai sai hawaye take don zuwa yanzu ta riga ta yi give up kuma da tunanin ko zata farka taga mafarki ne, Abba yayi kusan minti talatin yana masu nasiha most especially yafi karkata kan Maheer, daga karshe Abba ya mike yana kallon Aunty Mariya yace "Ba wani abu da zata tafi da shi yanzu?" Mayraah ta daga kai da sauri ta kalli Abba, Ammi ma kallonsa take, Aunty Mariya tace "Jakarta kawai zan dauko mata sai wayarta" Abba yace "Toh dauko mata" Mikewa Aunty Mariya tayi ta fita, Abba yana kallon Maheer yace "Ku tashi zan yi dropping din ku da kaina a gidan" Kuka Mayraah ta fara yi sosai tana kallon Ammi hankali a tashe, Ammi dake kallon Abba tayi kasa da murya tace "Yallabai bata da lafiya ne fa, ina ce dazu na gama maka bayani" Abba yace "Zai kula da ita a can gidan nasu" Bai sake sauraron Ammi ba ya fita daga parlon yace "Mariya ta taho min da ita parking space immediately" Mayraah ta kara rushewa da matsanancin kuka, Hukuncin Abba yayi mugun yi ma Aunty Mariya dadi don iya shegen Mayraah ya fara isanta kuma haka, haka Mayraah na ji na gani aka kai ta har motar Abba tana kuka, Aunty Mariya da su Mama Ladi da Yahanasu da frnds din Ammi ne suka rakata parking space din Mama Ladi na cewa "Hakan shine dai dai dama Uba ya kai er sa dakin mijinta da kansa, Allah maka albarka Mamuda, ita kuma Ammi Allah ya shiryeta" Sai da Aunty Mariya tayi ma Mayraah jan ido sannan ta shiga bayan motar, Abba bai yarda Maheer yayi driving din ba yace shi zai yi da kansa, Maheer ya koma front seat ya zauna Abba ya tada motar suka bar gidan, Sai kusan karfe goma da rabi na dare Abba ya isa gidan da ya mallaka masu su biyu, Babban gida ne hadadde a unguwar masu hannu da shuni cikin garin Abuja, Abba da kansa ya bude back seat Mayraah dake kuka ta sauko daga cikin motar, ya kama hannunta yayi leading dinsu har zuwa cikin parlon gidan, daga nan kuma ya kai ta har dakinta da dangin ubanta suka mata furnishing, ya juya yana kallon Maheer dake biye da su kawai a baya, Maheer ya sauke kansa kasa, Calmly Abba yace "Ga amanar daughter na Maheer, take care of her for me, Allah ya baku zaman lafiya...." Mayraah na ganin Abba zai fita ta mike ta rungumesa tana rusa kuka tace "Na shiga uku, don Allah Abba kar ka tafi ka bar ni, Wayyo Ammi" Shi dai Maheer bai yarda ya dago kansa ba.
[9/17, 10:56 AM] khaleesat Haiydar 📚✍️: It took Abba another 10 mintues to console Mayraah dake kuka a jikinsa, after calming her down daga karshe dai ya bar gidan, duk da haka bata daina kukan da take ba kamar ranta zai fita tana kiran Ammi, Maheer ya fi minti ashirin zaune parlor bayan Abba ya tafi, can ya daga kai ya kalli agogo dake nuni da karfe sha daya da yan mintuna, mikewa yayi yana tafiya slowly ya karasa kofar parlon ya kulle da makulli sannan ya tafi ya zuwa wani seperate daki bayan ya shiga ya kulle kofar, after taking his bath ya saka jallabiya yayi kwanciyarsa a dakin wanda shi ma aka yi furnishing, har bacci ya fara daukarsa ya mike zaune da sauri, sauka yayi daga kan gadon ya nufi kofa ya fita daga dakin, after walking toward her room ya bude kofar dakin a hankali yana leka cikin dakin, kwance ya ganta a kasan dakin bacci ya dauketa har sannan kuma bata cire lapayar jikinta ba, ya karasa ciki yana tafiya a hankali leaving the door open, remote din Ac ya dauka ya rage, har zai fita dakin sai yaji bazai iya barinta ta kwana kasa ba, ya kusa minti daya a tsaye kafin ya karasa inda take ya durkusa yana kallonta, he was just looking at her for some seconds, kawai sai kuma ya fasa tashinta ya mike ya dau duvet dake saman gado gently ya rufa mata a jiki sannan ya bar mata wuta mara haske sosai a dakin ya nufi kofa ya fita ya kullo mata kofar a hankali. Sai asuba Mayraah ta farka a dakin, ta dinga kallon duvet din jikinta da mamaki, sai kuma ta mike zaune da sauri tana bin dakin da kallo, kiran sallahn da ta ji ya sa ta gane Asuba yayi, ta buda ido sosai don har ta mance yaushe rabon da tayi bacci me nauyi haka daga dare har asuba, a hankali ta cire duvet din ta mayar gefe ta tashi tsaye, Lapayan jikinta ta kunce ta ajiye gefen gado, tana tafiya kamar me tsoron taka ƙasa ta isa press din dakin ta bude, kayanta ta gani well organized a ciki, sai kuma ta rufe ta juya ta shiga bandaki, sai da ta wanke baki tayi wanka sannan ta dauro alwala ta fito.... Tana zaune saman darduma bayan ta idar da sallah tayi nisa tunanin da take taji an bude kofar wani dakin ba wanda take ciki ba, sosai gabanta ya fadi ta takure waje daya ta dinga kallon kofar dakinta, bayan kusan minti daya bata ga an bude ba, a hankali ta mike ta kwanta gefen gado ta lumshe ido zuciyarta na bugawa. Har karfe sha daya na safe Mayraah na kwance dakinta tayi lamo gefen gado, ta dai hakura da tufka da warwaran da take ta yi a zuciyarta tun da gari ya waye, zuwa sannan dai ta fara jin yunwa sosai, ji tayi an bude kofar dakin, bata san sanda ta mike zaune da sauri ba tsabar yanda ta tsorata tana kallon kofar, yana tsaye bakin kofa ba tare da ya bari sun hada ido ba kamar yanda ita ma taki kallonsa, babu yabo babu fallasa yace "Fito ki dau breakfast" Ta wani daure fuska ta jingina da gadon ta dau pillow ta daura saman cinyarta, still kuma taki kallonsa, hade rai yayi yace "Ke.. ba da ke nake bane??" Ta wani kauda kai tana kara daure fuska taki ce masa komai, shigowa dakin da yayi yasa ta juya ta kallesa a fusace tace "To ni nace maka yunwa nake ji ne wai" Calmly yace "I will give you a dirty slap you if you tell me nonsense" Kallonsa Mayraah ta dinga yi bata ko kiftawa, fuska daure ya nuna mata kofa yace "Fita ki debi abinci, what is my business with kina jin yunwa ko bakya ji" Sauke idonta tayi don tunda take da shi bai taɓa ce mata zai mareta ba, Sounding very serious yace "Ba magana nake maki ba?" a hankali ta sauka daga kan gadon dama har sannan Hijab din da tayi sallah na jikinta, bata yarda ta bi ta inda yake ba ta zaga daya side din tana satan kallonsa ta nufi kofa ta fita, sai a sannan ta waigosa taga ya biyo ta a baya, da sauri take tafiya har ta shigo Babban parlon kafin ya iso har ta tafi dinning din ta debi abincin, shi dae bai ko kalleta ba ya zauna parlon, bayan ta zuba abincin tana tafiya a hankali ta koma dakinta, ajiye plate din abincin tayi ta koma kan gado ta zauna har sannan abinda yace mata ke yawo a kanta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, sai kuma ta fada kan gadon ta fashe da kuka, daga karshe yunwa ne yasa ta dau breakfast din da ya sandare a dakin ta fara ci bayan tayi sallahn azahar, tana cikin ci ya bude kofar dakin, da sauri ta mayar da plate din bayanta tana kallon kofar dakin, a takaice yace "Breakfast, Lunch, Dinner, duk ba sai kin jira an maki announcement ba, lokacinsu nayi ki fito ki nemar ma kanki alternative, i don't want to repeat this again, bana son in sake tuna maki...." Mayraah dai kallonsa kawai take har ya juya ya fita, tana ta zaune kamar bazata fita ba, amma can kasar zuciyarta shakkar kar ya dawo ya sameta take, hakan yasa ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta fita, bata gansa a parlon ba ta karasa dinning area taga an kawo lunch daga gida, dan kadan ta diba a plate, ta bar dinning din ta koma dakinta. Da daddare kamar yanda yace bata jira yayi reminding dinta ba ta fita parlor, zaune ta gansa da laptop gabansa, satan kallonsa tayi taga ko daga kai bai yi ba, tana tafiya kamar munafuka ta tafi dinning, kadan ta diba tuwon, har ta wucesa kuma bai daga kai ya kalleta ba, tana shiga corridor sai da ta sake juyawa ta kallesa still taga idonsa na kan laptop, turo baki tayi ta nufi dakinta. Washegari karfe tara da rabi Mayraah ta fito ba don tana jin yunwa ba sai don kar ya sake tuna mata kamar yanda yace, babu kowa parlon ta karasa dinning taga an kawo breakfast, duk wnn abincin da ake kawowa dai dai yanda Ammi tasan suke cin abinci take zuba masu sai ta kara kadan sbda mai gadin gidan, Mayraah taga babu plate a dinning din ta fara kalle kalle tana neman hanyar kitchen, inda take tunanin kitchen ne ta nufa ta bude kofar a hankali tana leka ciki, hada ido suka yi da shi ta koma baya da sauri kamar munafuka ta bar bakin kofar, ya gama hada coffee dinsa ya fito daga kitchen din, tana tsaye gefe daya ta sunkuyar da kai da kyar tace "Ina kwana" Ita kanta bata san sanda hakan ya fito bakinta ba, gani tayi yayi wucewarsa bai ko kalleta ba, ta bi sa da kallo har ta daina hangosa alamar dakinsa zai tafi, turo baki tayi ta jingina da bango ta rungume hannunta, nan da nan hawaye ya cika idonta, ƙin shiga kitchen din ta dau plate tayi ta wuce dakinta da sauri ta fada kan gado ta rufe fuskarta da pillow ta fara shesshekar kuka.... Mayraah na kwance tayi lamo kan pillow taji an bude kofar dakin, da sauri ta mike zaune tana kallon kofar, bai shigo dakin ba yana kallonta yace "What did i tell u yesterday?" Sauke idonta tayi kasa, yace "Ba magana nake maki ba?" Da kyar tace "Yanzu zan je in deba" Yace "Ke, kar fa ki bari in sake tuna maki, in ma baza ki ci ba ki fito ki diba ki ajiye a dakin, daga baya zaki iya zuwa ki zubar, i don't want to remind you this again" Da ido ta bi sa har ya bar bakin kofar, hawaye ya cika idonta ta sauko daga kan gadon ta fita daga dakin tana tafiya a hankali, bayan ta zuba abincin har zata wuce sai kuma ta tsaya tana kallonsa a hankali tace "Yaya in zuba maka?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Nace maki zan ci?" Sunkuyar da kanta tayi ta wuce daki. Haka nan Maheer ya ci gaba da bi da Mayraah a gidan, kwata kwata bai bata chance da fuskar fara sabon rashin kunyan da ya ga ta tsiro masa ba, a kwana ukun da suka yi tare a gidan sae dae ta fito ta debi either breakfast, lunch or dinner, a dar dar ma take fitowa daukan abincin, ko haduwa sai ya daina yarda su yi da ita, da yaji ta bude kofar dakinta zai bar parlor in dai yana parlon, deep down him he wish he isn't doing this to her, amma wannan kadai ne samun lafiyarsa don yafi kowa sanin wacece ita, avoiding dinta kawai yake by all means. Yau har kusan karfe tara na dare bai ga ta fito ta debi dinner ba, for the pass 3 days ana magrib take fitowa ta zuba abincin, ganin har 11 bata fito ba ya mike ya nufi dakin nata, bude kofar yayi ya ganta kwance ta rufa da bargo, da sauri ya karasa kan gadon ya cire bargon yana kallonta yace "Mimi are you okay?" ta bude idonta da yayi ja ta fashe masa da kuka ta rike hannunsa tace "Yaya cikina" Dagota yayi zaune, shi ma ya zauna yana facing dinta a hankali yace "Ba gobe bane Mimi?" Muryarta na rawa tace "Bai zo ba...." Goge mata hawayen fuskarta yayi yace "Bari in je in kawo maki magani" Mikewa yayi ya fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ya dawo da plate din abinci da ya debo mata da ruwa, ya ajiye abincin ya dagota yace "Ki ci kadan sai ki sha maganin" Cikin rawan murya tace "Bazan iya ci ba" Ya dau abincin ya fara bata yace "Za ki iya Mimi, kadan fa za ki ci...." Da kyar ta bude bakin ta amshi abincin da yake bata a baki, spoon biyu kawai ta yarda tayi tana langwabe masa, ya bude maganin da ya dauko ya bata da ruwa, ta amsa ta sha ta koma ta kwanta ta dukunkune waje daya, rufe mata duvet din yayi a jiki, yana zaune dakin har sai da bacci ya dauketa sannan ya mike ya fitar da sauran abincin da ruwa, kafin karfe biyu da rabi na dare ya shiga dakin nata ya fi a kirga yana dubata, ita kuwa baccinta kawai take, hakan yasa daga karshe ya tafi dakinsa ya kwanta don all through yana zaune parlor ne, har yayi bacci wajen karfe hudu yaji an bude dakinsa, kunna wuta yayi ya mike zaune yace "Mimi" ta nufosa da sauri ta durkusa kusa da gadon, tuni ya sauko kasa, ya duka kusa da ita yana kallonta yace "Ya zo ne?" Da kyar take gyada masa kai, ya dagota ya zaunar gefen gadon yace "Let me get you hot water" Ta rikosa cikin kuka tace "Wayyoo kawai ka min allura bazan iya ba wllh" Yace "Ai ba alluran, sai gobe zan siyo maki...." Ta rushe masa da kuka ta fada jikinsa tace "Na shiga uku, me yasa baka siyo ba" Lallashinta ya fara yi a jikinsa, yace "Bari ki kara shan maganin gobe sai a siyo a alluran da safe" a haka ya samu ta sakesa ya tafi ya dauko maganin da ta sha da daddare kafin tayi bacci, sai ana kiran asuba ya samu Mayraah tayi bacci, gently ya kwantar da ita saman gadon yana kallonta, tana sanye ne da rigar bacci da ya wuce cinyarta, ya sauke idonsa, bayan few seconds ya dau hular ta da ya fadi kasa ya ɗan dago kanta ya sa mata sannan ya rufa mata blanket a jiki, mikewa yayi ya fita daga dakin. Wajen karfe takwas na safe Maheer ya shigo dakinsa bayan ya fita da sassafe yaje asibiti saboda alluran nata, karasawa yayi kusa da gadon yana kallonta ya cire duvet din a hankali yace "Mimi" Ta bude idanuwanta da suka kumbura tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Da sauki?" Girgiza masa kai tayi, ya dagota yace "Toh bari ayi alluran" Da kyar tace "I want to ease my self" Yace "Ohk, come down" Saukowa tayi daga saman gadon, ya kalleta sannan ya kalli bedsheet din, a hankali yace "You are stained Mimi" Kallon gadon tayi, sai kuma tayi kasa da murya tace "Na manta ban sa pad ba" Yace "Shiga bandaki let me get you" Da kyar take tafiya ta shiga bathroom din sannan ya fita yaje dakinta, wani seperate demarcation ne a babban dakin nata inda aka ajiye mata 18 boxes dinta, kallon boxes din kawai yake yana tunanin ta ina zai fara duba pad, dawowa dakin yayi zai fita yaje ya tambayeta, har ya kai kofa yaga pad a gaban madubi ta ajiye, ya koma ya dauka sannan ya tafi press dinta ya bude ya dau underwear ya fita ya koma dakinsa, cire bedsheet din gadon yayi, ya saka wani, ya zauna gefen gadon yana jiranta. Wanka Mayraah ta daure tayi duk da azaban da take ji, kafin ta fito ya sake fita ya tafi kitchen ya hado mata shayi yana shigowa dakin yaji tace "Yaya pad din pls..." Ya ajiye shayin hannunsa ya dau pad din da under wear ya nufi bandakin ya ɗan bude kadan yana mika mata, amsa tayi tace "My hijab" a hankali yace "Ohk" Dakinta ya koma ya dauko mata Hijab din ya mika mata, bayan ta saka ta fito, kwanciya tayi gefen gado ta lumshe ido, ya duka kusa da ita yana kallonta yace "Sannu" Ita dai bata iya ta ce komai ba, yace "Ki sha shayi sai in maki alluran" Bai jira cewarta ba ya dauko shayin, ya ajiye sannan ya dagota, haka ya dinga lallabata ta sha shayin, har ta sha kadan ya ajiye sauran ya dauko ledan injection din ya hada ya dawo kusa da ita yana kallonta, buda ido tayi ganin alluran hannunsa ta daga hijab dinta, towel dinsa ne a jikinta, on a norms dama yawanci a cinya yake mata duk allura in tana cramps, bai cika mata a baya ba, calmly yace "A cinya za a maki ko baya?" Baya ta nuna masa sannan ta ɗan kwanta, ya sauke idonsa, bayan few seconds sai kuma yace "Bari dai ayi a cinya, kar ya dameki later on" Daga haka ya ɗan kara daga towel din yayi mata alluran a lap dinta, yana mata alluran ba dadewa ta fara bacci, ya gyara mata kwanciyarta ya cire hijab din jikinta ya lullbeta ya shiga bandaki don wanke zanin gadon. Wajen sha biyu saura Maheer ya shigo dakin, zaune ya sameta ta tashi bacci a lokacin, ya karasa har gaban gadon yana kallonta yace "How are you feeling?" Ta ɗan turo baki taki cewa komai, sai kuma ta kauda kai tana kallon different direction, shiru yayi yana kallonta, wato ta samu sauki bari ta ci gaba daga inda ta tsaya, dama ciwon cikin nata bai wuce na kwana biyu,

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login