Showing 423001 words to 426000 words out of 456519 words

Chapter 142 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70611

ruwan..." MD ya ɗan buda ido jin abinda Mama Ladi tace, Ihsaan dai tuni ta tafi ta dauko ruwan da drink, sai gata ta dawo parlon ta durkusa gabansa ta ajiye, shi dai kallonta kawai yake ganin ko alamar fara'a babu a fuskarta har a lkcn, Mama Ladi dake kallonsu kasa kasa ta gefen ido sai wani murmushi take tana cin gyadar hannunta, ita kuwa Mayraah Mama Ladi ce ke bata dariya ganin yanda take wani kallonsu kasa kasa tana murmushi tana taunar gyada kamar wata boss, Tsabar dariya sai da Mayraah ta sauko daga kan kujera ta zauna a carpet, Mama Ladi ta kalleta ta wani hade rai tace "Ji mahaukaciyar banza" Mikewa Ihsaan tayi zata bar wajen shi dai MD bin ta kawai yake da ido, da sauri Mama Ladi tace "Ke dawo ki zuba masa a kopi, haka ake yi a Katsinan naku zaki wani dungurar masa da lemo a gabansa ki tafi" Mikewa Mayraah tayi tana dariya har sannan tayi hanyar stairs da sauri ta bar masu parlon ganin wani shegen kallo da Mama Ladi ta bi ta da shi, Ihsaan ta koma ta duka gabansa ta zuba masa drink a glass cup sannan ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, mikewa tayi ta bar parlon tayi hanyar stairs, Mama Ladi kuwa kamar bakinta zai yage tsabar murmushi, sai da taga Ihsaan ta haura sama ta maido da dubanta kan MD tace "Sam bata shiga sabgar da ba tata ba, ba kuma ruwanta da hayagaga kamar er uwarta da kaga tana ta fara'a ba kwantral, sannan ka ga girman gidan nan wallahi kafin mu tashi bacci duk ta gyara ko ina, azababben tsafta gareta har ya wuce misali wllh, yanzu mai aikin gidan nan ma bata da wani amfani don duk wani aikin gidan Ihsani ce ke yi, er uwarta da kaga tana ta fara'a kamar wawiya ba abinda ta iya sai bacci da son jiki, sai ta kai karfe goma sha daya na safe bata tashi ba Al-qur'an, don ma Ammi na taka mata birki, kaga yanda ta wanke kofin nan kafin ta kawo maka to da Imani ce haka zata dauko kopin tana fara'a ta kawo maka" MD dake ta sauraronta murmushi kawai yake bai ce komai ba, har sai da tayi shiru sannan ya daga kai yace "Hutu suka zo kenan" Shiru Mama Ladi tayi, sai kuma ta fara matsar kwalla a hankali tace "Wani hutu Mendi? 'ya yan Marigayiyar matar Mamuda ne fa, marayu ne ba uwa ba uba a duniya sai tsinannun dangin ubansu yan katsina da suka handame duk gadon su, a takaice dai yanzu gatansu a duniya Ammi da Mamuda sai ni Ladi, don uwarsu mutuniyar kirki ce wllhi, duk in zamu hadu da ita sai ta ban dubu ashirin, ko a ranan da zata rasu dubu ashirin ta bani muna zaune da ita a parlor kafin a kirata ace yaran ba lafiya ta kama hanya ashe ajali ke kiranta..." Shiru Mama Ladi tayi tana matsar kwalla, kasa cewa komai MD yayi da farko don sosai jikinsa yayi sanyi, bayan few seconds a hankali yace "Allah Ubangiji ya gafarta ma iyayen su" Cikin rawan murya Mama Ladi tace "Ameen ya Allah, kuma a haka tsinannun dangin uban suka maka Mamuda a kotu wai sai ya fita sabgar yaran, duk hankalinsu ya tashi sun zata Mamuda zai kai su kotu a kan gadon yaran da suka handame shine suka riga makasa kotu, ai ko na ba Mamuda shawara bayan Usman yayi hayan tijararrun lauyoyi a tozarta yan iskan a idon duniya sannan su fito da gadon marayun duk inda ma suka kai" MD dake ta sauraron Mama Ladi yace "Ikon Allah" Mama Ladi tace "Wallahi kuwa, shekaranjiya aka kawo ma Mamuda sammaci, ni dai na kara tsorata da lamarin katsinawa wllh, ni ban ma taɓa bin hanyar garin ba ko da wasa" After few seconds MD yace "Ina da aboki lauya, a kasar waje yake aiki amma yana Nigeria yanzu haka, zan masa magana akan case din in sha Allah" Mama Ladi ta saki kabbara tace "Allah yayi maka albarka Mendi, kuma ana gana Shari'a kyau dama a aurar da marayun kawai su je su karasa karatu a gidan mazajensu" MD dake kallonta yace "Ohk, dama da maganar auren nasu kenan a kasa?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Aa ba haka zaka ce ba, ni ce dai nake ga hakan kadai ne rufin asirinsu tunda mata ne, sannan aure ne kadai zai kubutar da su daga tuggun dangin uban nasu, kaga ita wannan me washe baki kullum cikin fara'a dama Usuman ya kyasa ta tun da dadewa, yanzu ma bini bini zaka gan su tare a parlo tana zuba masa turanci, ita kuwa wannan kamilar da ake kira Ihsani so nake ace ita ma ta samu me tsafta da kamun kai irinta, to kaga ba ko ina suke zuwa ba tunda ance makarantar har an gama daukan dalibai sai wani shekara kuma, amma dai akwai wani ɗan aminiyar Ammi naga in dai ya zo sai yayi ta kallonta kuma shi ma yana da hankali da nutsuwa gaskiya..." Duk da karya kawai Mama Ladi ta lafta haka tayi keeping serious face kamar gaske, MD yayi shiru bai ce komai ba, Mama Ladi dai sai kallonsa take ta gefen ido.
Washegari karfe tara na safe jirgin su Mayraah yayi landing a Us after almost 14 hours of leaving Nigeria, Dad dinta har ya iso airport yana jiran saukan jirginsu, bayan ya ba MD hannu sun gaisa yayi ma Umman sa Side Hug yana murmushi yana kallonta a hankali yace "I miss you so much Mom" Hajiya Ramatu ta hade rai tace "Meye haka kai?" Aunty Halima dake dariya tace "Za ka fara ma Umma shagwaba ga dai Daughter dinka tana kallon ka" Sai a sannan Abdallah ya juya ya kalli Mayraah, ɗan murmushi Mayraah tayi ta gaishesa, ya sake Umman sa ya dawo gun Mayraah, giving her a side hug too yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "How are you daughter?" A hankali tace "I am fine" A haka duk suka shiga motar sa yayi driving dinsu zuwa gidansa dake Los Angeles yana hira da MD dake front seat a zaune, Mayraah ta dinga kallon Mansion din Dad din nata, yayi leading din su har ciki, Mayraah was soo happy to see her Mom, ko lura da Ceo dake dakin bata yi ba ta tafi da sauri ta rungume Mom dinta dake zaune, Aaria was so surprise and at the same time very happy to see her daughter, don ba ace mata har da ita za a zo Us ba, Mayraah ta ɗan buda ido ganin Ceo dake zaune a dakin tana kallonta, a hankali ta zamo kasa ta gaisheta tana murmushi, Ceo tace "Sannu Mary Ann..." Mayraah taji kunya sosai don har ta mance rabon ta gaisheta ko ta WhatsApp ko ta phone call, sunkuyar da kanta tayi, Aaria dai sai kallonta take tana murmushi, ta dauko one of the twin dake kwance kan gado ta mika mata, Mayraah ta amshesa tana kallon babyn da yau suka cika wata daya a duniya, sosai taga yaran ke kama da ita, dai dai nan Aunty Halima ta shigo dakin cike da murna tana congratulating din Aaria, Aaria ta mike ta rungumeta da fara'a tana welcoming dinta at the same time tana tambayarta ina Umma, Aunty Halima tace "Umma sallah zata yi tukunna tana downstairs..." Aunty Halima ta gaida Ceo da fara'a sannan ta karasa ta dau other twin din dake kwance. Kwana biyu kacal Hajiya Ramatu tayi a gidan only son din nata a Us, babu yanda Aaria bata yi da ita ta kara ko da wani kwana biyun ne ba amma taki, haka nan ita da MD suka koma Nigeria leaving Aunty Halima and Mayraah behind, 24/7 zaka tarar da Mayraah makale da yan kannen nata guda biyu tana renon su, sosai take jin yaran har cikin ranta, gashi sam basu da rigima, Daya anyi naming dinsa After Abba (Mahmud) Dayan kuma (Alhaji Kabir Saminu) ana kiransu da Shuraim da Sudais, akwati biyu Abba yayi ma babies din na kaya, Ammi ma tayi masu siyayya sosai, bayan tafiyar Hajiya Ramatu da MD da kwana biyu Ceo ta shirya ita ma zata tafi Canada, Gaba daya Aaria ta dawo bata da walwala ganin yayarta zata tafi duk da watan ta daya har da kwana biyar kenan a Us, Mayraah ta bude kofar dakin da Ceo take ciki a hankali ta shiga, Ceo tayi hanging call da take yi ta ajiye wayar tana kallon Mayraah tace "Come in Mary Ann" Mayraah ta karasa cikin dakin ta zauna kan kujera, Ceo na kallonta tace "Ya mai gidan naki?" Mayraah na wasa da fingers dinta tace "Yana nan lafiya" After few seconds silence Ceo tace "Hope you are taking no contraceptive Mary ann" Mayraah tayi jim don she wasn't expecting the question, can ta girgiza mata kai ba tare da ta kalleta ba a hankali tace "Aa bana shan komai" Ceo tace "Ohk good, nan gaba za ku kara sati daya a Usa kafin ku koma Nigeria ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh" Ceo tace "Alright then, i will get you some pills and their prescriptions yanzu kafin in tafi, sai ki fara sha tun daga yau kafin ku koma Nigeria..."
A kwana a tashi Mayraah da Aunty Halima suka fara shirin komawa Nigeria bayan sun yi kwana sha biyar a America, Aaria dai na zaune gefen gado tana ta kallonsu a sanyaye suna ta hada kaya, a haka Abdallah ya kai akwatunansu booth din motarsa zai kai su airport, Mayraah felt so bad leaving her mother and siblings, rungume Mom dinta tayi tana murmushin karfin hali, a hankali Aaria tace "Take care of ur self dear, ki gaida min Amminki da Abbanki da kyau, mijinki ma kice ina gaishe sa...." Mayraah tace "Za su ji in sha Allah" Dukawa tayi tana kallon cute siblings dinta dake kwance kan gadonsu tayi kissing dinsu gaba daya sannan ta mike ta fita daga dakin Aaria na biye da ita zata masu rakiya waje.... Sai washegari Mayraah suka sauka Airport din Abuja.
[10/27, 8:30 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Ammi ta shigo dakin da Mama Ladi ke ciki da sallama, Mama Ladi ta amsa tace "Ai na zata kin tafi bangaren mijinki ne kika bar ni parlon ki kamar mayya shine na dawo nan" Ammi ta karasa ta zauna tace "Kin gama cin abincin ne Mama?" Mama Ladi tace "Tsohon zance" Ammi tace "Yanzu Alhaji ke gaya min wata magana, shine nace bara in zo in sameki" Mama Ladi ta buda ido sosai tace "Wace magana?" Ammi tace "Wai Alhaji Saminu ne ya kira sa dazu bayan magariba...." Mama Ladi tayi saurin gyara zama tace "Wai me?" Ammi na murmushi tace "Za su zo nema ma wan Musharraf auren Ihsaan" Mama Ladi ta zaro ido ta dafe kirji tace "Ke don Allah fa" Ammi tace "Wallahi, kuma dama ta gaya min suna waya da shi" Nan da nan fara'ar dake fuskar Mama Ladi ya bace tace "Kaji makira, wato ni da nayi silan hadata da shi ni ta mayar er banza kenan da bata gaya min ba?? Ina ce ni na dinga cusata gun sa ba wani yayi min wahalan haka ba ko" Dariya Ammi tayi tace "Ai in kin lura ba wai tana da magana bane kamar er uwarta Mama, ita Eeman ko baka ja ta jiki ba nan da nan take shige maka ta saba da kai, ita kuwa Ihsaan tana da miskilanci ba lallai kasan zuciyarta ba, shi sa in zaki lura nafi jan ta a jiki kan Eeman, ranan tana min gyaran daki ta gaya min" Mama Ladi tace "Can ta matse mata, sam bana son hulda da munafuki a rayuwata, ni dai ba Allah ya gani saboda Marigayiya Amina nayi ba, banda haka ai Mendi ya fi karfinta, mutumin dake rayuwarsa a canada" Ammi tayi dariya sosai tace "Ho Mama, a ina kika ji Canada har kika iya fadansa kai tsaye babu kuskure" Mama Ladi tayi kwafa tana murmushi tace "In fa kina gidan Alhaji Saminu dole ne ma ki iya fadan sunan kasashen turai, baki ga Uban Mera a Amurka yake rayuwarsa ba, ai kullum yan gidan cikin yawon zuwa kasashen waje suke, to duk ba wannan ba, yanzu me shi Mamudan ya gaya ma Saminun da ya kirasa?" Ammi tace "Sanar masa yayi dangin ubansu na nan katsina" Mama Ladi ta hade girar sama da ta kasa tana kallon Ammi, can tace "Amma dai Mamuda wani lkcn yana abu kamar wanda bai yi boko ba, ina ruwanmu da dangin ubansu na katsina da har zai ce ma Saminu suna da dangin uba?" Ammi ta girgiza kai tace "Aa Mama, ko anki ko an so dangin ubansu ne baza a canza ma tuwo suna ba, yanda Alhaji ya gaya ma Alhaji Saminun haka ya kamata dama gaskiya, sun fi mu iko da yaran nan" Mama Ladi ta kyabe baki tace "Toh ai shikenan, kilan in suka ga Alhaji Saminun ma jiki na rawa za su amince su bada auren yarinyar, tun ban gansu ba na riga nasan mayun kudi ne hadamammu, ma'aikacin gwamnati ma nan ya gansu ya kyalesu, kawai yanzu abinda ya kamata shine Alhaji Saminun ya nema ma har Usman auren ita Eeman din, ina gaya maki da gudu za su bayar da auren yaran wllh" Ammi ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Usman da za a kai kudin aurensa nan da sati uku" Mama Ladi ta kalleta da sauri tace "Ban gane ba, dama ba son Eeman din yake ba duk wannan kusancin da naga suke da shi?" Ammi ta girgiza kai tace "Nayi masa maganar ta, uban ma yayi masa, Maheer yayi masa amma duk ya ki, yace shi kawai a matsayin kanwa take a gunsa ta yanda zata kawo masa kukanta akan duk abinda ya dameta a ko wani lkci" Mama Ladi dake kallon Ammi baki bude tace "Ji jaraba, amma da ai yayi niyyar aurenta sanda uwarta ke da rai, ko dai wiwi yake sha ne Usuman?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "To yanzu kam ya ki, uban kuma yace a kyalesa" Mama Ladi tace "Amma ban ji dadin wannan lamari ba wallahi, har ina murna yanda naga sun shaku tana masa turanci, yanzu shikenan Ihsaan sai tayi aure ta bar er uwarta a gida? A ina aka taɓa haka? Yan biyu ai rana daya ake aurar da su kamar yanda suka fito duniya rana daya" Ammi na murmushi tace "Aa Mama, ana yi, kilan kece baki taɓa gani ba, ita ma Eeman din Allah zai fiddo mata da miji in sha Allah...." Mama Ladi tace "Amma dai Usman gantalalle ne, sam ba a gane gabansa balle bayansa" Tagumi tayi ta e "Yanzu ta ina zan fara samo ma Eemani miji ni Ladiyo, abun ba dadi er uwarta tayi aure ta bar ta a gida wllh, ba don ba don ba ai da sai ace Mendi ya dakata har Allah ya fiddo ma er uwarta miji ita ma sai a hadasu" Ammi tace "Aa ba zancen dakatawa Mama" Mama Ladi tace "Ko da yake kada garin dakatawa lamarin auren ya bi ruwa in shiga uku, gwara kawai dayan ta tafi mu san daya ce ta rage mana, ita ma zan shiga in fita in samo mata nata mijin, to yanzu yaushe Saminun yace za su je katsinan?" Ammi tace "Gaskiya ban tambayi Alhaji ba" Mama Ladi tace "Ai ko don albarkacin zuciya me kyau irin na uwarsu to baza su taɓa tabewa ba a duniya, mijin marainiya duk Allah zai basu...." Murmushi kawai Ammi tayi bata ce komai ba, Mama Ladi ta gyara pillow ta kishingida tace "Ohh, yau sati nawa rabon Mashir da gidan nan, yaro duk ya talike gun Mera, wannan wannan da ba don er ki bace sai ince ta shanye maki ɗa ko ince ta asiricesa ta rabaki da shi kawai, huhuhu.... ko da yake ga kakarta can ita ma tana buga duniyancinta ita kadai ranta a kantamemen gidan Saminu, duk tayi bake bake ta hana kowa shigowa tun kuruciya, yana son kara auren ba wai bai so ba amma matar nan ta shiga ta fita ta hana, ni abun na daure min kai, da tsufanta ma ba lallai ta bar wata ta shigo gidan ba a yanda na lura da ita, ita kanta uwar Meran kinga ai Abdallan yaki wani auren har sai da ya jirata bayan kusan shekara ashirin da biyu sannan suka ci gaba da aure, kaf dangin nan ban ji ance ga me kishiya ba, ita ma uwar Mendi kin dai ga yara biyu ta haifa ma kanin Saminun, to har mijin ya mutu bata bar sa ya kara aure ba, suna da mugun tabon nan a pamilyn, to ga dai Mashir a hannun Mera sai yanda muka gani kuma" Ita dai Ammi bata tanka Mama Ladi ba.
Kamar yanda Mama Ladi ta fada kan dangin uban su Eeman hakan kuwa ya faru, don suna ganin Alhaji Saminu da tawagarsa ba shiri suka amshi kudin auren Ihsaan ba tare da wani bincike ba, a nan take kuma aka saka bikin wata biyu, tsabar mamaki Abba ya kasa cewa komai da Alhaji Saminu ya kirasa daga bisani yana sanar masa an kai kudin Ihsaan, ita kam Ammi bata yi mamaki ba don dama Mama Ladi ta fada. Mayraah na bacci a dakinta da rana wajen karfe uku taji ana kwankwasa kofa, ta mike xaune wondering who it could be, sauka tayi daga kan gadon ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita zuwa parlor, sai da ta fara leka window ta ga Mama Ladi tsaye da su Eeman, ta karasa ta bude kofar parlon tana murmushi ta basu hanya tace "Sannu da zuwa Mama" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ba shakka, yau dai nace bari mu zo da yan biyu mu gaisheku tunda kwana biyu hanya bai biyo da ku ta gidan Mamuda ba" Murmushi kawai Mayraah take har suka shigo parlon tana amsa gaisuwar

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login