Showing 396001 words to 399000 words out of 456519 words
ta daga ta mike ta shiga dakin kakarta... Washegari sai wajen karfe sha daya Ammi ta iso gidan ita da Aunty Mariya da Baaba yahanasu, Mama Ladi ce ta tarbesu ta kai su can wani bangare da ba jama'a sosai ta dinga jido masu duk abinda aka girka na biki, Ammi da Aunty Mariya mamaki yaki barinsu, Mama Ladi na fita Baaba yahanasu ta rike haɓa tace "Ikon Allah, kun ga wani kalan dangi irin na Ladi, wai ita ce me tarban baki, to duka duka yaushe ta zama er gidan bamu da labari" Ammi da Aunty Mariya dai basu ce komai ba, sai ga Hajiya Ramatu ta shigo tana masu sannu da zuwa da fara'a tace "Yanzu Hajiya Ladi ta sameni take ce mun kun zo" Ammi na murmushi tace "Ai kam dai, ya taro Hajiya?" Hajiya Ramatu tace "Alhamdulillah" Aunty Mariya da Baaba yahanasu suka mata Allah ya sanya alkhairi, ta amsa da fara'a tace "Bari in sa a kawo maku wainar shinkafa da miya, naga bata kawo maku ba" Tana fadin haka ta fita daga parlon, sai ga Mama Ladi da cooler cike da kaji ta ajiye masu tace "Wallahi duk wanda ma ya biya ma Mera kudin motar zuwa bikin nan ya cuci kansa yayi asaran kudin motarsa a banza a yanda kudi ke wahala yanzu, ni na taɓa jin kauyanci irin na Mera ma kuwa, sam bata da wayewa yanda ku ka san daga kauye ta zo bikin nan, ni ban ma san tana gidan nan ba sai dazu da safe ake gaya min, gidan nan fa cike yake da yan uwanta da sa'anninta mata har ma da wanda suka girmeta, ko wacce fa ta ci ado na kece raini ta caɓa kwaliyya a fuska tana sheki, amma Mera na can makale daki ko kayan kirki ina jin bata zo dashi ba gidan nan, wani ba sai yace dama lefen da Mashir din yayi mata na karya bane ayi zaton duk ya mayar kasuwa inda yayo renting su, to ni dai ba ruwana abun kunya da abun zagi kawai take ja mana a gidan nan ku ji in gaya maku, har sai da kakarta ta nuna min rashin jin dadin hakan, ni dai nafi tunanin don a kurnan asabe ta taso ne shi sa komai nata a kauyance ba gayu a lamarinta, kar fa ta sa Mashir ya fara hange hangen wasu matan a waje, bari dai inje in kira maki ita in ma daga nan tafiya za kuyi da ita to zai fi alkhairi gaskiya don nagaji da jin kunya, baku ji kunyan da ya lullubeni ba ganin shegen kayan jikinta yau" Daga haka ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai ga Mayraah ta shigo part din da su Ammi suke bayan Mama Ladi ta mata kwatance, Daga Ammi har Aunty Mariya kallon Mayraah suke, Yahanasu tayi kwafa tace "Sharri gun Ladi, wallahi shaidan ma jinjina ma Ladi yake akan iya sharri, kuma in ba ayi hankali ba sharri ne zai yi ajalinta, yanxu ina lefin kayan jikin Mera?" Ammi dai kallon tsadadddn lace din jikin Mayraah da mayafinta take wanda kudin lace din kadai yayi 160k, hatta dankunnen da ta saka na gold ne da tsarkansa kuma ba na lefenta ba don ko wata biyu ba ayi ba da Maheer ya siya mata, zoben hannunta ma gold din ne, shima kuma babu shi a lefe, Mayraah na murmushi ta karasa gun su Ammi ta zauna tana gaishesu, Aunty Mariya tace "Yaushe kika sa kayan nan Mimi?" Mayraah tace "Tun karfe bakwai na safe da nayi wanka" Yahanasu ta yi wani kwafan tace "Na fa ce maku tsabagen sharri ne irin na Ladi, mata ta zo gidan mutane tayi kalan dangi ko kunya bata ji, wannan ai mu zata dinga ja ma zagi wallahi" Ita dai Mayraah Murmushi kawai take don tun da garin Allah ya waye bata ga Mama Ladi ba tun ganin da ta mata da asuba, Ammi ta taɓe baki tace "Yi tafiyarki kinji Mimi, amma bana son wannan shegen zaman dakin da kike, ki tafi ki shiga cikin yan uwanki" Aunty Mariya tace "Haba Mimi sai kace ba wayayyiya ba, kema shiga cikinsu za ki yi ba wai ki makale a daki ba kamar kece amaryar" Mayraah dai tayi murmushi ta mike ta fita daga parlon, Yahanasu tace "Baiwar Allah, ni na zata ma zan ganta da juna biyu, to Allah dai ya kawo masu albarka" Aunty Mariya tace "Ameen" Bayan La'asar su Ammi suka bar gidan, karfe biyar da rabi kuma aka kawo amaryar Cousin din su Musharraf nan gidan don a ranan za ayi dinner, washegari a kai ta Abuja, ita kuma Farrah nan kaduna zasu zauna da mijinta.... Babu yanda Hajiya Ramatu bata yi da Mimi kan ta shirya aje dinner da ita ba amma sam taki wai kanta na ciwo, zuwa yanzu dai Hajiya Ramatu ta gama karantar Mayraah, ta gano kwata kwata bata son shiga jama'a ne, kyaleta kawai tayi ta fita zuwa gun wasu baƙi da tayi, bayan duk an tafi dinner gidan ya rage sai daidaiƙun mutane, Mayraah ta idar da sallan magrib ta dau plate din da ta ci abinci ta sauka downstairs da shi, masu aikin gidan su biyu ta gani a babban parlorn suna faman tsaftace ko ina na parlon, kallon yaran dake kwance kan 2 sitter suna wasa ta dinga yi, can ta karasa har inda suke tana kallonsu they are so cute and chubby, dariya suka fara mata, ta juya tana kallon daya daga mai aikin tace "Babies din waye wannan?" Mai aikin tace "Mamarsu tana kitchen zata dama masu abincin su, ina jin da ita aka kawo amarya daga kano" Dai dai nan Haseenah ta fito daga kitchen rike da bowl din Cereal da ta dama na yan biyunta, juyawa Mayraah tayi ta nufi sama bayan sun hada ido... Wajen karfe sha dayan dare suna waya da Maheer, a hankali tace "Toh train din babu na yamma ne?" Maheer yace "Sai Sunday Baby gal, don't worry in sha Allah zuwa 12 zan shigo Kd din sai in dauke ku" Shiru tayi, yayi kasa da murya yace "Amma wai me yasa baki son in zo in dauke ku wife?" Tace "Aa kawai dai bana son kayi stressing kanka ne, da ka bari zuwa Sunday din sai mu hau train kawai" Yace "No Baby gal, I've miss ur presence so much, ba wani stress before 12 in sha Allah zan shigo Kd din" A hankali tace "Allah ya kai mu" Washegari bayan azahar Ammi da Aunty Mariya da Maheer suka iso gidan Alhaji Saminu, tun karfe sha biyu Maheer ya iso Kaduna ya tafi gidan Aunty Mariya direct, Maheer bai yi niyyar shiga gidan Alhaji Saminu ba amma Ammi tace ya shiga yayi masu Allah ya sanya alkhairi, bai mata musu ba suka shiga gidan gaba daya, Mayraah dai na sama parlon kakarta duk da Maheer ya kirata ya sanar mata ya shigo kaduna, Har a sannan gidan Alhaji Saminu akwai baƙi sosai, ganin haka Aunty Halima tayi masu iso zuwa second parlor da babu kowa, Ammi ta zauna kan kujera tana kallon yan biyun da aka ma shimfida a kasan parlon su kadai suna kuka, ita ma Aunty Mariya kallon yaran take, haka ma Maheer da ya zauna kan kujera, Aunty Halima tace "Ko ina uwarsu ta shiga ta barsu a gantale a nan, ina jin daya daga wa enda suka kawo amaryar Bashir ne daga kano uwar tasu, bari in nemo ta" Aunty Mariya ta karasa ta dau daya daga yan biyu tana jijjiga sa. Ganin dayan ma na ta tsala ihu Maheer ya mike ya daukosa ya zauna kan 2 sitter, dai dai nan Haseenah ta shigo parlon rike da bowl din cerelac tare da wata budurwa dake biye da ita da ruwan gora, tana ganinsu Ammi ta sauke kanta kasa ta duka kan carpet ta gaishesu, amsawa Ammi da Aunty Mariya suka yi, Aunty Mariya tace "Bikin kika zo kema?" Haseenah ta girgiza kai tace "Aa, er kanwar mijin aunt dita muka kawo jiya, mijin nata ɗan gidan nan ne" Aunty Mariya tace "Ohk, bikin biyu ne dama, Allah ya sanya alkhairi" Mika mata Ayman Aunty Mariya tayi, Haseenah ta karbesa sannan ta kalli yarinyar dake bayanta tace "Firdausi amso Aryaan" Tana fadin haka ta mike tana kallon Maheer dake rike da Aryaan dake babbaka masa dariya kamar yasan ubansa ne ke rike da shi, shi ko sai kallon yaran yake, Firdausi ta amshesa daga hannun Maheer, Haseenah ta fita parlon Firdausi na biye da ita, Aunty Mariya tace "Ikon Allah yara sun girma sun yi wayo maa sha Allah" Ammi tace "Tun da na gansu na ganesu kawai dai nayi shiru ne" Shi kansa Maheer tun da ya kallesu sau daya yasan boys dinsa ne, Hajiya Ramatu ce ta shigo parlon, bayan sun gaisa, Maheer ya mata Allah ya sanya alkhairi, Ammi tace "To Hajiya mu za mu koma Abuja" Hajiya Ramatu tace "Au wai yau za ku koma, to mu je sama ku gaisa da yayata" Tare suka bar parlon zuwa upstairs, shi dai Maheer bai bar parlon ba yana zaune, su Ammi na fita da kusan minti goma sai ga Haseenah ta shigo parlon da yaran biyu, tana rike da daya, dayan kuma ta goyasa, zaunar da na hannunta tayi kusa da shi, na bayanta ma ta saukesa ta zaunar da shi kusa da ɗan uwansa, shi dai Maheer kallon kyawawan yaran kawai yake, ta zauna kan kujeran dake facing dinsa a hankali tace "Ko sau daya baka taɓa zuwa ganin yaranka ba Maheer, u are depriving them of father's love at der early stage in life, ka bi kayi blocking duk lines dina ta yanda bazan samu access da kai ba, da baka yi blocking dina ta WhatsApp ba, ko ba komai zan dinga tura maka hotunan yaranka kayi witnessing bit by bit growth dinsu" Dai dai nan aka Bude kofar parlon Mayraah ta shigo, ido hudu suka yi da Haseenah, ta dauke kai ta nufi Maheer, tana isa inda yake zaune ta dauke yaran dake gabansa one by one ta ajiyesu gefe daya, sannan ta zauna daga side dinsa kamar zata shige jikinsa tana facing dinsa ta langwabar da kai a hankali tace "Ya gajiyan hanya Honey?" Ya hade forehead dinsa da nata ya lumshe idonsa ya bude yana caressing hannunta, yayi kasa da murya yace "Billah i miss you so much wifey" Light kiss Mayraah tayi masa a lips dinsa tana kallon kwayar idonsa, Haseenah dai ta sunkuyar da kai ba tare da ta san tayi hakan ba ma, Kamar me rada Mayraah tace "Ammi tace ka fito mu tafi" Tana fadin haka ta mike ta dagosa yana rike da hannunta suka fita daga parlon....
[10/13, 9:31 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Sai da Mayraah ta ga Maheer ya shiga motarsa sannan ta koma cikin gidan wai zata dauko akwatinta shi dai kawai ya bi ta da kallo, a hankali ya jinginar da kansa da kujeran motar, har bayan minti sha biyar Maheer yana cikin mota shi kadai a zaune yana jiran fitowar Mayraah da su Ammi, gaba daya ya kasa cire image din kyawawan yaran nasa daga idonsa, sosai maganganun Haseenah suka tsaya masa a kai, but it wasn't his fault he couldn't show d babies love at their early stage in life, and he wish he could, ajiyar zuciya ya sauke yana duba agogo a wayarsa. Tare Mayraah ta sauko downstairs da Ammi da Aunty Mariya, Mai aikin gidan ta amshi akwatin hannun Mayraah ta fita da shi, Haseenah na zaune parlon tana rike da Ayman, mai aikin aunt dinta farida kuma na rike da Aryaan, Ammi ta karasa gun yarinyar dake rike da Aryaan don tun da suka shigo bata dauki yaran ba, amsan yaron tayi tana kallonsa, babu abinda yaran suka mance na Maheer, kamar an tsaga kara da ubansu, kana ganinsu kuma zaka san suna samun kulawa sosai, ita dai Mayraah na tsaye tana danna wayar hannunta without looking at their direction, Aunty Mariya ta amshi Aymaan hannun Hasinah tana masa wasa yana baɓbaka mata dariya, Aunty Mariya tace "Amma dai daga nan kano za ki koma, don naji yanzu ake shirin za a tafi da amaryan Abuja" Haseenah ta sauke kanta kasa tace "Eh gida za mu koma" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya tsare" Haseenah ta daga kai tana kallon Ammi tayi kasa da murya tace "Ammi nace in ba damuwa zan iya zuwa da yaran Abuja in kai maku su ko kwana biyu mu yi" Ba tare da Ammi ta kalleta ba tace "Wannan kuma sai an yi shawara da ubansu" A hankali Haseenah tace "To shikenan" Aunty Mariya ta zaunar da Aymaan kan kujera ta ciro wayarta a jaka tace "Ko hotonsu bamu da shi, Ammi kawo na hannunki in hada su in masu hoto" Ammi ta zaunar da Aryaan kusa da ɗan uwansa Aunty Mariya ta fara masu hoto, yaran ba dai fara'a ba sam basa gajiya da dariya, ita dai Ammi kallonsu kawai take, Aunty Mariya tace "Ikon Allah wannan dariya haka kamar sun san mu" Kallon Ammi da ta kasa dauke idonta kan yaran tayi tace "Taho ki zauna ai maku tare Ammi" Mayraah ta nufi kofar fita daga parlon ta fita, tun da ta fito kofar gida Maheer ke kallonta tana tafiya a hankali ta isa inda yayi parking ta bude front seat ta shiga, Maheer yace "Ina su Ammin fa?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Suna zuwa" Shi dai kallonta kawai yake, bayan few seconds yace "Is anything the Matter?" Daga kai ta kallesa tace "Like?" Yace "Naga kamar mood dinki ya canza?" Tayi yake tace "Mood dina ya canza kuma? Saboda me? Kawai dai na gaji ne gashi sai mun yi tafiyar kusan how many hours kafin mu isa Abuja" Maheer ya kamo hannunta yana murmushi yace "Coming from someone that sleep all through a journey" Murmushi karfin hali tayi tace "Toh ai shikenan tun da haka kace" Wayarta ta ciro a jaka tana dannawa don bata ma son conversation din ya ci gaba, bayan few minutes yace "Wai ina kika baro su Ammi, i tot tare za ku fito" Mayraah bata dago kanta ba tace "Suna sallama ne da mutanen gidan" Yace "Ohk, Mama Ladi na ciki ne?" Ta girgiza kai tace "Ban ganta ba yau, ban dai san ko tana gidan ba" Shiru Maheer yayi ganin yanda take amsa masa kamar bata son magana, tunani ya fara yi to ko yayi mata wani laifin ne bai sani ba, ko da ta shigo ta samesa da Haseenah shi dai ba magana taga yayi mata ba, even the boys a gabansa ta gansu a zaune ba wai ya daukesu bane, a hankali ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Mimi ko ni na bata maki rai?" Ita dai bata ce komai ba, yace "Plsss kinyi shiru" A takaice tace "Wallahi ba komai, kawai na gaji ne i want to see my self at home, i am so stressed" Yayi kasa da murya yace "In sha Allah yanzu za mu tafi, ko zaka ki shiga ki yi ma su Ammi magana lokaci na wucewa" Girgiza masa kai tayi, dai dai nan su Ammi da Aunty Mariya suka fito gidan tare da Hajiya Ramatu da Aunty Halima da suka masu rakiya, wai har da Haseenah a yan rakiya tana rike da Aymaan idonta na kan Maheer, shi kuma nasa idon na kan ɗan sa, Mayraah dai tun ta daga ma Grandma dinta da Aunty Halima hannu ta kauda kai, bayan su Ammi sun shiga motar Maheer ya ja motar suka bar layin, Aunty Mariya tace "Maa sha Allah, girman ɗan mutum dai ba wahala, yaran duk sun yi wayo, watansu nawa kenan yanzu?" Ammi tace "Na shidda za su shiga nake ji" Aunty Mariya tace "Allah sarki, to Allah Ubangiji ya raya masa su cikin aminci" Ammi tace "Ameen" Shi dai Maheer driving dinsa yake, Mayraah kuma tana danna wayarta, Sai da suka fara ajiye Aunty Mariya a gidanta, sannan suka dau hanyar Abuja, Ammi na kallon Maheer tace "Maheer wai aiki ne ya maida Usman kano yanzu?" Maheer yayi murmushi yace "Ammi Barrister ne shi fa, ina ne dama aiki bazai kai sa ba" Ammi tace "Aa naga yafi aikin a Kaduna ne da Abuja, yanzu kuma sai yace yana Kano, daga ajiye mu shekaranjiya ya kama hanyar kano" Duk da dariyan da ta ba Maheer haka ya dake yace "Ai mun yi magana da shi da safe, aiki yaje kanon" Ammi bata sake cewa komai ba, shi dai Maheer lkci lkci yake kallon Mayraah da ta jinginar da kanta da kujera idonta a lumshe, all through the journey Mayraah pretending tayi kamar tana bacci, ita kanta tayi mamakin rashin baccinta, ita da ana dau hanyar tafiya me nisa bacci ke dauketa, yau kam ta kasa, jin zuciyarta take kwata kwata ba dadi, gashi dai bazata ce ga abinda yake damunta ba but deep down she is not okay..... Bayan La'asar suka shigo garin Abuja, sai da Maheer ya fara kai Ammi gida, Maheer ya sauka motar ya fiddo akwatin Ammi, bude motar Mayraah tayi ita ma ta sauko, Ammi dake kallonta tace "Ko dai baki jin dadi ne Mimi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Kawai na gaji sosai ne Ammi" Ammi tace "Ikon Allah sai kace warce tayi wani aiki gidan bikin ke da kike makale a daki" Murmushi Mayraah tayi bata ce komai ba, Ammi tace "To in kun isa gida sai ki huta" Maheer zai shiga gida da Akwatin Ammi tace "Aa bani kawai ku yi tafiyar ku, Allah ya tsare" Security guard dake bakin gate ne ya amshi akwatin, Mayraah tayi ma Ammi sallama ta shiga motar, Maheer ya jira sai da Ammi ta shiga compound sannan ya zaga ya shiga motar suka bar layin, yana kallon Mayraah yace "Don Allah ki gaya min me ke damunki Wife" a bit pissed off Mayraah tace "How many times do i have to tell u i am stressed?"