Showing 252001 words to 255000 words out of 456519 words
ba, do u need anything?" Ta girgiza masa kai tace "Aa" Yace "I will be on my way" A hankali tace "Da wuri haka yaya?" Yace "In kina bukatan wani abu ki kirani" Ta gyada masa kai, Juyawa yayi har ya fara tafiya ya sake dawowa yace "Why don't u tell her u prefer hotel?" Ta zaro ido tana kallonsa, yace "Ohk kin fi son zama under same roof da katti ko? U are comfortable" A hankali tace "Yaya ni da ita kadai ne a gidan wallahi, kuma ai it's a privilege ajiyeni da tayi a gidanta a matsayina na karamar staff" Bai sake ce mata komai ba ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido, sai kuma ita ma ta juya tana tafiya a hankali ta nufi cikin gidan, tana shiga parlor ta kulle kofa, MD kadai ne zaune parlon zata wuce dakin da ta sauka yace "Hey come back here" Juyawa tayi ta kallesa, ko damuwa da hade ran da yayi bata yi ba, ta dawo parlon tana kallonsa, ya mike yace "Halan an gaya maki wasa ya kawo ki UK? Idan kina son haduwa da wani namiji me yasa baki biya kudin jirgi kin biyosa ba? Wato ga opportunity kin samu? ko kin zata yawon bude ido kika zo nan? Saboda kin ga Ceo na lallabaki ta kawo ki gidanta ta ajiye ki ko conference din ma baki je ba shine bari ki kira saurayinki, to let me give u this last warning har mu bar kasar nan bana son in sake ganinki da wani namiji don ba abinda ya kawo ki ba kenan, any body that wants to meet with u should follow u to Nigeria" A takaice ta juya ido tace "Har yayana? Kuma ai dai ban fita ba sai da na nemi permission daga wajenta kuma ta bani izini, why didn't u ask her before waiting for me?" Shiru tayi jin ana saukowa downstairs, Ceo tace "Ya tafi yayan naki ne?" Mayraah ta juya ta kalleta tace "Eh ya tafi" Ceo ta shigo parlon ta karaso ta mike ma MD takardun hannunta tace "Here" Juyawa Mayraah tayi ta nufi hanyar daki, magana ceo take masa amma hankalinsa na kan Mayraah har ta shiga daki. Da daddare Mayraah na kwance wajen karfe sha daya Maheer ya kirata, tana daga wayar ya ji muryarta yace "Me ya faru?" Ta mike zaune da kyar tace "Cikina" Maheer ya mike zaune daga kwancen da yake yace "When did it start?" Kamar zata yi kuka tace "Not long ago?" Yace "Did u take any drug?" Ta girgiza masa kai tace "Since 8 na bar parlon, ita ma kuma tace she will be going to bed early.... " Yace "Ko za ki je ki mata knocking, if not nasan baza kiyi bacci ba" Tace "Ni bazan iya tashinta ba, though it's not as if the pain is that much for now, kilan sai zuwa gobe da safe, i will try and sleep now" Yace "Are you sure" Tace "Yeah, yanzu ma ai na fara bacci ka kirani" Yace "Toh kiyi baccin Mimi, Allah ya sauwake, i pray bazai matsa maki ba anjima...." Ta ɗan yi murmushi tace "Bye" ta katse wayar ta koma ta kwanta, ba a wani dau lokaci ba bacci ya dauke ta, can cikin dare axaba ya tasheta ta sauko daga saman gadon duk da mugun sanyin da ake sai taji kamar zufa ma take, ta jawo wayarta da kyar ta duba agogo taga karfe biyu saura, ajiye wayar tayi, tun tana kokarin ganin ta jure kawai daga karshe ta mike zumbur ba tare da tasan ma tayi haka ba, ta murda makullin kofar ta bude da sauri ta fita, hasken reading lamp da ta gani study room dake parlon ya sa ta karasa can da sauri, tana isa ta durkushe wajen ta fashe da kuka ta ma kasa cewa komai, matsar da littafin gabansa yayi ya mike da sauri yana kallonta yace "Menene?" Cikin kuka tace "Wallahi cikina ciwo yake min ka taimaka min" Ya kunna wutan wajen ya durkusa gabanta da sauri yace "Ya yake maki?" Ta kasa ce masa komai, keenly yake kallonta seeing how she is reacting to the pain yace "Dysmenorrhea?" Gyada masa kai tayi da sauri, ya mike ya bar wajen, magani ya yafi ya dauko mata da ruwa a glass cup, hannunta na rawa ta amsa ta sha, shi dai yana duke gabanta yana kallonta, don bata daina kukan da take ba, bayan kusan minti goma yace "Tashi ki koma daki..." Ko rufe baki bai yi ba cikin rawan murya tace "Aa wallahi bai daina ba, kilan allura zaka min, dama allura ake min" Daga sama har kasa ya kalleta seeing how confident she still is in between pains, Bai yi niyyar mata alluran ba saboda ta riga da ta sha drugs, but ganin she is still in pain har karfe uku kawai ya hada alluran ya mata, nan parlon ta fara bacci ya tasheta ta wuce daki. Washegari har karfe takwas bata tashi ba, har sai da ceo ta shigo ta tashe ta, bayan ta fito daga wanka ta shirya sannan ta dau wani jacket dinta dake akwati ta sa sannan ta fita parlor, Ceo na kallonta tace "Breakfast yana dinning table" Mayraah ta nufi dinning din ta zauna. Wajen karfe goma na safiyar Mayraah na waje tare da Usman da zuwan sa kenan, yana kallonta yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki" yace "Me yasa baki kirani jiyan ba, though the ceo might not gree to that since...." Shiru Usman yayi bayan ya hango MD da ya fito daga cikin gidan, tunda Mayraah ta kallesa sau daya ta dauke kai gabanta na faduwa yake, kallonsa kawai Usman yake kamar yanda shi ma MD ke masa kallon cikin ido, har ya zo ya wucesu leaving his designer perfume scent behind, Usman ya dinga kallon jacket din da ya daura shoulders dinsa, can ya kalli Mayraah da ta juya kai taki kallonsu, a kan gado fa ta ajiye jacket din nasa ashe ya shiga ya dauka, Usman yace "Mayraah" Da sauri ta juya ta kallesa, yace "Wannan ba Jacket din da kika ce min Ceo ta baki bane?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Yaya shi ne, amma ai kilan shi ma ta basa ne ya sa...." Kana jin yanda take maganar kasan karya take, Calmly yace "Mayraah" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Whose jacket is that?" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Na shi ne, a airport ya bani saboda ni ban ciro nawa a akwati ba don ban san haka sanyin yake ba, shine sai ya bani nasa in saka" Kallonta kawai Usman yake, ta daga kai ta kallesa jin yayi shiru, after some seconds yace "To kin yi kokari" Tana ganin ya juya zai bar wajen ta marairaice tace "Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi ina tsoron kar ka min fada ne shi yasa nayi maka karya" Yace "Infact karya kike still kice min babu komai tsakaninki da wannan mutumin, saurayin ki ne" Mayraah ta buda baki tana kallonsa da mamaki, juyawa yayi ya bar wajen ta bi sa da kallo, tafi minti uku tsaye wajen daga karshe ta juya a hankali ta fara tafiya zuwa cikin gidan.....
[8/13, 3:32 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Yau ma dai kamar jiya Ceo bata bari Mayraah ta fita conference din ba tace mata tayi zamanta a gida akwai sanyi, Mayraah dai ta rasa gane amfanin zuwan ta kasar ga expenses na flight, tana zaune parlor ita kadai wajen karfe biyar saura tana karatun wani littafi da ta gani saman Centre table, the parlor was so warm hakan yasa bata jin sanyi duk da ta sa jacket dinta, not long ago mai aikin Ceo ta bar gidan bayan ta gama aikin da ta saba yi, bude kofar parlon aka yi ta daga kai ganin wanda ya shigo ta sauke idonta ta ci gaba da karatun ta without looking toward his direction again, he was smartly dressed in blue suit with white shirt a ciki, ya ajiye takardun hannunsa ya nufi Study room din Ceo ya dau wasu envelopes, dai dai nan ceo ta shigo parlon da wata baturiya da alamar kawarta ce, sai a sannan Mayraah ta ajiye littafin hannunta ta mike ta masu sannu da zuwa ta gaishesu da ladabi, Ceo na kallonta with concern tace "Kin ci abinci dai ko?" Mayraah tace "Eh na ci" Ceo tace "Ohk good, za ku je da Aliyu yanzu kiyi shopping duk abinda kike so, flight din ku na dare ne, you both will be leaving today not tomorrow, don gobe da asuba i have a flight to catch to US" a hankali Mayraah tace "To nagode Ma" Ceo ta mata murmushi tana kallonta, MD ya shigo parlon Ceo ta kallesa tace "Hope you are okay now?" Yace "Sure Ma'am" Tace "Ohk pls kar ku bata lokaci wajen shopping din so that she will get to arrange her things in order before leaving for airport" Zaunawa yayi Ceo ta zauna looking directly at him tace "idan kun koma Nigeria ka dau break din sati uku, you look stressed out... Ya kamata ka huta, Dr Ajay will take over till then" Yace "Ohk Ma'am, Thank you" Ta kalli Mayraah tace "Get ready...." Juyawa Mayraah tayi ta nufi dakin da take, karamin mayafi kawai ta dauka ta daura saman jacket din jikinta sai karamin handbag dinta sannan ta fito parlon, Ceo tace "Ki samesa a waje" sai a sannan Mayraah ta lura ya fita, tace "Ok Ma" daga haka ta fita parlorn, Mayraah wish she could tell her bata son shopping din saboda MD da tace zai kai ta amma bazata iya ce mata Aa ba, babban fargabanta ma kar su je shopping din su hadu da Ya Usman, da ya zata yi kenan? MD din da take avoiding bata son any type of encounter da shi ta yaya za su wanye lafiya wajen shoppin, tasan dole sai yayi displaying halinsa a can, tana isa gun motarsa ta bude front seat fuskarta babu walwala ta shiga ta zauna ta kulle motar, bayan few minutes ta ga ya gyada kai ya ja motar suka bar wajen, ta ɗan masa kallon gefen ido, a ranta ta riga tasan ko ta gaishesa ma ba lallai ya amsa ba shi yasa ta adana gaisuwarta kawai, suna isa mall din bayan yayi parking ya sauka, ganin haka ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga ciki, cart ya dauka, ita ma ta dau daya tana kallonsa, ya nufi wajen turarruka ta bi sa da ido, sai kuma ta tabe baki ta juya ta fara duba inda zata ga chocolates da zata zabar ma Maheer, yawanci duk kayan ciye ciye ta deba a mall din, daga karshe ta dau ma Maheer, Ammi da Abba turare uku, har zata bar wajen turarrukan sai kuma ta turo baki ta koma ta daukar ma Usman ma, iyakar abinda ta dauka kenan a mall din, basu wuce minti ashirin ba suka fito bayan yayi payment, mamaki ta dinga yi ganin he didn't create a scene with her in the mall, don ko bin ta kanta bai yi ba, ta zata nan ma sai yayi showcasing halinsa amma sai ta ga akasin haka, ta bude back seat ganin bai da alamar bude booth din motarsa ta ajiye ledojin siyayyan da tayi, bayan ta ajiye ta dawo gaban motar ta zauna keeping a straight face just as she saw him keep, driving kawai yake lokaci lokaci yana kallon agogon wrist dinsa.... Gaban wani apartment taga yayi parking daga karshe, ta juya tana kallonsa da mamaki, duk gidajen wajen iri daya kuma ko wanne da parking space dinsa a gaba sai garden ta baya, sauka yayi daga motar ita dai bata bude motar ba, yana kallonta da kyau yace "Ko ni zan sauko da ke?" Ta sake kallon gidan da ma anguwan gaba daya tace "Where is this?" Yace "Ni kike tambaya? Ki bari in kin shiga ciki sai ki tambayi warce tace a kawo ki, ai tana ciki she will explain" Mayraah dai kallonsa take ta kasa cewa komai, ya wani hade rai yace "Malama kina bata min lokaci" Bude motar tayi a hankali ta sauka tana kallonsa, ganin ya kulle motarsa da lock ya fara tafiya ta wani hade rai tace "To ban ciro ledan kayan da zan nuna mata ba ai" Banza yayi mata ya nufi entrance din gidan, ta wani hararesa sannan ta bi bayansa, yana bude kofar ya shiga, leaving the door open for her, ganin ta tsaya bakin kofa ya hade rai yace "Are you okay?" Ta sauke idonta sannan ta shiga parlon tana bin ko ina da kallo, kulle kofar yayi ta juya tana kallonsa, ya karasa cikin parlon ya zauna without looking at her, babu yabo babu fallasa ya nuna kofar wani daki yace "Go in there and meet her" Mayraah couldn't stop looking at him, ya mike yana mata wani kallo yace "Baki ji na ne? Ko bata gaya maki airport za mu tafi daga nan ba?" Ta sauke idonta ta nufi kofar dakin da ya nuna mata tana tafiya a hankali lokaci daya kuma tana waigosa, shi ko ya ciro wayarsa yana dannawa, a hankali tayi knocking kofar ya daga kai ya kalleta, yace "Bude Ki shiga" Bata san sanda ta girgiza kai ba gabanta na faduwa tace "Wallahi ba kowa a gidan nan ka kawo ni" Mikewa yayi ya saka wayar aljihunsa yace "Ashe kin san babu kowa, to yau sai kin min bayanin dalilin da ya sa kika raina ni kika zama kece Boss din ni kuma kika maida ni staff...." Ta marairaice masa tace "Don girman Allah kayi hakuri wallahi bazan sake ba kaji har na rantse" Tana ganin ya nufota ta bude kofar dakin da gudu ta shige zata kulle sai ta ga babu makulli jikin kofar, kasa kakkwaran motsi tayi gabanta na bugawa, ganin ya shigo dakin ta durkusa tana kallonsa ta kara marairaice masa tace "Sir plss i am sorry ka yafe min wallahi sharrin shaidan ne, i promise i will be obedient from henceforth" Ya kulle kofar dakin yace "Ohk shaidan ne yasa kika raina ni kike zagina ko?" hankalinta yayi mugun tashi amma taki nuna hakan a fuskarta ta mike ta koma can jikin bango tana kallonsa tace "Wallahi ban taɓa zagin ka ba, me yasa zan zage ka bayan ka girmeni kuma kai boss dina ne" har wani zufa ke keto mata a goshi duk da sanyin da ake, tana ganin ya nufota ta wani hade rai tace "Wallahi zan maka ihu fa" Ya wara ido yace "Oh Haba? To yi ihun mana ki ga ko yana da amfani" Ta wani turo baki ta rungume hannu tace "To oya yi hakuri, wallahi na daina abinda nake har abada...." Tana fadin haka ta tafi gefen gado ta zauna ta nuna masa dan nesa da ita tace "Ka zauna let settle this amicably now...." Kallonta kawai yake, bata jira me zai ce ba, using her fingers to count tace "Kaga na farko daga yau zan dinga gaisheka duk inda na ganka, kai ma kuma dole ka amsa baza kayi ignoring ba, sannan zaka dinga treating dina yanda kake treating sauran staffs don naga su baka masu masifa ni kadai kake ma, sannan baza ka sake ce in maka gyara a office dinka ba tunda ba aikina bane na cleaners ne, and u should apologize for calling my first class a botany first class, and i will also apologize for calling a whole qualified Medical Doctor a Quack...." Confidently take maganarta looking at him straight in the eyes, sai kuma ta tallabi chin dinta da hannayenta biyu tana juya idonta tace "I am waiting for ur feedback now" Kasa ci gaba da kallonta yayi ya dauke kai.... Ta mike tace "If you've finish deciding ina parlor ina jiran feedback" Daga haka ta nufi kofa gabanta na mugun faduwa don kawai karfin hali tayi take maganar nan da take, ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin, zaunawa yayi gefen gadon yana shafa kansa, sai kuma ya mike da sauri ya ciro wayarsa dake ring yaga ceo ce, zaro ido yayi ya fita daga dakin da sauri, ga mamakinsa bai ganta parlon ba, yana fita waje ya ganta can jikin mota a tsaye, dauke kai tayi bata sake kallon direction din ba, ita dai ba ta samu ta fito daga gidan lafiya ba, rufe gidan yayi ya karaso parking space din yana kallonta yace "Kin zata kina da wayo ko? Zaki gane" Ta marairaice tace "But i was waiting for ur feedback" Bude motar yayi ya shiga, ita ma ta bude front seat, sai da ya tada motar sannan yayi dialing number Ceo yace mata suna hanya, cikin yan mintuna suka isa gidan, Ceo ta dinga kallon ledan hannun Mayraah tace "Shopping nace kiyi what's this little thing u bought?" Mayraah tayi murmushi tace "Wannan ya isheni Ma" Ta kalli MD tace "Meye wannan din ta siya?" Yace "Na mata magana tace she doesn't need anything just chocolate" Mayraah ta kallesa da sauri, Ceo tace "Ohk then, je ki shirya a daki" Mayraah ta wuce dakin rike da ledojin. Karfe bakwai da rabi na dare suka bar gidan Ceo zuwa airport, ita da kanta tayi driving dinsu zuwa airport, Bayan Mayraah ta sauka, MD ya fiddo akwatinta a booth, Ceo ta mata side hug tace "Take care of ur self dear, my regards to ur parent" Jikin Mayraah yayi sanyi ta daga kai tana kallonta a hankali tace "Ma yaushe zaki zo Nigeria?" Ceo ta mata murmushi tace "Sai bayan wata biyu in sha Allah" MD dai na tsaye sai kallonsu yake, Mayraah tace "To Allah ya kai mu, thank you so much Ma, i appreciate" Ceo tace "You are welcome" Daga haka ta daga ma MD hannu, ta shiga motarta ta bar airport din, Mayraah ta bi motarta da ido babu ko kiftawa, lokaci daya ta juya